Wannan ya sa na ji gara ya ji da abu daya, wato gori da kuma tsangwama, amma bayan nan sha Allah ba zai rasa komai ba. Duk wani gata na duniya ni din nan zan ba shi. Daga yanzu da ya zo duniya Aunty zan diga ɗan ba, na fafutukar gina mishi rayuwarshi. Da ace za ku yi min izni, da na yi nesa da ku, zuwa wani waje na daban.”cikin kuka sosai take maganar
Kukan da ya sanyaya gwiwar Aunty Hajara sosai, saboda ta san wacece Asma’u, yarinya ce mai tarbiya, girmama manya da kuma tsentseni. Tana da ilmi sosai a ka wane bangare. Kamar yadda ta fada, su kansu basu taba kawo wannan abun kunyar a kanta ba.
“Ba na son in dorawa kowa wahalar shi Aunty. Ciki har da uban shi, ni din zan yi mishi komai da iznin Allah.”
“Ke har yanzu yarinya ce Asma’u, da uba ake ado ai. Koda za ki rike yaron nan dole uban shi ya san da zaman shi. Ba mu kadai za mu sha bakin cikin abin da ya faru ba. Ya kamata shi ma iyayenshi su ɗanɗana. Tabbas yaron nan bai yi komai ba. Kuma ni kaina zan taya ki rikon shi. Amma maganar tafiya wani wuri ki aje ta a gefe. Kyan ɗa ya gagara gidan uban shi. “
Shiru Asma’u ba ta ce komai ba, wannan ya sa Aunty Hajara ta ce” Me kike so a siyo mishi. Kune yaran zamani, kuma ke ce kika yi aure cikin ƴangayu masu kudi, kin fini sanin abin da ake siyawa yaro, don haka ki rubuta ni kuma ina zuwa sai in mika musu list din. Idan kudin basu fi karfinmu ba “
Mikewa Asma’u ta kuma yi hade da dakko, jotter cikin jakarta, ta zana kaf abin da take so ta mikawa Aunty Hajara.
Ta bi list din da kallo har zuwa karshe kafin ta ce” Asma’u kina da hankali kuwa, keke har biyu na gani, ga na zama ga na tafiya, ga durowa, ga hanger. Duk me za ki yi dasu? Wannan list din fa ya fi karfin 500k”
Kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce “Aunty ko 1million ne a sawo, akwai kudi a cikin account din”
Aunty Hajara ba ta kara cewa komai ba, ta mike zuwa dakinta don shirin zuwa kasuwa.
Bayan fitarta ne Asma’u ta dakko wayarta, hade da bude WhatsApp din ta. Kan lambar Mk ta hau. Hoton Babyn wanda ya fi ko wane kyau, kuma kamannin Mk din suka fito sosai ta dakko. Ta yi caption kamar haka
_2dys in the world_
Ta tura mishi. Ta fita hade da leka sauran groups tana ganin wainar da ake toyawa.
After 10mns da tura sakon sai ga kiran Mk din ya shigo.
“kin haihu?” abin da ya fara tambaya kenan bayan ta daga
“Eh” ta amsa kamar ba ta so.
Ya ɗan yi jim, alamun yana tunani kafin ya ce “Kina lafiya ko?”
Kamar yana gabanta kai kawai ta daga alamar eh
Suka kuma yin shiru.
“Astagfirullah!” ya fada a hankali cikin cunkusasshiyar murya.
“I’m so sorry Dear. Yanzu ya za a yi?”
“Ina son Babyn” ta yi saurin fada
“Kenan za ki rike?”
“Tare da kai”
“Na sani, and you know I will do everything for you all Asma’u. Har gobe ina sonki. Na ce miki mu yi aure, kin ce a’a. Ya kike so in yi?”
Shiru ba ta ce komai ba, wannan ya sa ya ce “Za mu yi magana.”
Daga haka ya yanke, lokacin da ya kira wayar ba haka ya so ya fada mata ba. Amma yana jin muryarta duk sai ya daburce, ya ji tausayi gami da kaunarta sun taso mishi sabo. Ya rasa wace irin kaddara ce a tsakaninsu da Asma’u. Ba ya iya yin komai wanda ranta baya so. Da zarar ya ga ranta a bace to shi kenan ya gama samun nutsuwa.
