Skip to content
Part 15 of 19 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ganin Uncle Najib sai ta ji daɗi, yana da kirki, su biyu kacal take gani a yanzu su sanyata farin ciki. Sai kuma Mama Halima

Ba don ya so ba, ya janye idanunshi a kanta, a zuciyarshi ya ce “Allah Ya yi halitta a wurin nan”

“Ina wuni Uncle” ta katse mishi tunanin shi bayan ta yi sallama.

A hankali ya amsa kafin ya katse ɗan shirun da ke tsakaninsu da fadin “Ya kamata ki koma makaranta”

Fuska ta kaɓe kamar za ta yi kuka ba tare da ta ce komai ba.

“What?”

Kamar za ta yi kukan ta ce “Ni ba na son zuwa yanzu”

Bai ce komai ba ya miƙa mata ledar hannunshi.

Hannu biyu ta sanya haɗe da karɓa. Ta bi umarnin da ya ba ta na cewa ta bude ledar

Daga tsayen da take ta buɗe bakin ledar, sabbin uniform ne a ciki dinkakkun, litattafai, jaka, sandals da Kuma socks.

Ta cire idonta daga cikin ledar zuwa kan fuskar Najib

“Ki tabbatar kin je makaranta ranar Monday, na gama miki komai za ki tafi tare da set din ki, duk da ana karshen zango ne”

Hannu ta sanye hade da dauke hawayenta, cikin kuka ta ce “Za su yi ta tsokanata”

“Shi ne me to? Bari ki ji karatun nan shi ne gatan ki a yanzu, ya kamata ki jure duk kalubalen yanzu da mai zuwa nan gaba. And idan kina so sai a nemar miki boarding, ki fara daga SS2 kenan.”

Shiru ta yi alamun tunani, kamar ba za ta ce komai ba, Sai kuma ta ce” Idan na tafi boarding din ba mai kular min da dabbobina ai, amma da na tafi boarding din”

Sai ya ƙara jin tausayinta ya kama shi, kafin ya yi magana Nasir ya shawo kwana a kan mashin din shi kirar LIFAAN. Dukkansu suka mayar da kallonsu a kanshi

“Don Allah ina zuwa Yayana ne ya zo” cewar Hafsat a lokacin da take kallon inda Nasir yake.

“No! Ni ma zan wuce ne, ki tabbatar dai kin je makarantar.” cewar Najib lokaci daya kuma ya kama hanyar barin kofar gidan.

Tun da ta taho Nasir ke kallon ta. Bayan ta karaso ne ya ce “Me ya sanya ki kuka?”

Ta share tambayar ta shi da fadin “Ya Nasir yau ka jima ba ka dawo ba”

Ya murmusa kaɗan kafin ya ce “Kin ga daɗewa ta ne, saboda dama jirana kike yi.”

A karo na farko ta kara murmusa, har fararen hakoranta suka bayyana.

“Waye wancan?” ya yi tambayar lokacin da yake sauke  ledar da ke gaban mashin din zuwa kasa

“Uncle ɗinmu ne mai English”

“Wai me?” ya kuma tambaya idanunshi a kanta yanzu .

Ledar hannunta ta mika mishi, cikin muryar da ke nuna rashin jin dadin abun da za ta fada mishi ta ce “Cewa ya yi, wai in koma makaranta ranar Monday, har ya hada min komai da komai ma.” ta kai karshen maganar cikin kuka

Yan janye idanunshi daga kallon abin da ke cikin ledar tare da fadin “To shi ne me a koke? Ba gata ta yi miki ba, ni kaina na fara wannan tunanin ai, ya riga ni ne kawai, ni hakan ya min daɗi, zaman me za ki yi a gidan.”

“Ni ma ina so, amma ba na son yara Sui ta tsangwamata da kyara ta.”

Yadda ta yi maganar sai ta ba shi tausayi. Cike da karfafa mata gwiwa ya ce “A wannan karon zan je makarantar, zan kuma dauki mataki, don haka kar ki damu.” Kai ta jijjiga alamar gamsuwa da jawabinshi, kafin ta ce “Ya Nasir Maman ta kira ka?”

“Ba wani ba shi kike son tambaya ba, abin da ma kike son tambayar kika waske na sawo miki yana nan cikin ledar.”

Da wata irin dariya ta kyalkyale, shi ma ya fara dariyar lokaci daya kuma yana tayar da mashin din

“Na gode” ta fada cikin dariya ganin yana kokarin barin wurin.

Haka ta dauke ledar guda biyu zuwa cikin gida.

