Skip to content
Part 25 of 26 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

RUMASA’U

Misalin karfe biyu na rana kanenta Anas ya shigo kanshi dauke da kwano.

Daga cikin daki ta amsa sallamar shi, kan kujera ya zauna bayan ya mika mata kwanon.

Fita ta yo da sauri ta wanki hannunta, saboda dama jira take yi, ba ta karya ba tun safe.

Bayan ta zauna kan kujerar ta shiga cin danwaken da sauri, a kokarinta na yi tsoron kar Allah Ya turo Aibo kamar daga sama ya loda mata rashin kirki.

“Yaya Ruma ina wayarki?”

“Tana wurin caji” ta amsa mishi cike da takaicin tuna ɓata wayar tata

“Wata waya na gani a wurin Malam Hudu kamar ta ki. Ya ce min a wurin Aibo ya saya”

Danwaken da ta sanya a baki ya yi tsaye cak, shi bai wuce ba, kuma ba ta fito da shi ba.

“Yaushe ka ganta?”

“Ya kai kwana biyu, da mu ka je gonar yamma”

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, saboda ta tabbata wayarta ce Aibo ya dauke ya siyar, kuma ko kwandala bai ba ta ba.

Bayan kayan lefe da samirunta kenan har da wayarta. Duk irin yadda take jin yunwa haka ta rufe danwaken ta boye shi inda Aibon ba zai gani ba

Sosai zuciyarta ke mata zafi, wata zuciyar fada mata take ta fadawa Yayanta Usman in ya so shi kuma ya fadawa Alaramma, a kwato mata wayarta.

Haka nan take biyewa Anas suna surutu, amma Sam hankalinta baya jikinta,hanyar da wayarta za ta dawo hannun kawai take nema.

Sai da aka kira sallahr la’asar sannan Anas ya tafi.

Tafiyarshi ba jimawa kuma Aibo ya dawo da damin iccenshi

Kamar kodayaushe ita ta gyara itacen ta kasa.

Shi kuma ya yi wanka ya fice.

Bayan ta yi sallah da wanka, kujera ta dakko ta dasa a tsakiyar gidan.

Duk yaron da ya shigo sayen iccen sai ta je babu, sannan ta zare mishi ido ta ce kar ya kara dawowa, idan kuma ya dawo sai ta ci uban shi.

Har dare kasuwar iccen ta tashi Ruma ba ta siyarwa da kowa iccen ba. Haka ta kwashe tas ta shigar kitchen.

Tun da ba za ta  iya fito na fito  da shi ba, wannan ita ce hanya ma fi sauki da za ta rage takaicin da yake cusa mata. Musamman na dauke mata waya.

Sai hadaya na dare ya shigo gidan, tun da ta ji shigowar shi ta tashi zaune daga kwanciyar da take. Saboda ya hana ta bacci idan bai dawo ba, wai ba sai ya yi ta tashin ta ba, idan zan karbi cinikin iccen shi.

Hannu ya mika mata ba tare da ya ce komai ba

“Ba a yi ciniki ba yau” ta fada a hankali

“Ban gane ba a yi ciniki ba, kina nufin babu wanda ya sayi iccen?”

Kai ta daga alamar eh, ba tare da ta yi magana ba.

Da sauri ya juya zuwa kitchen, Sai ko ya samu iccen a nashe alamun ba a siya din ba

Mamaki ya cika shi, ta ya za a ce yau din babu wanda ya zo sayen icce kamar ya zagi sama. Abu da har nema ake yi. Kullum ya yo sai ya kare.

Uffan bai ce mata ba ya haye gado ya kwanta, ita kuma ta koma kan doguwar kujerar da take kwance tun farko ta kwanta. Wani bangare na zuciyarta fes.

Daga wannan ranar Ruma ba ta kuma siyar mishi da iccen kamar da ba, bai fi ta yi mishi cinikin 200-300 ba, wani lokacin ma ba ta yi.

Shi ya sa iccea cike da kitchen saboda kullum sai ya fita.

Bangaren Aibo kuma ya fi karkata a kan ko Alaramma ne ya yi mishi wani siddabarun. Shi ya sa yanzu ba shi da customers.

Yau ma kamar kullum tun safe ta kasa iccen, amma har ya fita zuwa yo wani iccen bai ji ko yaro daya ya yi sallama zai saya ba.

Abin da bai sani ba shi ne, yanzu yaran tsoron zuwa gidan suke yi, saboda barazanar da Ruma ke yi musu.

