Skip to content
Part 24 of 26 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

*****

HAFSAT

Mama ba ta shigo asibitin ba sai karfe biyu.

Lokacin Hafsat zaune take gefen gado tana murza mai, sakamakon wankan da ta fito.

Shigowar Maman duk sai suka zuba mata ido, ko zama ba ta yi ba Juwairiyya ta ce “Ya aka karasa Mama?”

Murmushi Mama ta yi tana duban Hafsat wacce jikinta ya yi sanyi ta ce “Yo me fa zai faru, komai lafiya, idan Hafsat din ta ji sauki za a mayar da ita”

Duk suka yi shiru, alamun basu so jin hakan daga Mama ba

“Ya jikin Hafsat?” Mama ta tambayi lokaci daya kuma tana taba jikin

“Don Allah Mama ki yi hak’uri a kan abin da Babana ya yi miki?” cewar Hafsat kamar za ta yi kuka

Gefen gadon Mama ta zauna hade da dafa kafadarta sannan ta ce ” Babu komai ban kuma ji komai ba. Ba yau muka fara da Ayuba ba, wurin ƴansandan ne kawai ba mu taba zuwa ba. Amma Sha Allah zan rika kiyaye duk abin da zai kawo irin wannan abun. Saboda na san ba za ki ji dadi ba.”

Hawayen da dama ko wane lokaci a kusa suke, su ta fara fitarwa ba tare da ta ce komai ba

Juwairiyya ce ta ce” Don Allah ta ya Hafsat za ta warke, kullum kuka, ko abinci ba ta ci sosai. Sai kuka kawai “

Da ido Mama ta bi Hafsat cike da tausayawa, sai kuma ta janyo ta jikinta ba tare da ta ce komai ba.

A hankali take bubbuga bayanta alamun lallashi kafin ta ce” Ki yi hak’uri kin ji Hafsat, na san abin da yake sanya ki kuka, kuma na san dole ki yi kuka. Amma ki sani yanzu ba lokacin kuka ba ne. Lokaci ne na jajircewa hade da addu’ar ga wadanda kike yi ma kukan. Ki daina kuka kin ji. Har yanzu akwai abin da zai sanya ki yi farin ciki. Ni din dan zan yi kokarin ganin cewa kin yi farin ciki. Abin da kawai nake son ki gane shi ne za ki kara hakuri sosai a kan wanda kika yi a baya. Na so ki dawo wurina da zama, amma saboda wasu dalilai na hak’ura. Sai dai zan taimaka miki ganin ba ki jigata ba”

Hafsat dai kukanta take yi a hankali, yayin da Mama ke kara lallashinta, da fada mata maganganu masu  kwantar da hankali.

Sai yamma ta koma gida, tsawon wuni kuma abincin saye suka rika ci.

Nabila kuma sai karfe takwas da Tajuddeen ya kawo abinci ya tafi da ita

Safiyar da ta cika kwana biyu a asibitin likita ya ba ta sallama, shi ya sa ma Juwairiyya ta yi waya cewa ba sai Nabila ta kawo abinci ba, gasu nan za su taho gida.

Ita ce ta tattare kwanukan abincin ta zuba su cikin kwando.

Sai da ta kammala tattare komai sannan ta dubi Hafsat da ke zaune gefen gado ta ce “Za ki iya tafiya ai?”

Kai ta jinjina alamar eh.

Yau ne karon farko da ta fito wajen asibitin tun da aka kawo ta, saboda akwai toilet a cikin dakin.

Shi ya sa ta bude ido sosai tana kallon yadda tsarin ginin asibitin yake gwanin sha’awa.

Lokacin da suka iso reception ne ta dora idanunta a kan hoton wani mutum mai cikar zati.

Daga kasan hoton an rubuta *Dr Asad Abdulmumin (Magajin Gari)*

Sauran hotunan kuma da ke manne jikin bangon reception din duk certificate din yabawa da asibitin ne. Da kuma lasisin da ya samu daga hukumomin lafiya da ke nuna ingancinshi.

Bayan sun fito Hafsat ta ce “Asibitin nan yana da kyau da kuma girma.”

