Skip to content
Part 31 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Gajiya Mama Halima ta yi, ta kutsa cikin yan rabo, da ƴan daukar rahoto da masu son jin yadda aka haihu a ragaya.

Tsakanin Kuluwa da Amarya ta shiga ta hanyar ba kowa hak’uri, amma kamar tana zuga su. Saboda kowa kokarin juye abin da ke rashi yake alamun dama dukkansu suna da cikin juna, ranar haihuwar suke nema.

A lokacin Hafsat ta hango Mama Halima kamar daga sama.

Duk ɗokin da take na zuwa nata ba za ta iya kutsawa cikin mutanen ba, dole ta jira a inda take, sai dai duk wani motsi da Mama Halima za ta yi a idanunta ne.

Rigimar ba ta tsagaita ba sai da Malam Ayuba ya shigo gidan, ya rika zubar da na shi ruwan bala’in.

A hankali ma mata da yaran da ke cikin gidan suka rika fita daya bayan daya.

Sai a lokacin Hafsat ta je ga Mama Halima ta rike hannayenta alamun oyoyo.

Kallon tashin hankali Mama ke bin fuskar Hafsat da shi kafin ta ce”Me ya samu fuskarki haka kamar kin shiga filin boxing? “

Malam Ayuba ya yi caraf da fadin” Ai Yaya Halima wannan fada duk a kan abin da ya faru da Hafsat sannu ne… “

Ya shiga kora mata labari tun daga farko har karshe.

Jiki a mace Mama Halima ta ce” Ai da an bi abun a hankali. Duk cikinsu wanne ne ba na ka ba Malam Ayuba. Ita Hafsat din me ya kai ta, wa ke tunkarar ɓarawo kai tsaye? Ko namiji bai kamata ya tunkari ɓarawo kai tsaye ba. Saboda bai san da me ya zo ba. Bare ita mace, yanzu idan da wuka ya farke ta fa. Kul! Na kara jin kin yi irin wannan gangancin kin ji na fada miki “

“Ai idan har ina raye Yaya Halima Danjuma bai ci banza ba, shi da uwar shi sai sun biya abin da suka daukarwa Hafsat. Hinde ba ta ji dadin zama a gidan nan ba, to Hafsat kam sha Allah za ta ji, damuna nake jira ta wuce in gina mata daki, ta kwashe duk kayan mahaifiyarta ta mayar a ciki ta zauna. Wlh ni ma yanzu ba na jin dadin ganin kayan Hindatu haka jibge a tsakiyar gida hankalina tashi yake yi.”

Jin Mama Halima ba ta ce komai ba ya ce” Mu je dakin amarya ita ce kawai ta kirki mai tsabta kamar Hinde, za ki zauna ɗakinta hankali kwance, amma kin ga wadancan zaurin fitsari ma kadai ya ishe ki”

Kwance suka samu Amarya Murja wacce su Hafsat ke kira da Goggonmu.

Har zuwa lokacin ba ta huce ba, sai kumburi take yi

Mama Halima ce ta taya Malam Ayuba lallashi gami da ba ta hak’uri har ta ɗan sakko. Yayin da Malam Ayuba ke ta cin alwashi, musamman a kan Inna Kuluwa.

Nisawa Mama Halima ta yi sannan ta ce “Abin da ya faru ya riga da ya faru Malam Ayuba. Ina jin a bar wannan zancen shi yafi. A yafewa Danjuma shi ya fi. Sai a dauki mataki na gaba.”

“Ai, yaron nan ba ya ji Sam, ya bi ya lalace, shi ne namiji babba amma na banza. Kin ganshi nan ko ciro ba ya min a gona. Sai dai ya iya zuwa ya satar min idan amfanin ya yi”

“To a kan dai Hafsat ni zan yanke wata alaka da za ta kara hada shi da ita. Da farko dai ina godiya gami da farin cikin yadda ka tsaya a kan Hafsat karo na farko. Magana ta gaskiya duk yadda zan kwatanta maka farin cikin Malam Ayuba abun ya yi kadan. Ko ba komai ka nunawa duniya ita din ma ƴa ce. “

Murmushin jin dadi Malam Ayuba ya yi, a karo na farko Ya Halima ta yabe shi. Amma da kam Kamar suna ganin hanjin juna.

