Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Bakwai

0
(0)

<< Previous

Zaune take gaban mudubi ba don za ta yi kwalliya ba, tunda ta fito daga wanka ta saka wa jikinta riga da wando na Pakistan, ta ɗauko hula ta ajiye kan mudubin, anan ta shafa mai ta zauna ba tare da ta san asalin abinda take tunani ba. A hankali ta ɗauki farar hular ta saka a saman kanta, tana gyara zamanta, hasken hular na saka nata hasken ƙara fitowa. A hankali cikin sanyin yanayinta ta yi baya da kujerar da take kai ta miƙe tsaye. Madai-daicin tsayin da take da shi bai hana sirantakarta fitowa ba, duk da girman kayan jikinta.

Falo ta fito tana ganin Mami a tsaye hannunta riƙe da hijab.

“Ke ba da ke za a je ƙunshin ba?”

Mami ta buƙata tana kallon Waheedah da ta girgiza mata kai, girman yarinyar na bata mamaki, yadda shekaru suke gudu na tsoratar da ita, yanzun Waheedah ɗinta ce a aji shida sakandire, Waheedarta ce take shirin zana jarabawar gama aji shida, ko Amatullah ta gitta sai ta yi ta kallonsu, tana mamakin lokacin da rayuwa ta kawota inda take, da gaske haihuwa kyauta ce mai girma, kyauta ce da take wa fatan duk wani wanda Allah bai nufa da samu ba ya samu ko zai ji abinda ake ji.

“Jikina ya mon nauyi Mami, su je abinsu, na ce Amatu za ta saka min jan lalle idan za mu kwanta…”

Waheedah ta yi maganar tana katse wa Mami tunanin da take.

“Allah ya kaimu… Za mu fita kasuwa da Haj. Halima.”

Kai Waheedah ta jinjina tana faɗin,

“Saikun dawo…”

Tsaye ta yi har sai da ta ga Mami ta fita daga ɗakin tukunna, daga nan cikin ɗakin tana jiyo hayaniyar mutane da yake nuna alamun bikin da za su sha a cikin gidan, tun da satin ya kama ake hidima, babu kuma ranar da kanta ba ya mata ciwo, don ba wai tana son hayaniya bane, amma biki yara uku ita kanta ta san sai dai su yi haƙuri, Muhsin, Khadija da Babangida, da shi Babangida ma za a ɗaga, don ginin shi ko rabi bai kai ba, sai Kawu Hamisu ya bashi gida mai ɗaki biyu ya zauna har Allah ya hore mishi ya kammala nashi.

Ita duk ba wannan bane a ranta, Abdulƙadir ne manne da zuciyarta, za ta iya cewa tun tafiyar shi da rana ɗaya bai taɓa barin tunaninta ba. Lokuta da dama tana tashi daga bacci takan ji ƙirjinta ya yi mata nauyi da tunanin halin da yake ciki, shekara ɗaya akace zai yi ya zo gida, amma yanzu shekaru biyu kenan. Watannin baya kasa haƙuri ta yi, bata san lokacin da tambayar ko yana lafiya ta suɓuce mata a gaban Abba ba, shi ne ma ya ce mata ya je ya duba shi sau ɗaya. Yana lafiya, tukunna ta ji ta ɗan samu nutsuwa ta wasu fannonin.

Kan kujera ta zauna, niyyar kwanciya take, tunanin Suratul-Kahf da bata karanta ba na sauko mata, kasancewar ranar juma’a. Ta riga da ta saba da ta idar da sallar asuba take karantawa, yau ɗin bata samu wannan lokacin ba, saboda ta taya Mami gyaran gidan da aka bata, don duk wanda ya kwana, ana sallah suke ficewa su koma sashin Hajja. Tunanin ta je ta ɗauko Qur’an din take yi, Aminu ya shigo da sallamar da ta amsa mishi cikin sanyin murya.

