Skip to content
Part 32 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

HAFSAT

Tun da aka yi hutu sai ta zama less busy, ba ta da wani aiki sai hidima da dabbobinta, ta yo musu ciyawa, ta share makwancinsu.

Sai game da yawa, idan kuma Uncle Najib ya kira ta daga. Idan ta gaji karatun littafan English din da ya ba ta. Inda ba ta gane ba ta kira ya kara mata bayani.

Har sai ya koma suna lesson ta cikin wayar. Zai zuba isassun kudi ya kira ta, su yi lessons Har sai ya tabbatar ta gane sannan.

Hakan ba karamin kara bude mata kwakwalwa ya yi ba. Wata yar kamar magana da turanci dai ba doguwa ba tana iya wa.

Kalmar da ta yi mata wahala kuma sai ta duba dictionary don ta kara fahimta.

Da yamma kuma dabbobin take kwancewa zuwa bayan gari su dan taba kiwo, wannan yana debe mata kewa.

Saboda gidansu Farida ne kawai take dan zuwa, kuma faridar ta tafi hutu.

Sha’anin gidansu kam sai godiya, dama-dama ita yanzu Malam Ayuba na dan kula da ita. Safe zai ce ta ci abinci, haka ma da rana. Duk don saboda abin da ya gani ranar graduation.

Yanzu kam ya yarda Hafsat abun alfaharinshi ce, bai kamata ya yi mata rikon sakainar kashi ba. Yanzu mutanen gari har wani girma suke ba shi da shakkarshi.

Idan Hafsat ta zo karbar abinci wurin Maman Iyabo suna turanci sai ai ta kallon su. Dalilin da ya kara sanyawa Mama Iyabo kaunar ta.

Su Inna Kuluwa ne dai ke karbar takaici a hannun amaryar su Murja. Kullum shigo da sabbin tsare-tsare take a gidan. Kuma dole kowa ya bi. Duk da kai tsaye tsare-tsaren nata basu cika shafarsu ba. Amma kuma yadda Malam Ayuba ke bin umarninta kadai ya isa ya sanya su takaici

Duk ranar girkinta babu sakat a wannan gidan, Malam Ayuba wanka, goge kaushi, yin brush duk wani lungu da sako na jikinshi sai ya kalkale shi. A yi magana kadan ya ce Murjanatu ba ta son kazanta.

Kuma har zuwa lokacin girkinta take yi, ba ta saka kowa cikin harkarta a gidan.

Ko allura take so sai Malam Ayuba ya dawo ya sawo mata.

Yau Hafsat tun da ta dawo kiwo take neman wayarta amma ba ta ganta ba, haka ta gaji ta kwanta sai dai ranta babu dadi, saboda ta tabbata Uncle Najib ya kira har ya gaji, musamman yanzu da dare da za su yi bitar karatun su

Wayar ce hanya daya ja da take rage mata kewar Uncle Najib din, kuma take kara musu kusanci. Ga shi ta yi ɓatan dabo.

Tun tana daurewa ba ta yi kuka ba, sai gata zaune tana rigar kuka, ita da kanta ta lallashi kanta ta kwanta, amma maganar gaskiya wata irin kewar Uncle Najib din take ji

Ba ta san shi ne cikon farin cikinta ba sai yanzu da ta rasa igiyar da ke hada muryoyinsu.

Da safe ma haka ta tashi ba dadi, tana share garken dabbobinta ne ta ji Inna Kuluwa na fadin Ɗanjuma ya zo. Ɗanjuma shi ne babba a gidan daga nan sai ita. Idan ya tafi gantalinshi har mantawa da shi ake yi. Ga shi duka-duka bai fi shekaru 19-20 ba.

Har lakabi ake mishi da Ɗanjuma Gantali.

Jin labarin zuwan shi ya tabbatar mata da shi ne ya dauke mata waya. Saboda sata dai ko Azeez din cikin labarin DA MAGANA ya san da zaman shi.

Kuma a lokacin ne ta kara fahimtar babu awakinta guda biyu, kyalla da kuma uwar biyu, sannan ga sawun kafa nan ta bayan katanga har da takalmi guda daya da aka yar.

Wannan abu ba karamin kara ɓatawa Hafsat rai ya yi ba.

Haka ta fita ko lullubi babu zuwa bayan gidan tana duddubawa amma babu akuya sai sawun kafar mutum.

