Skip to content
Part 26 of 26 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

*****

ASMA’U

Zaune take a kan entrance, komai ba ya yi mata dadi, wani lokaci sai ta ji ina ace idan ta zo haihuwa kawai ta mutu ta huta.

Ba ta fuskantar tsangwama ko kyara amma ji take yi duk ta muzanta.

Duk lokacin da ta kalli turtsetsen cikin ta, Sai ta ji wani irin bakin ciki idan ta tuna ba ta hanyar aure aka same shi ba.

Ita da Mk babu magana mai dadi, kullum cikin fada, hade da dora mata laifin yadda ta bari cikin ya kai wannan lokacin. Wannan abun ba karamin kara bata mata rai yake ba. Shi ya sa ma yanzu ko kiran shi ba ta yi. Abin da ta sani kawai shi ne da zarar ta haihu lafiya, yaro ya isa yaye shi kenan aikinta ya kare, da kanta za ta je har garin su ta dire mishi yaro ko yarinyarshi.

Wayarta da ke kan cinya ce ta shiga vibration alamun kira na shigowa, ta zuba wayar ido, tana kallon sunan AG da yake yawo a kan screen, har kiran ya yanke ba ta daga ba.

Zuciyarta ta kasa aminta da shi, ta ya mutum zai ganta a hotel kuma ya biyo ta har gida wai yana son auranta. Ita kam ba ta amince da shi n gaskiya yake mata ba. Kila dai wata bukata tashi yake son cimmawa.

Mutum daya kullum zuciyarta ke fada mata ta kira, sai dai ta kasa ya n hakan, ba za ta iya ƙirga ko saunawa ta yi attempting din kiranshi ta fasa ba.

Ahmad namiji da ko wace mace za ta yi kewa idan ba ya tare da ita. Duk yadda yake kulafuncinta ko sau daya bai taba kiranta ba tun bayan da ta baro gidan. Wannan ya tabbatar mata da sosai ranshi ya baci da abin da ta yi.

Kiran da ya kara shigowa ne ya sanya ta saurin mayar da hankalinta a kan wayar. Yanzu kuma Lukman ne

“Na shiga uku!” ta fada cike da damuwa

“Don Allah ku bar ni in ji da abin da ke damuna mana, Haba!” ta kai karshen maganar kamar za ta yi kuka, lokaci daya kuma ta mike tsaye dakyar hade da kashe wayar baki daya. Wadannan kiraye-kirayen wani lokaci kara bata mata rai suke yi.

AHMAD

Misalin karfe hudu na yamma, aka sallame sallahr la’asar a masallacin kofar gidan Galadima.

Ba jimawa mutanen da ke cikin masallacin suka rika fitowa daya bayan daya. Har zuwa lokacin da Asad da Ahmad suka fito a tare. Suka shiga gaisawa da mutanen da ke kofar masallacin, abin da ya dauke su tsawon mintuna talatin. Saboda akwai wadanda suke yin gaisuwa da kuma rokon iri.

A tare suka jera zuwa cikin gidan.

“Asibiti zan koma fa” cewar Asad lokacin da ya fito da wayarshi daga aljihu yana kallon sakon da aka turo mishi.

Komai Ahmad bai ce ba. Wannan ya sa Asad ya kuma cewa “Za mu je tare ne?”

Kai ya girgiza alamar a’a

Gaisuwar da hadimai mata da ke cikin gidan ke mika musu ne ya hana Asad kara yin magana har suka isa falon Hajiya.

Dukkansu kasa suka zube, suna gaishe ta, ta amsa idanunta a kan Ahmad. Ta mayar da kallon ta kan Asad tana fadin “Abokinka kuwa yana cin abinci Asad, ko idanuna ne, amma kullum ya zo gida sai in ga gara bara da bana”

Asad ma ya mayar da kallon shi kan Ahmad wanda ya yi zugum ya ce “Ba idanunki ba ne Hajiya, dazu ma sai da wani abokinmu ya fada.”

Kafin Hajiyar ta ce wani abu Asad ya yi saurin daukar wayar shi da ke gaban aljihu, yayin da yake kallon Hajiya ya ce “Zan je asibiti, akwai tiyatar da zan shiga”

Hajiya ce kawai ta yi mishi fatan nasara, Ahmad dai komai bai ce ba.

Bayan fitar Asad din ne Hajiya ta ce “Ahmad! Kullum sai ka ce min komai ya wuce, bayan kullum jikinka yana nuna komai din bai wuce ba. Ta ya kake tunanin hankalina zai kwanta, kullum ina ganin ka kamar figaggar kaza?”

