Skip to content
Part 14 of 48 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ta san yanzu Ahmad ya kira ta, bai same ta ba saboda dama sau daya kacal yake kiranta a rana, safe ko rana, saboda inda yake babu network sai sun hau dutse. Idan bai same ta ba, zai  kira Hajiya, Hajiya za  ta aiko a duba ta, za a koma  fada mata ba ta nan, Hajiya za ta zo da kanta ta duba, da ba ta ganta ba za ta koma a rikice a fara tambayar dogarawa da jami’an tsaron da ke kofar gidan.

Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana tuna tashin hankali da damuwar da ahlin zasu shiga, musamman iyayenta da kuma Ahmad

“Ba da sona ba, Ku yafe min don Allah” ta yi maganar cikin ƙaramin sauti, hawaye masu dumi na zirarowa daga idanunta.

Kuka ta yi sosai, sannan ta mike zaune hade da dakko masararta da ke kan center table, ta rika taunata kamar mai cin kasa, sam ba ta jin test dinta, daga karshe ma cikin dustbin ta jefa ragowar, ta fada bayi hade da sakewa kanta ruwa.

Ta jima a bayin ruwa na sauka a kanta, kafin ta fito bayan ta yi alwala ta shiga ramuwar sallah.

Bayan ta idar ta sha kankana da ayaba, sauran tarkacen kuma ta sanya su a fridge.

Ba Ta samu bacci ba sai gab asuba, shi ya sa sai bakwai da wani abu ta farka, a gaggauce ta yi sallar asuba, kafin ta zauna a kan sallayar tana tunanin ko wane hali Ahmad yake ciki yanzu oho, ko Ummanta da Babanta sun sami labari oho.

Siririn tsoki ta ja, saboda tana ganin kamar ba ta biyo hanya mai ɓillewa wa ba, an ce kyan ɗa ya gagara gidan ubanshi, ya kamata ta koma gida, ko ba komai iyayenta zasu fi samun kwanciyar hankali.

“Da cikin?” ta tambayi kanta da kanta

“Ko dai in cire shi ne?” ta

 kuma tambayar kanta

Kai ta shiga girgizawa tana fadin “No! No!! No!!!” hankali

Kwankwasar kofar da aka yi ne ta sanya ta kallon lokaci a jikin tv, karfe takwas har da rabi.

Cike da mamakin yadda lokaci ya yi gudu ta isa kofar dakin tare da fadin “Waye?”

Daga can waje Lukman ya ce”Ni ne Madam”

Ta gane mai muryar shi ya sa ta murza key din hade da bude kofar.

Stoking ya yi cikin dogon bakin wando mai santsi da riga shirt fara sol mai dogon hannu, ya daura necktie baki wanda ya kara kawata kwalliyar tashi. Kamshinshi mai dadi ya cika wajen.

Yau ne ta kare mishi kallo sosai, sa’ar Ahmad ne, ko Ahmad zai girme shi bai fi da shekaru biyu ko uku ba, dan gaye ne shi sosai mai ji da kuruciya, akwai alamun nutsuwa sosai a tare da shi.

“Morning Madam”

“Morning” ta amsa kamar ba ta so

“What do you want for breakfast?”

“Empty tea” ta kuma fada a hankali.

“just?”

Kai ta jinjina a hankali.

Ganin ya juya ita ma sai ta koma ciki.

Bai jima ba ya dawo hannunshi dauke da madaidaicin faranti wanda ya doro cup of tea da chips.

Bayan ta bude mishi ya dora mata a kan center table din ya ja karamar kujera ya zauna, yana kare ma yanayinta kallo.

“What again?” ta yi saurin tambaya saboda yadda yake kallon ta

“Nothing!” ya fada tare da sauke ajiyar zuciya.

Tea din ta dauka, ta rika sipping din shi a hankali kamar ba ta so.

“Nawa ne charges dina?” ta katse musu shirun

“Har yanzu kudin ki basu kare ba”

Ganin ba ta ce komai ba ne ya ce “Me ya sa kika baro gida?”

Ta yi saurin juyowa tana kallon shi, yayin da mamakin tambayar da ya yi mata ya bayyana karara a kan fuskarta

Ya daga mata gira alamun jaddada abin da ya fada.

