Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Sha Shida

1
(1)

<< Previous

Tun da ta kwanta tunanin abin da ya ci ta ke yi, ko kaɗan zuciyarta ta ƙi samun nutsuwa, ita kanta Amatullah ce ta dafa musu taliya, da bata zuba musu tare ba, tana da tabbacin babu abinda za ta saka a cikinta. Don ta nemi yunwar da ta kwaso tun daga makaranta ta rasa, duk da ta san ba lallai ya amsata ba, bai hanata ɗaukar waya ta buɗe manhajar sada zumuntarta na whatsapp ba. Sunan shi ne a sama don shi ne mutum na ƙarshe da ta yi magana da shi.

‘Me ka ci?’

Ta tambaya, tana ɗorawa da,

‘In dafa maka indomie? Ko za ka sha Tea?’

Amatullah da ke kusa da ita ta gyara kwanciyar ta tana fadin,

“Adda Wahee… Ki rage hasken wayarki mana.”

Hannu takai tana rage hasken wayar tare da faɗin,

“Yi haƙuri…”

Bargo kawai Amatullah ta ja tana rufe jikinta har kai ba tare da ta ce komai ba. Hakan ya ba Waheedah damar mayar da hankalinta gabak daya kan wayar, don ba surutun take so ba dama.

‘Shi ne baka faɗa min za ka zo ba ko?’

Ta sake rubutawa tana tura mishi, da ta san zai zo ɗin da ta dafa mishi wani abu, lumshe idanuwanta ta yi tana jin da dare bai fara yi ba ita kam ko indomie ce da ta dafa ta kai mishi, a ƙasan zuciyarta take addu’ar kar ya zauna da yunwa. Alamar shigowar saƙo da ta ji yasa ta ware idanuwanta kan screen ɗin wayar da wani irin bugun zuciyar da ba zai misaltu ba.

‘Waheedah…’

Lumshe idanuwanta ta yi da ta karanta sunan nata da muryarshi, tana buɗe idanuwan da murmushi a fuskarta.

‘Waheedah…’

Ta ga ya sake rubutowa, sai da ta goge hannunta jikin wandon kayan baccin da ta ke sanye da su saboda zufar da ta ji ya mata, tukunna ta iya amsa shi da,

‘Hamma’

Rubutu ta ga ya yi, babu shiri ta tashi zaune, da ita kaɗai ce a ɗakin tsaf za ta yi ɗan ihun murna ko ya yake, yanzun ma gudun tashin Amatullah daga barci ne kawai ya hanata yin hakan, amma kanta har wani lilo yake, kamar tana saman gajimare haka take jinta, kafin ta karanta saƙon shi da ya shigo da wani yare daban da ya saka komai yi mata tsaye cik.

‘Kina so na?’

Karantawa ta ke yi tana ƙara maimaitawa cike da son fahimtar kalmamomin da ta ke jin kamar ba a yaren da take fahimta ya yi su ba, bai bari ta gama fahimtar su ba ya ƙara mata da,

‘Ba so na ‘yan uwa ba Waheedah… So na aure. Kina so na?’

Wayar ta ajiye jin kamar ta ɗauki wani irin ɗumi da yake barazar ƙona mata hannuwa, sauka ta yi daga kan gadon, fankar da ke cikin ɗakin ta ke jin ta mata kaɗan, zafi ta ke ji ba na zazzaɓi ba, zafi take ji dayai girmi ta ɗora shi akan tsantar girgiza da mamaki. Littafin Amatullah da ta yi assignment ta gani a ajiye, da sauri ta ɗauka tana fifita fuskarta da duk wani waje a jikinta da za ta iya. Zuciyarta kanta ta nutsu wani waje a cikin ƙirjinta don ta ji abinda ba su taɓa mafarkin ji ba su dukansu. Saƙon da ta ji ya sake shigowa ya sa ta ɗauki wayar sai dai ta kasa zama sam.

‘Ki amsani, zan ƙirga ɗaya zuwa goma. Karki amsa sai kina da tabbaci, idan ba ki da shi karki amsa, ni da ke za mu yi kamar ban tambaya ba, maganar ba za ta sake haɗa mu ba har abada.’

Gefen gadon ta zauna tana mayar da numfashi a hankali, ta runtse idanuwanta ta buɗe su kan saƙonnin nashi ya fi sau ashirin, so take ta tabbatar ba mafarki ta ke yi ba. Ba kuma tunaninta yake hasaso mata abinda zuciyarta ta ke burin ji ba, amma duk sa’adda za ta buɗe saƙon Abdulƙadir ɗin yake sake yi mata sallama.

