Skip to content
Part 11 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

HAFSAT

Babu abin da ke ba ta mamaki sai yadda mutane ke ta cin abinci har da hira, wato wanda ya mutu dai ya mutu, wanda kuma aka yi wa mutuwa an yi mishi. Ita yanzu abinci idan ba bude cikinta za a yi a zuba mata ba yaushe za ta cin shi.

Amma su kam durawa kawai suke yi , babu wanda ya damu da ta ci ko ba ta ci ba, an ce dai ta je ta zuba abinci.

Da ace Innarta na nan, hankalinta ba zai kwanta ba sai ta ga ta ci.

Wanda dai aka yi wa mutuwa shi aka yi ma wa, kuma shi ya san zafin da yake ji.

Tana kwance a wurin har mutane suka fara watsewa saboda shigowar dare Inna Tabawa kadai aka bari da Inna Laure a tare da Hafsat.

Sawu na daukewa su ma su ka yi bacci sai Hafsat da a lokacin  garinta ya waye saboda ko alamun bacci ba ta ji. Sai tunani kala-kala da ya cika mata zuciya, wani bangaren ya fada mata kawai ta sha guba ta mutu ta huta, saboda ita dai ba ta san ta yadda za ta fara rayuwa a wannan duniyar ba Inna ba.

Wani bangaren kuma sai nuna mata kuskuren da ke cikin aikata hakan.

Ta rika jin kamar ta gudu, Sai kuma ta tuno dabbobinsu, musamman wadanda ta sabu da su sosai, idan ba ta ya za su yi. Kila yunwa da kishin ruwa ce za ta kashe su, kamar yadda Inna ta tafi ta bar ta cikin kunci, ta san su ma zasu kasance a haka idan babu ita.

Ta mike zaune tana kallon gadon Inna wanda babu kowa a kai. Jiya kamar yanzu tana nan kwance suna bacci, kuma jikinta akwai sauki, saboda sai da suka sha hira ma da dare kafin su ka yi bacci.

“Mutuwa!” ta fada a hankali cike da jimami gami da tausayin kanta.

Tana zaune a wurin har aka kira sallahr farko, a lokacin ne kuma ta ji su Inna Kuluwa sun fito sun hura wuta, da alama koko zasu dama.

Ita dai da kyar ta rarrafa zuwa tsakar gida ta yi alwala, takamaimai ba za ta ce ga abin da ke damunta ba.

Kanta ya yi mata nauyi, ga idanunta bishi-bishi take gani, bakinta kam a bushe kamar babu yawu. Sai kirjinta da take jin kamar an yi mata ajiya.

Misalin karfe takwas na safe tana kwance a kofar daki, kamar daga sama ta ji sallamar Mama Halima.

Ba ta taba jin murya Mama Halima na kama da ta Inna ba sai yau, shi ya sa zumbur ta mike har ta na zubar da kokon da aka aje mata, kai tsaye ta nufi Mama Halima a guje hade da fadawa jikinta, Sai a lokacin kuka ya zo mata.

Mama Halima ta rungume ta tsam a kirjinta tana jin kukanta da yake kara narkar mata da zuciya hade da kara mata tausayinta.

Haka ta jawo ta cikin daki suka zube bakin gadon suka shiga kuka ba mai lallashi wani, Sai mutanen da ke shigowa gaisuwa da yan cikin gida ke ta basu hak’uri.

Cikin kuka Inna Halima ta ce “Ba a kyauta min ba, ace yar’uwata ta yi jinya, ba za a fada min ba, Sai dai a fada min labarin mutuwarta. Ba komai, abin da kuke so kun samu, ta mutu ta bar muku duniyar sai ku yi yadda kuka ga dama. Kuma duk wanda yake da hannu wajen cutawa yar’uwata wlh ban yafe ba, ita ma ba ta yafe ba, Allah Ya isanta”

“Haba Halima, kar ki bata zaman makokin nan mana, Ya kike zan ce irin haka, Hindatu dai kwana ya kare, sai dai mu yi mata addu’a.”cewar Inna Tabawa.