Account din shi ya shiga ya tura mata 50k. Tausayinta yake ji, ta rasa igiyar auranta ta dalilin shi, ga shi kuma ya bar ta da ta tashin hankalin rainon ciki da rainon yaro.
Sai bayan ya yi duk abin da yake ganin za ta yi farin ciki ne, sannan
tashin hankali gami da fargabar da ya ji tun farkon ganin hoton da ta mishi suka dawo mishi sabbi.
*****
HAFSAT
Yau Juma’atu babbar rana, ranar da kan biɗa kan samu, a ranar ne Hafsat su ka kammala Exam din 3rd Term in SS2. Yanzu kuma hankalinsu duk ya koma ne a kan bitar abubuwan da zasu gabatar a filin taro ranar graduation.
Musamman Hafsat da ku san za ta yi performing din abubuwa da yawa.
Akwai debate, quiz, career day, Sai Kuma cultural day. Da za su yi representing na al’adun kasarsu.
Shi ya sa ba ta da lokaci, ko wane lokaci cikin bita take.
Bayan sallahr la’asar ta dauki buhun ciyawarta don yo wa dabbobinta ciyawa, Sai dai tana fitowa suka yi kicibis da Uncle Najib.
Dama irin wannan ranar ce ya fi kawo mata ziyara
“Ina za ki je?” ya tambaya tun kafin ta gaishe shi
Kai tsaye ta ce “Ciyawa zan je”
Kai ya jinjina, kafin ya ce “Ba a samun masu siyarwa ne?”
“Eh ana samu, amma yanzu yamma ta yi akwai wahala a samu.”
Tsayuwarshi ya gyara sosai kafin ya ce “Sau nawa zan fada miki idan kina da matsala kai tsaye ki fada min. Ni ba kamar Nasir ba ne, ban san duka matsalolinki ba. Kawai ina magance wadanda na sani ne. Musamman wadanda suka shafi makaranta.”
Shiru ta yi komai ba ta ce ba
“Ta ya za ki samu lokacin bitar abin da aka koya miki, ga shi lokaci yana ta tafiya.”
Yanzu din ma shiru ta yi, sai wasa da take yi da bezar buhun da ke hannunta.
“Daga yau ba na son fita ciyawar nan, musamman da yamma.”ya kai karshen maganar hade da ciro kudi cikin aljihu ya mika mata
” Idan sun kare ki yi min magana “
” Na gode “ta fada a hankali bayan ta karbi kudin.
Ledar hannushi ya mika mata yana fadin” Sune kayan da za ki sanya, idan za ki yi representing fulani culture “
Hannu ta kuma mikawa ta karba, lokaci daya kuma tana bude Ledar hade da lekawa
” Saura ƙwarya, na sanya ana yi mata kwalliya ne, idan an gama za kawo miki, sannan gobe kin san dai za ku je school karfe goma ko? “
Kai ta jinjina alamar eh.
” To ya yi. Je ki ajiye kayan ki zo in raka ki ciyawar”
Ba ta jima a gidan ba ta fito, suka jera, ba ta sanin yana magana sai sun kadaice, amma a school kamar wani kurma, ga tsare gida babu wasa ko kadan.
Haka ya nade wando gami da hannun rigar shi ya rika tugar ciyawar, abin da sosai ya ba Hafsat mamaki, wani lokaci har tsaye take tana kallon yadda yake tugar ciyawar babu ƙyanƙyami ba komai.
Ita ce ke nuna mishi wacce dabbobin ba su ci, saboda tana sanya su zawo. Shi kuma a nan ya ƙara ilmi, bai san akwai ciyawar da dabbobi bassa ci ba. Ya dauka ko wacce ci suke.
Sai kawai ya nishaɗantu da zuwa ciyawar, da ya san akwai nishadi haka, da tun asali ya rika zuwa yana mata rakiya. Sai dai ya gano nishadin a kurarran lokaci. Saboda nan da sati daya ma baya kauyen.
