Skip to content
Part 22 of 28 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

HAFSAT.

Allah bai karbi addu’ar Hafsat saboda dai ta wayi gari a cikin masu rai a safiyar Lahadi, sai dai numfashin ne kawai ya bambanta da gawar, iya wahala tana cin ta.

Duk gidan babu wanda ya leko ta, sai Babanta ne y leko ta yanzu misalin karfe takwas da rabi na safe, saboda rahoton da Danliti ya kai mishi cewa ya kawo ma Tatuwa dumamen tuwonta na safe ya same ta ta mutu.

“Hassatu! Ke Hassatu!!” haka Malam Ayuba ya rika kwada mata kira daga bakin kofa

Da kyar ta yaye bargon, fuskarta ta bayyana, daga inda yake tsaye yana iya hango yadda idanunta suka kumbura luhu-luhu, fuskar kuma ta yi jawur alamun ta sha kuka ta gaji.

Baki bude alamun mamaki ya ce “Ke din ubanki kashe kanki kike son ki yi. Ko lokacin da uwarki Hinde ta rasu ba ki yi wannan kukan ba. Sai wani can da hanya ko ta rafi ba ta hada ku ba, kike neman kashe kanki a kanshi” ya karasa maganar cike da bacin rai, lokaci daya kuma ya shiga dakin, yana kallon abincin da aka jera mata ba ta ci ba, ko hannu ma ba ta dora musu ba.

“Ke!” Ya daka mata tsawa, “Wato abincin ma babu wanda kika ci, to tashi ki cinye su don uwarki, wai kodai rade-radin da ake yi na yaron nan yana lalata da ke gaskiya ne? To idan ba haka ba wannan tashin hankalin har ina?”

“Tashi na ce miki?” ya kuma da ka mata tsawa.

Ta tattara duk ragowar kuzarinta ta tashi zaune, ko sakan goma ba ta yi ba da tashin, ta fadi Liya saman gadon. Faduwar da ya tabbatar ma kanshi suma ta yi.

Cike da tsoro yake kallon yadda wuyanta ya lankwashe, jiki ba kwari ya gyara mata kwanciyar, cikin daga murya ya ce “Kuluwa, kawo min ruwa da sauri, yarinyar nan suma ta yi.”

Rufe bakinshi ba da jimawa Inna Kuluwa da sauran yaran gidan suka yiwa dakin tsinke.

Tun yana yayyafa mata ruwan, har ya shiga kwara mata shi a rude yana fadin “Innalillahi, kar dai yarinyar nan mutuwa ta yi.”

Suna tsaka da jimamin Mama Halima ta yi sallama, cike da tsoro a fuskar Malam Ayuba ya ce “, Ba dai muryar Halima nake ji ba?”

Yaran suka nufi kofar dakin don lekawa, zuwa lokacin tuni Mama Halima ta karaso kofar dakin.

” Ba dai ita din ma ta mutu ba?” cewar Mama Halima a firgice, ganin yadda mutanen dakin suka yi cirko-cirko, ga kuma Hafsat shimfide saman gado, babu marabarta da gawa.

Duk wani kuzari nata sai ta neme shi ta rasa, shiga cikin dakin ma sai ya gagare ta, ta yi tsaye a wurin tana sauraron yadda su Malam Ayuba ke kare kansu.

Malam Ayuban ne ya ce “Wlh kin ganta nan, bamu san ba ta da lafiya ba, kin ga abincinta duk ta ki ci, tun da yaron nan ya rasu take kuka”

Inna Luba ta ce “Wlh babu irin lallashin da ba mu yi wa yarinyar nan ba ta ki shiru ta ki cin abinci. Kin ga abincinta nan a jere, duk lokacin da aka gama sai an kawo mata”

Inna Kuluwa ta amshe da “Har cewa aka yi ta tashi a kai ta asibiti ta ce ita kanta ne kawai ke ciwo, ashe yarinyar nan ba ta da lafiya sosai, yanzu haka muna shirin kai ta asibiti sai ta suma”

Wani yawu mai Mama ta hadiye, sannan ta karaso cikin dakin jiki a sanyaye, hannun Hafsat ta daga gami da sakewa, Sai ya fadi yaraf saman gadon.

