Cike da mamaki Mk ke kallon Buhari da ke zaune a gefen katifa, bayan da su Cinnaka suka tura shi dakin suka daure shi, sannan suka kwance mishi daurin da ke kan fuskar shi.
"why you are here!"
" because of you"
"Why me?"
"I don't know" Buhari ya amsa, Sai kuma ya tuntsire da dariya tare da fadin "Green pepper!" Shi ne sunan tsokanan da suke kiran Mk da shi, a lokacin da suke lodge daya
Mk ya ɓata rai, saboda yanzu ba lokacin wasa ba ne ko tsokana, hankalinshi baya jikinshi, mahaifinshi yake tunani, saboda ya san sai. . .