Har zuwa la’asar da ta yi wanka gami da sallah, ba ta yi cinikin ko kwandala ba. Zuciyarta fes saboda kannen ta sun kawo mata abinci ta ci.

Don shi tuni ya ci ganye, ba ciniki to ba kudin abinci. Ita kuma har ta koyi rike yunwar safe sai rana ta karya, da dare ma ana fakar idanunshi a kawo mata abinci.

Tana tsaka da shara tsakar gida wasu yara suka yi sallama.

Ta amsa sallamar hade da dagowa tana kallon su

“Icce za mu saya, ni na dari uku, wannan kuma na dari biyu”

Fuska ta hade sosai tare da fadin “Babu.”

“Wannan fa, ko ba na siyarwa ba ne?” Daya daga cikin yaran ya tambaya

Ta nufo a fusace tana fadin “Ba na siyarwa ba ne, idan kuma kuka sake dawowa sai na ci ubanku” ta kai karshen maganar hade da jefa musu tsintsiyar da ke hannunta

Su ka yi hanyar kofa a guje, wannan ya sa suka yi karo da Aibo, da yake niyyar shigowa kanshi dauke da wani damen iccen.

HAFSAT

Safiyar monday, Misalin karfe bakwai da kwata na safe ta fito tsab cikin shirin zuwa makaranta.

Mutanen gidan duk suna cikin daki, idan ka dauke Babanta da ke cikin garken awaki, ba ta san me yake yi ba. Saboda tun asuba ta tsabtace garken, ta kuma zuba musu abincin da ta san za su ci har zuwa lokacin da za ta dawo makaranta.

Akwai almajirai biyu da Nasir ya dauka suke yo wo awakin ciyawa kullum, shi ya sa lokacin da ta tafi Dawuri basu galabaita ba.

“Sannu Baba.” ta fada lokacin da ta zo daidai saitinshi, saboda tun misalin karfe 6:30am ta gaishe su

“Yauwa Hassatu. Daga yau zuwa Laraba, ina son ki kwashe kayan dakin Innarkin can, saboda masu gyara za su zo. Za a gyara simintin dakin a kuma yi wa dakin shafen farar ƙasa.”

“To” ta amsa shi. Zuciyarta cike da mamakin dalilin da ya sa ya yi maganar.

A kan hanyar sai tunaninta ya zama biyu, ga na maganar Babanta, ga kuma kewar Yayanta Nasir.

Kai tsaye wurin mai shayi ta nufa, ta mika mishi 100 ta ce ya sanya mata.

Bayan ya hada ya kulle mata a leda hade da mika mata.

Jakarta ta bude wurin da ta aje bread din da ta gutsuro a cikin wanda Mama ta siyo mata.

Misalin 7:35am ta isa gate din makarantar, ganin Uncle Najib rike da bulala, ya tabbatar mata da ranar shi ke da duty.

Tun da ta sako kafafunta yake kallon ta

Sosai ta ɗashe, ta kara haske, yayin da fuskarta ta bayyana ramar da ke jikinta.

Yadda ya yi tsaye yana kallon ta ne ya sanyata tsarguwa, a duburce ta ce “Good morning uncle”

A sanyaye ya ce “Morning”

Har ta saba shi, Sai kuma ta tsinkayi muryarshi yana fadin “Zo nan Hafsat!” ta juyo a hankali zuwa wajen shi

Cike da tausayinta ya ce “Ba a fada miki a gida ina ta zuwa neman ki ba?”

Kai ta girgiza alamar a’a, waye ya damu da ita, bare ya damu da masu neman ta, har ya fada mata sun zo ba ta nan.

“Ina kika je?”

“Ba ni da lafiya ne, shi ne aka kai ni asibiti”

Ya sauke ajiyar zuciyar da ta bayyana, kamar ba zai ce komai ba, Sai kuma ya ce “Dama na je miki gaisuwa ne, I’m sorry please, Allah Ya gafarta mishi”

Ba tun yanzu take son yin kuka ba, tun da ta baro gida zuwa makaranta idanunta ke maiko.

Sai ko hawayen suka zubo sharr.

Idanunshi ya lumshe, baya son ana kuka a gaban shi Sam.

“Wuce ki tafi” ya fada da kasalalliyar murya.

Haka ta juya sabbin hawaye na kara zubo mata.

RUMASA’U

Tana kokarin daukar tsintsiyar da ta jefa musu Aibo ya shigo, aya bai diga mata ba, ya sauke itacen kanshi, ya kuma siyarwa da yaran icce ya sallame su.