Ta juyo kan Malam Ayuba tana fadin “Ayuba sai da na ce ma ka ba ni yarinyar nan, rikewa zan yi ba karɓe ma zan yi ba ka ƙi amincewa. Yanzu ga shi nan ta mutu, kamar yadda mahaifiyarta ta mutu cike da bakin ciki”

Malam Ayuba ya kankance idanu yana fadin “Dakata Halima, yau ko Yayar ma ba zan ce ba. Me kike nufi? Mune muka kashe Hafsat din? Kin fi ni sonta ne? Ƴata ce fa.”

“Na fi ka sonta, kai kuma ka fi ni son abun da uwarta ta mutu ta bar mata.” kai tsaye Mama Halima ta fadi maganar

“To je ki ma haka ne, akwai uban da ya isa ya hana ni yin iko da kayan Hafsat? Halima fitar min gida. Fitar min gida na ce miki. Ki bar ni in ji da abin da yake damuna. Duk kokarinmu akan yarinyar nan ba mu iya ba. Yanzu abinci kala nawa kika samu a gabanta. Kuma duk ba cikin dakin kika same mu ba”

Uffan ba ta ce mishi ba, ta cicciɓi Hafsat daga saman gadon zuwa jikinta

“Ina za ki je da ita?”

Ya yi saurin tambaya

“Asibiti” Mama Halima ta amsa mishi lokaci daya kuma tana dora Hafsat a bayan ta

“Ai tun da abun naki ya zama wulakanci babu inda za ki je da ita, aje min ƴa, idan ma ta mutu dai Ƴata ce. Ke duk lokacin da kika zo sai an yi bala’i da ke.”

“Ayuba, kai kanka ka san na fi ka danyen kai, koda zan dauki Hafsat ba zan hada da abun da ba ka son in taba din ba. Ita kadai zan dauka in bar ma abun da kake so din. Bare ma ni zan nemar mata lafiya ne kawai in maido ma ita.”

“Ba a son neman lafiyar ta ki, aje min yarinya.” ya fada a tsawa ce ganin tana niyyar fita daga dakin

“To za ka kwantota a bayana idan ka isa?” ta yi maganar cikin zafi.

“To zan yi karar ki kuma”

“Ina jiran sammace”

Ba ta jira jin wani abu ba ta fice

Inna Luba ta ce “Wannan mata akwai balaƴaƴ’iya wlh. Ni idan na ganta gabana ma har faduwa yake”

“Yo Halima kuma, ai ni da ita na yi kishi a gidan nan ba da Hinde ba. Matar da mu ka yi bugi-in – buga. Kin ga wannan hannun ita ta karya min shi” Cewar Inna Kuluwa

Ido Inna Luba ta fitar waje tana fadin “Haka take?”

“To ta ma fi haka, duk abin da zai taba Hinde ba ta son shi, kamar ita kadai ce ta san dadin ƴar’uwa, ai waccan matar yar bala’i ce”

Malam Ayuba ya ce “Aiko yau zan yi maganinta, wlh kararta zan yi.”

Ya kai karshen maganar hade da ficewa daga gidan a fusace.

*****

RUMASA’U

Dawowar Aibo, ba karamin takura ne a wurin ta ba, kullum cikin bauta mishi take, kuma ba godi bare na gode.

Sai baƙaƙen maganganu zagi da cin zarafi.

Karamin aiki ne a wurin shi ya dakko daga kan Baba Malam zuwa kanta ya zage su tsab.

