Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Tara

5
(1)

<< Previous

Washegarin ranar a kwance ya wuni, tunda ya yi wanka, karin safe ma bai yi ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya na safe. Ko da ya fita ya yi sallah a masallaci wajen ƙarfe ɗaya, yana dawowa ɗaki ya cire dogon wandon ya mayar da iya gwiwarshi, kwanciya ya koma ya yi. Idan abu ya riga ya wuce baya tunanin shi, baya wannan asarar, shi yasa bai san dalilin da Nuriyya za ta manne mishi cikin kai haka ba, ko idanuwan shi ya rufe ita yake gani, ta addabe shi, ta hana shi sakat, ya riga da ya faɗa wa kanshi tana da kyau, bai yi wa kanshi ƙarya ba tun farko, amma ta ƙi barin shi, wani in ya gani sai ya rantse da Allah hotonta ya ɗauka ya samu waje ya rataye cikin kanshi.

A hankali ya ja ƙaramin tsaki yana juya kwanciyar shi, yunwa ya ji ta fara mishi sallama, duk da bai karya da wuri ba, saboda shi mutum ne da baya wasa da abinci kwata-kwata. In har bai ci ba, to damar hakan ne bai samu ba. Ya miƙe yasa wani ya kawo mishi ɗin ne yake mishi wahala yau, lumshe ƙananun idanuwanshi ya yi, har lokacin Nuriyya na manne cikin kanshi, bacci ne ya fara fisgarshi a hankali. Cikin kunnen shi ya ji an turo ƙofar tare da yin sallama a hankali.

“Hamma”

Muryar da ya yi tunanin Nazir ne ta dirar mishi. Shiru ya yi bai amsa ba, yana fatan shirun ta sa ko waye ya tafi.

“Hamma ka zo in ji Hajja.”

Nazir ya faɗi yana riƙe da ƙofar ko da almatsutsan Abdulƙadir ɗin za su tashi. Ba zai tsaya ya sauke su akan shi ba.

“Kaina na min ciwo.”

Abdulƙadir ya faɗi ba tare da ya buɗe idanuwanshi ba, bai san kiran me Hajjon take mishi ba, ɓangarenta yasan a cike yake da mutane, ta kuma san ba son hayaniyar yake ba, za ta fara sakawa a kira shi. Ba kanshi yake ciwo ba, jikinshi ne baya jin daɗin shi. Turo baki Nazir ya yi don sai da Hajja ta balbale shi da faɗa tukunna ya zo kiran Abdulƙadir ɗin.

“Ta ce ka zo…”

Sake runtsa idanuwan shi Abdulƙadir ya yi.

“Zan ci ubanka idan na buɗe idanuwana kana cikin ɗakin nan.”

Yanajin ƙarar rufe ƙofa, ba tare da ya buɗe idanuwanshi ba ya gyara kwanciyarshi yana kwantawa kan bayanshi tare da ɗora hannuwanshi duka biyun kan cikinshi, bacci ne mai ƙarfi ya ɗauke shi wannan karon duk da yunwar da yake ji. Ba zai ce ga lokacin da ya ɗauka ba, baccin kuma yau ya yi ƙarfin da bai ji turo ƙofar ba sai bubbuga mishi ƙafa da ya ji ana yi, a tunaninshi Nazir ɗin ne ya sake dawowa, raini ya sa shi har da bubbuga mishi ƙafa wannan karon.

Cikin zafin nama ya yi amfani da inda yake jin hannun na bubbuga shi ya hasaso inda yake tunanin fuskar Nazir ɗin za ta kasance ya kai mishi wani ɓarin makauniya.

“Umm um um umm…”

Yassar ya faɗi yana jin wani yawu da yake tunanin jini ne na tattarowa yana cika mishi baki, don a mummuƙe Abdulƙadir ya same shi.

“Ba zaka fita ba kenan don uban ka?”

Abdulƙadir ya faɗi jin gurnanin da Yassar ɗin ya yi yana buɗe idanuwan shi tare da miƙewa ta sauke su kan Yassar da ke dangwalo mummuƙen shi yana dubawa, ware ƙananun idanuwanshi Abdulƙadir ya yi.

“Innalillahi… Hamma… Wallahi na ɗauka Nazir ne…”

Hannu Yassar ya ɗaga mishi kawai yana wucewa banɗaki ya kuskure bakinshi yana zuwa saitin mudubi, wajen har ya tara jini daga waje, buɗe bakinshi ya yi yana zira dan yatsa ya taɓa haƙorinshi na sama da ya ji kamar ya fara girgiɗi, sosai ya tattaɓa haƙoran duk da yake tunanin sun fara girgiɗi ya ji suna zaune dam, dubawa ya sake yi ya ga babu jini tukunna ya fito daga banɗakin yana samun waje gefen gadon ya zauna, ba zai yi ƙarya ba, ya maku yadda ya kamata.

