Skip to content
Part 17 of 19 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Sosai take ganin dawainiyar da yake da ita ta yi yawa, ko wace rawa takawa yake a rayuwarta. Da dai sayen magani kawai da aron littafi ke hadasu. Yanzu kuma kacokan rayuwarta ce a hannunshi, idan ta yi dariya shi ne, idan ta koka shi ne, idan ta ji dadi shi ne.

Ta bayan gari ya bi da ita zuwa makarantar, lokacin da suka isa, dalibai na shiga aji bayan an gama assembly. Kila shi ya sa Uncle Najib ya hangosu, kai tsaye kuma ya nufo su.

Nasir ne ya fara mika mishi hannu, suka gaisa cikin fara’a kafin Nasir ya ce “Muna godiya fa, dama Ina ta tunanin yadda zan shawo kanta ta dawo makaranta, Sai ga shi ka yi hakan cikin sauki”

Najib ya ɗan murmusa kadan ba tare da ya ce komai ba.

Tsayuwa Nasir ya gyara yana ci gaba da fadin “Na kawo ta ne da kaina saboda in yi ma godiya. Abu na biyu kuma Ina son zuwa wurin principal, ka san yaranan suna tsokanarta, a wannan karon wlh ba zan amince ba, duk wanda ya tsokane ta da kalmar batanci kotu ce za ta raba mu”

Shi ma Najib din tsayuwarshi ya gyara cikin muryarshi mara son magana sosai ya ce “Na ri ga na gama da wannan bangaren, Sha Allah babu abin da zai faru. Na sanya a rubuta min sunan duk wanda ya tsokane ta. Ita ma za ta iya kawo min sunan wanda duk ya fada mata wata magana mara dadi, ko ya yi mata abin da ba ta so.”

Cike da jin dadi Nasir ya ce” Kai amma mun gode gaskiya Allah Ya saka da alkairi. To ke dai kin ji yadda ya ce ko”

Ya karasa maganar yana kallon Hafsat wacce take can tsaye a gefensu, tun da ta gaishe da Uncle Najib ta dan matsa gefe kadan ko motsi mai karfi ba ta kara ba

Kai ta jinjina alamar ta fahimta

“Idan an tashi daga school din ki biya wajen Maman Iyabo ki karbi duk abin da kike son ci, na riga na yi mata magana” ya kai karshen maganar haɗe da ciro 200 ya mika mata

Ta shiga girgiza kai alamar ba za ta karba ba. Kaf idanunta a kan Uncle Najib da yake kallonsu.

“Ba za ki sayi komai ba?”

Kai ta daga alamar eh, lokaci daya kuma tana kyaɓe fuska alamun za ta yi kuka

“Idan kika yi min kuka Hafsat, zan rufe idona in karbi dorina in zane ki bayan na cire miki hajabin jikinka. Ke ƙaramar yarinya ce, yau kika fara zuwa school din?” a faɗace ya yi maganar wannan ya sa sautin kukanta ya fara fita a hankali

“OK, za ki yi kukan kenan? To ci gaba.” a fusace ya yi maganar hade da jefa mata 200,lokaci daya kuma ya juya kan Najib tare da mika mishi ya kara yi mishi godiya sannan ya juya kan mashin dinshi.

Zuwa lokacin Hafsat kuka take yi sosai, hannayenta du biyun a kan fuskarta.

Sai bayan da Nasir ya wuce ne Najib ya ce “Mu je aji” ba musu ta duka hade da daukar 200 ta bi bayan shi tana share hawayenta

Asalin class dinta SS1A nan suka shiga

Suna shiga ajin ya yi tsit, sosai tsoron Uncle Najib suke yi, yana da cika ido da yanayin bayar da tsoro. Ita kam za ta ce tun daga lokacin da ya zo zuwa yanzu ba ta taba ganin dariyarshi ba. Akwai tsare gida.

Da kai ya yi mata nunin ta samu wurin zama.

Ta karaso tsakiyar ajin sosai, sai ta rasa ina za ta nufa, duk kujera mutum hudu ne, amma a ajin akwai wadanda suke zaune mutum uku har mutum biyu ma.

Ganin ta yi tsaye ne ya sa ya karaso wurin kujerar Farida Bashir, su biyu ne a kan kujerar.

Da ido ya yi wa Farida alamar ta fito, jiki na rawa ta fita, ya yi ma Hafsat nuni da ta shiga ta zauna.