” Dole in fada Inna, ba ma son zaman makokin, kowa ya tafi, mu biyu aka yi wa mutuwa ni da Hafsat, bayan nan kowa murna yake ya rabu da ƙaya. Wlh duk wanda ya ɓata sunan ƴaruwata zuwa mayya Allah Ya hana mi shi jin dadin duniya da lahira. Allah ya isanmu”

“Halima ba dai za ki yi shirun ba kenan? To ki ci gaba don ubanki, tun da abun da ya kawo ki kenan” Cewar Inna Huraira da ta zo gidan da safe

“Ai dama ni ina da wannan ƙududun a raina, Hindatu ke hana ni magana, yau kuma tun da kasa ta rufe idonta a shirye nake in tsiyaye duk abin da yake damuna. Ƴan iska munafukai mahassada, In Sha Allahu abin kuke nema ba za ku samu ba”

“Wai tsaya Halima, duk da wa kike wannan maganar nan ne?” Inna Kulawa ta fada lokacin da ta fito daga cikin dakin ta. Saboda ita gabas ce ba ta juri zuga ba

“Da wanda ya tsargu, idan kin tsargu da ke nake kuluwa, bari in fito mu daku…”

Cewar Inna Halima hade da mikewa ta yi waje zuwa tsakar gidan.

“Ikon Allah! Halima kina cikin hankalinki kuwa, yau na ga yar banzar yarinya, wai ke ba mutuwa aka yi miki ba, daga zuwa ko numfashi ba za ki mayar ba, za ki fara bala’i” cewar Innar Laure lokacin da take fita tsakar gidan.

Daga can waje kuma Inna Kuluwa ta ce “A kan me zamu daku? Ki ji ma da baƙin cikin da ke damun ki, kuma ai idan ka ga sanda akwai labarin duka, duk abin da ka ji ana fada a gari to akwai alamunshi”

“Eh mana, tun da Kune kuka tsugunna kuka haifi maita kuka, dorawa yar’uwata don kawai ku samu damar bata ta ga mutane, to burinku ya cika, daga, karshe ma ta mutu ta bar muku duniyar kuka kuma ku ci uwarku da ubanku a cikinta” Cikin kuka Mama Halima ta karasa maganar

Yayin da mutane ke ta ba ta hak’uri hade da janye ta zuwa cikin daki, can kuma tsakar gida su Inna Kuluwa na ta kokarin kare kansu.

A cikin wannan ruguntsuminne aka aiko kiran Hafsat, wacce ke tsaye a tsakar gida tana kallo da kuma jin Ikon Allah.

Ko ba komai ta ji dadin yadda Mama Halima ta wanke su Inna kuluwa da sauran mutanen gari ta zage mata su tatas, ba tun yanzu take son ta daga murya ta zage su ba, Sai dai babu damar yin hakan, yau kam da Mama Halima ta yi musu wankin babban bargo sai take jin wani kaso na nauyin da kirjinta ya yi mata ya ragu, hatta ciwon kan da take ji yanzu sai ta ji ya yi sauki.

Daga haka ta nufi kofar gida, wani bangare na zuciyarta fes.

*****

Asma’u

Ba yau ne Hajiya ta fara cewa ta rakata unguwa ba, amma ta yau din kada mata gaba take yi.

Kodayake tun daga ranar da tabbatar mata kanta tana dauke da ciki, gabanta bai kara zama daidai ba, kullum cikin faduwa yake

Musamman idan ta ga kiran Ahmad ya shigo mata, Sai ta ji kamar kirjinta zai faso rigarta ya fito.

Wani abu da yake ba ta mamaki shi ne, Ahmad bai taba yi mata maganar ciki ba, ya san da shi bai san da shi ba, oho ita dai ba ta sani ba

Idan ya ji ya yi shiru, me ya sa ya yi shirun, ko jira yake sai ya dawo a turke ta.

“Tabbbb!” ta fada da hanzari, lokaci daya tana tuna irin kunyar da za ta sha, ba za ta bari a kai wannan lokacin ba, dole ta nemi mafita, amma ba za ta iya daga kai ta kalli Ahlin Ahmad ba, a lokacin da ake mata titsiye wai tana dauke da cikin shege

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!” ta fada a hankali.

Tausayin Ahmad take ji, bawan Allah, yana can yana fama, rayuwa a tsakanin mutuwa, burinshi kawai shi ne ya kyautata mata, ita kuma tana nan ta banzatar mishi da kanta.

A hankali ta lashi busasshen labbanta hade da shafa wuyanta wanda kasusuwa suka fito radau kamar wacce ta kwashe wasu watanni tana ciwo

Kwankwasa kofar da aka yi ne ta sanyata mayar da idanunta a kan kofar, har zuwa lokacin kuma hannunta na kan wuyan tana shafawa a hankali

“Waye?” ta dan daga murya

“Ni ce ranki ya dade! Hajiya ce ta ce ace miki ta shirya” cewar Asabe cikin ladabi daga waje.

“Ina zuwa.” Asma’u ta amsa a hankali.

Nan gaba kadan duk ma’aikatan nan sai sun fita daraja, duk wani girma da suke bata zai ƙaura, za ta zama abun zunɗe a wurinsu.