“Hamma…”

Abdulƙadir ya kira da alamun dariya a muryarshi ganin yadda Yassar ɗin ya nutsu. Gaba ɗaya fuskar shi Yassar yake ji ta ɗauki ɗumi kamar tana zazzaɓi ita kaɗai. Sai da ya tabbatar idan ya yi magana muryarshi ba za ta yi rawa ba tukunna ya ce,

“Don ubanka ba za ka buɗe idonka ba? Da ka cire min haƙori me za ka faɗa min?”

Sosai Abdulƙadir yake son danne dariyar shi amma ya kasa, sauka ya yi daga kan gadon yana miƙewa tsaye, sosai yake dariya.

“Inda Nazir dinene haka za ka kai mishi wannan dukan? Saboda kai ba ka da tausayi?”

Dariya Abdulƙadir yake yi.

“Wallahi ban san kai bane ba.”

Kai Yassar ya jinjina yana yin ƙwafa kawai. Gaba ɗaya duk wani ƙarfin gwiwa da ya shigo da shi ɗakin ya gama sacewa. Banɗaki Abdulƙadir ya wuce yana wanko fuskar shi ya fito, nesa da Yassar ɗin ya zauna, don yasan in ya yanke hukuncin rama dukanshi zai ji jiki. Tukunna ya ce,

“Menene kake tashi na?”

Sai da Yassar ya watsa mishi wani kallo tukunna ya ce,

“Hajja ta ce za ka ɗauki mutanen da za su kai Khadija, sai ka tabbatar ka tattaro su Zahra don kar su ce za su kwana…”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ɗin ya yi.

“Gaskiya babu inda zance…bari in kira su Zahra ɗin in musu kashedi kawai.”

Tsare shi da idanuwa Yassar ya yi cikin yanayin da ya sashi ƙara daƙuna fuska yana faɗin,

“An shiga rayuwa ta wallahi… An takura ni gaskiya.”

Kallon shi dai Yassar ya ci gaba da yi ba tare da ya ce komai ba. Abdulkadir din baya son yana kallon shi haka, baya so yana kallon shi kamar ya yi wani laifi. Me yasa za a ce ya fara kai mutane wani waje, Hajja ta san a gidan in ba ita ba sai Abba, ko yara ba a sakawa ya kai makaranta. Balle ya zo ya fara ɗibar wasu mutane kamar direba.

“Ba zaka je ba ka ce Abdulƙadir? Kai tsaye ba za ka je ba? In ce maka Hajja ta ce ka yi abu kana faɗa min ba za ka je ba? Don Ubanka ba za ka shiryu ba, ba za ka gane girma kake yi ba ko?”

Yassar yake faɗi ranshi a ɓace, bai san lokacin da Abdulƙadir ɗin zai gyara wannan muguwar ɗabi’ar ta rashin ganin kan kowa da gashi ba. Kicin-kicin Abdulƙadir ɗin ya yi da fuska.

“Ni dai an shiga rayuwata gaskiya.”

Ya sake maimaitawa yana saka Yassar faɗin,

“Ya yi kyau”

Ya ja ƙafafuwanshi yana ɗorawa kan gadon, wayarshi ƙirar blackberry curve 2 ya zaro daga aljihu yana ci gaba da dannawa. Sake daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi yana kallon Yassar ɗin, yasan ranshi ne ya ɓaci, bayan Abba a gidan babu wanda yake ƙoƙarin guje wa fushinshi irin Yassar, fiye da Hajja don yasan ita da wuri take sakkowa.

“Wace unguwa ce?”

Ya buƙata muryar shi can ƙasan maƙoshi, inda yake Yassar bai kalla ba, ballantana ya yi ƙoƙarin kula shi.

“Hamma ka ji … Wacce unguwa? Ƙarfe nawa za a tafi?”

Shirun Yassar ya sake mishi.

“Bana so ina magana ana mun shiru, ka sani kuma, ina tambayarka ka yi banza ka ƙyale ni.”

Yanayin yadda ya yi maganar ya sa Yassar faɗin,

“Faɗa za ka yi min Abdulƙadir?”

Ƙanƙance idanuwa Abdulƙadir ya sake yi.