A darare ta zauna, saboda Farida na daya daga cikin wadanda take tsoro a ajin, saboda ita ce monitor, kuma ita din diyar wani babban ɗansiyasa ne a ƙauyen maƙeran. Babanta har vice Chairman local government ya taɓa rikewa. Tana da yar gadara ta dalilin wannan ga shi kuma tana da kokari sosai, Hafsat ce kawai take nuna mata yatsa a ajin a wajen kokari.

Bayan ta zauna ne ya umarci Farida ma ta zauna.

Sannan a hankali ya ce “kin  ji duk abin da na fada miki game da ita ko?”

Da sauri Farida ta daga kai.

“Duk inda za ku in ganku tare, daga yau ita ce kawar ki, kuma aminiyarki”

Duk ajin babu mai jin abin da Najib ke fada, daga Hafsat, Farida sai kuma Ni’ima Abdullahi da ke kan kujerar ita ma.

Yana gama fadin haka ya juya zuwa wurin allo, hade da rubuta darasi da kuma topic din da za su yi. Kasancewar dama shi ke da period din ajin double first and second.

Sosai Hafsat ta ji dadin darasin, saboda duk abin da ya koya ta gane kaso tamanin cikin dari. Bayan ya fita me mai Hausa ya shigo, daga nan kuma aka fita break.

Zaune ta yi kan kujerar tana kallon yadda daliban ke fita zuwa filin break, tsuuu ta yi, tana jiran tsokanarsu, Sai dai har suka gama ficewa babu wanda ya aiko mata da ko mugun kallo.

Wannan ya sa ta dan samu kwarin gwiwar fiddo biscuit dinta ta fara ci hade da kora pure watern hannunta.

Tana zaune a wurin Farida da Na’ima suka shigo. Gabanta ya shiga faduwa, saboda ta tabbata tsiya ce ta maido Farida, ga mamakinta kuma sai ta ji Faridan ta ce “Ba za ki fita break fast ba?”

A hankali ta girgiza kai alamar a’a

“To ba za ki sayi komai ba, mu sawo miki?” Na’ima ta tambaya

Nan ma kan ta girgiza alamar a’a

“Uncle mai English ya ce idan kina son wani abu, ki fada a sawo miki?”

Karon farko da ta bude baki a hankali ta ce “Ina da biscuit”

“To shi kenan” suka amsa gabadaya, har sun juya da niyyar tafiya sai kuma Farida ta waigo hade da fadin “Akwai wanda ya tsokane ki?”

A hankali ta shiga girgiza kai tare da fadin “A’a”

Daga nan suka juya zuwa kofar fita daga ajin.

Yau ce rana ta farko da ta zo makaranta har aka tashi babu wanda ya hantareta, saboda koda aka tashi tare suka jera da Farida, Na’ima da sauran kawayen su Faridar har inda Hafsat ta dauke hanyar zuwa gida tana fadin “Na gode”

Cike da kulawa suka amsa mata tare da fadin gobe kar ta makara, ana taren yan makara.

Lokacin da ta shiga gidan kowa na tsakar gida har da Babanta, daga yadda ta ga gidan ta san ba a yi abincin rana ba.

Har ƙasa ta duƙa ta gaishe da Babanta, ya amsa hade da fadin “Har kin fara zuwa makarantar ne? Nasiru ya ce sai ranar Litinin kuma.”

“Ai yau litinin din Baba” ta amsa daga duƙen da take”

Jin bai ce komai ya sa ta mayar da gaisuwarta wurin sauran matan gidan. Wannan karon kuma Inna Kuluwa ce ta amsa Inna Luba ba ta amsa ba, Sai a lokacin ne Hafsat ta lura da ran Inna Lubar a ɓace yake.

Ta mike zuwa daki, bayan ta canja kaya zuwa riga da zane gami da hijabi, kwano ta dauka ta kunshe a hijibinta zuwa wurin Maman Iyabo.

Shinkafa da miya da nama ta karbo har da ruwa, wai haka Nasir din ya ce a ba ta.

Lokacin da ta dawo gidan Baba ya fita, sai su Inna Kuluwa da suke gulmar shi.

Tana tsaka  da cin abinci ne ta ji Inna Kuluwa na cewa “Waɗannan yan kudin da ya samu ne yake ganin karanshi ya kai tsaiko har yake rarumo aure”

Inna Luba ta karbe da “To yanzu idan Tatuwar ta tashi a dakin ina za ta koma?”