“Ina ganin ka duba cikin dabbobin Hafsat, idan akwai wacce kake sha’awar kiwo sai ka dauka. Sauran kuma zan kira Bammi daga nan zuwa gobe ya zo ya kwashe su zuwa can, ka ga an kashe rigima”

“Shi kenan ma wlh” karon farko Murja da ta sanya baki

Mama Halima ta cika idanun Malam Ayuba, Sai ya rasa ta ina zai fara cewa zai dauki wata akuya ko tunkiya a cikin dabbobin Hafsat din.

A sanyaye ya ce “Ai, hakkinta ne Yaya Halima ni an ba ni nawa. Sai dai in ce Allah Ya jikan Hindatu, shawarar nan kuma da kika kawo ta yi daidai, haka ya kamata a yi. Sai ki kira Bammin ki shaida mishi.”

Yau dai mamaki  Malam Ayuba yake shayar da ita. Kamar ba shi ba, ba ta taba tsammanin zai amince ba, shi ya sa ma ta ce a cikin dabbobin ya zabi duk wadanda yake so, don ma kar ya kawo matsala, Sai ga shi cikin sauki ya amince.

Yau ma zaman Mama Halima da Hafsat a dakin amarya ne, sosai kuwa Amarya ta saki jiki da Mama Halima suka hira. A nan ne ma take sanar mata mijinta rasuwa ya yi, tana da yara hudu da shi. Amma duk suna wurin kakarsu ta wajen uba da shi ke duk maza ne.

Su Inna Kulawa kuwa sai waƙe-waƙen habaici da jefar da kwanoni a tsakar gida.

Misalin karfe shidda na yamma Tukuro ya zo daukar awaki kamar yadda mahaifinshi ya shaida mishi. Sai da ya zo wa da Mama Halima nono mai kyau da fura.

Ba a kora awakin ba sai da aka nemo Malam Ayuba, sannan Tukuro ya kora su zuwa Ruggarsu.

Bangaren Hafsat sai ta ji kamar an kwashe mata ƴaƴa zuwa wani wuri daban. Ko kuma ƴan’uwanta. Saboda sune dai abokan hidimarta.

Sune suke maraba da ita a gidan, sune suke kukan rashinta, kuma sune suke murnar dawowarta

Ita kanta a cikinsu take shiga ta rage kewar abin da ya dame ta.

Ko ranta ɓace yake ta shiga cikinsu sai sun yi abin da ya ba ta nishadi. Musamman kwamanda, yana da fada, ko ita ta yi mishi wargi sai ya ce zai tunkuye ta. Shi ya sa mutanen gidan ko ta wajen shi basu bi, yanzu ya kawo duka. Kuma ko za za su rama sai da jifa ko daga nesa

Idan kuwa ya kwance ba ta nan, Sai dai su shige daki a rufe kofa. Babu mai iya kama shi sai Malam Ayuba ko kuma ita.

Ranar dai Inna Halima da Hafsat a dakin Amarya Murja suka kwana, kasancewar Malam Ayuba ba a dakin yake ba.

Kashegari d safe ta nemi alfarmar tafiya da Hafsat Dawuri, duk da hutun saura sati biyu ya kare. Malam Ayuba kuma bai musa ba. Misalin karfe 11am suka bar kauyen makera zuwa Dawuri.

ASMA’U

Kwance take saman gado ta yi rringigine, yayin da ta dora Abdallah a kan cikinta hade da jinginar da shi jikin kafafunta da ta tankware. Wannan ya ba shi damar zama din-gir-gir yana wasannin shi. Yayin da ita kuma hankalinta ya tafi a chat din da take yi da AG.

A yanzu shi kadai ne namijin da take saurare, saboda tuni ta toshe Lukman, ina ita ina auren saurayi da guntun kashinta a ɗuwawu.

AGn ma ta so toshe shi, amma ya ƙi tosuwa, saboda sosai ya samu karɓuwa a wajen ƴan’uwanta musamman Aunty Hajara da mahaifinta. Ita Momy ba sosai ta waye shi ba.

Sallamar Momy ce ta sanyata mayar da hankalinta kan kofar shigowa, Sai kuma ta tashi da sauri tana fadin “Oyoyo Momy! Sannu da zuwa.”