‘Ɗaya…’

‘Biyu…’

‘Uku…’

Ta karanta kafin zuciyarta ta fara mata ihu tana sanar da ita yaddda take musu wasa da dama ƙwara ɗaya tal da suka samu a wajen Abdulƙadir ɗin. Ta san shi, kamar yadda ya faɗa ne, idan har ya gama ƙirga goman da ya ce maganar ba za ta sake haɗa su ba har abada. Sai dai yanzun ma bata san yadda akai maganar ta haɗa sun ba, ko a mafarki bata taɓa tunanin hakan za ta faru da ita ba.

‘Hamma… Hamma ka ce wani abu, ka gaya min ba mafarki nake ba, ka ba ni wani tabbacin banda wannan…’

Ta rubuta, sai ta tsinci kanta da gogewa.

‘Huɗu…’

‘Biyar…’

‘Shida…’

Kai take girgiza mishi tana soma rubuta,

“Ina sonka, ban san ko tun yaushe nake sonka ba, ina sonka fiye da yadda zan taɓa faɗa maka Hamma Abdulƙadir, tare da kai zuciyata ta fara buɗe idanuwa, kai zuciyata ta fara dokawa…’

Bata san me yasa ta sake gogewa ba, kalamai take nema, amma ta rasa, har lokacin jin komai take kamar a mafarki, kamar tana tura mishi amsar zata farka.

‘Bakwai.’

Kai ta sake girgiza wannan karon a fili ta ce.

“Ka tsaya Hamma, don Allah ka tsaya…”

Idanuwanta ta lumshe tana sake buɗe su kan wayar tata.

‘Takwas…”

Wani irin yanayi ne ya bayyana kan fuskarta, muryarta a karye ta ce,

“Hamma mana, don Allah ka tsaya…”

Nutsuwarta take son tattarowa ko da abinda yake faruwa zai kasance mafarki, bata so ta manta komai, saƙonnin nashi ta sake karantawa tana lumshe idanuwanta ta adana su wajen da ta san ba za su taɓa ɓace mata ba ko da ta farka tukunna ta buɗe idanuwan nata.

‘Tara…’

Ta karanta.

“Bansan ya zan ci gaba da rayuwa bayan abin nan ba Hamma, idan mafarki ne ka taɓa ni ta fannin da bana jin zan koma dai-dai wannan karon… Ka fifita min wutar burina ka dawo min da komai baya…”

Ta ƙarasa maganar da wani irin sanyin murya, sosai ta ke jin in har mafarki ta ke yi a gefen soyayyarshi da ta ke wahalar da ita, burin samun shi zai zauna, za ta dinga kallon shi tana jiran ya sama mata wajen zama a rayuwarshi ko da bata samu a zuciyarshi ba.

‘Ina son ka, ina son ka da aure Hamma Abdulƙadir.’

Ta tura mishi tana jiran ta ji ta farka daga baccin da ta ke yi, alama ta gani na cewar ya karanta saƙon, kafin ta ga ya sauka daga kan WhatsApp ɗin, wani irin numfashi da bata san tana riƙe da shi ba ta saki, ita ma kashe data ɗin ta yi ta ajiye wayar tare da miƙewa. Banɗaki ta shiga ta tara ruwa tana wanke fuskarta, har lokacin numfashi ta ke mayarwa kamar wadda ta yi gudu. Zuwa yanzun bata da kalaman da za ta fassara abinda ta ke ji . Ta kai mintina goma tsaye a banɗakin ta dafe sink, amma idan ka tambayeta ba za ta ce ga asalin abinda ta ke ji ko ta ke tunani ba.

Alwala ta ɗaura ta fito daga banɗakin, dogon hijab ɗin da take sallah da shi ta ɗauko ta saka jikinta. Dardumar da ta yi sallar isha’i tana shimfiɗe bata naɗe ba, kai ta hau ta fara jero salloli tana roƙon tabbatar alkhairi a koma menene yake shirin faruwa tsakaninta da Abdulƙadir ɗin, don tun daga yadda take son shi ta san abin ya fi ƙarfinta, yanzun ma ba za ta iya ba, ba kuma za ta ɓata darenta tana tunanin abinda baya ƙarƙashin ikonta ba, gara ta buɗe wa Allah zuciyarta, sosai kuma ta samu nutsuwar da take jin ta ƙwace mata, akan dardumar bacci mai nutsuwa ya ɗauketa.

*****

Tana da darasin safe, gashi ta tashi da wani irin sanyin jiki, har iskar da ta ke shaƙa daban ta ke jinta yau ɗin, bata sake shiga wani yanayi ba sai da ta ci karo da saƙon Abba.

‘Assalamu Alaikum. Waheedah ki same ni kafin ki wuce makaranta.’