Juwairiyya ta ba ta amsa da “Ai duk garin nan, babu wani asibiti mai kyanshi. Ke zan iya ce miki duk yankin nan ma”

“Na ga alama, amma akwai kudi na sani”

“Ba kuma sosai ba fa, idan kika danganta shi da sauran asibitocin kudi, wadanda ko rabin shi ma basu kai ba. Amma za ki ga suna charges sosai fiye da shi”

Kai Hafsat ta jinjina tare da fadin “Na ga hoton wani mutum, wai Dr Asad, shi ne mai asibitin?”

“Eh shi ne, babban likita ne, ɗan gidan magajin gari ne”

“Ai na gani a rubuce. Ni sunan na shi ne ma ya min dadi. Wai Asad.”

Juwairiyya ta yi dariya mai sauti kafin ta ce “Ki sanya wa yaron ki na fari”

Hafsat ta ma ta murmusa kadan kafin ta ce “Idan ana maimaita sunan Aunty Ju ai sunan Ya, Nasir zan ta sanyawa yarana.”

Kafin Juwairiyya ta ba ta amsa, wata farar moto mai kyau ta shigo cikin asibitin sakamakon bude mata gate da aka yi.

“Yauwa to kin ga wannan motar da ta shigo yanzu ita ce ta Dr Asad din. ” cewar Juwairiyya

Hafsat ta kara ware ido sosai tana kallon motar da ke kokarin parking, a, wata farfajiya mai kyau. Wacce da alama dama don ita aka tanadi farfajiyar

“Don Allah Aunty Ju jira in gan shi. Ina son ganin shi” cewar Hafsat a lokacin da take dakatawa da tafiyar da take yi.

Juwairiyya ma sai ta tsaya, lokaci daya kuma tana dariya.

Suna tsaye a wurin, kofofin motar guda biyu suka bude.

Wasu maza biyu suka fito, tsawonsu daya, haka yanayin kirar jikinsu ma.

Dukkansu sanye suke da baƙin wando, gami da farar shirt din riga mai dogon hannu. Stocking da kuma baƙin talkami covern da ke ƙafarsu ba karamin karawa kwalliyar tasu kyau ya yi ba.

A jere suka fice daga wurin parking din, yayin da suke jefa kafa a tare cikin nutsuwa, har suka shige ta wata kofa.

Cike da takaici Hafsat ta ce “Kamar sun san ina son ganin fuskokinsu, basu juyo ba”

Juwairiyya da ke ta dariya ta ce “Gaskiya basu duba miki ba”

Karon farko da Hafsat ta yi dariya tana fadin “To a cikin su biyun waye Asad din”

Ta yi tambayar lokacin da suke ficewa daga gate din asibitin

Juwairiyya da ke kokarin tare keke ta ce “Ina zan sani, da dai ace sun waigo ne, yadda suka juyawa bayan nan komin su iri daya ai ban iya ganewa. Tun da dama ba wani farin sani na yi mishi ba”

Kadan-kadan suke taɓa hira a mashin din har suka iso gida.

Wanka ta fara yi hade da canja kaya zuwa doguwar riga mara nauyi, ta sha tea kadan da bread gami da magungunanta sannan ta kwanta.

Zamanta gidan Mama ba karamin kewa ya cire mata ba, ji take kamar ta yi ta zama. Kowa a gidan kokarin faranta mata yake yi.

Sai dai ranar lahadi da misalin karfe goma na safe, suka dauki hanyar Maƙera don mayar da ita gida. Tajuddeen ke ta tuki yayin da Mama take a gefen shi. Hafsat, Juwairiyya da Nabila kuma suna a baya.

Suna taba yar hira.

Yayin da Hafsat ke kallon gonannaki da suke wucewa. Shukoki sun fito gwanin sha’awa.

Can kasan zuciyarta kuma, wani irin babu dadi take ji, karon farko da ta yi tafiya ta dawo garin Makera babu Innarta babu Ya Nasir. Karon farko da za ta je ta rayu da kanta ba tare da wani a gefen ta ba. Karon farko da za ta rayu babu wanda zai saurari kukanta bare ya share mata hawaye.