“Commander an diro…”

Ya faɗi yana dariya tare da wucewa kitchen. Muryar shi Waheedah take ji ta dira kunnuwanta da wani irin yanayi, kafin ma’anar kalaman nashi su zauna mata, zuciyarta ta ji ta fara tsalle-tsalle da take tunanin kashedi ne, don yadda ta fara doka mata, in bata miƙe ba, tana jin tsaf za ta fito daga ƙirjinta ta yi ƙafafuwan kanta ta fice daga ɗakin don neman duk inda Aminu ya ce Abdulƙadir ɗin yake. Miƙewa Waheedah ta yi tana saka hannu ta dafe ƙirjinta, inda take jin zuciyarta na ƙara gudu da duk daƙiƙa. A bakin ƙofa ta zira takalman banɗaki da bata san ya akai suka zo wajen ba. Manya-manya ne, karamare kafarta na yawo a ciki amma bata ma kula ba.

Tafiya kawai take kamar wadda aka sakawa batira, ƙafafuwanta take takawa tana nufar ɓangarensu, ba don sun taɓa doguwar maganar da tsayinta ya wuce mintina biyar ba, amma tana jin wata irin sanayya da ta yi mishi da take tunanin sai dai su goga da Hajja in aka zo maganar sanin halayen shi. Abdulkadir ɗin da ta sani ba zai shiga cikin gida ba, idan wani ne daban ya shekara biyu baya gida, yana zuwa ɓangarensu zai wuce ya ga mahaifiyar shi, banda Abdulƙadir. Zai iya jira, da ya shiga hayaniyar da take ɓangaren Hajja gara ya jira. Tana da tabbacin yana ɓangarensu.

Nan kuwa ƙkafafuwanta suke ɗaukarta, bayanshi ta fara hangowa, zata rantse da Allah ba girma kawai ya ƙara ba, har da tsayi, jakace rataye kan kafadar shi, rigar jikinshi ta kamashi kamar za ta buɗe, damtsen hannun shi ta bi da kallo da ya kusa ‘yar siririyar cinyarta. Sosai take takawa, bugun zuciyarta na ƙaruwa, wani irin ɗumi take ji jikinta ya ɗauka kamar zazzaɓi na shirin kamata. Tsaye ta yi a bayan shi tana kasa motsa laɓɓanta, hannunta ɗaya na kan ƙirjinta kamar mai son kare zuciyarta da take tunanin za ta iya fitowa a kowanne lokaci.

Hannunshi Abdulƙadir ya kai yana sake ƙwanƙwasa ƙofar, yana jiyo kiɗan da suka kunna har nan inda yake tsaye. Tsaki ya ja yana addu’ar wanda zai zo ya buɗe ƙofar ya kasance ƙasa yake da shi, yadda zai zabga mishi marin tsayuwar da ya sha a bakin ƙofa, in ba wulaƙanci ba, ya za su kunna kiɗa su kuma kulle ƙofa daga ciki. Yana shigowa gidan ya fara da na sanin zuwa. Bai san meye a maganganun Yassar da sukan yi tasiri akan shi haka ba, amma sai ya sauke mishi saka shi zuwan da ya yi. Baya son hayaniya irin haka, saboda ya san dole sai wani ya ɓata mishi rai, ga hannun shi yana saurin tashi, yanzun abin har ya fi na da.

Yana sane ya ƙi zuwa hutun sallar da sukan zo na kwana biyu ko uku in ya yi tsayi. Bawai don bai yi kewar gida ba, sosai yake jin kewarsu, musamman Hajja da Zahra, babu wanda ya gani tunda ya tafi daga Abba sai Yassar. Don shi kusan duk wata biyu sai ya je ya duba shi, kafin ya tafi kuma duk zuwan da zai yi sai sun yi faɗa. Sai da ya ja dogon tsaki tukunna ya ƙara ƙwanƙwasa ƙofar da ƙarfi wannan karon. Alama ya ji ta cewar akwai mutum a bayan shi, kafin ya tsayar da hankalin shi waje ɗaya, yana jin shiga da fitar numfashin Waheedah da take yin shi a tsorace.