Haka kawai ta ji zuciyarta na mata rawa, duk da ba yau bane ranar farko da Abban yakan mata irin saƙon ko idan za su yi magana ko kuma zai bata wani abin. Yau ɗin ne dai ta ke jin kiran kamar zai zama na daban. Sa’adda ta gama shiryawa sai da ta biya ɗakin Mami ta yi mata sallama tukunna ta fita zuwa ɓangaren Abba. A bakin ƙofa ta tsaya ta ƙwanƙwasa, sai da ta ji ya yi magana tukunna ta tura ɗakin da sallama tana shiga. Waje ta samu kan kafet ɗin ta zauna don shi ma anan yake zaune ya miƙe ƙafafuwan shi.

“Ina kwana Abba…”

Ta gaishe da shi cikin sanyin muryar ta.

“Waheedah…”

Ya kira yana ɗorawa da,

“Kin tashi lafiya? Ya makarantar?”

Hijabinta da ta ji ta danne ta ɗan ɗaga tana gyara zamanta sosai.

“Alhamdulillah…”

Wani numfashi Abba ya ja yana kallon yadda ta ke komai nata cikin sanyi. Da tunaninta ya kwana a ranshi, har zuwa safiyar ranar yana jinjina wa ƙaddarar da ta haɗa ta da Abdulƙadir, don ko a tunaninshi ya kasa dai-daita dacewarsu. Idan zaɓi za a bashi na ya aurar da ita cikin yaranshi, yana jin Yazid kaɗai zai iya aura wa ita

hankalin shi a kwance, yana da tabbaci akan Yazid zai riƙeta da amana, don ba zai ce ga rana ɗaya da ya ji an yi wata hayaniya da shi ba tun yarintar shi. Muryarshi ɗauke da nauyin da yake jin dukkan jikin shi ya mishi ya soma magana.

“Abdulƙadir ya sameni jiya. Na san halin shi, na san ba zai sameni ba tare da amincewarki ba, amma ina so in tabbatar daga bakinki Waheedah, amana ce ke a wajena kamar yadda su ma suke amana, ban yi wa kowa maganar ba tukunna, ki faɗa min idan kin amince da auren shi…”

Kanta a ƙasa yake tunda ya fara magana, bata taɓa tsintar kanta cikin kunya irin wadda ta ke ji ba, wasu za su ce kamar ƙasa ta tsage su shige, a irin kunyar da take ciki bata jin za ta iya jiran ƙasar ta tsage, ita take so ta narke ta sulale ta bi ƙasar ta shige cikinta. Ga zuciyarta da take wata irin dokawa kamar za ta fito daga ƙirjinta.

“Ki min magana Waheedah, karki ji nauyina, idan har ba ki amince da shi ba ya zo ya sameni ki faɗa min, wallahi in dai ina numfashi babu wanda zai miki dole akan komai na rayuwa…”

Shirun ta sake yi tana ƙara sadda kanta ƙasa, numfashi Abba ya sauke.

“Aure ba abu bane da akan yi don kowa na yi, ba kuma abu bane da ake fatan idan an yi a fito, aure abu ne da ake fatan idan har an yi ya zama na har ƙarshen rai, shi yasa ba a son gaggawa a cikin duk wani abu da ya shafe shi, ba a kuma son tursasawa, da fahimtar juna ma dole sai an haɗa da haƙuri a zamantakewar da za a tashi a kwana ƙarƙashin inuwa ɗaya. Ki min magana Waheedah, ba zan samu nutsuwa akan maganar nan ba…”

Kanta da ta ke jin ya yi ma siririn wuyanta nauyi na ban mamaki yau ta samu ta motsa tana ɗaga shi a hankali, da ace nutsuwar Abba bata kanta da bazaie ga ɗaga kan ba.

“Kin amince da auren shi?”

Abba ya tambaya yana son tabbatar wa, kan ta sake ɗaga mishi a hankali. Wani numfashin ya sauke, yana jinjina wa ƙarfin ƙaddara da take zuwa ƙarƙashin ikon Allah. Kai ya jinjina.

“To Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

Ƙafafuwanta Waheedah ta tattara, har lokacin ta kasa ɗago fuskarta, jikinta gaba ɗaya ya ɗauki ɗumi da kunyar Abba da take ji, miƙewa ta yi da ƙyar tana juyawa cikin sauri da nufin barin ɗakin.

“Ki zo ki karɓi kuɗin makaranta.”

Abba ya faɗi yana saka hannu a aljihun shi, amma kamar maganarshi ta ƙara tunzurata, da gudu ta fice daga ɗakin tana ja mishi ƙofar. Murmushi Abba yake.

“Oh Allah mai iko.”

Ya faɗi, ya jima wani abu bai bashi mamaki ba irin na daren jiya zuwa safiyar yau. Da gaske Abdulƙadir da Waheedah suke yi, yadda yake jinshi zai kwana biyu yana jinjina al’amarin. Wayarshi ya ɗauka ya kira Mami don ya sanar da ita kafin ya samu dangin Baban Waheedah ɗin da maganar, duk da sun jima da nuna mishi yana da damar yanke hukunci akan rayuwar Waheedah ɗin ba zai hanashi nuna musu godiya da halaccin da suka yi mishi ba, zai same su da maganar duk da yasan ba zasu ƙi kowa yake son haɗa ta da shi ba, balle kuma idan sun ji jinin shi ne.