“Magana nake maka ka yi shiru ka ƙyale ni.”

Kai kawai Yassar ya jinjina.

“Ya maka kyau.”

Ya ƙarasa maganar yana miƙewa ya fice daga ɗakin, Abdulƙadir na binshi da faɗin,

“Kaifa ka ƙi bani amsa, ban yi fushi na bar maka ɗakin ba kai ne za ka fita? Hamma bana son irin haka… Hamma… Ok ya maka kyau.”

Wucewa Yassar ya yi, yana jin ‘Ya maka kyau’ ɗin da Abdulkadir ɗin ya faɗi da ta sa shi jin son komawa yasa belt ya zane jikin Abdulƙadir ɗin, sai dai alƙawari ya yi wa kanshi ba zai biye wa Abdulƙadir ɗin ba, don idan akwai mashi a kusa, tsaf takaicin da zai ƙunsa maka zai sa ka soka mishi ba tare da ka sani ba. Idan ya biye wa Abdulƙadir zai dake shi sai ya karya shi, yana kuma da tabbacin duk da ba zai rama ba, bakin shi ba zai yi shiru ba. Addu’ar shiriya ya yi mishi kamar ko da yaushe.

*****

Sai da ya ɗauro alwala tukunna ya fito daga ɗakin da nufin zuwa masallaci don ya ga la’asar ta kusan ƙarasawa, yana da tabbacin ana gab da kiran sallah.

“Zahra”

Ya kira da ya hango ta taho, tun jiya yake mamakin girman yarinyar, wai har ta gama sakandire, Yassar ne yake faɗa mishi ta nemi gurbin karatu a jami’ar Bayero dake nan Kano ɗin ma da yake mishi zancen girmanta. Duk da ta tsallake aji uku, kasancewar tana da ƙoƙari sosai. Takowa take a hankali tana nufo inda Abdulƙadir ɗin yake.

“Yanga za ki tsaya min?”

Ya faɗi yana kallonta, kai ta girgiza mishi tana saurin faɗin,

“A’a…”

Ta ƙarasa inda yake tsaye da sauri. Kallonta Abdulƙadir ya yi, ɗankwalin lace ɗin da ke jikinta ne ta ɗora saman kanta ba tare da ta ɗaura ba, in dai Zahra ce ba za ta taɓa yin abu irin na mutane ba ya sani, ko makaranta za ta je hijabinta in ba ya hannu lokacin za ka ga tana saka shi.

“Ki kawo min abinci…da ruwa, ki kai min ɗakina a buɗe yake…”

Amsa shi ta yi, tana shirin juyawa Abdulƙadir ya ce,

“Ki faɗa musu ni zan dawo da ku daga wajen kai Adda… Duk wanda na nema sai ya ji a jikinshi.”

Ware idanuwa Zahra ta yi, gabanta yana faɗuwa kafin ta daƙuna fuska.

“Ba ki ji ni ba sai na watsa miki mari.”

Sake daƙuna fuska ta yi, da gaske Hajja take ba za su kwana ba ɗin dai, bayan Adda Khadee ɗin da kanta ta ce musu za su kwana tun kafin bikin.

“Zan faɗa musu.”

Zahra ta amsa tana wucewa, yana kallonta ta sha kwana, tunawa yayii bai ma tambayeta wacce unguwa ko kuma ƙarfe nawa ba, bin bayanta ya yi tunda ta riga da ta sha kwana ko ƙwala mata kira ya yi ba lallai ta ji shi ba, gashi yau baya jin hayaniya kwata-kwata. Zahra kuwa tana shan kwana ta ci karo da Amatullah.

“Kin san Hajja ta sa Commander ne ya kai mu?”

Dafe ƙirji Amatullah ta yi.

“Kice min wasa kike yi? Haba dai Commander… Ina ce Hamma Yazid za mu bi.”

Kai Zahra ta girgiza wa Amatullah ɗin.

“Yanzun ya yi min magana da kanshi, wai kar ma mu bari ya neme mu idan an kaita ɗin.”

Buga ƙafafuwa Amatullah ta yi cike da rashin jin daɗi.

“Allah dai ya haɗa mu da jarabu da ƙwai…”

Turo baki Amatullah ta yi tana faɗin,

“Ai gara Jarabu da ƙwai akan Hamma A…”

Haɗiye maganar ta yi ganin Abdulƙadir ɗin a tsaye ya diro musu kamar mikiya. Yadda ya tsareta da idanuwa yana tabbatar mata da maganar yake so ta ƙarasa, wani abu da ta ji ya tsaya mata a wuya ta haɗiye, a daburce ta ce,

“Hamma A… Hamma Aminu.”