Juyawa ya yi gaba ɗaya, yana tsorata Waheedah da take tsaye, ta kuwa yi baya gaba ɗaya, cikin zafin nama ya riƙo hannunta, sai da ya ga ta tsaya da ƙafafuwanta tana ware mishi idanuwanta da suke cike da tsoro tukunna ya saki hannunta, yana mamakin yarinyar da ya bari ce a gaban shi, komai ya canza tattare da ita banda farinta, runtse idanuwanshi ya yi yana sake buɗe su akanta, ta yi wani irin girma na ban mamaki, farin da rashin ƙibar yana nan, sai dai za a iya kiranta da budurwa, duk da a idanuwanshi tana nan a ‘yar yarinyarta.

Waheedah kuwa ɗayan hannunta ta saka tana kama wanda Abdulƙadir ya saki, zuciyarta na ci gaba da lugude a cikin ƙirjinta, numfashinta ma kokawa take da shi cikin yanayin da kusanci da shi haka kaɗai yake bayyanawa, sosai ya canza mata, kuma ba askin kanshi kaɗai bane yasa fuskar shi canza mata, dan ya aske shi ƙasa sosai. Abdulƙadir da yake tara suma, fuskar shi ta yi mata fayau da askin da akan kira buzz a turance. Ga tabbai ƙananu a fuskar da bata san yadda akai ya ji su ba. Tabon da yake gefen goshinshi ne kawai tsohon abu a fuskar shi, don tasan dashi tun kafin ya tafi.

Idanuwanta ta sauke zuwa wuyanshi, inda yake da wani dogon tabo daga gefen mummuƙenshi zuwa wuyan, yana ɓace ma ganinta daga inda rigarshi ta lulluɓe, wani abu na matsewa a zuciyarta, hannunta take jin yana mata ƙaiƙayi haka kawai, so take ta kai shi kan tabon da alamu suka nuna sabo ne sosai, ta kuma ƙirga duka ƙananun da take gani kan fuskarshi, yadda in ya sake dawowa za ta ga ko ya ji wani sabon ciwon ko bai ji ba. Ƙofar da Abdulƙadir ya ji an buɗe yasa shi ɗan juyawa, kafin ya sake juyowa yana mayar da hankalinshi kan Waheedah.

Yana mamakin yadda ta tsaya tana kallon shi, kamar tana son buɗe har tsokar jikin shi ta ga ko yana ɓoye wani abu cikin ƙasusuwan shi, yana kuma mamakin tsoron da yake cikin idanuwanta bai hanata ƙare mishi kallo haka kamar ta aike shi ba, ba tun yanzun yake kula da ita ba. Ko abu su Zahra suke son tambayar shi ita ɗin suke sawa, haka za ta kalle shi cike da tsoron shi da baya hanata yi mishi tambayar, ƙarfin halinta ba zai gaji da bashi mamaki ba. Bai san dariya mai sauti ta kuɓce mishi ba, sai da ya ga yadda ta haɗiye wani abu da ya fi ƙarfin yawu.

“Hamma”

Ta furta, muryarta can ƙasan maƙoshi, idanuwa Abdulkadir ya kafeta da su, yana sata sake haɗiye wani abu da take ji tokare da maƙoshin ta. Za ta rantse tana jin zuciyarta ta yunƙuro mata da tambayar da ta jima tana wa iska a ɗakinsu, tunda shi ɗin da take son tambaya baya nan.

“Shekara ɗaya aka ce Hamma…. Shekara ɗaya aka ce za ka yi ka zo… Me yasa ka daɗe?”

Wata gajerar dariyar Abdulƙadir ya tsinci kanshi da sake yi.

“Shi ne gaisuwar?”

Ya buƙata, muryar shi na nutsar da gudun zuciyarta. Ta ɗauka girmanshi zai sa muryar shi ta canza ko ta ƙara buɗewa, tana nan yadda ta santa, shi ɗin ne kawai ya canza a bayyane. Ɗan murmushi ta ji ya ƙwace mata.

“Ina wuni…”

Kai Abdulƙadir ya girgiza kawai.

“Ki kawo min abinci.”

Ya faɗi maimakon amsa gaisuwarta, ya juya ya sa hannu ya tura ƙofar. Akan ce idan ka girma, rana da abubuwa na sa haskenka ya ɗan dishe. Baya jin ko wahala za ta sa Waheedah dishewa, da tunanin farinta da yake ji cikin idanuwan shi har lokacin ya shiga ɗakin yana faɗin,

“Uban waye ya kunna kiɗa ya kuma kulle ƙofa daga ciki?”