*****

“Ina za ki je?”

Muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta, yana saka ta gyara zaman jakar da ke kafaɗarta tukunna ta juya tana sauke idanuwanta akan shi. Jikin shi sanye da riga fara ƙal, sai wandon sojoji gajere da silipas ɗin wanka a ƙafafuwan shi.

“Hamma”

Ta kira da wani yanayi a muryarta, wani irin son shi ta ji ya taso mata har yana wa numfashinta barazana. Ta san ya kamata ta sauke idanuwanta daga kanshi, ta daina kallon shi, amma zuciyarta ce da iko kan idanuwanta wannan karon, ta kuma nuna mata bata gaji da kallon shi ba. Shi ma idanuwan shi ya ƙanƙance akanta da da ƙyar take ganin ƙwayar cikin su, fuskarshi a kumbure take har idanuwan da alamar rashin wadataccen bacci.

“Ina za ki je?”

Ya maimaita tambayar yana kallonta, tsaye yake ya hango hijabinta da yake share harabar gidan, blue ne mai hasken da ya yi mishi kyau sosai. Ba don baya ganin masu saka hijab ba, amma kowa zai gani da hijab ita ce mace ta farko da take zuwa mishi a rai, kuma bai taɓa ganin wadda hijab yake ma kyau kamarta ba, zai rantse yanayin tafiyarta a cikin hijabanta daban yake. Kamar hijab ɗin na bata wani asirtaccen confidence da idanuwa ba sa iya gani, sai ya ga kamar ba Waheedah mai sanyin halin nan ba, kwarjininta daban yake mishi in tana cikin hijabanta.

Idanuwanta take raba mishi, wannan karon cike da wani yanayi da ya saka jikinshi ɗaukar ɗumi, kalar hijabin ya ƙara mata farin da yasa shi furta,

“Wanne irin mai kike shafawa?”

Da mamaki bayyane a fuskarta ta ce,

“Vaseline”

Ƙanƙance mata idanuwa ya ƙara yi.

“Yana ƙara haske?”

Dariya ta yi tana girgiza mishi kai.

“Hamma Vaseline fa.”

Kafaɗunshi ya ɗan ɗaga mata, ba zai sani ba, tunda haske take ƙara mishi a duk ganin da zai mata.

“Ina za ki je?”

Ya sake tambaya a karo na uku. Da murmushi a fuskarta har lokacin ta ce,

“Makaranta”

Ta ɗauka wani abu zai canza tsakaninsu da maganar auren, amma bata ji komai ba ita kam, banda soyayyar shi da duk lokacin da za ta ɗauka babu wani waje a jikinta da ya rage wanda ba ya dokawa da soyayyarshi, sai ta sake jinshi a wani wajen da bata san yana motsi ba. Babu abinda ya canza, shi ɗin ne dai, Hammanta, Sadaukinta, ko babu maganar auren bata jin akwai inda za ta kai soyayyar shi.

“Da sassafen nan? Waye zai kai ki?”

Abdulƙadir ya faɗi yana katse mata tunanin da ta ke yi.               

“Ina da class, na ma makara, napep zan hau…”

Kai ya fara girgiza mata yana sa ta ɗorawa da,

“Ina zuwa Hamma, ba kullum ake kai ni ba.”

Kan Abdulƙadir yake girgizawa har lokacin, yaushe Waheedah ɗin ta yi girman da za ta je makaranta, ta tafi ita kaɗai bai zauna mishi ba sam.

“Na iya zuwa Allah.”

Ta faɗi ganin shakkun da ke cikin idanuwan shi.

“Ki jira ni ina zuwa…”

Cewar Abdulƙadir ɗin yana juyawa da sauri. Binshi ta yi da kallo har ya shige ɓangaren su, idanuwanta akan kofar tana jiran fitowarshi da dukkan zuciyarta. Bai fi mintina biyar ba ta ga ya fito yana takowa zuwa inda take, tari ta ɗan yi da yadda zuciyarta ta matse cikin ƙirjinta kamar akanta yake tafiyar.

“Mu je…”

Ya yi maganar yana yin gaba, ta bishi a baya har wajen motar Yassar, mukullin yasa ya buɗe ƙofar, ita kuma ta zagaya, sai da ya zaro wayarshi daga aljihun bayan wandon tukunna ya shiga ya zauna, hannu ya miƙa ya buɗe ma Waheedah ɗayan ƙofar ta shigo ita ma. Wayarshi ya ɗora kan cinyarta kamar babu inda zai iya ajiyewa a cikin motar gaba ɗaya. Ɗaukar wayar ta yi ta riƙe a hannunta, tana jin shi ya tayar da motar yana jansu suka fice daga gidan.