Ba zai iya misalta yadda yake ji gami da tafiyar ba, ji yake ina ma shekara biyu ake yi. Ko kuma dai yana rayuwa ne a Dawuri, wanda a kullum idan ya so zai iya zuwa ya ganta, ya kuma koma gida. Sannan zai samu saiƙin cika ƙudurorinshi a kanta.
Duk yadda Hafsat ta so hana shi daukar buhun ciyawar ya ki. Haka dauka hade da dorawa saman kai.
Suka fara tafiya, yana gaba tana bin shi a baya, tun tana kumshe dariyarta har ta kufce mata
Da sauri ya juyo yana kallon yadda take dariya, sosai, abin da bai taba gani ba. Shi kukanta kawai ya sani.
Sai kawai ya yi murmushi ya juya ya ci gaba da tafiya, saboda ya fahimci abin da ya sanya ta dariyar.
Har kofar gida ya kai mata, ita kuma ta karasa shigarwa gida tana mishi godiya.
*****
MK
Tun daga lokacin da Asma’u ta turo mishi sako hade da hoton sabon Babynshi bai kara samun nutsuwa ba. Ya tufka ya kuma warware. Ya haɗa biyar amma ta ƙi ba shi goma, yadda ya wuni zur hankali a tashe haka ya kwana ko runtsawa bai yi ba. Da alama shi a ranar ne ya yi tashi naƙudar.
Babban tashin hankalinshi shi ne Asma’u ta kawo mishi yaron nan, bai san ina zai tona rami ya shige ba saboda kunya.
Yadda ake ganinshi da mutumci, da kuma yadda mahaifanshi suke mishi kallon ma fi kololuwa a hankali, idan wannan abun ya bayyana mutumci ya zube
Ba iya mutumcinshi ba, har da zuriyarsu. Sannan za a samu abun da za a baci mahaifinshi ga mi da yi mishi gori a siyasa. Musamman yanzu da yake neman reps.
Ana fitowa sallahr asuba ya yi wa gidansu Khalid babban abokinshi tsinke.
A waya ya kira Khalid din, wannan ya sa salin-alin ya fito ya bude mishi gate suka shiga gidan a tare.
Bayan shigarsu cikin dakin ne Khalid ya kalle shi yana fadin “Lafiya? Kamar hankalinka a tashe.”
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, yana fadin “Idan akwai abin da ya fi tashin hankali shi nake ciki Khalid”
Hankalinshi ya kara tattarawa kan abokin nashi sosai.
Saboda tun yarinta suke tare, amma bai taɓa ganin shi cikin damuwa irin yau ba.
“Ina jin ka” cewar Khalid idanunshi a kan Mk din
“Ka tuna yarinyar nan ta Jama’a, wacce har take kiran wayarka idan tana nema na?”
“Asma’u wai, ba ka ce ta yi aure ba?” Khalid ya amsa
“Eh ta yi. Amma watanni baya can mun hadu da ita a Nasara, kuma har shaidan ya shiga tsakaninmu, mun aikata ba daidai ba”
“Subhnallah!” Khalid ya ambata a hankali, ba tare da nuna razani a kan fuskarshi ba
Mk ya ɗora da faɗin “Yanzu haka dai ta haihu” ya kai karshen maganar hade da nuna mishi hoton yaron da ke cikin wayar shi
Khalid ya karbi wayar yana karewa hoton kallo kafin ya ce “Tubarakhallah Ma Sha Allah. Kuma wlh sosai kuke kama”
“Wannan shi ne tashin hankalina Khalid”
“To me kake so a yi?” Khalid ya tambaya har zuwa lokacin idanunshi na a kan hoton yaron. Saboda sosai yaron ya burgeshi Tubarakhallah.
Gwauron numfashi Mk ya sauke, cikin nazarin abin da yake son fada. Ya san waye Khalid duk abin da suka tattauna a nan, to a nan din zai bar shi. Shi ya sa mai kai tsaye ya tunkare shi da maganar.
“Ni kawai ba na son maganar nan ta iso garin nan. A rufe maganar nan Khalid. Saboda idan ta iso garin nan kai kanka ka san akwai matsala. Don haka ka yi tunani wane malami ka sani, da zai yi mana aiki a danne maganar nan.”