Ruma kam tun da ya shigo ta shige dakin, ba ta son ya yi mata jaraba a gaban yara.

“Munafuka, algunguma, macuciya mai baƙin hali” abin da ya fara fada kenan lokacin da ya shigo dakin.

“Wato ashe ke ce ke korar masu siyen iccen ko, ki ce ba ki yi ciniki ba. Munafuka yau dai idanuna sun kwashe min ai”

Komai ba ta ce ba, sai baki da take zumburawa.

Ba ta yi aune ba ta ji saukar mari fas! A kuncinta, kafin ta dawo hayyacinta, ta rika saukar duka ko ta ina, da rarrafe ta fito tsakar gidan, tana kuka a hankali. Yayin da shi kuma ke kara sauke mata buhunnan tijarar da ke kanshi. Ranar kam gori ta sha shi. Babu abin da bai kira ta da shi ba.

Haka ta ci kukanta ta more babu mai lallashi.

Bai fita gidan ba sai bayan sallahr isha’i, saboda masu shigowa sayen icce. Wannan ya sa ba a samu kofar shigo mata da tuwon darenta ba.

Haka ta kwanta, amma fir bacci ya ƙi zuwa, ga ciwon jiki, ga idanunta daya da ko gani ba ta yi, ga kuma yunwa. Yayin da zuciyarta ke ta mata sake-saken abubuwa marasa kyau.

Tana kwancen ta ji shigowarshi, har ya gama buruntunshi ya kwanta ba ta motsa ba.

Ba za ta iya sani ko karfe nawa bna dare ba, amma tabbas ta san dare ya yi, saboda masallacin Alaramma da suke karatun sun raba tsakiya, wannan ya tabbatar mata kodai karfe daya da rabi na dare ko karfe biyu.

Cikin sanɗa ta mike hade da gyara ɗaurin zanen ta, ta saka hijabinta tare da takalminta.

A hankali ta fita zuwa kitchen inda tarin iccen Aibo yake, ta shiga daukar ko wanne tana juyawa har ta zaɓi wanda take ganin ya yi mata.

Da sanɗa ta kuma komawa dakin, tsaye ta yi, tana kallon yadda ya yi rub da ciki yana ta sauke minshari.

Ta jima tsaye a kanshi tana kara tace ingancin abin da take son yi.

Rufe idanunta ta yi hade da daga iccen ta shimfida mishi shi a tsakiyar baya.

Kafin ya gama tantance abin da ke faruwa ta kuma aje mishi wani. Ganin ya mike zaune a kidime, ya sanyata yada katon iccen ta yi waje da mugun gudu.

*****

HAFSAT

Safiyar laraba haka Baba ya hana ta zuwa makaranta, wai sai ta kwashe kayan dakin nan tas.

Ya tattaro kannenta manyan suka da shi kanshi, suka shiga kwasar kayan suna tsauna su a cikin zaure. Tun Hafsat na yi abun zuciyarta na kuna har ta gagara rike hawayenta. Tana kwashe kayan tana kuka. Ko jikin Malam Ayuba, damuwarshi dai a kwashe.

Sai wajen shadaya na safe suka kammala, zuwa lokacin gidan ya haukace, saboda zauren bai dauke su kayan ba. Wasu duk a waje aka aje su, musamman gadajen biyu da kwanoni.

Zuwa azuhur kuwa sai ga masu gyara, biyar na yamma sun ga komai daki ya fito fes.

Hafsat dai na tsakar gida tana kallon Ikon Allah.

Ba ta tashi sannin Allah da girma yake ba, sai da dare ya yi. Ko wace mace ta tsince yaranta zuwa daki, a ka bar ta a tsakar gida, daga karshe ta koma kitchen ta kwanta, sai dai cikin dare ruwa mai karfi ya dakko, wanda ya tilasta mata fita kitchen din, saboda bambancinsu da waje kadan ne.

Zaure ta koma, nan ma feshin ruwa ya kuma koro ta. Ta shiga bubbuga kofar dakunan su Inna Kuluwa nan ma babu wanda ya bude. Ta koma kofar dakin Innarta duk da ta san a rufe yake. Sai ta tsugunna a wurin ta fashe da kuka, kuka take ruwa na dukanta, sai da kankara ta fara kwalarta sannan ta nufi dakin kaji ta rarrafa ta shige.

Haka ta tsugunna a ciki ta ci gaba da rera kukanta, ba a dauke ruwan ba sai gaf asuba.