“BUK, old site”

Ta ce mishi.

“Na ce miki ban sani ba?”

Kai ta girgiza mishi.

“Me yasa kike faɗa min to?”

Ya sake maganar yana ɗan kallonta kafin ya mayar da hankalin shi kan tuƙin da yake yi. Har malamansu gaba ɗaya ya sani, ba zai ce ga course ɗin da take da shi ba a ranar, amma idan ya duba wayarshi zai iya faɗa mata, a cikin labaranta gaba ɗaya yasan hakan, me yasa take tunanin bai riƙe ba? Don bai amsa ba ba ya nufin bai karanta ba, ba ya nufin hankalin shi ba ya kai. Shiru ta yi bata amsa shi ba, tunda ta san halin shi.

“Ba ki ci abinci ba…ba ki ci komai ba kika fito.”

Ya yi maganar kamar tunanin ya faɗo mishi. Girkin Mama ne har ranar, da yunwa ya tashi ya kuma je ɓangarenta bata gama ba, lokacin da ya shiga ma ake fere doya. Ko da yayi maganar da alamar tambaya ne, Waheedah bata jin za ta amsa shi, ba zai sauke mata faɗan shi da sassafe ba.

“Kin san yadda abincin safe yake da muhimmanci?”

Murmushi ta ji ya ƙwace mata, ba abincin safe bane kaɗai yake da muhimmanci a wajen Abdulƙadir, duka abinci na da muhimmanci don ba ya wasa da cikinshi ko kaɗan. Wani shago ya hango, hakan yasa shi tsayawa, ba tare da ya ce mata komai ba ya fice daga motar. Wayarshi da ke hannunta ta latsa don taga ko ƙarfe nawa, zuciyarta ta yi tsalle zuwa maƙoshinta ganin hoton da ke kan wayar. Hannuwanta ne babu tantama, da ƙunshinta da bata manta ranar da ya ɗauka ba.

“Hamma”

Ta faɗi da wani irin yanayi a muryarta tana shafa screen ɗin wayar. Dai-dai lokacin da Abdulƙadir ya buɗe motar ya shigo yana ɗora mata leda akan jikinta da kashedin,

“Karki sake fitowa ba ki ci wani abu ba.”Ba ta abinci ta ke yi ba, kallon shi ta ke tana jin wani irin yanayi da ba zai fassaru ba, har suka ƙarasa makarantar babu wanda ya sake cewa wani abu. Har department ɗinsu ya kaita yana zaune cikin motar sai da ya ga ta shiga aji tukunna ya sauke numfashin da bai san yana riƙe da shi ba, kafin ya yi wata irin hamma, ba wani bacci ya samu ba jiya, yana kwance yana tunanin yadda akai rayuwa ta kawo shi inda yake yanzun. Sai dai zuwa safiyar yau komai ya mishi dai-dai. Tana son shi, zai aureta, ya riga da ya gama duk wani tunani da zai yi akan hakan. Yanzun ya ga garin da aka kai shi ne abinda yake ranshi, sai ya yi magana da Hajja don ya ji ko nawa ne zai tara. Juya motar ya yi yana nufar gida.

*****

Sallar Azahar ya dawo, yana kwance a ɗaki ya ji an turo ƙofar kamar za a karyata.

“Abdulƙadir me ka yi?”

Ya ji muryar Yassar ɗin ranshi da alamun a ɓace yake. Sai dai a iya tunanin Abdulƙadir ɗin bai san ya mishi wani abu da zai ɓata mishi rai ba. A nutse ya tashi daga kwanciyar shi ya zauna yana daƙuna wa Yassar ɗin fuskarshi cike da rashin fahimta.

“Ka ji ni ai, me ka yi?”

Yassar ya sake faɗi yana jin yadda yake gab da kwashe Abdulƙadir ɗin da mari. Aiki ya fita, yau da wuri yake tashi, yana dawowa yake jin ana maganar auren Abdulƙadir ɗin da Waheedah cikin wata shida tare za a haɗa da na su Yazid. Maganar yake ji kamar wasa, sai da ya tambayi Mama ta ce mishi da gaske ne, Abba da kanshi ya fada musu. Ya san halin Abdulƙadir zai iya cewa fiye da kowa a gidan, ya san yadda yake son kanshi fiye da tunani, amma bai ɗauka ya kai haka ba. Bai ɗauka ya kai ya yi amfani da soyayyar da Waheedah ɗin take mishi ta wannan fannin ba.

“Kai min magana yadda zan gane Hamma.”

Abdulƙadir ya faɗi a kasalance, bacci yake ji, kuma da niyyar yin baccin ya kwanta.

“Waheedah… Me ka yi Abdulƙadir…”

Ɗan dafe kai Abdulƙadir ya yi yana faɗin,

“Oh… Aurenta zan yi…”

Numfashi Yassar ya ja ta baki yana fitar da shi ta hancin shi.

