Skip to content
Part 10 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Cike da mamaki Mk ke kallon Buhari da ke zaune a gefen katifa, bayan da su Cinnaka suka tura shi dakin suka daure shi, sannan suka kwance mishi daurin da ke kan fuskar shi.

“why you are here!”

” because of you”

“Why me?”

“I don’t know” Buhari ya amsa, Sai kuma ya tuntsire da dariya tare da fadin “Green pepper!” Shi ne sunan tsokanan da suke kiran Mk da shi, a lokacin da suke lodge daya

Mk ya ɓata rai, saboda yanzu ba lokacin wasa ba ne ko tsokana, hankalinshi baya jikinshi, mahaifinshi yake tunani, saboda ya san sai ya fi kowa damuwa da rashin dawowarshi.” Mtswww!” ya ja dogon tsoki yana kallon Buhari “Tun yaushe kake a nan?”

“Almost 2wks.”

Ido Mk ya fitar waje alamun mamaki yana fadin “And you’re sitting comfortable like this, kamar kana dakin Mamanku”

Cike da taikaci Kb ya yi maganar, kamar zai rufe Buhari da duka.

“To me kake so in yi, in yi taurin kai su harbe ni, kamar yadda suka shaida in? A part from that, Duk saboda waye nake a nan din” cikin fada-fada Buhari ya yi maganar

“Saboda waye?” Mk ya tambaya rai bace

Buhari ya mike hade da daidaita tsawon shi da Mk yana fadin “Ina zaune a wurin nan ne saboda kai, saboda kawai an ga hotona da na ka, zamana wurin nan ya sa na rasa abubuwa da yawa, na jefa mutane da yawa cikin ta hankali, musamman  mahaifiyata. Kuma duk saboda kai , da ace basu same ka ba, kila a nan zan kare rayuwata, idan sun gaji da ajiyata su kashe ni . But thank God you’re here, now I’m safe”

“Me ya sa suke nema na?” Cewar Mk cikin sanyin murya

“Who know” In ji Buhari lokaci daya kuma ya zauna gefen katifar ranshi na zafi.

Sai yanzu yake kara jin takaicin tsarewar da aka yi mishi, saboda kawai an ga hotonshi tare da kb, wannan zai zame mishi izna nan gaba, ba shi ba dora hotuna randomly Musamman a social media kamar Facebook.

MK ya zauna kusa da Buhari duk suka yi shiru, kowa da abin da yake tunani.

Turo kofar da aka yi ne ya sanya kb mikewa tsaye, har lokacin da Wizi ya shigo hannunshi dauke da farantin da ya ɗora wasu Mk abincinsu.

Wani irin mugun kallo kb ke aikawa Wizi, har zuwa lokacin da ya aje abincin

“Zo ka kwance ni, I want go home” Cewar Kb lokacin da Wizi ya dago daga aje farantin abincin.

“Ka kwance ni na ce” cikin tsawa Mk ya yi maganar.

Wizi dai komai bai ce ba, Sai ma nufar kofar fita da ya yi

Kb ya taka da ɗan sauri duk da ɗaurewa da aka yi mishi ya jawo wuyan rigar Wizi ta baya hade da fizgo shi.

“Kwance ni na ce ma. Ni ba wawa ba ne da za ku zo ku daure ni a nan ba tare da laifin komai ba, me na yi maku, me kuke nema a wajena? “

Wani naushi Wizi ya kai mishi,  dama a kufule yake da kb saboda wahalar da suka sha kafin samun shi.

Kafin Mk ya dawo hankalinshi Wizi ya fice daga dakin.

Buhari da yake kallon ikon Allah da karfin hali irin na Mk ya yi saurin mikewa ya tallafe shi a kan kirjinshi

After some minute ya dawo cikin hankalinshi yana kallon Buhari ya ce “Ina yake?”

Buhari ya kumshe dariyarshi ba tare da ya ce komai ba.

A kufule Mk ya fara bugun kofa yana fadin a zo a bude shi, shi gida zai tafi.

Ganin babu alamun tahowar wani ya sanya shi juyowa cikin dakin rai bace.

Ya rarumi farantin da aka zubo musu abinnci da niyyar yin fatali da shi, Buhari ya yi caraf ya rike farantin yana fadin “Ban da abinci kam, idan ka zubar da wannan waye zai kawo mana wani, ga mari ga tsinka jaka, ga zaman wuri daya ga kwana da yunwa, bar mu mu ji da abu daya dai.”

Ya saki farantin ya juya kan tv ya fusgota tare da makata da bango, labulayen da ke cikin dakin ma duk ya tsinko su.