Zahra da yanayin Amatullah ɗin ya tabbatar mata da Abdulƙadir ɗin ne ya ƙaraso wajen yasa ta juyawa ta kuma matsa kamar za ta haɗe da bangon wajen, da yanayin fuskarshi ya tabbatar mata da ya ji ta.

“Yaushe Aminun ya zama Hamman ki?”

Abdulƙadir ya faɗi yana tsare su da idanuwa. Alamun motsi ya yi su biyun suka kwasa da gudu, kai ya girgiza murmushi na ƙwace mishi.

‘Jarabu da ƙwai.’

Ya maimaita cikin zuciyarshi wani murmushin mai sauti na ƙwace mishi.

“Sai na ci uban yaran nan Allah…”

Ya yi maganar a fili yana juyawa. Masallaci ya fita abinshi. Sanda ya dawo hanjin shi har naɗewa suke waje ɗaya. Ɗakinshi ya nufa kai tsaye yana tunanin ganin abinci bai ga komai ba, tabbas sai ya zane jikin Zahra. Fita yake shirin yi ya ji an ƙwanƙwasa ƙofar tare da yin sallama cikin sanyin muryar da ya tabbatar mishi da Waheedah ce.

“Shigo”

Ya faɗi. Da ƙafa ta tura ƙofar saboda farantin da yake hannunta, tukunna ta shiga ɗakin. Zahra ta sameta ta ce Commander ya ce ta kai mishi abinci. Hakan ya yi mata daɗi, tun safe take jin ganin shi, ta fito ya fi a ƙirga amma bata ga giccin shi ba, bata son fito da hotunan da ya bata jiya daga inda ta adana su, saboda gidan cike yake da mutane. Farantin ta ajiye mishi a ƙasa tana mayar da hannunta ɗaya baya kamar mai ɓoye wani abu.

“Ina wuni.”

Ta gaishe da shi.

“Lafiya…”

Ya amsata a taƙaice yana jan farantin gabanshi.

“Akwai wainar shinkafa, ban saka maka ba saboda na san baka ci.”

Da mamaki Abdulƙadir ya ɗago yana sauke mata ƙananun idanuwanshi. Baya tunanin ko Hajja ta san baya cin wainar shinkafa, don da bakinshi bai taɓa cewa kowa yana cin abu kaza ko baya ci ba, idan ya je ya duba ya ga ita aka yi ficewa yake ya nemi wani abin daban ya ci. Ganin kallon da yake mata ya sa ta jin zuciyarta na bugawa, tana mamakin yadda idanuwanshi suke birkita mata lissafi, duk k

Ƙanƙantar su.

“Ban taɓa gani ka ci ba, idan ka shigo an yi baka ɗiba kake fita.”

Waheedah ta yi mishi bayani, Idanuwanshi ya ɗauke daga kanta, yana jin jikin shi ya ɗauki ɗumi na daban. Abu ne da bai taɓa tunanin wani ya yi damuwar da zai kula ba. Plate ɗin shinkafa da miya har da latas da ta zubo mishi ya ɗago yana ɗora shi kan cinyar shi, yadda yake motsa abincin a nutse take bi da kallo, kafin ya ɗiba abincin yana fara kaiwa bakinshi. Idanuwanta Waheedah ta ɗauke daga kanshi, tana ɗan sa hannu ta dafe ƙirjinta da yake dukan uku-uku. Passport ɗinta ne da ta gama bincika duk wasu da take da su ta ɗauko wanda ta yi tunanin ta yi kyau a ciki ta ke riƙe da shi a hannunta.

Tun jiya da tunanin ta bashi ya zo mata zuciyarta take dukan uku-uku da tunanin abinda zai iya biyo baya. Ta san babban cikin su ba zai wuce ta sha mari ya ce ta raina shi ba, amma son ya tafi da wani abu da nata ne ya fi ƙarfin duk wani tunani da take yi, yadda ya bar mata wani abu nashi duk da ko bai yi ba ta san zai kasance manne a zuciyarta har ya dawo, haka take so ko yaya ne ita ma ya tuna da ita, ta gama tattaro karfin gwiwarta amma ganin shin da ta yi ya tuna mata yadda a ƙasan komai  akwai tsoronshi a shimfiɗe. Kalle-kalle take cikin ɗakin, a drawer ɗin gefen gadon ta hango wallet ɗinshi, ƙarasawa ta yi wajen tana zama.