Ya ƙarasa maganar yana ƙare musu kallo, ɗakin kusan cike yake da mutane, baƙin fuskar da ba zai wuce dukkansu ahalin Bugaje bane ba, don ga kamannin nan yana gani, wasu kuma ya gane su.

“Ubanka ne, nace ubanka ne ya kunna.”

Abdulƙadir ya ji muryar Yassar cikin kunnuwan shi, kafin ya ji hannun Yassar ɗin kan wuyan shi da ya yi wa wani irin riƙo da yasa Abdulƙadir ɗin riƙo hannun Yassar da ya kasa ɓanɓarewa.

“Hamma za ka kashe ni…me yasa kake min hakane a gaban yara… Ka sakeni don Allah.”

Abdulƙadir yake faɗi, yana raina ƙarfin shi da yake tunanin ya ƙaru saboda yanayin horon da ya samu a makaranta.

“Daga zuwanka, shi yasa babu wanda ya yi kewar ka.”

Cewar Yassar da ya saki wuyan Abdulƙadir ɗin yana tallabe mishi bayan kai.

“Ɗan banzan yaro kawai.”

Idanuwa Abdulƙadir ya sauke kan Salim da yake kallon shi yana murmushi.

“Idan na ƙaraso sai na tabbatar laɓɓanka sun yi kumburin da zaka kwana biyu ba ka emurmushi da su ba.”

Miƙewa Salim ya yi yana wucewa ɗakinsu, ba akan shi Abdulƙadir zai fara sauke ƙurar NDA da ya kwaso ya shigo da ita ba. Dariya Yassar yake yi, Abdulƙadir ɗin ya wuce bayan ya watsa wa duk wani da suka haɗa ido da shi a cikin ɗakin harara. Ɗakinshi ya wuce yana murɗa ƙofar ya ga ta buɗe. Shiga ya yi da takalman shi, ɗakin a share yake, sai dai akwai kaya kan gadon, juyowa Abdulƙadir ya yi da nufin zuro kai ya ji wanda ya shigo mishi ɗaki ya zuba mishi kaya akan gado.

“Nine, ni nake kwana a ɗakin da aka fara hidimar biki…”

Yassar ya faɗi muryar shi ɗauke da gajiya da rikicin Abdulƙadir da baya ƙarewa . Yana yawan zuwa dubo shi a makarantane, tun ranar farko da ya je ya ga halin da yake ciki, ya sha wani irin duka ga zazzaɓin da yake da tabbacin dukan ne yasa mishi shi, gashi ya rame sosai, da ya dawo gida har kuka ya yi wa Abba da faɗin ya je ya dawo da Abdulƙadir ɗin, tunda zama sojan ba wahayin shi aka saukar mishi ba. Don yana da tabbacin rashin kunya da bakin shi zai sa su mishi dukan da zai yi ajalinshi wata rana. Abba ya ce shi ya ji zai iya, abar shi, ƙila sanadin sojan yasa shi fara ganin kan mutane da gashi.

Amma hankalin Yassar ɗin ba a kwance yake ba, ba zai ƙi ace kullum ya je ya duba halin da yake ciki ba, ya ji daɗi ma yanzun da wayar hannu ya yawaita, ko baka je ka ga mutum ba, za ka ji muryar shi, amma zai yi ƙarya idan yace ba ya addu’ar kar Abdulƙadir ya yi abinda za su yi mishi dukan mutuwa a NDA ɗin nan, don ya ga alama abin babu sauƙi.

“Kaine mutum na farko da zan kulle ko kwana biyu ne Hamma, saboda kana mun abinda kake so a gaban yara.”

