Skip to content
Part 3 of 19 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

9:00am

Alhaji AG zaune cikin katafaren falonsa, yayin da ya jingina bayansa a jikin kujera, har yanzun kayan dazun ne a jikinsa, idan ka dauke babbar rigar da ya cire.

Tun da ya shigo gidan matarsa za ta iya kirga maganar da ya yi.

Kuma tun misalin karfe takwas na dare ya shigo, amma har yanzu da agogo ya nuna goma da mintuna wata doguwar magana ba ta shiga tsakanin shi da matarshi ko yaranshi ba.

Yara ma baccin dole suka yi, ita ma ba ta matsa ba, don kuwa idan yana a irin wannan yanayin baya son yawan magana.

Yanzu ma shiru suke kamar kurame.

Shi dai AG abin da ya faru yau a hotel din shi ne yake damunshi, bai taba jin son wata mace ya shige shi farat daya ba, kamar yadda son yarinyar da ya gani tare da Kb yau ba, yanzu yake ganin rashin wayonsa na kin bin bayansu da ya yi.

“Yanzu a ina zai sake ganin ta to? “ya tambayi kansa tare da muskutawa yana shafa fuskar shi

” Na yi rashin dabara. “ya kara fada a zuciyarshi.

Duk su biyun suka juya wurin kofar da ake kwankwasawa a hankali.

Shi ne ya mike zuwa wurin kofar, maigadin ya yi saurin dukawa tare da fadin” Dama wani ne ko *Haka* ya ce ace ma ya zo”

Ko ciki AG bai koma ba, ya biyo bayan maigadin zuwa farfajiyar gidan, saboda ya fahimci abin da maigadin yake nufi.

Hacker ne ya zo, kuma shi ne ya nemi da ya zo din.

Bayan gajeruwar gaisuwa cikin mota suka koma, zama su ke da wuya AG ya ce “As usual! Wani aiki nake so ka min. Kuma cikin gaggawa please”

Ya jinjina kai ba tare da amsa ba

AG ya jawo wayar da ke gaban aljihunshi, ya shiga ciki ya yi yan danne-danne sannan ya ce”Na tura ma picture a WhatsApp dinka, sunanshi Muhammad K Muhammad. Ka lalubo min shi, sannan ka kutsa cikin akwatin sirrin sa, ka duba min chat dinsu da duk wata mace… “

Ya ɗan yi shiru sai kuma ya dora” Kodayake idan ka samu damar shiga akwatin sirrin na shi, ka sanar min, za mu yi binciken tare. “

Hacker ya kuma jinjina kai alamun yana fahimta

” Please kar ka yi wasa da wannan aikin, saboda ya fi  duk wani aiki da ka taɓa yi min muhimmanci”

Hacker ya kuma jinjina kai, alamar ya fahimta, lokaci daya kuma ya karewa hoton da AG ya tura masa kallo.

Kudi masu yawa ya aje masa a kan cinya tare da fadin “A sayi data.”

“Na gode”,  cewar Hacker lokaci daya kuma yana kokarin fita daga cikin motar.

Wannan kenan.

           *******

*Mk & Asma’u*

A yayin da a can Malamawa a zuriyar Baba Malam da Alaramma bakin labari ke shirin riskarsu, Alhaji AG kuma yake zaune cikin zaman jiran tsammani

A nan dakin hotel  bacci ne ya kaurace a idon Mk tun bayan da abin da kullum yake mafarkin samu ya same shi a zahiri, imagination dinsa a kan Asma’u ya tabbata gaskiya. Amma sam ya kasa samun farin cikin da yake tunanin samu.

Da farko dai maganganun mutumin hotel din can ne ke kara ɓata mishi rai, gani yake ba a taɓa raina mishi wayau ba irin yau, ta ya zai gan shi da mace ya nemi ya sayar mishi da ita, ba tare ya san wacece ita a wurin shi ba. Matarshi ce, budurwarshi ce, kanwar shi , duk bai tuna wannan ba ya nemi sayen Asma’un. Sosai ranshi ya baci, kuma duk yadda yake kokarin tursasa kanshi a kan ya manta da lamarin zuciyarsa ta ƙi yarda da hakan, sosai yake jin bacin rai duk lokacin da ya tuna.