Buhari dai kallon ikon Allah kawai yake yi. Har Mk ya gama fashe-fashen shi ya koma kusa da Buhari ya zauna, zuciyarshi na zafi.

Buhari dai abincinshi ya ci hankali kwance ya yi sallah sannan ya haye katifa ya juyawa Kb baya da yake ta kumburi kamar zai aman wuta.

*****

Rumasa’u.

Misalin karfe hudu na yammaci kofar masallacin Alaramma a cike , sakamakon sallahr la’asar da aka fito, ma fi yawan mutanen wurin almajiran makarantarshi ne.

A hankali suka fara watsewa zuwa makaranta musamman da suka ga Alaramma ya fito daga cikin masallacin.

Daga inda yake tsaye ya kwaɗawa Usman kira.

Cikin hanzari Usman ya nufo shi wuyanshi rataye da casbaha lokaci daya kuma yana tauna aswaki.

Daga nesa da Alaramma ya duka cike da girmamawa ya ce “Ga ni.”

“Ba na son yaron nan Aibo ya kara sati daya ba tare da ya dawo nan ba, da shirin shi ko ba shiri.”

Cewar Alaramma cikin bayar da umarni.

Usman ya shiga gyada kai alamun ya ji, ya kuma bi.

Daga haka Alaramman ya wuce, Usman kuma ya mike zuwa makaranta.

Ango Aibo tun bayan da aka lullube Ruma aka kai mishi, wanshekare ya fece, ko sau daya basu hadu da Ruma ba.

Ba shi kadai aka nema aka rasa ba, har da Auwalu, tun bayan da suka fahimci Aibo  ya koma wajen neman kudin shi, babu wanda ya kara bi ta kanshi, Sai yanzu da ya cika wata uku yana kokarin shiga na hadu sannan Alaramma ya waiwaye shi.

Ita dai Ruma ko sau daya ba ta taba jin ta damu da rashin ganin Angon nata ba, rayuwarta take yi cikin jin dadi.

Ga kayan gararta, manja Mangyada, manshanu, taliya, fulawa, buhun masara buhun shinkafa, ga dakakken yaji na daddawa da na cin ɗanwake.

Abin da ta ga dama shi take kwaɓawa ta ci.

Yau wainar fulawa, gobe shasshaka, jibi ɗanmalele, kullum dai abun kwadayi take yi, ba ta rasa kudi, kullum sai Alaramma ya aiko mata da dari biyar na cefe ne.

Da kudin take amfani a turo mata video a wayarta (no kira) babu Sim a ciki sai memory Ya Usman ne ya ba ta, da yake sauran duk mazajensu sun siya musu.

Shi ya sa a cikin watanni ukun ta yi yar ƙiba abun ta, iyakacinta kawai ta ci ta kwanta, kannenta su shigo su yi tsallen-tsallensu kafin lokacin makaranta.

Ranar da ba makarantar dare kuma, ta kunna musu kallo a waya har zuwa lokacin da bacci zai daukesu.

Rayuwarta dai take yi mai dadi hade da kwanciyar hankali.

Da ace Alaramma ya yi shawara da ita da bai sa an yi wa Aibo kiranye  ba.

Sai dai kwana biyu bayan da Alaramma ya sanya Usman yin aiki a kan Aibo, cikin dare Ruma na kwance a tsakar  gida ta daura net saboda zafi, cikin baccinta ta ji abu ya fado tsakar gidan jib.

A firgice ta bude ido, ta yi arba da duhu-duhun mutum.

Ba ta san lokacin da  fit ta fito daga cikin net din ba hade da fasa kara, ta nufi kofar fita waje a guje.

Cikin hanzari Aibo ya cafkota tare da fadin “Gidan ubanwa za ki je? Namijin baƙonki ne? ba Allah kadai ya san ko maza nawa suka tsallaka ki ba, ƴar iska munafuka, za ki wani fasawa mutane ihu, me ye ba ki sani a wurin namijin ba?”

Ruma dai kafe shi da ido ta yi jikinta na rawa.

Ya saki damtsen hannunta da ke rike a cikin hannunshi yana fadin” Wa ma ya san ko maza nawa ki kawo a gidan da ba ni nan, ni dai ai an cuce ni, kuma Allah Ya isa” ya kai karshen maganar hade da nufar kofar ɗaki.

A hankali ta sauke ajiyar zuciya tare da bin bayanshi da kallo, duk da ba  wani fahimtar maganganunshi ta yi duka ba, ta san dai baƙar magana ya fada mata ko ma baƙaƙe.