Kai ya aje kasa ba tare da ya ce komai ba, wannan ya da ta dora “Ko so kake kowa ya san abin da ya faru ne? Duk wani abu da muke ganin zai sanya hankalinka kwanciya Ahmad yi muke yi. Ko kuma mu goya ma baya ka yi. Amma har yanzu ka ki samawa kanka salama. So kake wata cutar ta kama ka, ka ga sai ka jefa mu cikin tashin hankali. Kalli yadda kake wa aikinka rikon sakainar kashi Ahmad. Ka ce ba ka son garin Jama’a, mahaifinka ya shiga ya fita da kudi da rokon Allah aka mayar da kai Maina. A Mainar ma ka ki aikata abun kwarai, yau kana gida jibi kana wurin aiki. Wane irin abu ne haka? “

Yanzu din ma shiru ya yi bai ce komai ba, kuma ta san idan za ta kwana tana fadan ba zai ce komai din ba. Wani lokaci sai ta ji kamar ta dauke shi ta goya a baya, ko ta rungume shi ta rika jijjihashi tana lalllashinshi

Tsawon wata takwas kenan da abun nan ya faru, amma har yanzu ya kasa cire abun a ranshi, kullum sai karewa yake kamar kudin guzuri, Sai tsawo kamar ramar rani.

Kwadon zogalen da ya ce yana so ta aje mishi a gaban shi hade da mika mishi ruwan wanke hannu. Tana fadin “Akwai ragowa cikin fridge idan Asad din zai ci”

Da Bismillah ya fara cin zogalen bayan ya wanke hannu , yayin da Hajiya ke ta kara mishi nasiha cikin tausasan kalamai

Abin da ba ta sani ba shi ne, Sam yanzu ba ya jin dadin komai, ciki har da rayuwar, wani lokaci sai ya ji Ina ma a kore shi aikin. Ko kuma a kashe shi ya huta.

Duk lokacin da ya tuna abin da Asma’u ta yi mishi sai ya ji kamar ya bude wa kowa wuta. Idan kuncin ya yi mishi yawa ne yake zuwa gida ya ga ƴan’uwa sai ya ji dan sauki a zuciyarshi. Kamar yanzu din ma da duka-duka satinshi biyu a Maina ya dawo gida.

“Ka je barga din ne(fada)”

Girgiza kai ya yi alamar a’a

“Amma dai na fada ma Galadima ya ce ka rika shiga kana zama, ko ba komai za ka ga yadda abubuwa ke gudana”

“Ni hayaniya ce ba na so” ya fada a hankali

“Ahmad to ya za ka yi, tun da shi ne gadonka”

Ya ture bowl din zogalen gefe yana fadin “That is the reason Hajiya, Sam ba na son sarautar nan, da ranka, amma an kosa ka mutu saboda kawai wani ga gaje ka. Haba wane irin abu ne wannan. It’s means fa ka tsarewa mutum wuri.”

Murmushin manya Hajiya ta yi, kafin ta ce “Ai kyawun ɗan kwarai ya gaji ubansa Ahmad. Duk wani jinin sarauta burin shi ya gaji sarautar. Ka ganni nan mace da ace a zamaninmu irin na da ne, da abin da zai hana ban hau kujerar Wazircin Karofi ba mutuwa na yi.”

Cike da mamaki yake kallon ta, Sai kuma ya murmusa karo na farko. Amma bai ce komai ba.

Wannan ya sa ta dora da” A matsayinka na babba kuma namiji a gidan nan, lallai ka sanyawa ranka cewa duk ranar da ba ran mahaifinka kai ne za ka gaje shi. Saboda ba zamu Bari wannan sarautar ta bar gidan nan ba. “

A karo na biyu ya kara murmusawa, ita ma sai ta yi murmushin tare da fadin” Har zogalen ya ishe ka? “

Kai ya daga alamar eh, yana kuma kallon bowl din zogalen.

” Ba ka ci da yawa ba Ahmad. Don Allah ka saki jiki ka rika cin abinci. Wlh ba na jin dadin ganin ka haka. Kullum a bushe. Babu kwarjini irin na da, da cika ido. To wace mace ce ma za ta so ka yanzu a haka don Allah”

Yanzu kam murmushin da ya yi har sai da jerarrun fararen hokaransa suka fita. Shi yanzu a lissafinshi ma ai babu aure. Ba ya jin ma zai kara yin wani aure. Na ji dadi Ai shi ne gari. Haihuwa daya kuma horar ƙaniya in ji mata.

Hajiya ta katse mishi tunani da fadin “A karo na biyu Ahmad ka je ka ga Mami, kila a wannan karon ku daidaita, ina yi maka sha’awar auran ta, Sha Allah ba za ka yi kuka da zabin nan ba.”