Abu na biyu kuma shi ne, wani abu mai kama da nadama ne yake kokarin bijiro mishi. Game da abin da ya faru tsakaninsa da Asma’u, yana jin kamar bai kyautawa kansa ba, da ya kusance ta ba tare da aure ba.

Ya sauke ajiyar zuciya hade da haska fuskarta da hasken screen din wayarsa, bacci take yi  sosai, ta rufe rabin jikinta da bargo.

Ya lumshe ido tare da mayar da kansa a kan filo ya kwantar. Bawai Asma’u ba ta gamsar da shi ba ne, ta yi hakan, amma kuma abun da yake ji mara dadi ya hana shi samun Nishadi.

Wani irin tausayinta yake ji, ya san shi ne igiyar da ya janyo ta zuwa nan.

Sun yi fada da ita sosai, fadan da ya sa ta rufe duk wasu hanyoyi da zai iya samun ta, shi kuma wutar kaunarta da take ci a zuciyarshi ne ya sanya shi nemo hanyar da suka kara jonewa.

Ina ma ace ta hanyar aure ya samu Asma’u da zai iya bugar kirji ya ce a nan wajen ya samu macen da ko wane namiji ke fatan samu.

Har cikin zuciyarsa yana son Asma’u, bai taba son wata mace kamar yadda yake sonta ba.

Ya sha tambayar kansa kodai asiri ta yi masa, amma abin da ya fahimta shi ne, bayan So akwai wata shakuwa ta musamman a tsakaninsu kamar ta miji.

Kai tsaye yake yin abu ko fada mata, ko zai mata dadi ko ba zai yi ba, hakan ya sa wani lokaci yake kallonta kamar matarsa, don ko matarsa ma ba lallai ne ya rika fada mata magana kai tsaye ba kamar yadda yake fadawa Asma’u.

Ya kuma juyowa a karo na biyu yana kallon ta,  ido ya lumshe  hade da

 janyota zuwa jikinsa ya rungume ta, cike da tausayinta.

Har zuwa lokacin da suke shirin rabuwa Mk bai kara yin wani abu na nuna alamar son kusantarta ba, wannan ya jefa Asma’u cikin tsoro gami da shakku

Tambayoyi kala-kala ne ke yawo a kanta.”Bai samu biyan bukata da ita ba ne, ko kuma yadda yake tunaninta bai same ta haka ba, ko ta yi abin da ba ya so ne?”

Saboda yadda ya ɗokanta da kuma yadda yake cin alwashin haduwarsu, shauki da kuma tarin soyayyar da ya yi alkawarin nuna mata ba ta tsammaci za, ta tsaya iya haka ba.

Duk lokacin da ta yunkura da niyyar yi mishi maganar abin da ke mata yawo a zuciyarta

 sai ya yi mata kwarjini.

A haka ya rakota inda za ta samu keke, suka rabu ko wanne zuciyarsa kunshe da mabambantan abubuwa.

Malamawa.

Baba Malam wanda ya kasance mahaifi ga su Alaramma shi ne ya ja su sallahr asuba kamar yadda ya saba.

Bayan an idar  almajirai da wadanda suka yi sallah a masallacin suka rika miko gaisuwa, ciki har da yaran shi hudu maza

Malam Balarabe , Malam Yunusa(Mahaifin Ruma) Alaramma da kuma Malam Nura.

Usman na gefe tsugunne, tun da ya gaishe da Baba Malam wanda ya kasance kaka a gare shi bai matsa a wurin ba.

Har sai da kowa ya gama mika gaisuwarshi sannan Baba Malam ya juyo inda Usman yake tsugunne ya ce “Shehu Usman! Akwai wani abu ne?”

Usman ya kara yin kasa da kai alamar girmamawa ba tare da ya ce komai ba

Baba Malam ya kara gyara zaman shi yana fuskantar Usman din sosai ya ce “Ina jin ka, yi magana kanka tsaye.”

Nisawa Usman ya kara yi saboda ya rasa ta ina zai faro maganar, ta sama, ta kasa, ko  ta gefe

Baba Malam ya kuma cewa “Shehu menene ya faru? Ka fada min ko menene.”

Cike da girmamawa Usman ya ce “Dama wani abu ne ya faru.”