“Yauwa” Momyn ta amsa hade da zama gefen katifar tana daukar Abdallah da yake washe mata baki

Suka shiga gaisawa kafin Momyn ta ce “daga nan Sabuwar unguwa nake, Sai na ce bari in biyo mu, gaisa”

Cike da jin dadi Asma’u ta ce “Aiko mun gode, ita ma Auntyn ba ta jima da, barin gidan ba, tsohuwar kasuwa ta tafi. Little ne ke yawan kashi, shi ne za ta samo mishi saƙe-saƙi” ta kai karshen maganar da duba agogon wayarta da ya nuna biyar na yamma saura.

“Ba dai har ya fara kashin haƙoran ba?”

Hannuwa Asma’u ta watsa tare da fadin “Ban sani ba wlh, kila haƙoran ne.”

“Amma kuwa da ya yi sauri duka-duka watanshi nawa. Ba yanzu yake cikin na biyar ba?”

“Haka dai ma Aunty ta ce”

Momy ta bi Abdallah da kallo wani abu mara dadi yana yi mata yawo, duk lokacin da ta kalle shi sai ta ji babu dadi. Iyaye ne kawai za su fahimci abin da take ji

Ga dai yaro tubarakhallah, son kowa kin wanda bai samu ba. Kubul-kubul da shi, ga kuzari ga shi bai rasa komai ba.

Sai dai ko labarin mahaifinshi ba a yi, Asma’un ba ta yi ba, su ma basu yi ba. Duk lokacin da ta yunkura da niyyar yi kuma sai ta ji kamar an rufe mata baki.

Hira sosai suka yi da Momy, kafin ta ce ta yi mata rakiya ba tare da ta jira dawowar Aunty Hajara ba.

*****

MALAMAWA

Tun bayan da Mk ya yi wa Alaramma maganar yana son Ruma, Alaramman ya yi hirar da Malam Balarabe da kuma Baba Malam.

Kai tsaye Malam Balarabe ya ce to a kafe shi, saboda bai kamata su bari ya kufce musu ba. Haka ma ƴan’uwanshi a mallake su, ta yadda babu wanda ya isa ya ja da maganar auran.

Shi kanshi Alaramma ya yi na’am da wannan shawara. Alhaji Bashir ba karamin mutum ba ne a ƙasar ma gabadaya.

Ace ɗanshi yana son ƴarsu wacce ta yi abin da a zuriyarsu ba a taba yi ba, lallai ya kamata su yi yadda ya kamata wurin ganin bai kufce musu ba. Tare da cusa mishi kaunar Ruman, ta yadda zai ji idan ba ita ba, zai iya yin komai ma.

Koda kuwa zai ji labarin abin da ya faru da ita tun farko, to ba zai bijire ba.

Malam Nura da Malam Balarabe su ka yi aikin da kansu.

Shi ya sa Mk ya susuce, ba shi da wata magana sai ta Ruma, saboda tun asali ma sonta yake ba karami ba, ballantana kuma an kara mishi. Shi ya sa yake mata wani irin so na fitar hankali.

Duk ƴan’uwanshi babu wanda bai san da maganar Ruma ba, haka babu wanda ya kawo matsala ko kushe ga auran, duk kuwa da yadda Mk ya sanar musu da Ruma bazawara ce ko idda ma ba ta yi ba.

Yadda yake ƙirga kwanakin da ya rage na iddar Ruma ko kudi za a ba shi a kwanakin ba lallai ya kiyaye haka ba.

Tun ba ace an ba shi ba yake ta hidimar gyaran ginninshi da hada lefe. Bai ƙi ba a ranar da ta kare idda ace ya taho da mutanenshi a daura musu aure.

*****

HAFSAT

Hafsat kam an zama ƴan gari ƴan maraya. Duk da ƴan matan gidan basu nan suna makaranta, kasancewar a wannan shekarar duk suka shiga high institution, Jin dadin zaman gidan take yi.

Saboda akwai Ya Tajuddeen, shi ne ya zama kawarta, da yamma ya dauke ta a mashin ya yi ta zagaye muhimman wurare da ita yana nuna mata.

Kamar yau ma misalin karfe biyar na yamma suka fita, ita dai kamar kullum sanye take da farin jalbab. Fuskar nan fayau sai farar hoda.

