Ta san yanzu Ahmad ya kira ta, bai same ta ba saboda dama sau daya kacal yake kiranta a rana, safe ko rana, saboda inda yake babu network sai sun hau dutse. Idan bai same ta ba, zai kira Hajiya, Hajiya za ta aiko a duba ta, za a koma fada mata ba ta nan, Hajiya za ta zo da kanta ta duba, da ba ta ganta ba za ta koma a rikice a fara tambayar dogarawa da jami'an tsaron da ke kofar gidan.
Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana tuna tashin hankali da damuwar da. . .