Tun da Tajuddeen ya yi parking a kofar gida, yara suka yayyame motar suna kallo, wasu kuma Hafsat din ce abun kallonsu. Kamar ya suka fara ganin ta.

Ba yabo ba fallasa su Inna Kuluwa suka tare su, aka gaisa a mutumce, suka yi wa Hafsat sannu da jiki kafin suka koma kan harkokinsu.

Su kuma dakin Inna suka gyara, hade da saukewa Hafsat tsarabarta, suka ba su Inna Kuluwa tasu. Sannan suka fito don zuwa gidansu Nasir gaisuwa.

Da sallama suka shiga gidan, Hajiya Mariya mahaifiyar Nasir ta amsa, lokaci daya kuma tana yi musu kallon rashin sani.

“ku shigo” ta fada lokacin da take takawa a hankali zuwa cikin falonta

Babban falo ne sosai, da aka baje shi da jan carfet da kuma kujeru jajaye. Labulayen ma jajaye ne. Sai dan karamin tv a kan farin stand na glass

Mama ce kawai ta zauna a kan kujera, amma Tajuddeen da su Nabila duk a kan carfet din suka zauna.

Bayan sun gaisa ne hade da yi mata gaisuwa Mama ta ce “Hajiya na ga kamar ba ki shaida mu ba”

“Wlh kuwa ƴan nan, ban shaida ku ba, yi hak’uri sai kin ba ni sani”

“Sunana Halima, ni yayace a wurin marigayiya Hinde mahaifiyar Hafsat, can gidan Malam Ayuba mai kayan miya”

“To! To!! To!!! Allah sarki yanzu kam na gane ki. Ko ba Halima ta can Dawuri ba”

“Ni fa Hajiya”

“Allah sarki. Na gode, Allah Ya saka da alkairi”

“Babu komai Hajiya, ai tun kwana biyu da rasuwa na zo gaisuwa, Sai kuma na riski Hafsat ba lafiya. Ba ta san ma inda kanta yake ba. Shi ne na dauke ta zuwa asibiti”

“Allah sarki. Yarinyar Hinde ko? Mutuniyar Nasir. Tana ina ban ganta ba”

Mama ta nuna Hafsat wacce ta aje kai kasa hawaye na diga, yau kam ji take kamar babu wani sauran dadi ko farin ciki da ya rage mata a duniya. Yau dai ta tabbatar da mutuwar Nasir, saboda ga shi ta ji daga bakin mahaifiyarshi. Sabanin baya da take ganin kamar idan ta zo za ta same shi.

Hajiya ta bi Hafsat da kallo, Sai ta kasa rike hawayenta, cikin muryar kuka ta ce “Nasir ya sha fada min yana tausayin Hafsat. Komai ya samu akwai ka son Hafsat a ciki. Ko sati ba a yi ba, na yi mishi maganar aure, Sai ya ce min in yi hak’uri Hafsat yake son ta kammala makaranta. Tausayinta yake ji. Baya son kowa ya aure ta sai shi.”

Ta dakata saboda yadda kuka ya ci karfinta, Sai da ta daidaita muryarta sannan ta dora” Na ce mishi ai namiji mijin mace hudu, ya ce min ba zai yi mata kishiya ba har abada. Lallai Nasir na sonki Hafsat ya tafi da tausayinki, gami da burirruka masu yawa a kanki”

Mai neman kuka, bare an, jefe shi da gatari, ai tuni Hafsat ta duke kan carfet din ta shiga rera kuka kamar a ranar ya rasu.

Falon duk sai ya koma kuka ake yi, idan ka dauke Tajuddeen da ya fice zuwa waje zuciyar babu dadi.

Haka suka fito da Hafsat tana kuka, kuka sosai har da suƙewa.

Koda suka koma can gida aikin lallashinta suke yi.

Sai misalin karfe biyar suka baro garin Maƙera, kowa zuciya babu dadi. Tun ba Hafsat ba, da take ta kuka kamar an ce mata shi ne karshen matsalolinta.