Sai lokacin Abdulƙadir ya ɗauke idanuwanshi daga kan abincin da yake ci ya kalleta, ganin wallet ɗinshi ya yi a hannunta ta buɗe.

“Kin ban ajiya ne?”

Ya buƙata yana tsareta da idanuwa, tunda ta shigo yake tunanin ta ƙara haske, sai lokacin ya kula da lace ɗinta farine da ratsin ja ko stones ɗin jiki ne ja ba zai tantance ba, shi ya ƙara fito da haskenta da ya yi mishi yawa a ido. Kai Waheedah ta girgiza mishi zuciyarta take ji ta dawo wuyanta, idanuwanshi ya ɗauke daga kanta yana ci gaba da cin abincinshi, hakan ya bata damar saka mishi hoton cikin ƙaramin wajen da za ka iya ajiye hoto tukunna ta ɓalle wallet ɗin tana ajiye mishi inda ta ganta. Sosai zuciyarta take dokawa har wani zazzaɓin faɗuwar gaba take ji a jikinta.

Ga zufa da tafukan hannunta suke yi, miƙewa ta yi.

“Ina za ki je?”

Abdulƙadir ya tambaya, bai jira amsarta ba ya ɗora da,

“Ki jira in gama ki tafi da kwanonin.”

Komawa Waheedah ta yi ta zauna, idanuwanta kafe a ƙasa, shirunta Abdulƙadir ya ji ya mishi yawa, hakan yasa shi kallonta, kanta a ƙasa yake.

“Waheedah?”

Ya kira cike da alamun tambaya, ta ɗago tana sauke mishi manyan idanuwanta da yake da yaƙinin za a iya cire huɗun nashi a ciki har a samu ragowa, har mamakin yanda za a ce idanuwan mutum ne da wannan girman yake, yana son ganin tsoronshi cikin su saboda girman da sukan ƙara yi mishi.

“Lafiyar ki?”

Ya tambaya, tambayar shi kanshi tana ba shi mamaki, haka kawai yana son jin tana lafiya, da bata mishi surutunta yau. Kai Waheedah ta iya ɗaga mishi, yadda ya kira sunanta na sa har lokacin zuciyarta dokawa take har cikin kunnuwanta. Numfashi ya sauke, ita kaɗai take amsa mishi magana haka, surutun nata yake son ji, tana amsa mishi magana da kai. Abincin shi ya ƙarasa ci yana cire robar ruwan daga kan farantin ya ɗago da shi ya miƙa wa Waheedah da ta miƙe tsaye, gara ta fita, kanshi yake jin ya mishi nauyi yau ɗin nan, Nuriyya ta ƙi ficewa daga cikin shi, ba zai ƙara da tunanin ko lafiyar Waheedah ƙalau shi yasa take mishi shiru-shiru ba.

*****

Tsaye yake jikin motar Abba yana jiran wanda zai kai ɗin su fito, an ce mishi sharaɗa ne, ya gane ta wajen don akwai abokinshi a gurin unguwar. Waheedah ya hango tana takowa inda yake, tafiyarta yake kallo kamar bata son taka ƙasar da kyau kar ta tsage ta rufta da ita. Hijab ne mai hannuwa a jikinta har ƙasa. Yana son hijab, don matar shi ba za ta saka mayafi ta fita wani ƙaton banza na kallonta ba, kwalliyarta a cikin gida za ta yi iya idanuwan shi. Kalar hijab ɗin ruwan ƙasa mai cizawa, a ranshi yake tunanin ko Waheedah bata san tana da haske bane, duk kayan da za ta sa ƙara mata haske suke suna saka ta shigar mishi ido. Yana son mace mai duhu.

‘Kamar Nuriyya.’

Wata murya cikin kanshi ta furta mishi tana saka shi sauke numfashi, duk da ba ƙarya ta faɗi ba, yanayin kalar Nuriyya haka yake son macen shi ta kasance.

‘Har yanayin jikinta da komai nata.’

Muryar ta sake faɗa mishi tana saka shi girgiza kai, kamar yana son faɗa mata kar ta yi musu haka shi da ita, kar ta ja musu raini. Ƙarasowa Waheedah ta yi tana faɗin,

‘Hamma baka shirya ba, yanzun fa za’a tafi, dangin su angon har sun zo.”

Sosai ya ji daɗin saukar muryarta da ta katse mishi tunanin da yake da yake da tabbacin babu abinda zai ja mishi sai rainin da ya fi tsana a rayuwar shi. Kafin maganganun Waheedah ɗin su zauna mishi suna saka shi kallonta cike da rashin fahimta.