Koda ta yo sallama ma babu wanda ya amsa, wannan ya sa ta wuce cikin dakinta kai tsaye.

Ledar Uncle Najib ta fara zazzagewa, uniform ne Kala biyu, sandals biyu socks kafa hudu, school bag Mai kyau Irin ta yan birni wacce ake goyawa. Sai litattafai, pencil, biro, cleaner, calculator, Oxford dictionary, Ababio Chemistry, duo wani dai abu da ya san za ta buƙata sai da ya saya.

Sai ta riƙa jin ma ta kosa Monday din ta yi, dokin da murnar ganin kayan ta mantar da ita duk wani kalubale da take hange.

Ta mayar da komai tsab, sannan ta janyo ledar Ya Nasir.

Abin da ta ƙagu ta gani shi ta fara laluba, cikin sa a kuwa ta jiyo shi, da sauri ta dakko haɗe da yage ledar, litattafan suka zube tsakiyar daki.

Ta rika bin su ɗaya bayan ɗaya tana karanta sunayensu zuciyarta fal farin ciki. Gefe ta ajiye su ta shiga zaro sauran kayan akwai package na kayan kwalliya, wanda yake dauke da mai lotion, cream, sabulun wanka, vasseline, roll on, body spray, powder, cleanser da kuma audugar goga cleanser.

Suma gefe ta ajiye, kafin ta hango wata kula mai kyau, tana buɗewa ta ci karo da pepesoup na kaza, wannan kam ta san daga Maman Halima ne.

Akwai pants vest masu kyau, har da takalma slippers fashion guɗa biyu.

Ajiyar zuciya ta sauke, samun mace mai zumunci da son kyautatawa ɗan’uwa da son zumunci kamar Mama Halima a wannan lokacin akwai wahala.

Tsakanin inda Nasir yake aiki da Dawuri tafiyar 30mns ce a kan mashin, a cikin mota kuma ba ta wuce 15mns.

Wannan ya sa duk wani abu mai kyau na zamani wanda ƴanmatan birni ke amfani da shi Mama Halima sai ta sawo ta aiko mata da shi ta hanyar Nasir.

Ba iya kayan sanyawa ba, hatta abinci sai ta yi mai dadi ta aiko mata da shi. Shi ma kuma Nasir din duk lokacin da zai dawo akwai tsarabarta, kifi ko nama, youghurt da minerals haka yake sawo mata.

Shi ya sa kallo daya za ka yi wa jikinta ka fahimci ba abin da mutanen gidansu suke ci take ci ba.

Da ace abincinsu za ta tsaya jira za ta mutu, saboda duk wanda ya yi abinci sai ya sallama masu uwa sannan, idan ya rage ta je ta zuba, idan bai rage ba kuma oho.

Don Nasir har ruwa pure water sawo mata yake yi, musamman lokacin da ta yi ciwo, gwaji ya nuna tana da typhoid, shi ne ya cewa Malam Ayuba Hafsat ta daina shan ruwan rijiya sai na leda.

Kai tsaye Malam Ayuba ya ce shi ba zai iya wannan gagason gashin mara ba ɗa ba. Shi ya sa ko da Nasir ɗin yake sawo mata basu damu ba.

Kuma idan za ta ci raƙumi da kaya, a gidan ba mai daga kai ya kalle ta, bare ya nuna yana son ci.

Sosai abun ke damunta, har so take ta basu abu su karba, ko su da kansu su gani su nuna suna so. Gabadaya dai sun rufe ta, babu mai bi ta kanta. Ba kowa ne zai gane rashin dadin irin wannan zaman ba, sai wanda ya tsinci kanshi a cikinshi.

AHMAD

Haka nan ya kasa nutsuwa da maganar da Hajiya ta fada mishi, ya so kiran Aunty Safiyya ma, sai kuma ya hak’ura.

Da safe kuma ya so zuwa wurin service din ya kira, sakamakon wani operation na gaggawa da ya taso da safe shi ne ya hana shi zuwa.

Hakan kuma a bangaren Hajiya sai ya yi mata dadi, saboda ko ba komai ya kara bata damar zurfafa bincike.

Tun jiya da dare take tuntuɓar duk mutanen da ta san Asma’u za ta iya zuwa wajen su, amma ba ta je ba.

Da safen ne ta ɗan samu information ƙyas ta bakin wani hadimi, shi ma ya ce wani mai shago ne ya sanar mai, wai da idanunshi ya ga lokacin da Asma’u ta tare abun hawa ta hau.

Wannan bayani ba ƙaramin girgiza Hajiya da Hakimi ya yi ba.