“oho mishi, Sai dai idan dakin amaryar za ta zauna, ko kuma ta koma dakin kajin su” Inna Kuluwa ta ba ta amsa

“Wannan ma zai faru ne bayan mun bari an yi auran ko? Babu yar iskar matar da za ta shigo mana nan wlh. Jummai ta yi min kwarwar wani malami can Malamawa. An ce aikinshi kamar yankar wuƙa. Can za mu je, daga nan a yi mana kiran kasuwa kin ga ciniki ya ja baya”cewar Inna Luba

Inna Kuluwa ta caɓe da “Aiko Dije ta taɓa min hirar wannan malami, an ce yana aiki sosai. To sai mu sanya ranar zuwa”

Duk hirar da suke yi Hafsat na ji, duk a hirar abu daya ne ya fi tayar mata da hankali shi ne batun karbe dakinta. Idan har haka ta faru to Dawuri za ta gudu wurin Mama Halima, ba za ta zauna a dakin ko wace mata ba. Ita kanta tana addu’ar Allah Ya sa su je wurin Malamin kuma aikin na shi ya yi tasiri.

Wannan kenan, bari mu leka Asma’u a can hotel.

*****

ASMA’U

Farkawarta bacci ta ji babu abin da take so sai gida, zaune ta yi saman gadon tana jin kamar ta janyo hasken asuba, minti-minti take duba agogon da ke jikin wayarta. Yanzu ma da ta duba karfe uku daidai ya nuna mata.

Dogon tsoki ta ja, hade da mikewa ta shiga tattara duk wani abu da ta san nata ne. Sai da ta tabbatar ta tattare komai kafin ta shiga wanka hade da dauro alwala, raka’a biyu na nafila ta gabatar, kafin ta shiga wayarta ta lalubo qur’an App din ta shiga karantawa. tana kan sallayar har aka kira sallahr shiga, kafin ta yi Raka’a’tanul fijr, ta dora da sallahr asuba.

Tana idarwa ta sagala Jakarta a kafada. Tsaye ta yi a cikin ɗakin, ji take idan ta zauna kamar lokacin ba zai yi sauri ba. Idan ta gaji da tsayuwar sai ta shiga safa da marwa. Karfe shidda daidai, ta fito daga dakin hade rufewa. Reception ta nufa hade da ajiye musu key din, kafin ta nufi kofar fita daga hotel din, wanda ya yo daidai da fitowar wani matashin saurayi tare wata budurwa, wacce za ta iya yin sa a da Asma’un.

“Maryam!” ta ji ya kwaɗa kira, ganin ba kowa a wurin sai ita kadai ne ya sanya ta juya.

“Yanzu don Allah da wucewa za ki yi ba za ki tsaya mu gaisa ba. Mimi (ya kira sunan wacce suke tare) ga Queen da na ce miki mun yi school tare”

Wacce aka kira da Mimi ta dan saki fuska hade da kallon Asma’u lokaci daya kuma ta ce mata “Ina kwana”

Kamar wawuya haka Asma’u ta amsa, tana kallon yadda saurayin ke nuna da gaske ya santa har kira mata sunan wasu yake yi, ya ce suna ta tambayarta, ko ya ce yanzu suna ina.

Wata tambayar ta amsa wata kuma ta yi shiru.

Sai da ya matso daf da ita ya ce “I’m sorry please, don Allah ki jira in yi ma wannan rakiya, just 2mns.”

A, hankali ta ce “Sauri nake yi.”

“Na sani, ko nawa kike so wlh zan ba ki”

Cike da mamaki take kallon shi kafin ta ce “Ita kuma waccan ɗin fa?”

Ba tare da ya kalli inda Mimi take ba ya ce “Na sallame ta, ko ban sallame ta ba, zan yi hakan saboda ke”

“Ikon Allah” ta fada a bayyane, a zuciyarta kuma tana mamakin yadda maza da kuma mata suka mayar da zina ba komai ba. Ko lafiyarsu ma bassa tunani, kawai daga ganinta bai san tana lafiya ko a’a ba, shi dai kawai ya biya bukatarshi.

Yau kam ta ga bariki, yana tare da mace amma tsabar iya bariki ji bi yadda ya loda ta a kwali, yana fada mata wai ga friends din shi da suka yi school tare ita kuma ta yarda.

“Sanya min lambarki, kin san yanzu ba ni da ita.”

Wayar ta karba, hade da sanya mishi lambar da ita kanta ba ta san ma yadda aka ya ta rubutata ba.

“Na kira a kashe.” ya yi maganar idanunshi a kanta

“Eh na kashe ne”

“ok” ya amsa ta lokaci daya kuma yana saving lambar.