Jin dadin minti biyar ya jefata cikin tashin hankali da nadamar da ba ta san ranar karewarsu ba.

Sannu a hankali ta mike ta nufi kofar fita lokaci daya tana warware bulun hijabinta, ta dora shi a kan atamfam cotedivoire blue.

Kai tsaye farfajiyar gidan ta dosa, tun daga nesa ta hango Hajiya tsaye, dogarawa da ƴan aiki suna ta kwasar gaisuwa.

Mace ce ai fara’a, hak’uri gami da dattako, ba ta shiga abin da bai dame ta ba tana da kawar da kai, kawaici gami da kyautatawa.

A, halin yanzu ita kadai ce mata a wurin Hakimi, Allah Ya yi wa abokiyar zamanta rasuwa wajen shekaru goma baya.

Duk wata hidimar yara ita ce ta ci gaba da yin ta, yara 23 da uku ne suke karkashinta, da yawansu a hannunta suka girma. Har yanzu kuma ita ke jagorantar duk wani abu da ya shafe su.

Kyakkyawa ce sosai, fara doguwa mai matsakaicin jiki da yalwar gashin kai.

Ku san kominta ne Ahmad ya dakko, Sai dai dibar jini, wani lokaci sai ya ɗan rikide zuwa kamanni Hakimi.

Tun da dogarawan nan suka hango ta, suka juya kanta.

Suka shiga watso mata kirari. A da kirarin baya sanya ta jin komai, amma yanzu kam ya fara ratsata da an fara mata shi, Sai ta ji kanta ya yi gingimeme, tana takawa dakyar cike da kasaita. Sosai sarauta ta fara ratsa jininta.

A haka suka raka jikin motar da Hajiya ke tsaye tana murmushi irin na ji dadin nan, tun ba da ta ji suna cewa sai ta Asma’u ta haifi ƴan biyu.

Bayan sun daidaita a cikin motar ne direba ya ja suka fice daga cikin gidan.

Asma’u ta juya kanta gefe tana kallon shaguna da kuma gidajen da suke wucewa.

Garin Dawuri, gari ne mai kyau da ya cika da masu ilmi, boko da kuma na addini, suna da masu kudi sosai, ƴankasuwa da manyan manoma.

Shi ya sa garin yake da kyan tsari da kuma dadin zama.

Tafiya ba mai nisa ba ta kaisu Ireland, sabuwar unguwa ce, wacce ma fi yawan mazauna cikinta ƴan boko ne, manyan ma’aikata.

Haka suka rika tafiya a hankali har zuwa lokacin da suka isa gate din gidan Malama Saratu.

A waje direba ya yi parking motar su kuma suka sauka zuwa cikin gidan.

Malama Saratu kawa ce sosai a wurin Hajiya, shekarunsu ma za su zo daya, ba yau ne ta fara rako ta gidanta ba.

Malama Saratu tana da kirki kamar dai Hajiya, abin ya sa gidanta ya dan fita kan Asma’u tun watarana da suka zo gidan suka iske diyar Malama Saratu mai suna Mami ta zo weekend.

Bayan sun fito ne Hajiya ke fada mata, ta so Ahmad ya auri Mami amma ya ki, kuma yarinyar tana son shi.

Hajiya ta zauna kan kujera, Asma’u kuma ta zame kasa ta zauna kamar dai yadda take yi duk ranar da ta yo mata rakiya.

Sai da ta bari sun gama gaisawa sannan ta gaishe da Malama Saratu kanta a kasa.

Daga nan ta yi shiru tana sauraron hirarsu wacce duk a kan yara ne. Sai daga baya ne Hajiya ta ce “Ga ƴarki nan, ki yi mata hoto(scaning)”

Gaban Asma’u ya shiga faduwa dam-dam kamar ta tashi ta ruga, ji take kamar scaning din zai fada musu abin da ke cikin ta ba na Ahmad ba ne.

Murmushi Malama Saratu ta yi, hade da umurtar ta da ta shiga dakin

Kamar jikakkken biredi haka Asma’u ta ja jiki labo-labo zuwa dakin, kafin Malama Saratu ta biyo ta.

Ba jimawa ta yi mata scaning din, Asma’u na zaune har ta yi printing out na result din, sannan ta ta ce “Mu je wajen Hajiyar taku”

Ta bi bayanta jiki ba kwari, yanzu kam hirar duk a kan cikin jikinta ne, a nan ne ma ta ji Hajiya ba ta fada wa Ahmad maganar cikinta ba, wai ta bari sai ya dawo, ta ga yadda zai yi.