“Me ye baƙonki a wurin namiji, me ye ba ki sani ba”

Ta ƙara maimaita maganarshi, a cikin zuciyarta, lokaci ta dauka tana nazarinta, amma Sam ba ta gano me yake nufi ba. Yar iska da ya ce mata kadai ya fi mata ciwo, saboda har kwalla ta zubar.

Aibo kam bayan ya shiga dakin tsaye ya yi a tsakiyar dakin yana karewa ko ina kallo.

Dakin ciki daya ne kato, a shafe shi da siminti lukui, ya sha bugun kwano sai dai ba Celine .

Funitures masu kyau, gado 6 by 7,sif me biyu, kujeru guda biyar, sosai dakin ya yi kyau, duk da ba wani fadin tsakar daki, bai wuce a shimfida tabarma guda daya ba.

Ya jefar da ledar hannunshi a kan kujera ya fada kan gadon wanda ya sha gyara da zanen gado mai laushi.

Ya kara mimmikewa sosai, yana jin da wayonshi dai yau ya san ya hau gado mai kyau kamar wannan, tun yana yaro a kan tabarma yake kwana saboda fitsari, lokacin da ya fara girma aka kawo shi makarantar allo, daga nan ya wuce neman kudi, a can wurin neman kudin  ma a kan tamfal suke kwana.

Ai bai jima da kwanciya ba, bacci ya dauke shi.

Yayin da Ruma ta koma cikin net dinta ta kwanta ranta a jagule.

*****

Juma’a 11:00 am

HAFSAT

Tsugunne take a turken awaki tana ba wata jaririyar akuya nono, wacce uwar ba ta shayar da ita sai an rike ta. Tun da Inna ta Kwanta ciwo kula da dabbobin suka dawo kanta, kuma tana jin dadin hakan, musamman yadda suka saba da ita.

Daga inda take tsugunnen ta rika jin kakarin Inna tana kuma kwada mata kira

Da sauri ta saki akuyar ta kwasa da gudu, wurin sauri har tana ball da Danladi wanda ke zaune a kasan bishiya yana cin abinci.

Tana isa dakin ta iske Inna a tsakiyar dakin tana aman jini

A matukar firgice ta mamutseta tana fadin “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Inna! Kin ci wani abun ne?”

Ta shiga girgiza kai a wahalce, saboda yunkurin aman da ta yi, duk ya jigatata. ta ce “Ban ci komai ba, samo min ruwa.”

Da sauri ta sake ta hade debo mata ruwan ta mika mata, ta kuskure baki sannan ta sha wani.

Hafsat kuma ta shiga gyara wurin, tana tsaka da gyara wurin Inna ta kuma cewa “Hafsa kai ni waje, wani aman nake ji, kar in bata dakin nan, kin ji sai karni yake yi”

Da sauri ta saki abin da take yi, ta kama ta zuwa waje, a hankali suke tafiya har suka isa wajen garken awaki, Inna ta duka a wajen ta shiga kwarara wani aman, har da gulama-gulaman jini.

Hafsat da ta gama rudewa cike da rashin sanin abun yi ta koma gefe ta dora hannu a kai ta shiga rera kuka, irin kukan nan mai nuna tsananin tashin hankalin da mai shi yake ciki.

Bayan ta gama aman, da kanta ta dauki butar da Hafsat ta ciko da ruwa ta wanke bakinta, sannan ta kwanta daga gefen inda ta yi aman tana mayar da numfashi a hankali.

Idanunta da suke lumshe ta bude hade da zuba su a kan Hafsat wacce ke tsaye tsakiyar gida ta yi gwaɓe-gwabe da hawaye.

Da kyar ta daga hannu ta yafito Hafsat din, Sai a lokacin ta samu kwarin gwiwar takowa inda Inna take, ta duka saitin fuskarta tana kuka.

“Ki daina kuka, addu’a za ki yi min kin ji” cewar Inna a hankali, tana mayar da numfashi.

Hafsat dai kukanta kawai take sha.

“Ki daina kuka na ce” Inna ta kuma fada cikin sigar lallashi tana daukewa Hafsat hawayen da basu nuna alamar tsayawa.

Ta shiga yunkurin wani aman daga kwancen da take, a wahalce ta rika yin shi, lamarin da ya kara tayar da hankalin Hafsat, ta dago ta zuwa jikinta, cikin kuka take fadin “Inna! Inna!! Sannu, kodai kin ci wani abun ne kin manta?”

Duk abin da ke faruwa matan gidan da ragowar yaran suna tsaye cirko-cirko suna kallo.

Da alama Inna ta yi nisa da hankalinta, wannan ya sa Hafsat kwantar da ita a wurin ta yi kofar dakinsu a guje ta dakko hajabi, ta yi hanyar kofar fita gidan a kidime, a kan hanya ta karasa sanya hijabin.