“Wanne irin shiri?”

Ɗan kallonshi Waheedah ta yi tana rausayar dakai, ta ganshi da wando iya gwiwa sai riga blue mai haske da ta yi mishi kyau na ban mamaki a idanuwanta, amma duka cikin abokan angon da suka zo da motocin da kuma ‘yan gidan nasu da za su taya hidimar ɗaukar amaryar manyan kaya ne a jikin su.

“Baka sa kaya ba.”

Ta faɗi, tana saka shi ƙanƙance mata idanuwanshi. Haka Yassar ya yi mishi maganar sake kaya da zai fito, itama ta zo tana mishi yanzun.

“Tsirara kika gan ni? Me ya sami kayan da suke jikina? Me yasa bazan je da wannan ɗin ba? Su ba kaya bane?”

Kallonshi Waheedah take yadda ya ƙanƙance ido yana mata masifa kamar jiranta yake yi dama, ita ba da tunanin komai tai mishi magana ba, idanuwanta ta ji sun cika da hawaye. Ba tare da tunanin komai ba ta sake cewa,

“Allah ya ba ka haƙuri…”

Wani murmushi Abdulƙadir ya yi mai sautin da ke fassara ya kasa yarda shi Waheedah ta ce ea ‘Allah ya ba ka haƙuri’. Duk da bai ji raini a muryarta ba, baƙar magana ce ta faɗa mishi saboda yana magana mai tsayi da ita.

“Baƙar magana za ki faɗa min? Saboda kin ga haƙorina? Maganar da nake da ke ta sa za ki fara rainani ko?”

Hawayen da take tarbewa ne suke zubowa, yana ƙara harzuƙa Abdulƙadir ɗin saboda baya son kuka marar dalili, idan za ka saka shi a gaba kana mishi kuka gara ya tabbatar ya baka dalili me ƙarfi na yin kukan.

“Me na yi miki?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi, hawayenta na sake zuba, faɗanshi take ji har ƙasan zuciyarta, inda ta san zai mata faɗan ba zata soma mishi maganar kayan da ya sa ba.

“Raini ne yasa kike min kuka?”

Abdulƙadir ya sake tambaya yana tsareta da ƙananun idanuwanshi. Kafin ya ja tsaki yana wucewa ya nufi ɓangarensu, kayan da Yassar ɗin ya fito mishi da shi don ya saka ya ƙi ya ɗauka tare  da jan wani ƙaramin tsakin, don bai san dalilin da yasa shi yake sake kayan jikin shin ba, tunda bai ga abinda suka yi ba. Ko motsi Waheedah bata yi ba daga inda ya barta, hannu take sakawa tana share ƙwallar da ta ƙi daina zubar mata har lokacin, fuskarta ta yi wani irin ja, abinka da farar fata. Anan Nuriyya da tun jiya da suka dawo ta kwanta ba tare da ta ce mata komai ba ta sameta.

Tunda aka fara hidimar a gidansu Waheedah ɗin take kwana, duk da ko babu hidima tana kwana wasu lokutan, kusan rabi da kwata na rayuwarta tare da su take yinta a gidan. Yau da safe da ta tashi ma bata kula Waheedah ɗin ba, saboda haushinta take ji, haushin kowa da komai take ji, da ta isheta ce mata ta yi kanta ke mata ciwo, harda bata paracetamol ɗin rainin hankali.

“Ke kuma lafiya? Me aka yi miki?”

Nuriyyan ta tambaya tana taɓe baki, hannu Waheedah tasa tana share ƙwallarta, muryarta a dishe ta ce,

“Hamma Abdulƙadir ne ya sauke min faɗan shi.”

Dariya Nuriyya ta yi saboda har ranta ta ji daɗi, Abdulƙadir ɗin ya tabbatar mata da Waheedah kamar kowa ce a wajen shi, babu wani special treatment da take samu.

“Abin dariya ya baki ko?”

Waheedah take faɗi tana hararar Nuriyyan da ta sake yin wata dariya tana riƙo Waheedah ɗin tare da dora kanta kan kafaɗar Waheedar.

“Sorry ƙawata. Halin Hamma wanne ne baki sani ba?”

Jinjina kai Waheedah ta yi, ta san shi fiye da zaton kowa, faɗan shi ne ba za ta taɓa sabawa da shi ba, duk yadda take da tsoron duka gara ya daketa da ya yi mata faɗan shin nan mai tsaya mata a rai.

“Na sani Nuriyya, bana son faɗan shi ne kawai.”