Gida ta koma hade da sako hijabinta ta rika bin sawun tana kuka, har zuwa cikin wata gona mai duhun dawa.

Bakin gonar ta zauna tana kuka, saboda tsoron shiga ciki take yi. Yau sai kukan ya hade mata biyu, na rashin Innarta, na rashin Nasir, batan wayarta da kuma sace mata akuyoyinta.

Kuka ta yi sosai har fuskarta ta yi ja sannan ta dawo gida.

Babu wanda ya yi maganar ɓatan awaki, ko basu lura ba ne, ko kuma sun lura kawai bai shafe su ba ne shi ne ba ta sani ba.

Daga wannan lokacin ta kara tattara kulawarta a kan dabbobin, ko bacci mai nauyi ba ta yi. Ta yadda ko banban motsi suka yi tana ji.

*****

DAWURI

Misalin karfe tara na dare Galadima ne kishingide cikin falonshi na alfarma da ya sha kayan alatu irin na saurata.

Idanunshi a kan TV inda yake kallon News @9

Daidai lokacin Hajiya ta shigo cikin shiga ta alfarma kamar ba dare ba, kamshinta mai dadi ya cika falon, farantin da ke hannunta ta ajiye kusa da shi cike da girmamawa ta ce “Barka da hutawa ranka ya dade”

Rashin amsawarshi ba ta dame ta ba, saboda dama idan yana kallon news din bai cika magana ba.

Kan daya daga cikin kujeru ln alfarmar da ke falon ta zauna tana kallon New din ita ma.

Bayan an gama ne ya tattara hankalinshi a kan ta yana fadin “” Barka da dare “

Da hanzari ta sakko daga kan kujerar ta shiga tsiyaya mishi furar cikin dan karamin cup ta mika mishi.

Ya karba hade da yin Bismillah ya kai bakin shi. Suna hira kadan-kadan wacce ta shafi ahlinsu.

Daidai lokacin Ahmad ya shigo tare da sallama, duk suka zuba mishi idanu har ya kara so ya kai kasa ya kwashi gaisuwa a nutse.

Bayan sun amsa mishi ne ya dauki daya daga cikin cups din da ke kan tiren ya debi fura da ke girke cikin wani koko da aka kayatashi da kwalliya irin ta sarauta.

Zaman shi ya gyara a hankali yake sipping din furar.

Galadima ya aje cup din a kasa hade da mikewa zaune sosai ya ce “Ya gajiya?”

“Akwai gajiya sosai”

“Ai fa an taba yan baka, kura ta saci kalangu, me ye abun gajiya Ahmad ba a kasa ka je ba, sannan koda ka isa din ma a zaune kake me ye abun gajiya?”

“Hayaniyar fa Hajiya”

“To naɗin sarauta fa ka je, ta ya ba za a yi hayaniya ba?”

“Shi ya sa ni ba na son zuwa tarukan nan. Ni wannan kirarin da wannan bushe-bushen damuna suke yi”

Cike da damuwa ya yi maganar

Hajiya ta ce “Ahmad kamar babu jinin sarauta a jikinshi wlh. Ai burin ko wane jinin sarauta shi ne ya ji ana busa mishi algaita, fadawa na kawo gaisuwa wannan ai shi ne sarautar.” ta yi maganar idanunta a kan Galadima

“Ya fi gane ya ji shi a cikin daji tsuntsaye na yi mishi kuka” Cewar Galadima.

Murmusawa Ahmad ya yi hade da ajiye cup din da ya sha furar ba tare da ya ce komai ba.

Galadima ya dora da, “kuma Ina son ka rika zuwa irin wadannan tarukan a madadina, wannan zai sa ka kara fahimtar mulki, da yadda ake yin shi. Mutane su sanka sosai kai ma ka san wasu. Kuma zai kara ba ka damar sanin halayen mutanen da ke zagaye da mu”

“Atoh! Kullum ina fada mishi wannan sai ya ce shi bai son hayaniya. Kuma idan ya yi shigar sarautar nan kar ka ga yadda yake yin kyau wlh. Kamar a sace shi a gudu”

Galadima ya Murmusa cike da jin dadin yadda Hajiya ta yabi Ahmad

Ahmad din ma murmushin kawai ya yi yana wasa da kafet din da ke shinfide a tsakiyar falon

“Lokacin da mu ka je taron yaye dalibai a garin Maƙera na so ace tare muka je da shi. Ba mamaki ya samo mata”

Ido Hajiya ta fitar tana fadin “Wani Ahmad din ko ba wannan ba.”