Kamar mahaukaciya haka ta shiga kasuwa neman mashin ko mota, ga jikinta duk jinin aman Inna.

Duk mai mashin din da tara ta ce ya zo ya kai Innarta asibiti sai ya nuna ba zai je ba, wani kai tsaye yake fada mata, wani kuma sai ya dan waske mata ya ce ba mai, ko mashin din ya lalace. Wani ko fuskar shi kadai ke labarta mata abin da ke cikin ranshi

Ganin kamar tana bata lokacinta ne, ya sanyata juyawa shago Nasir, shi kadai ta san zai taimaka mata, fatan Allah Ya sa yana nan bai tafi wurin aiki ba.

Sai dai abin da ta zata din shi ta taras, shagon Nasir a rufe ta kuma san yana wurin aiki.

Cike da rashin sanin abun yi ta kama karfen barandar shagon ta rungume, tashiga rera kuka mai ban tausayi.

Su biyu ne kawai zasu iya taimaka mata, Nasir da Uncle Najib, kuma duk basu nan, saboda Uncle Najib jiya Alhamis ya tafi gida weekend.

Ta saki karfen a hankali ta nufi hanyar gida tafiya take salo-salo, tana jan ɗankwalinta a kasa, wanda ya jike jagab da hawaye gami da majina.

yanzu kam ba kuka take yi ba, wata irin suya zuciyarta take yi, wani irin kunci da ɓacin rai take ji.

Yau kam ji take ina ma zargin da mutane suke yi a kansu gaskiya ne, da duk sai ta lashe mutane garin nan kaf babu wanda za ta bari.

Ba ta san tsanar da suke musu ta kai haka ba, mahaifiyarta rai a hannun Allah, a rasa wanda zai kai ta asibiti. Wane irin rashin imani ne wannan.

Da wannan tunanin ta shiga gida, yadda ta bar mutanen gidan haka ta taras dasu.

Sai dai a yanzu akwai mahaifinta wanda ya yi tsaye a kan Inna da take kwance a inda ta bar ta.

Tun da ta shigo suka zuba mata ido har da mahaifin nata, ta karaso inda Inna take kwance, ta duka hade da sanya ɗankwalinta tana share mata jinin da ke gefen bakinta da kuma hancinta

“Ta fa rasu!” ta ji muryar mahaifinta ya ratsa dodon kunnenta.

Ta yi saurin dauke hannunta daga kan fuskar Inna tana kallon mahaifinta, wanda shi ma ita yake kallo.

“Allah Ya yi mata cikawa Hindatu lokaci ya yi.” ya kara jaddadawa Hafsat wacce ta saki baki, tana kallon mahaifin nata.

A ranar ne ta fahimci kukama rahama ne, sannan ƙarami abu ake wa kuka, babban abu sai dai a yi shiru zuciya ta rika suya.

Saboda can jikin katangar ta koma tazauna hade da jingina bayanta, tana kallon yadda mutane ke shiga, suke kuma fita a cikin gidan.

Daga bisani ma sai kawai ta zame ta kwanta a kasa. Tana kallon lokacin da Mahaifinta ya kama gawar Inna zuwa dakinta.

Daga nan kuma ba ta san ma abin da ake yi ba duk da idanunta a bude suke.

Jin an kama mata hannu ana kokarin tashinta ne ya sanya ta dagowa tana kallon mai daga tan.

Wata makociyarsu ce, cike da tausaya ta ce “Sannu Hafsat kin ji, tabbas ke aka yi wa mutuwa. Allah Ya jikan Hindatu, Ya gafarta mata, Ya saka mata zaluncin da aka yi mata, yau dai ta tafi ta bar duniyar, Sai kuma a bi wani sarkin”

Hafsat dai bin ta take yi salo-salo har ta shigar da ita dakin Inna Kuluwa.

Sai a lokacin ne Hafsat ta ga gidan damkam da mata, abin da ba taɓa tsammani ba.

Ta kasa gane murna suka zo ko jaje, lokacin da Inna na fama da ciwo ko sannu babu wanda ya taba zuwa ya yi mata, Sai yanzu bayan ba ta za su zo su wani cika gida don munafurci.

Har aka yi wa Inna wanka aka haɗata tana ɗakin Inna Kuluwa wacce ta ga ta yi mugun la’asar, Inna Luba kam har da kuka.