Abdulƙadir ya faɗa babu alamar wasa a muryarshi, hannu ya ga Yassar ya kawo, da sauri ya rufe ƙofar yana dariyar da ya manta rabon da ya yi irin ta. Kan gadon ya ƙarasa yana kwanciya, ƙafafuwanshi a ƙasa, duk da ba takalman bane suka hana shi ɗora ƙafafuwan kan gadon, ra’ayin kwanciyar a haka kawai yake ji. Iskar gida kanta daban take da ta NDA, gyara kanshi ya sake yi, farar rigar Yassar da ke gefe yasa Waheedah faɗo mishi, ba don kalar nata farin iri ɗaya ne da rigar ba, ko kusa ba su da alaƙa, kawai ya tsinceta a ranshi ne, ya fi alaƙanta hakan da jiran da yake ta kawo mishi abinci, don yunwa yake ji ta fitar hankali.

*****

Kitchen ta koma, tana jinta kamar akan iska take tafiya, tanajin yadda zuciyarta ta lulluɓe da wani nishaɗi da idan ta bari ya fito fili tsalle-tsalle zata fara kamar ƙaramar yarinya, ba tana cikin ƙunci bane a shekaru biyun nan, sosai take zagaye da ‘yan uwanta da suke sakata farin ciki, amma nishaɗin da take ji yanzun ganin Abdulƙadir ɗin ne kawai yake bayyana shi. A litattafan Hausar da ta karanta ta ga soyayya kala daban-daban, shi yasa ta saka wa kusancin da take ji da Abdulƙadir ayar tambaya, don har yanzun bata jin yana da suna a zuciyarta. Don abinda take ji akan shi ya sha banban da duk wata soyayya da take gani a litattafai.

Abinda take ji akan Abdulƙadir bata san tun yaushe ya fara ba, kawai buɗe idanuwa ta yi a kusa da shi ta ji zuciyarta na wata irin dokawa, idan so ne ya kamata ta fara tunanin ko shi yana jin kalar kusancin da take ji akan shi? Amma har ƙasan zuciyarta bata damu da ko yana ji ko baya ji ba, asalima tanajin nata ya ishesu su biyun ma. Kuma tana jin tsoron shi kamar yadda su Zahra suke jin tsoron shi. sai dai akwai wani ƙarfi da yake tasowa daga zuciyarta koda yaushe yana danne tsoron in tana son magana da shi.

Da murmushin da ya kasa barin fuskarta take zuba mishi shinkafa da miyar da Mami ta girka, ta kuma san saboda Amatullah ta dafa, don ba za ta ci abincin da bata san wa ya dafa ba, haka za ta wuni tana shan shayi, ƙyanƙyamin da yarinyar take da shi har mamaki yake ba wa Waheedah. Salad ta zuba mishi a gefe da su tumatiri da ta yayyanka har da kokomba. Bata san waye da waye bai ci abinci ba, amma naman da ke miyar kusan fiye da rabi ta zuba wa Abdulƙadir ɗin.

“Tunda shi baƙo ne.”

Ta furta wa kanta, Allah kaɗai yasan kalar abincin da suke ci acan, gara yau ya san ya zo gida. Babban faranti ta samu ta ɗora ƙaramin a ciki tana rufewa, tukunna ta sa cokali a gefe. Ruwa ta ɗaukar mishi da kofi duk ta sa cikin farantin tukunna ta ɗauka tana ficewa zuwa ɓangaren su Abdulƙadir ɗin, sai da ta ƙwanƙwasa suka ce ta shiga tukunna ta cire takalmanta a wajen ta shiga.

“Ina Hamma Abdulƙadir?”

Ta yi tambayar tana kallon Naziru da ya nuna mata ɗakin Abdulƙadir ɗin da ɗan yatsan shi, yana mayar da hankalin shi kan kallon da yake, don shi kaɗai ta samu a falon ma, da alama kowa ya fice hidimar gaban shi. Abinda bata sani ba shi ne Abdulƙadir ya fito ya zare wayoyin speakers ɗin da suka kunna kiɗan da shi. Da ya ji bai hana kiɗan yi ba, ya je ya raba extension ɗin da kayayyakin suke jone da socket ɗin ɗakin gaba ɗaya yana zubarwa a ƙasa ya juya ya koma ɗaki bai ce wa kowa komai ba. Yassar ne ya ce su haƙura kawai su ƙyale shi, shi yasa kowa ya fice daga ɗakin. Shi kanshi Nazir ɗin sai gaban tv ɗin ya koma sosai don ya rage maganar ta yi ƙasa yadda kunnuwanshi ne kawai za su ji.