Da rarrafe ta kuma fita, kayan jikinta ta cire ta shanya kan igiya, ta yi alwala ta shiga zaure ta sanya uniform din makaranta, Sai dai kuma babu wurin sallah, saboda gidan kaf a jike yake. Haka ta yi tsugunne a zauren, kuka ne har ta gaji da yi sai dai ajiyar zuciya.

Sai da Inna Luba ta bude kofa, sannan Hafsat ta roke ta ta san mata wurin sallah.

Yau kam tun bakwai ta fita zuwa makaranta, biscuit Kawai ta saka cikin jakarta, saboda har zuwa lokacin akwai ragowar biscuit din da Nasir ya siya mata. Akwai ma kwali guda ba ta fasa ba wanda Mama ta siya mata. Tana da garin kwaki ma da kuli da kakke, duk Mama ta sawo mata.

Babu dalibai sosai a makarantar lokacin da ta isa, haka ta wuce ajinsu, bayan ta zauna ta fitar da biscuit dinta, tana ci tana kukan abin da ya faru jiya.

Zuwan su Farida ne ya dan rage mata damuwa, sai dai har aka tashi kanta ciwo yake yi.

Uncle Najib kuma bai shigo ajinsu ba, Sai dai ta hange shi kawai daga nesa.

Bayan an tashi haka suka jero kamar ko wane lokaci, su Farida ne ke ta hirarsu yayin da Hafsat hankalinta ma baya wurin, tunanin inda za ta kwanta yau take yi.

Sun shigo cikin kasuwa ne ta ji Ni’ima na cewa “Hafsat Maman Iyabo na miki magae”

Da sauri ta juyar da ganinta wurin shagowMaan Iyabon

“” Ka zo” cewar Maman Iyabo lokaci daya kuma tana ya fito Hafsat din da hannu.

Su Farida suka wuce ita kuma ta shiga cikin shagon

“Heee! Tana ta nemanka, tana ta nemanka ba ta ganka ba, ina ka je”

“Ban lafiya ne?”

“Eyyah! Sorry, ba ta san gidanka ba, da ta je ta gano ka” cewar Maman Iyabo cike da tausayi

“Me ya sa ba ka zuwa karbar abinci yanzu?”

Shiru Hafsat ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Kafadarta Maman Iyabo ta dafa cike da tausayi ta ce “ka rika zuwa kullum kana karbar abinci, ba sai ka biya kudi ba ka ji ko”

Kai Hafsat ta jijjiga alamar to, hawaye na gangaro mata.

Maman Iyabo ta zubo mata wani abincin ta mika mata.

Haka ta iso gida tana kuka, ji take kamar yanzu ne aka yi mata mutuwa.

A tsakar gidan ta zauna,  ta dibarwa kannenta abincin ta basu, ta ci ragowar.

Bayan ta gama dakin kajin ta shiga gyarawa, saboda zuwa yanzu ta fahimci nan ne dakin ta.

Dakin yana da girma sosai, kawai dai ba za ta iya mikewa tsaye ba.

Sai da ta sharo shi tsab, ta dauki katifa daya ta shigar ciki, duk wasu kayan amfaninta sai da ta shigar dasu ciki, shi kenan daki ya yi fes, matsala daya ba a mikewa, ba a shiga a tsaye ba kuma a fitowa a tsaye, bayan nan ba shi da wata matsala, saboda ba ya yoyo. Sabanin dakin su Inna Kuluwa da komai kankantar ruwa sai wani wurin ya yi zuba.

Sai ta tsinci kanta a mai farin ciki, sabanin jiya da ta wuni da bakin ciki da bacin rai.

Dare na yi na rarrafa ta shige dakinta, saboda dama ba ta dawo ta samu kajin ko daya ba. Ba ta san ya aka yi dasu ba.

Bacci ta yi sosai sai asuba ta farka. Ta yi alwala ta shimfida tabarma a zaure ta yi sallahrta, kafin ta yi shirin tafiya makaranta.

Lokacin da ta dawo ne ta iske mutane musamman makota, an daura manyan tukwane, wai abincin yan tarewar amaryar Malam Ayuba za a yi.

Ko a jikinta, haka ta rika shiga da fita a dakinta, wasu suka tausaya mata, wasu kuma abun ya basu dariya.

Zuwa dare yan tarewa suka iso da Amarya, abun mamaki har da su DJ suka taho, aka rakashe sosai, sai wajen 11pm Kowa ya watse.

<< Abinda Ka Shuka 24Abinda Ka Shuka 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×