Ga horon yunwa da yake mata, yanzu ba ta abinci sai na saye, dari biyu kacal yake ba ta daga safe har dare. Kuma ba ta isa ta aika gidansu ta ce a ba ta abinci ba. Babu ma yaran aiken, saboda a hankali ya kori duk wasu kananan almajirai da suke zuwa wurin ta. Kannenta ma tsoron shi suke yi, shi ya sa idan yana gidan basu cika zuwa ba sai da dalili.

Itace yake yo wa na siyarwa, iyakacinshi kawai dakko itacen ya kawo gida, daga nan duk wata sauran wahala kuma tata ce.

Ta faskara, ta kasa, ta kuma siyar. Idan ruwa ya sakko komin dare ita ce ke fitowa ta kwashe su zuwa dakin sanwarta. Kuma idan ya dauke gari ya sha iska, ita ce ke fito da shi don ya sha iska.

Wannan shiga da fitarwar kadai ya isa ya ramar da ita, bare azo ga batun hantara da zama da yunwar da take yi.

Wani sabon zalunci da ya  ɓullo mata da shi shi ne kwashe kayanta na lefe yana siyarwa, wai ai na shi ne ba nata ba.

Yanzu ma a gabanta ya takarta duk kayan shafar da ke cikin akwatin ya zuba a leda ya fice dasu.

Zuwa yanzu ya siyar da turmi biyar da kayan shafa kenan. Saura turmi bakwai, eanerwears, takalma, gyale da kuma jaka guda daya.

Baki ta tabe cikin jin zafin abun, sannan ta mike zuwa waje, saboda ta san yanzu yara za su fi fara zuwa sayen iccen.

Haka ta shiga faskara manya-manyan, ta gama sannan ta kasa iya yadda ya kayyade mata, saboda idan ya yo iccen, ya kan ce mata naira kaza yake son a siyar. Kuma ya kan kayyade kudin da ya san akwai wahala iccen ya kai wannan kudin, shi ya sa wani lokaci sai da dabara take samu iccen ya kai kudin da ya ce. Wani lokaci kuma sai ta tsakuri wani abu a cikin kudin abincinta.

Wannan kenan

AG & ASMA’U

Zaune yake a gefen gado, yayin da ya tallafe kumatunshi da hannayenshi biyu. Kallo daya za ka yi mishi ka fahimci yana cikin damuwa.

Damuwar da zuciyarshi ta kasa boyewa har fuskarshi za ta iya labarta wa mai kallon shi.

Yau kwananshi uku kenan, amma bai samu abin da ya zo nema ba, ya rasa abin da ya fi tayar mishi da hankali, tsakanin rashin ganin Asma’u da kuma rashin lafiyar yarinyar shi Nawwara.

Yanzu haka suna asibiti ba ta san waye a kanta ba.

Idan har bai samu abin da yake so yau ba, Sha Allah gobe zai bi jirgin karfe takwas zuwa gida. In ya so ya bar komai a hannu Tumbaga kamar yadda sojan ya fada mishi Tumbaga shi ne sunan shi.

Wayarshi da ke ƙasan pillow ta shiga vibration, daga yadda yake zaune ya mika hannu haɗe da janyo ta.

Bai san dalilin da ya sanya gaban shi faduwa ba, ganin sunan Tumbaga

“Sir! Idan babu abin da kake yi, ka zo yanzu mun samu wani officer mai wannan sunan, kuma yana da ƴa Asma’u” cewar Tumbaga, bayan AG ya daga kiran.

“OK! Ok! OK!!….” Haka AG ya rika maimaitawa da sauri, lokaci daya kuma ya mike tsaye yana kallon kayan jikinshi. Yadi ne baƙi mai taushi irin toyobon nan babba, tun misalin karfe shadaya na safe da ya yi wanka ya sanyasu, bai fita ba sai da aka kira sallahr azhur, kuma tun da ya dawo sallahr yake zaune bai motsa ba.

Mai nema a duhu bare an haska, ai 10mns yana kofar barrack din.