Wucewa Waheedah ta yi, tana ƙwanƙwasa ɗakin.

“Shigo…”

Abdulƙadir ɗin ya faɗi, a hankali ta tura ƙofar tana shiga tare da yin sallama. Tashi zaune Abdulƙadir ya yi yana kasa haƙuri da ta ajiye mishi farantin, yasa hannu ya karɓa, a kan cinyar shi ya ɗora yana buɗewa tare da saka cokali a ciki ya fara cakuɗa gefe, tukunna ya ɗiba yana zubawa a bakin shi. Yadda ya sauke numfashi na sa Waheedah jin da tana da iko kullum sai ta aika mishi abinci Kaduna. Ta san ya kamata ta tafi, amma ƙafafuwanta kamar an dasa su a wajen, bayanta ma ta jingina da bangon ɗakin tana kallon yadda yake cin abincin da sauri-sauri. Abincin ya mishi daɗi sosai, bai damu da tsayuwar da Waheedah ɗin ta yi ba, ko ƙofar ɗakin da ta bar mishi a hangame. Haka kawai ya ji ya kasa ce mata tsayuwar me take mishi a ɗakin har lokacin.

Bata san me yasa take jin son mishi magana haka ba, jikinta har ɗumi yake ɗauka da yanayin son mishi maganar.

“Dame ka ji ciwo Hamma?”

Ta tambaya, yadda ya ɗan tsaya, kafin ya kai cokalin abincin bakin shi yana juyowa ya sauke mata ƙananun idanuwan shi yasa zuciyarta dokawa cike da tsoron shi da bai hanata sake faɗin,

“Yaushe za ka tafi?”

Abincin Abdulƙadir yake taunawa a nutse, inda wani ne ba ita ba, zai ji kamar ya raina shi da yawa da har zai yi tsaye yana jero mishi tambayoyi, amma a muryarta yake jin yadda tsakaninta da Allah ta yi tambayar, babu raini ko wani abu, kawai tana son sani ɗin ne. Amma daga haka raini yake farawa, shiru ya yi ya ƙyale ta yana cigaba da cin abincin shi.

“Su ne basa barin ku zuwa? Ko kai ne kawai ka ƙi zuwa? Hamma ka ga wani tabon fa har a gefen kuncinka… Da me ka ji ciwuka haka don Allah?”

Waheedah ta ci gaba da jero mishi tambayoyin da take jin suna fito mata a sauƙaƙe, kamar sun yi shekaru masu yawa a tare da shi. Kamar ta yi sabon da za ta yi labari da shi mai tsayi ba tare da fargabar komai ba haka take jinta, duk da a ƙasan zuciyarta wani abu yake faɗa mata ba amsa za ta samu ba, itama ba tana tambayar shin bane don ya amsata, tana tambayar ne kawai saboda tana son magana da shi ko da ba zai amsa ba, in dai yana jinta ya isheta.

“Ko kun fara fita aikin soja ne?”

Ta buƙata, tana ware idanuwanta, zuciyarta cike da wani sabon tsoro da tunanin abinda hakan yake nufi.

“Hamma kun fara zuwa yaqi ko? Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…oh Allah na… Ko harbi ne tabon wuyanka? Oh Allah na.”

Cokalin Abdulƙadir ya ajiye cikin abincin shi yana faɗin,

“Fitar mun daga ɗaki Waheedah…”

A daburce ta ce,

“Na’am…”

Don tunaninta ya yi nisa cikin kalar tashin hankalin da take gani a fina-finan sojojin da take cikin kallo yanzun duk idan ta samu lokaci. Yazid kan bar mata laptop ɗinshi in ya samo, sai ta kalla a ciki.

“Ki fitar mun daga ɗaki kafin in watsa miki mari.”