“Waye ya ce maka gida na baro?” ba tare da ta kalle shi ba ta yi maganar.

“fuskar ki, da yanayin ki” ya ba ta amsa

“Idan haka ne, me ye naka a ciki?” har zuwa lokacin ba ta kalle shi ba, kuma sipping din tea din ta take yi a hankali.

“Saboda zuciyata ta kamu.”

“Da me?” ta yi saurin tambayarshi

“Kaunar ki.” ya fada kai tsaye

Karon farko da ta yi murmushin da ya kasa fahimtar na menene.

Dukkansu suka yi shiru, Asma’u kuma tana yin break din ta a nutse, tamkar ba ta san da zaman Lukman a wurin ba.

Bayan ta gama ta mike tsaye lokaci daya kuma tana goge hannun ta da tissue.

Ta kalle shi tare da fadin “Ina son dakin idan ba damuwa.”

Shi ma ya mike tsaye idanunshi a kanta kafin ya ce “Na fada miki gaskiya ne, zan karbe ki no matter how hard, and Ina shawartarki ki koma gida, koma menene zai fi idan kina gida. A nan ba za ki yi mutumci ba, sannan za ki rika haduwa da mutane daban-daban, wadanda zasu kara lalata miki al’amuranki.”

“Lalacewar lamari na nawa kuma, ai tuni lamari ya riga da ya lalace” ta fada a zuciyarta, a zahiri kuma ta ce “Please I need space”

“ok” ya fada hade da mikewa ya fice daga dakon

dakin

Bayyanannar ajiyar zuciya ta sauke, yayin da take bitar kalaman Lukman a zuciyarta.

Cike da mamaki take kallon kofar da ake knocking, ba tare da ta tambayi waye ba, ta isa wurin kofar tare da budewa.

Ganin saɓanin Lukman ba karamin tsorata ta yi ba “Waye kai, me kake so?” cike da tsoro ta yi maganar ganin yana kokarin shigowa dakin

“Haba Gimbiya, ki bari mana in shiga sai in fada miki”

“Ka shiga ina?” yanzu kam rai a ɓace ta yi maganar

“Yi a hankali Hajiya ba abun fada ba ne, ko nawa kike so zan ba ki, muddin za ki amince min, tun jiya na ga shigowarki, kuma nake ta bibiyar ki”

“Mtswww” ta ja tsoki hade da rufe kofar da karfi, tana jin wani irin zafi  kirjinta. Mamaki take babban mutum kamar wannan amma yana yawon hotel da mata.

A karo na ba adadi ta yi dialing lambar Kb, har zuwa lokacin a kashe take.

“Na shiga uku ni Asma’u!” ta fada cike da rashin sanin abun yi

Kuka dai ta yi shi har ta gaji, shi ya sa ma yanzu ta koma gefe gadon ta zauna zuciyarta na yi mata wani irin ɗaci, da ace za ta iya kashe kanta da ta gwada, sai dai bayan zafin da take tunani za ta fuskanta har da haɗuwar da Allah ma. Ta san ba za ta iya jurewa azabar wuta ba, ya fi ta lallaɓa ta karasa rayuwarta cikin neman gafarar abin da ta aikata.

Tsalle ɗaya ta yi zuwa rijiya ga shi dai tun ba aje ko ina ba ta gama dubun ba ta yi alamar fita ba, a maimakon hakan ma ƙasa take ƙara yi.

Maganganun Lukman suka faɗo mata. Gaskiyarshi zamanta a nan ba mutumci wai zuwa maka da kare, babu abin da zai jawo mata sai ƙara damewar abubuwa, koma dai menene ya fi mata ta tafi gida.

Ko ba komai za ta ketare zunubin tayar da hankalin iyayenta.

Bari mu leka Ahmadu.

AHMAD POINT OF VIEW

Kamar ko wane lokaci misalin karfe biyar na yamma ya Parker motorshi a inda ya saba parkawa duk lokacin da ya zo yin waya,

Yanzu ma Dutsen cike yake da mutane kamar yadda ya saba zuwa ya taras.

Lambar Asma’u ya fara kira, ya kuma duba lambar cike da mamakin yadda ya ji an ce a kashe, saboda Asma’u ko bacci take yi ba ta kashe waya.