Duk suka yi dariya, lokaci daya kuma Hajiyar ta ce Asma’u ta ta tashi su tafi.

Kai tsaye mota ta shige, ta bar su a farfajiyar gidan suna hirarsu.

Zaune kawai take cikin motar amma hankalinta ba ya jikinta yana wani wuri daban, wayar da ke cikin jakarta ta fitar a karo na ba adadi ta shiga kiran lambar Mk. Har yanzu a kashe take.

Wata zuciyar ta fada mata ta je Facebook ta yi mishi magana, saboda ku san ko wane lokaci yana online.

Da sauri ta amince da shawarar, ta shiga Facebook ta yi searching sunanshi.

Ba ta san lokacin da ta sillar da wayar ba saboda cin karon da ta yi da post masu yawa da ke nuna Mk ya bace sama da sati biyu.

“Na shiga uku!” cike da tashin hankali ta fada idanunta a warwaje

Ado direba ya juyo da sauri tare da fadin “Me ya faru ranki ya dade?”

A lokacin ne ta san a bayyane ta yi maganar, ba ta tanka mishi ba ta shiga maimaita kalmar Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un ba adadi.

Sai da ta hango Hajiya na zuwa ne ta daidaita nutsuwarta.

Kamar dazu, yanzu ma shiru suka rika tafiya, ita dai Asma’u tashin hankali ne sosai a kasan zuciyarta, wanda take jin kamar ta ɓalle murfin motar ta fita a guje.

Suna isa gida ba ta saurari masu yi musu sannu da zuwa ba, ta yi hanyar part din a matukar kidime.

Tun a farkon kofa ta yage hijab din jikinta ta rike a hannu zuwa cikin babban falon.

Saman kujera ta fada ta shiga rera kuka mai sauti, abubuwa sun damalmale mata, ta rasa hanyar warwaresu, daga wannan sai wannan.

Kbn ma da ya kasance last hope din ta shi kuma ya ba ce

“Na shiga uku! Ina kb ya shiga? Me ya sa ya bace?” ta yi maganar a bayyane cike da ɗimuwa.

D, hanzari ta mike zuwa dakinta, durowarta ta bude, ta ciri dogayen riguna guda biyar.

Ta dakko wata karamar jaka ta zazzage abun da ke ciki.

Ta shirya dogayen rigunan, ta juya kan sarkokkinta, ta ware nata, ta ware wanda Ahmad ya siya, misalin wadanda ya siyo mata a matsayin tsaraba yayin da ya yi wata tafiya, ko ya yi mata kyauta haka nan, da kuma na cikin lefenta

Wadanda ta siya yayin yin wani biki ko sallah ko za ta yi tafiya su kadai ta zuba a cikin jakar.

Ta rika bude duk wani wuri da ta san ta ajiye kudi ta kwasosu ta shirya su cikin jakar. Sannan ta shiga kintsa dakin, cikin kankanen lokaci ta mayar da komai yadda yake.

Gefen gado ta zauna tana mayar da numfashi a hankali, yayin da zuciyarta ke ta karfafa mata gwiwa a kan abin da take da niyyar yi.

A kasalance ta shiga zare rigar da ke jikinta, ta maye gurbinta da wata doguwar rigar mara nauyi. Ta yi rolling veil bayan ta saka facemask.

Karamar possernta ta bude, I’d card din ta na zabe da katin dan kasa da ATM card dinta duk suna ciki.

Wayar da ke gefenta ta dauka hade da zare Sim din ciki ta jefa shi cikin possern. Kafin ta saba karamar jakar ta fice zuwa dakin Ahmad.

Wurin ajiyar takardunshi ta lalubo jotter hade biro ta aje akan durawar mirror ta shiga rubutu.

Bayan ta gama, ninke takardar ta yi hade da rubuta sunanshi a baya da babban baƙi. Ta saka ta cikin lokar mirror saboda ta san Idan har yana gida, kullum sai ya taba wurin.

Juyawa ta yi kan hotonshi ta narke idanunta kallo take mishi irin na ba kyauta din nan ba, kamar Ahmad din ne a gabanta, hawaye suka shiga sauka daga idanunta zuwa kan tattausan kumatunta, ta jima a haka, kafin ta juya zuwa kofar fita.

A kan entrance din ta ta tsaya tana jira a tayar da sallah a masallacin kofar gidan, kamar 2mns kuwa aka shiga sallahr sai da ta bari an yi raka’a biyu za a je ta uku sannan Sadaf-Sadaf ta fice daga gidan tare da yakinin babu wanda ya ganta.

<< Abinda Ka Shuka 10Abinda Ka Shuka 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×