Yau kam kai tsaye Unguwar kofar fada ya yo da ita.

Tun suka fara hangen katangar bayan gidan Galadima ya shiga kora mata zance “Kin ga waccan katangar?”

Kanta ta karkato hade da leka katangar da yake batu a kanta

Katanga ce mai bisa sosai, sannan doguwa a tsayi. Wacce ke dauke da farin fenti, yayin da aka kawatata da zane iriena gidajen sarauta da kaloli daban-daban

Sai dogayen fulawoyi masu kyau, da suka yi mata kawayanya yayin da furanni wasu daga cikin bishiyoyin suka baibaye ta.

“Na ganta” ta amsa a hankali ba tare da ta dauke idanunta a kan katangar ba.

“Nan shi ne gidan Hakimin Dawuri Galadiman Tanga, wands kika bar fura lokacin taron makarantarku”

Kai ta jinjina tare da fadin “na gane shi, daga waje ma gidan ya yi kyau bare kuma daga ciki”

“Bari ma mu ɓulla gaban gidan  ki gani.”

Basu ɗau lokaci ba suka shiga kwanar gidan, daga dan nesa Tajuddeen ya Parker, ita kuma ta sauka hade da jingina bayanta da mashin din, shi kuma ya yi tsaye yana shafa

wayar shi, lokaci daya kuma yana amsa mata tambayoyi gami da kara mata haske a kan wani abun.

Gidan take karewa kallo tare da mamakin girmanshi, ba mamaki kila komai akwai cikin gidan har da filin kwallo.

Ga wani tafkeken farin gate da aka kawata shi da wani zane na golden color wanda Shi ma ya yi kamar zanen saurautar.

Sannan in daga can gefe, akwai wata farfajiya da aka zagaye da wasu karafa masu kauri da tsayi, nan kuma dokuna ne masu yawa a ciki.

Kofar gidan kuma dogarawa ne hade da jami’an tsaro.

Ga motoci masu kyau guda goma jere a kofar gidan. Bayan mutanen da suke shiga gami da fita.

“Kin gama kallon mu tafi?” Cewar Tajuddeen

Dariya ta yi kafin ta ce “Ina son shiga ciki.”

Ido ya zaro kafin ya ce “Ba ni da alaka ta kusa ko ta nesa da su da zai sa in shiga gidan. Ni ban ma taba shiga ba”

Cikin wata dariyar ta ce “Sai ka ce ni ka kawo zan gaishe da Galadiman, ni kuma sai in ce mishi ni ce na ba shi fura a wurin taro”

Cikin dariya ya ce “Ki hau mu tafi, wane irin kalen dangi ne wannan”

Mashin din ta hau, har zuwa lokacin  dariya take yi .

“Can kuma ina ne?” cewar Hafsat a lokacin da take hango wasu gine-gine masu kyau guda uku a jere.

Sai da ya sha U-turn Har gaban gine-ginen sannan ya yi parking. Ba tare da ta sauka ko shi ya sauka ba, ya nuna mata gini daya wanda aka rubuta *AMI PHARMACY* kenan.

Hafsat ta bi katon pharmacy din da kallo, wanda hade da rubutun jiki wanda aka yi shi da kalar lemon green. Sai Kuma ta sauke idanunta a cikin store din gabadaya.

Daga inda take za ta iya hango ma’aikata sama da biyar, yayin da Customers har layi suke yi, don sun tasar ma hamsin.

Masu karamin karfi da ƴan’uwanta mutanen karkara sune suka kwashe kaso biyu bisa ukun Customers din.

“Allah sarki, ƴan’uwanmu ƴan kauye talakawa sune suka fi yawa”

“Wurin ya fi sauki magani ne, kuma ko wane kalar magani akwai”

Kai ta jinjina a hankali, hade da dora idanunta a kan daya ginin wanda aka rubuta *AMI SHOPPING COMPLEX*

Nan ma katon wuri ne, daga inda take tsaye ba za ta iya hango komai da ke cikin shagon ba.

“Can kuma me ake siyar wa?”

Cikin tsokana ya ce”Idan kika shiga ciki sai kin ɓata, kasuwa guda ce a ciki “

Daga kan mashin din ta sauko, tana fadin” Mu je in ɓata din”

<< Abinda Ka Shuka 30Abinda Ka Shuka 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×