Iyakar tunaninta ba ta tuno wani abu da zai sanya Asma’u guduwa ba.

Na farko ba auran dole aka yi mata ba, duk basu yi wata doguwar soyayya da Ahmad ba, amma ko makaho ya laluba zai fahimci tana son shi, ba a rage da komai ba, na daga muhalli, sutura, abinci da kuma kula lafiyarta, idan ba dai ko irin abun nan da Hausawa ke cewa ba, mace kamar rogo take, ta ƙi gidan daɗi.

Ko kuma ace wai idan dadi yay wa mutum yawa sai ya ce Allah kashe ni.

Wunin ranar dai cikin tattauna batun  Asma’u suka yi shi.

Wani irin tausayin Ahmad Hajiya ke ji, shi mutum ne mara son hayaniya, mai sanyin hali da iya danne damuwa.

Ko ta ina za ta fara fada mishi wannan batun oho?

Yana can a tsakanin rayuwa da mutuwa don kawai ya rufawa kanshi da iyalanshi asiri, ga shi kuma za a kara mishi wata damuwar, da ace maganar za ta binnu tabbas da ta binne ta, ta shanye duk tashin hankali ita kadai

Tana kan sallayarta bayan ta idar da sallahr la’asar kiran Ahmad ya shigo, Sai da gabanta ya fadi kafin ta daga kiran. Suka gaisa cike da girmamawa, ta tambaye shi wurin aiki, ya amsa mata da komai lafiya.

A nutse ta ce mishi “Ahmad za a iya ba ka permission zuwa gida kuwa?”

Ya ɗan yi shiru kafin ya ce “To abu ne dai mai wahala, kasancewar ni ne ke leading team din, amma Idan zuwan nawa yana da muhimmanci sosai zan iya haɗa kai da ma’aikata in taho ko ba tare da sanin office ba”

“To kana ganin hakan ba matsala?” Hajiya ta tambaya a hankali.

“In Sha Allah komai ba zai faru ba, saboda kafin a san bana wurin na koma, Sai dai ko idan zuwan nawa zai dauki lokaci”

Cikin sauri Hajiya ta ce “Ba zai dauka ba Sha Allah”

Hira kaɗan suka kara suka yi sallama yadda ba ta yi mishi maganar Asma’u ba, shi ma sai bai yi mata ba duk da zuciyarshi na cike da son sanin me ya faru da ita.

Amma kam yau shi ne ma fi kololuwar fargabar shi. Saboda ko yanzu ya kira layin Asma’un bai shiga ba

Abubuwa marasa kyau ne suke zuwar mishi cikin rai.

Jiki ba ƙwari ya riƙa gangarowa daga kan Dutsen, gaf zai sauka sai kuma ya koma baya.

Lambar Asad abokinshi da ke can Dawurin ya laluba.

Bayan Asad din ya dauka, suka tambayi lafiyar juna da yanayin aiki.

Ahmad ya dora da tambayar lafiyar mutanen gidan, shi kuma ya amsa mishi da kowa lafiya, wannan ya tabbatar mishi ba abin da yake tunanin ya faru ba ne, wato ko Asma’u ta rasu ne.

Bayan sun yi sallama da Asad office din su ya kira, ya fara neman alfarmar tafiya gobe, bai sakko kan dutsen ba da Sai da ya bi duk wasu hanyoyi da ya san zai samu damar tafiya a gobe,, kofofin da zasu ba shi matsala kuma ya toshe su.

Karfe hudun asubar ranar ya baro wurin aikin na shi zuwa gida, tafiyar da ta dauke shi awanni sha biyar, saboda sai karfe bakwai cif na dare ya iso.

Kai tsaye kuma ɓangaren Hajiya ya tunkara. A lokacin Hajiyar na  sallahr isha’i ne, ba ita kaɗai ba, hatta masallacin kofar gidansu sallahr ake yi, wannan ya sa ba kowa ne ya ga dawowarshi ba.

Zaune ya yi har Hajiya ta idar sallah hade da addu’o’inta, cike da kulawa ta ce “Magaji ka iso?”

Ya amsa da Eh, kafin ya zame ƙasa ya shiga gaishe ta cike da girmamawa.

Muryarta cike da wani irin sanyi na tausayinshi ta amsa.

Ahmad yana son aikinshi, yana girmama shi, yana ɗaukar duk wani abu da ya shafi aikinshi da muhimmanci. Shi ya sa ta san ba ƙaramin abu ne zai dago shi a yanzu daga kan aikin shi zuwa gida ba.