“Ba ka son ta Abdulƙadir, me ka yi haka?”

Kafaɗu Abdulƙadir ɗin ya ɗan ɗaga mishi.

“Tana sona…”

Wata dariya Yassar ya yi ba tare da ya sani ba ma.

“Wai ma me ya faru ka sameni kana ta hure-huren hanci kamar dragon… Ba jiya kake min maganar yadda take sona ba?”

Kai Yassar ya dafe yana sauke numfashi, sosai yake jin yadda ya kusa kwaɗa ma Abdulƙadir mari.
“Da na ce tana sonka ban ce ka je ka ce za ka aureta ba ka shirya ba.”

Gyara zaman shi Abdulƙadir ɗin ya yi.

“Eh haka Abba ya ce ba a aure babu shiri, shi yasa ba za a yi nan da sati biyu ba, tare da na su Hamma Mubarak za a haɗa, wai za a yi su lefe… Zan je in ma Hajja maganar ma… Zan tara kuɗin in sha Allah, albashina da ɗan yawa… Zai isa idan na tara…”

Ciwon kai Yassar ya ji ya saukar mishi, abinda yake nufi daban, abinda Abdulƙadir yake fahimta daban, ba shiri na hidimar aure yake mishi magana ba, shiri na zaman aure da yake buƙatar fiye da soyayya.

“Abdulƙadir … Ba ka son ta.”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Tana sona Hamma.. Me yasa ba zai ishe mu ba?”

Ya ƙarasa maganar yana jin ranshi ya soma ɓaci, bai ga dalilin da zai sa Yassar ya dinga maimaita mishi magana ɗaya kamar ita ce abu mai muhimmanci a maganar auren, ya tambayi Waheedah ta ce tana son shi da aure, shi ma kuma a shirye yake ya yi zaman aure da ita, bai kuma san mene ne ya fi wannan muhimmanci ba.

“Bacci nake ji… Don Allah ka bar ni ni kam. Na riga da na gama magana da Abba, auren nan zai faru… Maganganun duk da muke ɗin nan ba su da wani muhimmanci tunda ba za su canza komai ba.”

Abdulƙadir ya yi maganar yana komawa ya kwanta tare da jan mayafi ya rufe jikin shi. Kai Yassar yake girgiza mishi yana da na sanin furta mishi cewar Waheedah na son shi, har ga Allah bai taɓa tunanin ba soyayya suke ba, da ya sani da ba zai taɓa tayar wa da Abdulƙadir da maganar ba, amma lokaci ya ƙure. Kamar yadda Abdulƙadir ɗin ya faɗa ne, maganganun shi ba za su canza komai ba.

“Don Allah karka cutar da ita, karka yi amfani da soyayyar da take maka ka cutar da ita Abdulƙadir , marainiya ce, karka cutar da ita…”

Yassar ya yi maganar da wani irin yanayi a muryarshi, a ƙasan zuciyarshi yana addu’ar kar Abdulƙadir ɗin ya taɓa da na sanin auren Waheedah ɗin, don yana jin ya yanke hukuncin aurenta cikin gaggawa, ko da ya shirya zaman aure da ita, ya yi gaggawa ya gane hakan a jiya kawai. A wani ɓangaren yana fatan akwai wani ɓangare a ƙirjin Abdulƙadir ɗin da yake doka wa Waheedah ba tare da ya sani ba.

“Ka ja min ƙofar in ka fita.”

Abdulƙadir ya amsa kamar bai ji maganganun da Yassar ɗin ya yi ba.

“Allah ya tabbatar da alkhairi…”

Cewar Yassar yana ficewa ya ja wa Abdulƙadir ɗin ƙofa, idanuwan shi ya lumshe, don ba shi Yassar zai saka tunani ba, bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi.

*****

Ba za ta ce ga yadda satika biyu suka wuce mata ba, ta san dai a cikinsu abubuwa da dama sun faru, har da maganar da Mami ta yi mata kan auren Abdulƙadir ɗin ita ma kamar Abba tana son ƙarin tabbaci ne. Da ta samu ɗin kuma addu’a ta yi musu.

“Allah yasa alkhairin juna ne ku, Allah yasa muku albarka a tafiyar da ke gabanku Waheedah, Allah ya yafe wa mahaifinki ya kyautata makwancin shi.”

Ko ita kaɗai ta zauna addu’ar Mami kan sanyaya wajejen da bata san suna mata zafi ba. Tun ‘yan gidan na mamakin maganar auren su ma har sun daina, don Zahra ma sai da ta ce mata,

“Lallai ma, ki rasa wa zaki aura a duniyar nan sai Hamma Abdulƙadir? Ya gama zane ki ya lallaɓo kuma za ki aure shi…Taɓɗi…”

Dariya kawai takan yi, Mubarak ma da ya kai ta makaranta a cikin satikan sai da ya yi zancen.