Yasa kuma ba dai rashin caji ba, saboda ko ba nepa suna da sola.

Ya kara gwada kira a karo na ba adadi, hakan dai aka kara maimaita mishi

Dalilin da ya sanya canja akalar kiran kan Hajiya

“Assalamu Alaikum!” daga can ɓangaren Hajiya ta fada

Ya amsa sallamar, kafin ya shiga gaishe ta, ta amsa cike da kulawa, ta shiga tambayar shi yanayin aiki, shi kuma yana amsa mata da abun da ya dace.

Bayan karamar hira ya ce “Na kira layinta a kashe.” tun da ya fadi haka ta fahimci wa yake nufi

“A kashe kuma? Ai kuma bamu jima da dawowa da ita daga gidan Malama Saratu ba. Amma bari in aika Asabe ta duba ta” cewar Hajiya tare da yanke kiran, lokaci daya kuma tana juya akalar kiran a kan Asabe

Cike da girmamawa Asabe ta amsa kiran

Hajiya ta ce “Je ki sashen Magaji ki dubo min matarshi”

Cikin hanzari Asabe ta juya, ba, ta jima ba ta dawo

“Hajiya ba ta nan”

Cike da mamaki Hajiya ta ce “Kamar ya ba ta nan?”

“Ni dai na leka kitchen da ƙaramin falonta duk ban gan ta ba” Asabe ta amsa cike da ladabi

Shiru Hajiya ta yi kafin ta ce “Tashi mu je”

Asabe na gaba Hajiya na bin ta a baya suka yi wa part din Asma’u tsinke, ko wane lungu da sako sai da suka duba amma ba Asma’u babu mai kama da ita. Ga wayarta a kashe.

Cikin rashin sanin abun faɗa Hajiya ta kira Ahmad, wanda dama yake ta faman jiran kiran Hajiyar

“Na manta sun fita ita da Yayarka Safiya, kuma ka ga wayarta nan a falo tana caji” Hajiya ta ƙirƙiro karyar da ba ta shirya mata ba.

Ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin “Shi kenan zan dawo gobe, magriba ta gabato.”

“To Allah Ya kai mu”

Daga haka suka yi sallama, yayin da Hajiya ta kasance cikin saƙe-saƙe, saboda ta kasa hasaso haƙiƙanin abin da ya faru da Asma’u. Haka ta koma ɓangarenta zuciyarta damfare da abubuwan da ta kasa gasgatawa.

*****

RUMASA’U

Kwance take tsakiyar ɗaki, yayin da wata irin baƙar yunwa ke rarukar cikinta, rabon ta da abinci tun daren jiya, ga shi har karfe biyu na rana.

Duk wani abu da take sarrafawa mai sauri Aibo ya kwashe shi ya sayar, yanzu ba ta da komai sai masara. Saboda hatta manja da mangyaɗa sai da ya ƙarar mata dasu. Kyauta ta mugunta yake mata dasu, wani lokaci kuma ya siyar.

Tana daga kwancen ta ji shigowar Salmanu, da sauri ta miƙe zaune tare da kwala mishi kira.

Ya amsa lokaci ɗaya kuma yana tahowa inda ya jiyo muryarta

“Ba ku zauna karatun rana ba har yanzu?”

“Mun zauna tawadata na zo dauka.” ya ba ta amsa

Ta marairaice kamar za ta yi kuka kafin ta ce “Don Allah Salmanu ka je gidanmu wurin Yaya, ka ce na ce idan an yi abinci a zubo min, amma kar ka bari Babanmu ko Yaya Usman ya sani don Allah”

Salmanu ya gyaɗa kai alamar ya fahimta.

Bayan ya tafi komawa ta yi ta kwanta, lokaci ɗaya kuma ta addu’ar Allah Ya sa akwai abincin bai ƙare ba.

Tana kwance a wurin Salmanu ya dawo, kanshi ɗauke da samira, wani sanyi dadi ya baibaiye ta

Da sauri ta mike ta karbi samirar haɗe da buɗawa

Yawunta ya tsinke lokacin da ta ji karo da dambu jar masara ya sha tafasa sabon toho, kasancewar ana yanayin farkon shigowar damuna.