AG

Tun da ya koma hotel din sai ya kasa tsugum, gani yake kamar ya ga samu kuma ya ga rashin. Ko ya ga tsulum ya ga kuma tsame. A daddafe ya yi sallahr la’asar.

Ya fito daga cikin hotel din hade da daukar napep drop, da kanshi yake kwatanta mishi inda za su je, har suka yi burki a kofar gidan Aunty Hajara. Wani sanyi dadi ya lullube shi ganin gidan bai bace mishi ba.

Bayan ya sallami mai keken ya shiga kwankasa kofar a hankali

Kamar mintuna biyar ya ji ta kun mutum, alamun ana zuwa.

Gabanshi ya shiga faduwa, saboda bai san me zai ce ba, idan Aunty Hajara ce ta bude kofar kamar dazu.

Gabanshi ya tsananta faduwa lokacin da ya ga kofar tana budewa, har fuskar Asma’u ta bayyana.

Da sauri ta saki kofar hade da ja baya, har yanzu dama ba ta warware daga rudanin da ta shiga dazu ba, yanzu kuma ta kara kicibis da fuskar shi.

Ba zuciyarta kadai ba, hatta yaron da ke cikinta harbawa yake yi.

Yadda ta aje fasta tana kallon shi baki bude kamar ta samu hoto ya sanya shi ya dan matso kusa da ita yana fadin “Na ji dadi da ke ce kika bude kofar, wurin ki na zo.”

“Waye kai wai? Me kake so a wajena? Ya aka yi ka san Babana?”

Duk tambayoyin lokaci daya ta jere su kuma a rude”

“Sunana Abubakar Garba..”

“Ba sunanka tambaye ka ba.” ta yi saurin katse shi

“To sonki nake yi, ko shi Mk din bai fada miki haka ba, tun ranar da na fara ganin ki?”

Cike da mamaki take kare mishi kallo kafin ta ce “Ya aka yi ka san Babana?”

“Saboda a wurin shi zan nemi auranki Asma’u”

Idanun ta lumshe cikin rashin sanin abun yi, kafin ta bude su a kanshi tana fadin “To ni ba na sonka, ba kuma zan aure ka ba. Don Allah kar ka kara zuwa wurina” Ta kai karshen maganar hade da kokarin rufe kofar

Da sauri ya kai hannun shi kan kofar yana fadin “Idan kika rufe bamu gama magana ba, zan ci gaba da zama a nan har zuwa lokacin da za ki bude kofar ki fito mu yi maganar da ta kawo ni”

“Menene ya kawo ka? Ba maganar aurena ba, kuma na ce ban yi.” a fusace ta yi maganar

Yadda ya kafe ta da idanu ne ya sanyata saurin janye nata, lokaci daya kuma tana sassauta fushin da ke kan fuskarta.

Siririn murmushi ya yi kafin ya ce “Kina da fada. Irin ku kuma kuna da saurin mance abu da yafiya”

Komai ba ta ce ba

“ko ba haka ba ne?”

Yanzu din ma ba ta amsa ba

Tsayuwarsa ya gyara idaninshi a kanta ya ce “Ba a neman aure cikin aure, ga shi dole kin sanya ni na yi hakan, zuwa fa na yi kawai mu yi magana”

“Mene ne?” ta tambaya a dan fusace

Wayar shi ya mika mata yana fadin “Ki sanya min lambarki a nan. Saboda gobe zan tafi gida, yarinyata tana asibiti kwance.”

Ta dago kai hade da kallon shi. Ba tare da ta ce komai ba ta karbi wayar da yake miko mata, ta sanya mishi lambar tata.

Ya karbi wayar hade da sauke numfashi a hankali. Yana fadin” Kar ki ki daga kirana, idan ba haka ba zan dawo”

Yanzu ma komai ba ta ce ba.

“Shi kenan je ki ciki, ki cigaba da kumburin”

Dama abin da take so kenan, da sauri ta rufe kofar zuwa cikin gida. Ita har yanzu ma ba ta yadda shi din mutum ba ne

Abin da ya yi mutane basu cika yin shi ba. Ko ya aka yi ya samu address nata oho.

*****

<< Abinda Ka Shuka 23Abinda Ka Shuka 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×