Cike da zolaya Tumbaga ya ce “Kana son yarinyar nan fa”

AG ya murmusa kadan kafin ya ce “Sosai, da ka san process din da na bi kafin yanzu, da ka kara gasgata ina sonta”

“To Allah Ya sa ta karbe ka, ka san mata”

Gaban AG ya fadi, saboda shi bai taba kawo ma kanshi ma Asma’u za ta iya kin shi ba, sai yanzu da Tumbaga ya fada. “Bari fada don Allah”

Tumbaga ya yi dariya yana fadin “Za ta so ka ma Sir!”

Ba tare da wani bincike ba suka shiga cikin barrack din, AG ya bude ido yana kallon yadda aka zuba gine-ginen cikin tsari gwanin sha’awa

Babu abin da ya fi daukar hankalinshi irin yadda aka sassaka jiragen sama kala-kala, ko wane kuma da sunan shi.

Haka yay ta nazarin wurin da suke wucewa har zuwa lokacin da suka isa kofar wani office da aka rubuta *WING COMMANDER*

Tumbaga ne ya kwankwasa duk da kofar a bude take. Daga can ciki aka ce “Yes come in”

Tumbaga ne kawai ya shiga, ya sarawa na kan teburin sannan ya shaida mishi yana tare da bakon.

Alhaji Abdullahi ya umurci da ya shigo da shi. Tumbaga ya kuma juyawa suka shigo tare da AG.

AG ya kwashi gaisuwa sannan ya zauna kan kujerar da Alhaji Abdullahi ke nuna mishi, Tumbaga kuma ya fita don ya basu wuri.

Ta ka san ido AG ke satar kallon Alhaji abdullahi, wanda a shekaru zai ta san ma shekaru 55-57. Dogo ne sosai mai madaidaicin jiki. Yana da kwarjini sosai gami da cikar kamala. Idan ba karya idanunshi ke fada mishi ba, ya kan ga yanayin fuskar Asma’u kadan a kan fudkarshi

“Aka ce kana nema na?” Alhaji Abdullahi ya katse mishi tunanin

Nutsuwarshi ta tattara wuri daya kafin ya ce “Eh to, ku san haka ne, amma ina cigiyar wata yarinya ne Asma’u Abdullahi. Kuma an tabbatar min a nan cikin barrack din suke, kafin suka tashi zuwa cikin gari, sakamakon gini da mahaifinta ya yi”

Tun da ya fara maganar Alhaji Abdullahi ke kallon sa har zuwa lokacin da ya kai karshe.

“Kai a ina ka san Asma’un?”

Zama AG ya gyara sannan ya ce “A Nasara ne”

Alhaji Abdullahi ya kankance idanunshi a kan AG yana fadin “Kai ne ka kama mata daki a hotel?”

Gaban AG ya fadi, Sai cike da mamaki yake tunanin ya aka yi ya san an kamawa Asma’u daki a hotel.

Cikin sauri ya shiga girgiza kai kafin ya ce “Wh ba ni ba ne”

“A Nasara, a ina ne ka san ta to?” Alhaji Abdullahi ya kuma jefa mishi wata tambayar

Busassun labbansa ya lasa kafin ya ce “A tasha na gan ta za ta shiga mota”

“Ita ce ta ba ka address din nan kenan?”

Ganin dabara na neman kare mishi ne ya sa ya ce “A’a, na nemo address din ne a media”

Idanu Alhaji Abdullahi ya zubawa AG a kokarinshi na gano gaskiyar maganar da yake fada mishi

“Ni ne Abdullahi. Kuma ni ne mahaifin Asma’u.

 Idan babu damuwa  ka tashi mu je inda Asma’un take, ka ga ko ita ce wacce kake nema din.”

Ku san a tare suka mike, Alhaji Abdullahi ya yi gaba, AG ya bishi baya har cikin mota.

Babu bata lokaci suka fice daga cikin barrack din.

*****

HAFSAT

<< Abinda Ka Shuka 21Abinda Ka Shuka 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×