Lokacin da take zuba wa Salmanu a murfin samirar ne Aibo ya shigo. Ba tare da ta kawo komai a ranta ba, ta ci gaba da abin da take yi.

Mitsi-mitsi da idanu ya yi kafin ya ce “Ina aka samo wannan dambun?”

“Daga gida aka kawo min” ta amsa shi.

Da sauri ya fisge samirar yana fadin “Oh! Idan ba na nan gida kike aikawa a karɓo miki abinci ko? Salon ki ja min sharri, ace ina barin ki da yunwa?”

Da sauri ta ce “A’a. Ban taba aikawa ba”

“Ba ga shi kin ce wannan dambun daga can yake ba. Ko da kafafunshi ya zo?”

Bai jira cewar ta ba ya juya kan Salmanu haɗe da kai mishi wani mangari, a ɗari Salmanu ya yi waje, dalilin da ya sanya shi juya kan Ruma, ita ma sai ta yi saurin da No kofa ta sanya sakata

Watsar da dambun ya yi a tsakar gida hade da ficewa.

Sai da tabbatar ya yi nisa sannan ta fito, idanunta ƙur a kan dambunta da ke yashe cikin turɓaya.

Yadda take jin yunwa ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta duƙa ta kwashi ko kaɗan ne.

Haka ta duƙa ta riƙa dibar na sama-sama ɗin, wanda ƙasa ba ta taɓa sosai ba.

Bayan ta gama ta koma jikin katangar kitchen, tana ci hade da hawaye.

Bai shigo gidan ba sai can dare, a lokacin kam Ruma kanta ne ke mata wani irin ciwo, kamar zai fashe.

Ƙara mai ƙarfi ba ta so, shi kuma ya shigo da wayar shi (Sha kiɗanka baƙauye) ya kure volume yana jin Waka.

Jin kanta na ƙara tsananta mata ciwo ne ya sanya ta fita waje ta zauna. Har sai da ya gama jin kidanshi ya kashe don kanshi sannan ta shiga dakin.

Lokacin da gari zai waye kam ko mikewa da kanta ba iya yi sai rarrafe, shi kansa sai abun ya fara ba shi tsoro, saboda ya tabbata idan Alaramma ya ji abin da ya faru ya kaɗe har ganyenshi

Shi ya sa da sauri ya fita waje ya siyo mata koko har da Sugar da kosai.

Lokacin da ta sha kokon amai tai ta zabgawa, sosai ya tsorota ya kira Usman.

Haka aka siyo mata maganin amai ba tare da cewar likita ba.

Wunin ranar dai Ruma cikin wahala ta yi shi. Aibo kam ya kasa ya tsare, baya fita ko ina, tsoron shi kar ya fita Ruma ta fadawa masu shigowa yi mata sannu halin da take ciki. Ya ci ƙaniyanshi a hannun Alaramma.

HAFSAT

Yau Jumma’a da misalin karfe biyar na yamma, kwance take a dakin Innah, yayin da hannunta ke riƙe da littafin Gorar Duma.

Yanzu shi ne abokin hirarta, shi ya sa Nasir ke da sawo mata su, duk lokacin da ya shiga kasuwa, ko kuma ya yo mata renting.

Gidan babu mai shiga harkar ta, idan dai ka ji maganarta to da dabbobinta ne, ba ta san ka yi abu ba daidai ba a yi ma faɗa gata ne ba sai yanzu.

Ba ta san ace, yi shara, yi wanke-wanke, yi wanki duk yana cikin gata ba, Sai yanzu da ba ta da wanda yake sanyata wadannan abubuwan.

Ta yi nisa sosai a cikin littafin ta ji tashin muryar Inna Luba tana cewa “Ke Tatuwa, ba ki ji ana kiran ki a kofar gida ba”

Da wani irin hanzari ta wilƙito daga saman gadon zuwa kofar dakin tana fadin “Ban ji ba wlh.”

Ganin babu wanda ya yi alamun zai ƙara tanka mata ne ya sa ta koma cikin ɗakin haɗe da sanyo Army green color din hijab dinta ta fito zuwa kofar gida.

<< Abinda Ka Shuka 13Abinda Ka Shuka 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×