“Zuciyarki bata kyauta miki ba Waheedah… Ta rasa wa za ta janyo muku sai masifaffen nan. A ƙafa aka ɗaura min Abdulƙadir sai na tsinke na yi ta kaina…”

Shi ma dariyar ta yi mishi a kunyace. Ba za su taɓa fahimtar yadda take son Abdulƙadir ɗin ba, ita kanta ba za ta ce ga yawan soyayyar da take mishi ba, halayenshi kaf babu wanda ya taɓa damunta balle ya ɗaga mata hankali, faɗanshi kan tsaya mata a rai duk idan ya yi mata shi wasu lokutan , tana kuma tsoron faɗan nashi, sai dai bai taɓa zama dalilin da zai hanata tunkararshi da kowace irin magana ba, kuma bai taɓa sa ta ji soyayyarshi ta yi ko alamar dishewa ba. Tana son shi da duk wani abu da yake tattare da shi.

Kwata-kwata tun satin farko ta ke neman wayar Nuriyya bata samu ba, sau biyu ta biya ta makarantarsu bata samunta, sai a sati na biyu ne ta sameta a waya ashe bata jin daɗi ne, har gida ta je ta dubata take kuma faɗa mata sa ranarta da Abdulƙadir, ta yi mamakin da.

‘Allah yasa alkhairi’

Kawai Nuriyya ta furta, sai dai Waheedah ta yi mata uzurin cewar don bata da lafiya ne, ta dai gyara mata gidan da ya yi kamar ya yi wata bai ga tsintsiya ba, ga tarin wanke-wanke, kusan duk wani abu da yake kitchen ɗin bashi da a kyau. Ko ina ta gyara mata tsaf, har girki ta yi mata tukunna suka yi sallama ta bar gidan. A satin kuma sai da ta koma dubata har sau biyu, zancen bikinta dai bai sake haɗa su ba, za ta yi ƙarya wannan karon in ta ce ranta bai mata wani iri ba. Ta dai sake yi mata uzuri da rashin jin daɗin auren Anas da ta ke yi har lokacin, hankalinta bai yi kwanciyar da za ta yi rawar ƙafa kan nata auren ba.

Ranar lahadi ce, ba makaranta ke akwai ba, takan je Islamiyya a ranakun hutun ƙarshen mako, amman ranar Abdulƙadir zai wuce, an tura shi Minna. Ya ce mata ba dawowa zai yi ba sai bikinsu, ba zai tafi bata ganshi ba, text ɗin shi ta gani a wayarta,

‘Ina wajen motar Hamma Yassar.’

Miƙewa ta yi zuciyarta na dokawa kamar za ta fito waje. Hijabinta ta ɗauka ta saka, tukunna ta ɗauki ledar da ke ajiye kan gadon, addu’a ta ke yi kar ta ci karo da Mami a falon don bata san kalar kunyar da za ta ji ba. Ita da Abdulƙadir ɗin ba wani lokaci suke samu su kaɗai ba tun bayan maganar, yanzun takan samu ya amsata dai-dai a WhatsApp, wani lokacin kuma yana kira, duk da hirar ita za ta yi mishi, ko in tana mishi a WhatsApp zai kirata ya ce bacci yake ji ta ƙarasa mishi labarin zai gani da safe.

Wasu lokutan kuma in tana makaranta ya ce karta taho ta jira shi zai je ya ɗauko ta. Banda wannan babu abinda za ta ce ya canja, in sun haɗu za ta gaishe shi kamar da, zai sa ta yi mishi abu kamar yadda yakan sa ta yi mishi a baya. Allah ya amshi addu’arta bata samu Mami a falon ba, kamar marar gaskiya haka ta fice da saurinta. Wajen harabar motocin ta same shi ya jingina bayanshi da motar, jikinshi sanye da rigar saƙi ta sanyi marar nauyi, dogon hannu ne amma ya ja hannuwan rigar sosai, sun tattare daga wajen damtsen shi.

Kallon shi ta yi tana ɗaukar hotunan shi cikin kanta don ya mata kyau sosai da sosai.

“Tafiya zan yi Waheedah…”

Ya faɗi lokacin da ta ƙarasa ta tsaya a gefen shi, kai ta jinjina mishi, tana sane da tafiyar kamar tare za su yi ta, don tana jin yadda zai tafi da fiye da zuciyarta, har da kaɗan daga cikin ruhinta. Ledar da ke hannunta ta miƙa mishi ya karɓa yana riƙewa.

“Ka kula da kanka Hamma… Banda ƙin shan magani don Allah…in ba ka jin daɗi ka je a duba ka kaji?”

Ta ƙarasa maganar tana kallon shi, ta san yana kula da kanshi takowanne fanni banda lafiyar shi, saboda ba ya son magani, bata taɓa ganin mutumin da ba ya son magani irin shi ba.