Ya dago daga sunkuyar da kan da ya yi kasa yana kallon ta. Shi ya rasa abin da ta hango a wurin Mami. Shi yarinyar ba ta taba burgeshi ba. Kuma ba ya jin zai iya zaman aure da ita ko na minti daya.

Jin bai ce komai ba ya sa ta dora” Duk kalli sa’aninka Ahmad har da masu yara hudu. Kalli Asad da aka yi auranku rana daya matarshi na da cikin yaro na hudu, amma kai shiru, abun yana damuna sosai ” yadda ta karasa maganar cike da damuwa ne ya sa ya ce” Komai yana da lokaci Hajiya. Ni ma lokaci yana zuwa sha Allah. Amma don Allah ki cire batun Mamin nan”

“Wai me ya sa ba ka son yarinyar nan ne, ga ta kyakkyawa, ga ilmi, ga tarbi ya. Ahmad me ye matsalar ta”

Kanshi ya sosa mara yalwar gashi sosai ya ce “Ba komai wlh. Ni kawai zaman auran ne ba zan iya yi da ita ba.”

Rike da haɓa alamun mamaki Hajiya ke kallon shi, sannan ta ce “To Allah Ya zaɓa ma fi alkairi. Amma don Allah ka yi kokari kar a rufe shekarar nan Ahmad ba ka yi aure ba”

Yanzu kam murmushi ya yi ba tare da ya ce komai ba.

Sai ma ya mike yana fadin “Zan je in dan watsa ruwa Hajiya”

“To” ta amsa shi, yayin da jikinta yake a sanyaye gami da shi. Dama da ya aka samu ya yi auran farin. Ga shi yanzu za a kara dorawa daga inda aka tsaya.

RUMASA’U

Gudu take yi, irin gudun nan na ceton rai, abin da ba ta sani ba shi ne Aibon ma bai biyo ta ba, har zuwa lokacin bai gama gasgata abin da ya faru ba.

Kamar saukar ungulu haka ƴan cikin masallacin suka ga Ruma ta fado, wannan ya sa dole aka dakatar da karatun saboda kukan da take yi a kidime.

A kidimen suka shiga tambayarta lafiya. Cikin kuka ta rika nuna kofar masallacin da hannu tana fadin “Bugu na zai yi”

Sai a lokacin suka ga kumburin da ke idon ta.

Cike da zafi Alaramma ya ce “Sha’aibun ne ya yi miki wannan dukan?”

Kai ta jijjiga alamar eh.

A fusace ya fice daga masallacin yayin da sauran ƴan cikin masallacin suka rufa mishi baya, kar ya je ya yi ba daidai ba. Saboda yana da zafi sosai

Tun da ya shiga cikin gidan yake durawa Aibo zagi, a tsakar gida ya samu wani faskare ya fada dakin Ruma, yana fadin “Don ubanka ni za ka tozarta, ni za ka tonawa asiri, ni za ka nunawa ban isa ba. Waye kai don ubanka? In ba ka ƴa da hannuna, in biya maka sadaki, in yi maka lefe in ba ka wurin kwana ka rasa abin da za ka saka min da shi sai rashin mutunci. Yau jinina ne abun wulakantawa a wurin ka Aibo”

Yana fadan hade da shirga mishi faskare da ke hannunshi a duk inda ya samu. Yayin da Aibo ke ihu sosai yana neman taimako hade da ba Alaramma hak’uri.

Daidai lokacin su Malam Balarabe suka shigo, suka rike Alaramma suna ba shi hakuri yayin da Alaramma ke kara harzuka. “Me ye ban yi mishi ba? Hatta ciyar da matar waye ke ciyar mishi da ita? Ashe kai ba mai rufa min asiri ba ne? Saboda kaddara ta fada ma yarinyar shi ne ta zama a bar wulakantawa. To sakarta. Ka sake ta na ce.”

“A’a kar a yanke hukunci cikin fushi mana” cewar Malam Balarabe

“Wlh sai ya sake ta. Sannan ya kwashe komin shi ya bar min gida”

Aibo dai kuka yake gami da magiya, saboda ya san wannan rikicin zai iya sanadiyyar lalacewar rayuwarshi. Ba a sa-in-sa da Alaramma.

Kamar ba dare ba, nan- da-nan sai mutane suka fara taruwa. Yayin da rikicin ke ta kara tsawo. Saboda Alaramma da kanshi ya shiga daki ya tattaro duk kayan Aibo ya watso waje.

Bala’i har asuba, dalilin da ya sa dole Aibo ya yanke igiyar auransu daya. Sai dai kam cike yake da nadama. Ba nadamar sakin Ruma ba, nadamar abin da zai je ya zo.

<< Abinda Ka Shuka 25

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×