Taɓe baki Nuriyya ta yi.

“Ni dai mu je…”

Ta ƙarasa tana kama hannun Waheedah ɗin don su samu mota, cikin abokan angon wani ya leƙo kai yana wa Nuriyya murmushi.

“Ya za ku wuce direban naku?”

Ya faɗi yana ɗan daga mata gira, dariya Nuriyya ta yi ganin bai ko kalli inda Waheedah take ba. Murfin motar za ta buɗe don ta shiga, kamar daga sama ta ji an ce,

“Ina za ki je?”

Juyawa ta yi zuciyar ta na dawowa maƙoshinta, ƙamshin turaren shi na cika mata hanci, shaddar jikin shi ta yi matuƙar amsar shi, jikinta har wani ɓari yake, kafin ta kula da idanuwan shi tsaye suke kan Waheedah. Wani tuƙuƙi ta ji ya taso daga ɗan yatsan ƙafarta yana samun wajen zama a maƙoshinta. Yana fitowa bai ganta wajen motar ba, hijabinta ya hango, ranshi a ɓace yake har lokacin, bai ma san wa ya ce ta bar wajen ba.

“Na ce ki bar wajen ne?”

Ya tambaya, kai Waheedah ta girgiza mishi, kalar faɗan da yake ji yau na bata mamaki, tunda dama ba shi ya kirata ba, ita ta same shi a wajen, yadda ya kafeta da ido ya sa ta wucewa ta gaban shi kamar ƙwai ya fashe mata. Wani kallo ya watsa mata mukullin motar da ke hannun shi na suɓucewa ya faɗi, kafin ya yunƙura Nuriyya ta tsugunna ta ɗauko mishi tana sauke idanuwanta cikin nashi, wani irin abu na tsirga mishi da yasa gashin da ke bayan wuyan shi miƙewa. Hannu ya miƙa mata ta saka mishi mukullin a ciki. Yana duk wani ƙoƙari da zai iya kar ya riƙe hannunta ya jujjuya shi ya ga ƙunshinta dakyau.

Idan akwai abinda yake ƙara burgeshi bai wuce ƙunshi ba, ko bai san yarinya ba ya ga hannuwanta ɗauke da ƙunshi sai ya sake kallo, musamman na Nuriyyan da yake baƙi da ja. Gashi ‘yan yatsun nata jan lallen ya kama. Wani abu ya haɗiye  da ƙyar yana tsintar kan shi da faɗin,

“Wa ya yi miki ƙunshi?”

Murmushi Nuriyya ta yi saboda shi ne karo na farko da ya yi mata wata magana da ba amsa gaisuwa bace, banda jiya da yace ta rufe mishi ƙofa.

“Wata mata ce.”

Ta amsa tana saka shi ware ƙananun idanuwanshi da ya tabbatar a waje ya yi maganar, kai ya ɗan ɗaga mata yana juyawa. Takun tafiyar da yake ji ya tabbatar mishi da Nuriyyan na biye da shi. Zuciyar shi dokawa take sosai, ga tsikar jikinshi da yake ji tana miƙewa, baya so ya juya ya sake faɗin wata maganar da bai yi niyya ba, shi yasa ya ƙyale ta. A tsaye wajen motar ya samu Waheedah. Zagayawa ya yi ya buɗe motar ya shiga, wannan karon bai ce ma Waheedah ta shigo ba, da kanta ta buɗe ƙofar ta shiga. Bata kula da hararar da Nuriyya ta watsa mata ba, don ita ta so ta shiga gaban motar.

Babu yadda za ta yi haka ta buɗe bayan ta shiga, duk da gabanta na faɗuwa kar ya koreta, bai ce mata komai ba, zuciyarta har wani tsallen murna take, murmushi ya ƙi barin fuskarta har lokacin. Ɗan tashi Abdulƙadir ya yi yana saka hannunshi a aljihu ya ciro links ɗin da ke cikin aljihun tukunna ya zauna. Waheedah ya miƙa wa links ɗin, bata ce komai ba ta karɓa tana gyara zamanta don ta saka mishi a hannun da ya miƙo mata ɗin. Cikin yanayin da yasa murmushin da Nuriyya take ya ɓace ɓat daga fuskarta, kallon su take yi har Waheedah ɗin ta ɗaura mishi link ɗin, ya janye yana miƙa mata ɗayan hannun nashi, saka mishi ta yi tukunna ta gyara zamanta ba tare da ta ce komai ba.

‘links ne kawai, kema don ba zai yiwu ya baki bane kisa mishi shi yasa ya bata.’