Shiru Khalid ya yi alamun nazari kafin ya ce” Akwai wani Malami a can kauyen Malamawa, zai iya wannan aikin “
Ajiyar zuciyar jin dadi Mk ya sauke yana fadin” Tashi mu tafi”
“Malamawar wai?”
“Eh.” Mk ya amsa, ya dora da fadin “Babu bukatar ɓata lokaci Khalid daga yanzu zuwa ko wane lokaci komai zai iya faruwa.”
Wannan ya sa Khalid miƙewa ya canja kaya zuwa manya, suka fice zuwa gidansu Mk, shi ma ya canja kayan sannan ya yi wa mashin din shi roba-roba key suka nausa.
MALAMAWA
Rumasa’u jin ta take yi, kamar an karɓota daga hannun kidnappers, daga lokacin da aka yanke igiyar auransu da Aibo ta dawo gida.
Ita ba ta jin wani canji na irin ka saba da dakin kankan nan. Hasalima yanzu jin ta take yi mai ƴanci. Musamman da ya kasance akwai dakin Goggonta, tarkacen ciki aka fitar, ta share dakin tas, aka shigar mata da katifa da sauran kayan amfaninta
Shi ya sa cikin wata daya da sakin auran sosai ta yi kyau, ta yi ƴar ƙibar ta abun ta.
Aibo kam shi ya san inda take, ita kam ba ta ce ga duniyar da yake ba, ko sunanshi ba ta son a ambata, bare kuma ta gan shi. Yanzun ta fi mayar da hankali a kan bitar karatunta na alqur’ani, inda ta fara daga farko, za ta rubuta a allonta, bayan ta tabbatar ta iya, Sai ta wanke ta kuma rubuta aya ta gaba.
Ɓangaren su Mk kuwa 12:00am cif suka iso kofar gidan Alaramma, sai dai sun yi rashin sa’a, saboda a, wannan lokacin ne yake shiga gidan marasa lafiya, sai lokacin sallahr azhur yake fitowa.
Wannan ya sa aka shimfida musu tabarma a karkashin bishiyar bedi (maina) suka zauna, suna kallon yadda mutane ke ta harkokinsu. Lokaci daya kuma sun taba hira.
Mk da yake ki shingide ya mike zaune, idanunshi a kan wasu yara mace da namiji da suke fada gindin rijiya, ana kokarin raba su.
Daidai lokacin kuma Ruma ta fito hannunta riƙe da bokiti wanda aka zubo surfaffiyar masara za ta kai gidan Alaramma.
Da ido Mk ya bi ta da kallo har ta shige gidan. Ba ta jima a ciki ba, ta kuma fitowa yanzu kam saɓe take da wani yaro a kafadarta, Mk ya kuma bin ta da ido har ta shige gida.
Ya kasa danne abun da yake ji sai da ya ce “Wato akwai kyawawan mata a kauye Khalid, wani lokaci rashin gyara da yanayin kauye ke ɓoye kyawun su”
“Sosai fa, tun da na shigo wlh nake ganin kyawawa, na dauka idona ne kawai”
Cewar Khalid cikin gasgata maganar Mk
“Ban da ina cikin tashin hankali da na jaraba sa a ta.”
Khalid ya yi murmushi ba tare da ya ce komai ba.
Daidai lokacin kuma aka kira sallah. Ba jimawa suka hango Alaramma tare da masu take mishi baya sun tunkaro masallacin.
Bayan an idar da sallah ne Alaramma ya ce su Mk su biyo shi.
Cikin gida ya shiga hade da bude dakin da ke cikin zauran gidan. Take wajen ya bude da wari gami da kamshin magunguna kala-kala. Warin magunguna kadai ya isa ya tadawa mai aljanu, aljanu.
Bayan sun gaisa Alaramma ya basu hakurin jiranshi da suka yi, saboda an fada mishi isowarsu.
Suka amsa da ba komai kafin Alaramman ya ce “Ina jin ku”
Khalid ne ya gyara zama hade da fadin “Wata matsala ce ta kawo mu. Rufin baki muke so a yi mana. Akwai wani case ne a kasa Malam, muddin ya tashi akwai kura, shi ya sa muke son a danne maganar kar ta tashi”.