Tana daga cikin dakin taga an fito da gawar Inna cikin makara ta rika bin gawar da kallo har ta bacewa ganinta, daga nan dai ba ta san me ya faru ba. Sai dai ta farka ta ganta kwance a kan gadon Inna, gidan wayam sai su Inna Kuluwa da wasu ƴan’uwan Inna, wadanda ko duba ta basu zo sun yi ba, Sai yanzu take ganinsu.

Babu wanda ya lura da farkawarta, shi ya sa ta lumshe ido tana sauraron hirar su

Inna Huraira ce ta ce “Hindu kam an dace, Allah Ya jikanta, an ce mutanen da suka halarci sallahr gawarta da wadanda suka rakata sun fi dubu biyu, kaf masallacin izala da darikar nan aka hadu aka yi mata sallah”

“Allahu Akabar!” cewar Inna Murja cike da jimami kafin ta dora

“Allah sarki Hindatu, mace mai hak’uri da son zumunci ga kyauta, Allah ka yafe mana abin da mu ka yi. Kai! Kai!! Kai!!! Hindatu ki yafe mana kin ji”

Baba Rakiya ta karɓe “Gaskiya Yaya Hinde kam akwai hak’uri, ga aikatawa zumunci, shi ya sa aka ce ta yi aman jini kafin ta cika, an ce idan mamaci ya yi aman jini ya amayar da bakin cikin da ya kunsa a duniya “

“Allahu Akabar!!!”

Suka hada baki gabadaya.

Kafin Inna Tabawa ta ce “an ko fadawa Halima can Dawuri”

“Malam ya ce ba shi da lambarta, amma dazu da aka fito masallacin la’asar ya ce zai fita ya nemo, ban sani ba ko ya samu” Karon farko da Inna Kuluwa ta sanya baki

“Gaskiya ya kamata ta ji, uwa daya uba daya ta fi karfin wasa” Inna Tabawa ta kuma fada.

Goggo Rahane ta ce “Aiko a wurin Ashiru ba za a rasa ba, idan bai samu ba, Sai a tambayi Ashirun”

“To kin ji” Cewar Inna Tabawa.

Duk surutun da suke yi Hafsat na jin su, motsin kirki ba ta yi ba, haka ko tari bai kufce mata ba.

Ita ta rasa dalilinsu na zuwa suka cika  daki, ita fa mantawa take dasu a matsayin ƴan’uwan Inna, saboda basu da wani amfani.

Tun daga lokacin da ƙaddarar nan ta fadawa Inna babu mai son raɓarta, ba mai son ya ji an ce ya hada jini da ita, sai yanzu za su zo su cikawa mutane daki da wani shegen surutansu.

Sai yanzu suke fadin alkairinta, Sai yanzu suke fadin hak’urinta, Sai yanzu suka san an zalunce ta, Sai yanzu suka san basu kyauta mata ba.

“Mtswww!” cike da takaici ta ja tsakin da ita kanta ba ta san ya fito ba

Duk sai suka rufu a kanta kowa da abin da yake fada, amma aya ba ta diga musu ba, sakkowa kawai ta yi daga bisa gadon ta yi alwala ta shiga ramuwar sallah.

Sujuddar karshe duk sai ta rasa me ma za ta roka, ta yi shiru cike da tausayin kanta ta dade a haka sannan ta mike zaune, bayan ta sallame ta kwanta a inda ta yi sallahr tana jin shigowar ƴan gaisuwa, da muryoyin masu matsa mata ta ci abinci.

Ita ji take ma kamar ta manta yadda ake tauna abinci, har zuwa lokacin ba ta yi kuka ba, zuciyarta ce kawai ke ta suya, kuma babu wanda zai ce ya ji muryarta ta yi magana. Ji take kamar wasa Inna ta tafi ta bar ta, imagining yadda za ta rayu ba Inna take yi.

“Hafsa yau ba za ki je makarantar ba ne? Hafsa ba za ki ci wannan abinci ba ne? Me kike so ki ci? Tashi ki yi wanka, me kike so da sallah? Mu je kasuwa ki zabi duk abin da kike so?”

Ta shiga tariyo kulawar Inna a kanta, yanzu duk ta rasa wannan kulawar.

Wanda ya yi rayuwa irin tata ne kawai zai iya kintata halin da take ciki, ta runtse ido gam, a kokarinta na samo ruwan hawaye, kila ta, samu saukin suya da kuma nauyin da kirjinta ya yi, amma ko dogo daya ba ta samu ba.

Sai kawai ta ci gaba da rufe idon, tana kuma jin yadda kirjinta ke karta yayin da wani lokaci take bude bakinta don taimaka wa hancinta wajen shaka da kuma fitar da numfashi.

<< Abinda Ka Shuka 9Abinda Ka Shuka 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×