Abdulƙadir ya faɗi can ƙasan maƙoshi, saboda dariya na gab da ƙwace mishi, yana kallon tsoron da ya cika idanuwanta kafin ta fice da sauri kamar za ta faɗi. Sai da ya tura ƙofar tukunna wata irin dariya ta ƙwace mishi, yana mamakin yadda Waheedah ta kasance mai hankali kuma marar hankali duk a lokaci ɗaya. Hannu yasa ya shafi tabon da haukanta yake mata tunanin na bindiga ne.

“Wai yaƙi…”

Ya faɗi yana ƙara yin dariya.

“Wallahi Waheedah bata da hankali… Yaƙi fa.”

Abdulƙadir ɗin yake maimaitawa har lokacin yana dariyar da yake jin fitowarta tun daga zuciyar shi. Abincinshi ya ƙarasa cinyewa tas ya sha ruwa, tukunna ya ajiye farantin a ƙasa, gani ya yi uku da kusan rabi, hakan yasa shi miƙewa ya kwance takalman ƙafar shi, tukunna ya shiga banɗaki don ya ɗauro alwala, fuskar shi ya kalla a mudubi, murmushin da yake bayyane a jikinta na sa shi janye idanuwan shi daga kan mudubin, don yanayi ne da ya zame mishi baƙo, ya kwana biyu bai yi nishadiu irin na yau ba. Tsintar kanshi ya yi da murmushin har ya idar da alwala ya fito, waje ya samu ya zauna yana jira a kira sallah don ya wuce masallaci.

*****

Dinner za su yi da daren ranar, duk da Abba ya nuna duk wannan bidi’ar ba sonta yake yi ba, haka ya haƙura ya ƙyale su ganin sun kafe. Dogayen riguna ne suka yi anko iya su ‘yan cikin gidan. Material ɗin wine color, YA yi matuƙar kyau. Mami ta yi wa Nuriyya ankon da duk sauran ɗin mkunan da ta yi wa Waheedah. Yanzun ma tare duk suka fito da za a tafi, yanayin ɗinkin ya zauna wa Nuriyya sosai, da wahala ta gitta ba ka sake kallonta ba, ko don kwalliyar da ta sha, kusan duka ‘yan gidansu Waheedah ɗin Nuriyya ta yi musu kwalliyar su. Ga ƙunshi an sha, kamar su ne amaren. Nuriyya ta rataya mayafinta a kafaɗa, yadda su Zahra ma sukayi.

Itakame Waheedah fuskarta fayau take, banda hoda da ta murza sai Vaseline da ta shafa wa laɓɓanta, ɗaurin ɗankwalinta ma mai sauƙi ta yi. Sai dai kalar kayan ya amshi farar fatarta, ta yafa ƙaton mayafinta a kafaɗunta duka biyun, duk da haka wani iri take ji, wuyanta da yake a buɗe, ita kam wannan mayafin asarar kuɗi ne, don ta san ana gama bikin za ta ajiye shi, ta fi gane wa hijabanta. Motar da za a ɗauke su ciki ta cika tsaf, bata samu waje ba.

“Yanzun don Allah sai ku tafi ku bar ni?”

Waheedah ta faɗi cikin sanyin murya, tana ɗorawa da,

“Nuriyya don Allah ki rungumeni…”

Dariya Nuriyya ta yi.

“Ki yamutse min riga? Wallahi ba zai yiwu ba.”

Sake marairaicewa Waheedah ta yi

“Toni ki tashi in rungume ki.”

Maryam, ‘yar yayan Abba da ke zaune gefen Nuriyya ta kwashe da dariya.

“A wace cinyar za ki rungumeta? Mansur mu je don Allah…”

Maryam ta ƙarashe maganar tana miƙa hannu ta ja murfin motar don ta ga alamar in suka biye wa Waheedah za su ƙara ɓata lokaci, ba zata rasa wanda za ta biyo ya kawota ba. Kuma za a daddawo ɗaukar sauran mutane dole dama. Waheedah ɗin kanta ta san hakan, kawai dai ta so ta bisu ɗin ne tunda duk sa’anninta na cikin motar, ga Nuriyya kuma, kafin dai ta gama sanyin jiki duk sun shige. Tsaye ta yi a wajen tana jin idanuwanta sun cika da hawaye.