“Me dadi ko akasin sa?” Baba Malam ya tare Usman.

A daburce Usman ya ce “To ga shi nan dai”

“Ina jin ka” cewar Baba Malam da alamar kosawa.

Shiru Usman ya yi kafin kuma ya ce “Dama Ruma ce ba ta da lafiya, amma tana can na kai ta ɗakin Iya.”

“Subhnallah! Me ya samu Rumasa’un?”

Usman ya kuma yin shiru har sai da Baba Malam ya kuma maimaita tambayarshi, sannan cikin rashin jin dadi ya ce “Baba Malam abun ne ba dadin ji, ban san ta ya zan fara fada ba, kuma ban san wa zan fara fadamawa ba, da abu ne  wanda zan iya rikewa kowa bai ji ba, da na yi hakan. Don Allah ku yi hakuri”

Zuwa lokacin kam Baba Malam jikinsa ya fara mutuwa, amma cikin yanayin boye damuwarsa ya ce

“Subhnallah! Abun ya kai haka? Kar ka damu Allah ba ya dorawa bawansa komai face abin da bawan zai iya dauka. Ka fada min menene, mun yi imani da ƙaddara mai kyau da akasin ta.”

Usman ya runtse ido gam, yana mai jin dacin abin da zai fada, a cikin yanayin ya ce” Haihuwa ta yi Baba Malam. “

Cikin rashin fahimta ya ce” Wacece ta haihun? “

Shiru Usman ya yi, zuciyarsa na yi masa daci da jin zafin furucin da ya yi.

Jin ya yi shiru ya sa Baba Malam ya ce” Wacece ta haihu? “

Hawaye masu zafi suka sakko mishi ba tare da ya goge su ba ya ce” Ruman”

Baba Malam ya yi saurin dagawa daga dukar da kan da ya yi yana fadin “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Subhnallah!!” haka ya rika maimaitawa tsawon lokaci har nutsuwarshi ta fara dawowa jikinsa kafin ya ce

“Rumasa’un ce ta haihu. Allah mai iko, yau kuma haka ka nufe ni da gani, a cikin zuriyata. Allah na gode maka, Allah ka bamu nauyin kirjin ajiye wannan kaddarar.”

Duk suka yi shiru, kafin Baba Malam ya ce

“Ka ce Rumasa’un tana gidana ko?”

Kai Usman ya jinjina alamar Eh.

“Ka fadawa Kakar taku ne?”

“A’a! Lokacin da muka shiga tana sallah.”

Baba Malam ya jinjina kai. Kamar ba zai kara magana ba, Sai kuma ya ce

“To je ka kira min iyayenka maza, su same ni a gidan.” Ya Kai karshen maganar ta shi hade da yunkurawa ya mike zuwa kofar fita daga masallacin hannunshi rike da zabgegen carbinshi.

Usman ya bi bayanshi cikin rashin kuzari.

Ba jimawa suka hallara dakin Iya wacce ta kasance mahaifiya a wurin su.

Ruma na can manne a ƙaramin gadon Iya cike da tsoro gami da fargaba, ji take kamar ta yi layar ɓata. Ba ta taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba. To ina ma ta san tashin hankalin. Ko lokacin da take da cikin Goggo (mahaifiyarta)ita ce ta buda mata matsalar da take ciki, ba, wai hankalinta ne ya sanar da ita ba

Baba Malam ya yi gyaran murya cikin nutsuwa ya ce “Na san ba ku saba in kira ku a irin wannan lokacin ba, to wani al’amari ne babba ya faru, wanda ya tilasta ni ta raku a nan.”

Ya nisa a hankali kafin ya dora “Daidai iyawa ta na ba ku tarbiya, ba na jin a cikinku wani zai ketare iyaka zuwa ga haramun . Ni dai Allah Ya sani, kuma ya gani ban taɓa aikata wani abu makamancin abin da ya faru yau a zuriyarmu ba. Ban sani ba ko ku, kila shi ya sa hakkin ya bibiyi yaran mu. Tun da manzon Allah S. A. W ya ce duk abin da ka yi sai an yi ma ka. Wannan magana gaskiya ce, sannan akwai ayoyin cikin Suratul-Noor da suke bayyana mana waye mazinaci da sakamakon shi.”