“To ka je ka yi wanka mana, ka ci abinci, zuwa lokacin Babanka ya shigo. Sai ka zo ku gaisa.”

Bai yi gardama ba ya mike haɗe da ɗaukar jakarshi ya sagala kan kafadarshi, Hajiya kuma ta dakko mishi makullin ɓangaren nasu.

Karon farko da ta kasa hak’ura ta lalubi lambar mahaifiyar Asma’u, saboda ta tabbata idan har Asma’u gida ta tafi, to zuwa yanzu ta isa.

Amma yanayin yadda suka gaisa da mahaifiyar Asma’u ya tabbatar mata ba ta je gidan ba. Saboda har tambayarta ta yi, ya su Asma’un?

Wannan ya ƙara ninka mata damuwarta, gefen gado ta zauna hade da tattauna al’amarin da zuciyarta.

Ta kofar baya ya kuma bi zuwa apartment din nasu.

Ya shiga da Bismillah bayan ya bude part din, komai yana nan yadda yake, idan ka ɗauke rashin Asma’u.

Wannan ya ƙara tabbatar mishi da zaton da yake na ba ta gidan.

Dakinta ya fara yiwa tsinke, ya yi tsaye a tsakiyar ɗakin yana nazarinshi, komai yana nan yadda yake, idan ka dauke shimfidar gadonta da ta ɗan yamutse.

Wardrobe din ta ya buɗe, nan ma kayan sun ɗan yamutse, saɓanin da da suke a shirye tsab.

“Ina ta je, me ya sa ta tafi?” ya yi tambayar a hankali hannunshi rike da murfin wardrobes din

Ya shiga tunanin tun daga tafiyarta gida zuwa dawowarta ko akwai wani abu da ya yi mata na ɓacin rai. Iyakar tunaninshi bai tuno wani abu da har zai sanya ta bar gidan ba.

” To ko da suka je gidan Malama Saratu wani abu ya faru tsakaninta da Mami ne, da ya tayar mata da kishi har ta tafi?” ya kara tambayar kansa, a kokarinshi na lalubo abin da zai sanya ta barin gidan.

Ya jima a wurin tsaye, kafin ya juya zuwa dakinshi. Jiki a mace ya sauke jakar hannunshi haɗe da ɗaura towel. Toilet ya shiga ya yi wanka tare da ɗauro alwala. Jallabiyarshi blue mai maiko ya sanya ya gabatar da sallahr magariba da isha’i saboda sune ake bin shi.

Bayan ya idar ne, ya wuce babban falo, saboda yana sallah ya ji shigowar Asabe, ya san kuma abinci ta kawo mishi.

Tea mai kauri ya haɗa kawai ya sha, sannan ya koma dakin na shi da zummar shiryawa don komawa wurin Hajiya.

Wasu ƴan canjin kudi da ya zube a kan gado, su ya kwashe lokaci daya kuma yana bude lokar mirror da niyyar zuba su ciki, ya ci karo da fara ƙal ɗin takarda an rubuta sunanshi da manyan baƙi, ba sai ya tambaya ba, ya gane rubutun Asma’u ne, dalilin da ya sanya shi sauri wajen fito da takardar.

Zaman shi ya gyara sosai a gefen gadon tare da bude takardar.

Ya shiga karantawa kamar haka

*”Assalamu Alaikum! Ina yi maka barka da lokacin da kake karanta wannan wasiƙar, idan safiya, rana, yamma ko dare.

Ya Ahmad ina sonka, ko don saboda kyawawan halayenka, kai mutum ne na gari. Na yi baƙin cikin rabuwa da kai. Ina kuma taya duk wacce za ta same ka a matsayin miji murna. Ni ba ka yi min komai ba, idan ma ka yi na yafe ma. Na san za ka shiga damuwa, baƙin ciki, tashin hankali idan ka samu labarin ba na gida. Ni da kaina na tafi, sannan a duk inda nake ka sanyawa ranka ina lafiya.

 Ya Ahmad ƙaddara ce ta faɗo min, wacce ban taɓa tsammaninta ba, ina da ciki na wasu kwanaki, kuma cikin da na san ba naka ba ne, idan ka lissafa da kyau kuma za ka gasgata ni. ina jin kunya da nauyin familynka masu karamci, ba zan iya bude ido in kalle su a lokacin da gaskiya ta bayyana ba, kuma ba zan iya bari ka reni yaron da ba na ka ba, ba ka cancanci haka ba. Shi ya sa na tafi. Ka yafe min”.

<< Abinda Ka Shuka 14Abinda Ka Shuka 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×