“Waheedah ke ba ki tafi ba?”

Ta ji muryar Yazid, juyowa ta yi, ƙwalla cike da idanuwanta.

“Wai ba waje…”

Dariya Yazid ya yi, yarinyar bata da wahalar kuka ya kula, sai dai akwai wani abu tattare da sanyin halinta da yake ji har ƙasan zuciyar shi.

“Yanzun Abdulƙadir zai fito, sai ku wuce tare…ina zuwa zan yi abu.”

Yazid ya ƙarasa yana wucewa da sauri, aikam Abdulƙadir ɗin ne ya fito, jikin shi da shadda ruwan toka mai cizawa, ta manta ranar ƙarshe da ta ganshi da manyan kaya, sosai ta ga ya yi mata kyawun da ta ji yasa zuciyarta ta matse waje ɗaya. Sai ƙamshi yake zabgawa, hular da take hannun shi ya saka saman kanshi yana ƙarasowa inda take, ya miƙa mata wallet ɗinshi da agogo yana da links ɗin hannuwan rigar.

“Riƙe min…”

Hannuwanta biyu ta ware mishi ya saka a ciki, yana ɗaukar link guda ɗaya ya fara sakawa a jikin hannun rigar yana zabga tsaki.

“Me yasa Hamma zai min wannan hannun shirmen?”

Da sauri Waheedah ta ce,

“Kawo in sa maka.”

Ƙananun idanuwan shi ya ƙara ƙanƙance mata.

“Kin iya?”

Kai ta ɗaga mishi, kayan hannunta ya karɓa, yana miƙa mata ɗayan hannun shi, kamawa ta yi tana ɗan rausayar da kanta gefe.

“Sai ka ɗago hannunka.”

Ta faɗi a hankali, gyara mata hannun Abdulƙadir ya yi yana kallon yadda ta nutsu tana saka mishi link ɗin, sai ya ga kamar ta fi ɗazun yi mishi haske, ko don ƙwan fitilar da ya haske mata fuska ne, bai sani ba.

“Ɗayan hannun…”

Cewar Waheedah tana jin wani gajimare na mata yawo a kanta. Miƙa mata Abdulƙadir ya yi yana ware mata tafin hannun shi ta ɗauki link ɗin. Saka mishi ta yi, sai ya tsinci kanshi da miƙa mata agogon. Karɓa ta yi ta ɗaura mishi, wallet ɗin ya miƙa mata, ya san yana da aljihu a wando da rigar kayan da suke jikin shi, kawai yanajin bata ta riƙe mishi ne.

“Kin shirya? Mu je?”

Ya tambaya, ta ɗaga mishi kai, har ya numfasa ya yi mata maganar ta buɗe bakinta ta amsa shi, sai ya tuna Waheedah ce, ta saba amsa mishi magana da kai, saboda shi ya saba ƙyaleta duk idan ta yi. Wucewa kawai ya yi tana bin bayanshi, sai da suka ƙarasa tukunna ta ga ɗayar motar Abba ce za su fita a ciki, zagayawa Abdulƙadir ya yi yana buɗe motar ya shiga, har ya kunna bai ga alamar Waheedah za ta shigo ba.

Numfashi ya sauke yana rasa kalar Waheedah, kafin ya miƙa hannu ta ciki ya buɗe ƙofar, yana ganin ta yi baya tana murza hannunta da alamar ya bugeta.

“Sai na ce ki shigo?”

Ya buƙata a faɗace, yana jin gajiyar da bai san daga inda ta fito ba. Idanuwanta take ware mishi, don ta ji ba cewa ya yi ta shiga ɗin ba, tambayar ta ya yi, kai ta girgiza mishi a hankali, da alama tana jiran ya bata umarni ta shiga ɗin tukunna, numfashi ya sake saukewa a karo na farko, baya jin zai iya masifa.

“Shigo Waheedah…”

Ya faɗi da gajiya a muryarshi, shigowar ta yi tana rufe murfin ƙofar. Tana jin daɗin yadda ƙamshin da yake yi ya cika motar.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Abdulkadir | Babi Na Bakwai”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×