Ya kuma nisawa yana kallon yadda yaran na shi suka nutsu, alamun suna sauraronshi. Ya dora da” Koma dai menene, mun karbi wannan ƙaddarar, muna rokan Allah kuma ya bamu ikon cinye ta. Sannan ya gafarta mana abin da muka aikata ba daidai ba. “

Dukkansu suka amsa da amin.

Ya kara da cewa” Ina mai baƙin cikin sanar da ku cewa, ƙaddara mara kyau ta fadawa Rumasa’u, wacce bamu taɓa tsammani ba. Yau da asuba Usman ya sanar min cewa Ruma ta haihu ba tare da aure ba”

Iya da ke jan carbi ta sake carbi cike da firgici, ba ita kadai ba dukkansu sun firgita da jin furucin.

Ruma kam ihu ta fasa hade da durowa daga gadon ta nufi kofar fita, duk wani rashin karfin jiki na mace sabuwar haihuwa ita ba ta jin shi,

Cikin sauri Baba Malam ya ce “Kar ka bar ta ta fita Nura, rike ta.”

Caraf kuwa Malam Nura ya rike ta, Sai ta kuma rudewa ta shiga kwala ihu hade da rokon ta tuba ba za ta ƙara ba.

“Ki rufewa mutane baki kar ki tara mana jama’a, wadanda basu san me yake faruwa ba, yanzu sani” cewar Baba Malam bayan ya mike tsaye

Kamar ba ta ji me Baba Malam din ya fada ba, saboda ko kadan ba ta rage sautin kukanta ba, sai da Alaramma ya daka mata tsawa, tsawar da ta girgiza duk kayan cikinta, sannan ne ta dan rage gunjin da take yi.

Malam Nura kuma ya tura cikin dakin sosai.

Ya dubi yaran nashi daya bayan daya sannan ya ce “Yanzu ba lokacin tashin hankali ba ne, lokaci ne na a rufe wannan magana kar ta fita. Kai Nura tambayi Rumasa’u wa ye da alhakin wannan abun.”

Daga zaunen Malam Nura ya dora idonshi kan Ruma wacce ke tsaye ta danne bakinta da hannayenta.

Tun kafin ya yi magana ta ce” Malam Auwalu ne, wlh shi ne. Don Allah ku yi min rai. Na tuba Baba Malam Nura don Allah ku yafe min”

Malam Balarabe ya nisa a hankali a kasalance ya ce “Wane Malam Auwalun?”

“Kanen Goggo Mariya”

Ruma ta amsa da sauri

Tun da ta fadi haka duk suka gane wanda take nufi, Auwalu kanen matar Alaramma ne (Uwargidan) a hannun Alaramma ya yi karatu har ya sauke, sannan yana daya daga cikin almajiran da ba ya da shamaki a kaf gidajen biyar. Kuma shi ne wanda zai auri Ruma yake ba sako ya kawo mata idan zai zo gida, kasancewar suna yin aikin karfi a wuri ɗaya ne.

Cikin zafi Alaramma ya ce “Ni wannan yaron zai yi wa haka? Sai na kashe shi don ubanshi sai na shafe labarinshi a doron kasa, ni zai tonawa asiri ya watsa min kasa a ido ya ja min abun fada a wajen maƙiya.”

“Na ce maka ba na son hayaniya ko, ban san a daga maganar nan wani ya ji”cewar Baba Malam yana kallon Alaramma da yake ta huci kamar zai yi aman wuta.

” Yunusa! “Baba Malam ya kira sunan mahaifin Ruma, kasancewar tun da ya dukar da kai bai dago  ba, kuma bai ce komai ba.

” Ka yi hakuri ka ji, kaddara ce”

Numfashi ya sauke ba tare da ya ce komai ba

Yayin da Alaramma ke ta ruwan masifa da cin alwashi kala-kala a kan Auwalu.

Su Malam Balarabe, Malam Nura da Baba Malam ne ke ta tausarshi.

Kafin Baba Malam ya umurce su a kan su ta shi zuwa gidan Malam Yunusa domin ganin abin da aka haifa ya kuma ce Malam Nura ya nemi Auwalu a waya ya fada mishi ya zo suna neman shi yau ba sai gobe ba.

<< Abinda Ka Shuka 2Abinda Ka Shuka 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×