“Ki bar ni ba yaro bane ni…”

Ya yi maganar yana tsareta da ƙananun idanuwan shi, ita kaɗai take tsira shi da maganganu haka, take mishi kamar yaro ba tare da ta nuna alamar ta raina shi ba. Yadda ta ke nuna tsoron shi yakan ga hakan har cikin idanuwan ta, amma baya hanata faɗa mishi duk abinda ta yi niyya. Ledar da ke hannun shi ya buɗe don ba zai iya jira sai ya ƙarasa ɗaki ba, in ya ƙarasa ɗin ma jakarshi zai ɗauka Yassar ya kai shi tasha.

“Ba anan za ka buɗe ba Hamma…”

Waheedah ta yi maganar da murmushi a fuskarta.

“Saboda me?”

Ya tambaya yana saka hannun shi cikin ledar.

“Saboda haka kowa yake yi.”

Agogo ya ji cikin ledar ya ɗauko yana fitowa da shi tare da faɗin,

“Ni ba kowa bane ba.”

Ya ƙarasa maganar yana miƙa mata agogon ta karɓa, hannun shi ya miƙa mata, akwai wani agogon a ɗaure, na sojoji ne ma, kwance mishi agogon ta yi ta ɗaura mishi wanda ta siya ɗin, dubawa ya yi yana jinjina kai, nashi agogon ta miƙa mishi tana jin zuciyarta ta matse waje ɗaya.

“Ki ajiye min, idan na dawo zan karɓa…”

Ya faɗi, yanayinta yasa shi son ya bar mata wani abu, agogon ne kawai abinda yake dashi a yanzun. Ko da bata bashi wani ba ya yi niyyar cirewa ya ɗaura mata, ganin ta yi tsaye tana kallon agogon kamar ya bata wani ɓangare na zuciyarshi yasa shi karɓar agogon daga hannunta, ɗago idanuwanta ta yi tana ware su kan fuskarsa. Bai manta kashedin Yazid na cewar ba muharramar shi bace, ya daina taɓa ta, kawai ya yi watsi da kashedin ne ya kamo hannunta yana zagaya agogon a jiki tare da ɗaurawa. Dariya ya yi har haƙoran shi suka fito, ta jima bata ga haƙoran shi haka ba in ba magana yake ba.

“Wahee…”

Ya faɗi yana sa tsikar jikinta miƙewa.

“Wanne irin hannu ne wannan?”

Ya yi maganar da dariya a muryarshi ganin agogon na yawo, kwancewa ya yi yana saka shi cikin tafin hannunta ta dumtse.

“Ki kula da kanki Waheedah…”      

Kai kawai ta iya jinjina mishi, ƙafafuwanta kamar an kwance abubuwan da suke ɗaure da su saboda sanyin da ta ji sun mata. Numfashi Abdulƙadir ya sauke har lokacin yana riƙe da hannunta da yake jin shi ɗan ƙarami a cikin nashi, tsintar kanshi ya yi da faɗin,

“Ki ce wa duk wanda zai kulaki a makaranta mijin da za ki aura soja ne. Ki faɗa musu Second Lieutenant A. Bugaje ne, yana da kishi fiye da tunani.”

Murmushi mai sauti ta ji ya ƙwace mata, duk da idanuwanta cike suke taf da hawaye, kewar shi ta fara danneta tun yana tsaye a gabanta. Bata san hawayenta sun zubo ba sai da ta ji yatsun ɗayan hannunshi ya share kuncinta.

“Ba a san matar soja da rauni ba.”

Ya faɗi yana mata murmushi, zuciyarshi yake jin ta yi wani shiru, hawayenta sun tsaya mishi a maƙoshi, da gaske Yassar yake, tana son shi, a fuskarta yake karantar hakan, yana mamakin yadda ya ɗauke shi tsawon lokaci bai ga hakan ba. Har a ƙasusuwan shi yake jin aurenta ne zaɓi mafi girma da ya taɓa yi a rayuwar shi.

“Matar Sadauki.”

Ta yi maganar tana saka idanuwanta cikin nashi. Kai ya jinjina mata yana maimaita.

“Matar Sadauki…”

Sunan na zauna mishi a duka jikin shi, wannan karon ita ta yi dariya. Za ta yi kewar shi ta sani, amma ya bata abinda zai riƙe ta har ya dawo.

“Allah ya tsare maka hanya ya sauke ka lafiya.”

Amsawa yayi da,

“Amin…”

Yana dumtsa hannunta da ke cikin nashi kafin ya saki, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Zan kiraki…”

Kai ta ɗaga mishi, tukunna ya juya, agogon shi da ke hannunta ta dumtsa tana sauke numfashi mai nauyin gaske, idanuwanta akan shi har ya ɓace ma ganinta.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×