Daidai lokacin motar Lukman ta shigo kwana, tun da ya ga Asma’u kuma sai ya rage gudu, har ya tsaya saitinta.

Ba ta san waye ba, sai da ya sauke glass din, tun kafin ya ce ta shiga, ta zagaya daya bangaren ta zauna.

“Don Allah ki bude wayar zan kira ki”cewar mutumin

” To, “ta amsa, bukatarta kawai ya rabu da ita, shi ya sa ma ta shiga motar Lukman tun bai yi mata tayi ba

Cike da mamaki Lukman ke kallon ta kafin ya ce” Ina za ki je da sassafe haka? “

” Gids”ta amsa kai tsaye

Da wani mamakin yake kallon ta sannan ya ce “Gida kuma? To shi kuma waccan waye?”

“Ban san shi ba”

Da wani mamakin yake kallon ta, kamar ba zai kara magana ba, sai kuma ya ce “Shi ne kuma kika ba shi lamba”

“Ni ma ban san wace irin lamba ce na ba shi ba, kawai so nake ya kyale ni”

Har zuwa lokacin kallon mamaki yake mata, ba tare da ya janye idanunshi a kanta ba ya ce “Kika ce gida za ki?”

Kai ta daga alamar eh.

“Yanzu ke don Allah da wani dalili bai taso ni ba, haka zan zo in samu ba ki nan, kin yi min adalci kenan?”

Komai ba ta ce ba, illa wasa da yatsun hannunta da take yi

“Ina zan kai ki yanzu?”

“Inda zan samu motar Jama’a”

“Ke ƴar Jama’a ce?”

Kai ta gyaɗa alamar eh

“Ina son shiga ciki zan dauki flash ne”

Kamar za ta yi kuka ta ce “Don Allah ka kai ni tashar tukun, wlh ji nake kamar in tafi da ƙafa”

Murmushi ya yi tare da fadin “Kodai kiranye aka yi miki ne?”

“Mene ne haka?” ta yi saurin tambaya

Yanzu kam dariya mai sauti ya yi hade da juya kan motar zuwa hanyar da ya fito.

Har suka isa tashar hira suke, hirar da ma fi yawanta a kan yadda ya shaƙu da kuma yadda zai yi kewarta ne, yayin da ita kuma take yi mishi godiya a kan dawainiyar da rika yi da ita har kawo yanzu da take zaune a cikin motar shi.

Bayan sun isa, da kanshi ya yi mata booking ya biya kudin kafin ya dawo wurin motarshi inda take tsaye tana kallon duk zirga-zirgar da yake yi.

“Are you alright?” ya yi tambayar lokacin da ya iso ganin yadda ta yi shiru kamar akwai abin da ke damun ta.

“Na ƙosa in tafi ne” ta fadi abin da shi ne ya fi damunta, don da gaske ta ƙosa a tafi din

Karo na ba adadi ya yi dariya tare da fadin “Anya ba kirannye aka yi miki ba”

“Me ye shi?” ta kuma tambayarshi a karo na biyu.

“Manta kawai” ya fada hade da gyara tsayuwarshi kafin ya ce

“Haka za ki tafi ba ki ba ni lambar ki ba, kuma ban san sunan ki ba?”

Yadda ya yanke hukuncin maganar a shagwabe sai ya ɗan ba ta dariya, Sai dai ba ta yi ba, a maimakon hakan ma hannu ta mika mishi alamun ya ba ta wayar.

Lambobinta du biyun ta sanya mishi, na, tsoho da kuma sabon layinta ta mika mishi bayan ta yi saving.

Ya karɓi wayar idanunshi a kan sunan da ta rubuta a hankali ya ce “Asma’ullahil-husna. Sunayen Allah kyawawa. You deserved the name. You’re very beautiful. Kina da kyawu mai daukar hankali da rikita duk wani namiji. Ciki har da ni. Ina jin kamar in kai ki gidan nan da kaina, daga nan in miƙa kokon barata na auranki. Da gaske Asma’u ina sonki.”

Dole ta janye idanunta zuwa wani ɓangare, saboda ba za ta iya jure kallon da yake yi mata ba.

Lukman ya cancanci a so shi, daga lokacin da ta taho zuwa yanzu shi ne namiji na farko da ya kasance tare da ita, ba tare da ya yi mata maganar banza ba, wannan kaɗai ya isa ya nuna mata nagartarshi.

<< Abinda Ka Shuka 16Abinda Ka Shuka 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×