Nuriyya take faɗa wa kanta duk da wata murya na gaya mata,

‘Ita ma ɗin ai ba ƙanwarshi bace, babu abinda ta haɗa da shi, agolar gidan su ce.’

A karo na farko da ta ji dama Waheedah ta zo a ƙanwar Abdulƙadir ɗin da hakan zai fi mata, saboda babu wani chance na soyayya a tsakanin su. Ƙirjinta take jin yana mata zafi da abinda take jin kishi ne na fitar hankali, tasan Abdulƙadir ya mata nisan da ba zai misaltu ba, shi yasa duk kyan da yake mata, da yadda yake sak da zaɓin mijin da take burin samu bata taɓa ɗaga burinta akan shi ba. Haka take so ya yi ma Waheedah nisa, ko kaɗan bata son wani kusanci da ya banbanta da wanda yake nunawa tsakanin shi da kowa. Idan ba za ta same shi ba, Waheedah ɗin ma ba za ta same shi ba.

Abdulƙadir kuwa kokawa yake da yadda komai na jikinshi yake son juyawa ya sake kallon Nuriyyan, kafin ƙanwar Abba ta buɗe motar ta shigo tana faɗin,

“Abdulƙadir…”

Damar ya yi amfani da ita ya juyo.

“Anty… Ina wuni.”

Ɗan ware idanuwa Anty Maryama ta yi, duk da ta ga Abdulƙadir ɗin ya girma, tana tunanin hankali ne ya zo mishi har yau take samun arziƙin gaisuwa.

“Lallai Abdulƙadir an girma…”

Ta faɗi tana saka shi daƙuna fuskar shi. Irin abinda ba ya so kenan, sai ka gaishe da mata sai ta dinga nuna maka kamar an haifeka a gabanta, ko Hajja da ta haifeshi ba ya so tana ce mishi yaro a gaban ƙannen shi. Nuriyya ya ɗan kalla yana sata sauke idanuwanta daga kanshi babu shiri. Juyawa ya yi yana gyara zaman shi. Anty Hafsatu ce ta shigo itama yana jin motar ta yi ƙasa saboda nauyin da suka yi mata. Tayar da motar Abdulƙadir ya yi.

“Ka tsaya Hajiya Hassana ta ƙaraso, gata can ta taho.”

Anty Hafsatu ta faɗi tana sa Abdulƙadir faɗin,

“In ba saman motar za ta shiga ba nan dai ai ya cika.”

Abdulƙadir ya ce yana yin baya da motar, ganin da gaske tafiyar zai yi ya sa Anty Hafsatu rufo murfin motar.

“Mutum nawa suke zama a baya? Ka jira ta zo Abdulƙadir.”

Daƙuna fuska ya yi yana faɗin,

“Gaskiya ta shiga wata motar. Ba ki ji yadda motar ta yi ƙasa ba da kika shigo… Inba so kike muna tafiya muna gurzar titi ba.”

Buɗe baki Anty Hafsatu ta yi cike da mamaki.

“Ka ci uwaka Abdulƙadir, kana jina!”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ɗin ya yi, yana shirin yin magana Waheedah ta ce,

“Hamma…”

Yadda ta yi maganar cike da roƙo yasa shi harararta cike da alƙawarin sauke mata wata masifar. Bata damu ba indai zai yi shiru, bata so su Anty Hafsatu su ce ya musu rashin kunya, kuma ta san idan maganar ta yi tsayi ba a iya rashin kunya zai tsaya ba, Abdulƙadir zai iya fita ya bar su a motar ko su su fita subar shi a ciki. Bata son hakan ya faru, Nuriyya dake gefe tana kallon su ta taɓe baki.

‘Allah ya miki baƙin shisshigi.’

Ta faɗi a ranta, koma menene ɗin bata ga matsalar Waheedah ba tunda dai su Anty Hafsatun jinin shi ne, ita kuma bare ce, amma ji yadda ta yi mishi magana kamar tana da wani muhimmanci a wajen shi. Tun su Anty Hafsat suna mita har suka yi shiru, saboda radio ɗin da Abdulƙadir ya kunna ya ƙure maganar, basu ce ya kashe ba, tunda babu wanda in har yana zuwa gidan bai san halin Abdulƙadir ba. A haka suka isa gidan Adda Khadija ɗin, da duk da ba babba bane yanayin ginin ya yi wa Abdulƙadir kyau. A cikin motar ya zauna bayan ya faɗa ma Waheedah inta shiga cikin gidan ta ce ma su Zahra su fito su tafi.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×