“Wannan din dai, na yi mishi sha’awar yara  da yawa a wurin taron.”

Cikin murmushi Hajiya ta ce “Ba Za su burge shi ba. Ni nan har na gaji da, yi wa Ahmad sha’awar ƴanmata na kyale shi. Mata nawa n yi mishi ta yi ya watsa min kasa a ido, ballantana a kauye masu secondary, wanda ya ƙi masu degree”

Kai Galadima ya daga yana kallon Ahmad.

Murmushi ya yi da har fararen hakoranshi suka bayyana,amma komai ba ce ba.

Girgiza kai Hajiya ta shiga yi cike da takaici, saboda sosai rashin auran Ahmad na damunta haka yadda ko wacce ya nuna baya so, shi ma yana damunta.

“Ka gani ko. Ai ka fita batunshi. Ni ban da ina jin tausayinshi da tuni na, sanya an daura mishi aure da duk wacce hankalina ya kwanta da ita”

Nisawa Galadima ya yi kafin ya ce “abi a hankali Sa’adatu ba sauri ake yi ba”

A wannan gaɓar Ahmad ya ce “Ki yi hak’uri Hajiya zan yi. Ba na son yin gaggawa ne, amma ban damu ko a kauye ko a birni nae. Kawai dai ina son mai hankali, mai dan shekaru wacce ta san rayuwa sosai.  Ita  Zaitun da kike magana yarinya ce karama duka fa 19yrs gare ta idan ma ta kai. “

Hajiya ta rike haba cike da mamaki kafin ta ce” To su kuma su Mamin fa? “

Ya yi shiru bai amsa ba.

” Shi kenan ya isa, Allah Ya zaba ma fi alkairi. “

” Amin Ya Rabbb “Cewar Hajiya

Ahmad dai bai ce komai ba

Sai ma ya mike ya yi musu sai da safe.

*****

HAFSAT

Tun daga lokacin da aka kwashe mata dabbobi biyu ba ta kara sakin jiki ta yi bacci ba, duk wani babban motsi a kan yi shi a kan kunnenta ne.

Kamar ko wane lokaci idan an yi ruwa an dauke gari ya kan kasance shiru, yau din ma hakan ne ya faru.

Tun misalin sha biyu na dare aka fara ruwan, bai tsaya ba sai misalin karfe uku na dare, har zuwa lokacin ma yana, sauka chaf-chaf.

Ku san a kan kunnen Hafsat aka fara ruwan har aka dauke.

Kuma a cikin kunnenta ta ji karar wani abu gum! Kamar a diro katanga saitin dabbobinta. Saboda ta ji sautin tashinsu gabadaya alamun sun firgita.

Sai kuma ta ji kukan tunkiyarta uwar garke sau daya, daga nan Commander ma ya yi kuka sau daya. (wani babban rago ne, wanda baya daukar raini, shi ke jagorantar garken dabbobin nata. Shi ya sa ta sanya mishi commander “

A hankali ta mike zaune hade da lekawa ta yar karamar windows din da ke dakin, Sai take ganin kamar duhun mutum a cikin garken.

Can kuma sai ta ji kukan akuyarta yar fara. Ita dama ba ta iya jurewa sabon abu, ta faye koken banza.

Cikin rashin tsoro Hafsat ta rarrafo daga cikin dakin zuwa waje.

Fitar ta tsakar gidan taga ana kokarin fita da akuyar daga cikin garken zuwa saman katanga.

Da gudu ta yi kan mai daukar Akuyar tana fadin “Waye? Ina za ka kai min Akuya”

Daidai lokacin ya yi sama da akuyar wanda hakan ya tabbatar mata akwai wanda zai karba daga can waje.

Ai da sauri ta rike wandonshi kam ta wurin kugunshi cikin daga murya take fadin “Baba! Babanmu!! Inna Kuluwa! Ga wani nan zai daukar min akuya. Babanmu”

Abun ka da dare take muryar tata ta karade ilahirin cikin gidan har da makota.

Irin riko da kuma ihun da take yi, gami da kukan akuyar ya sa ɓarawon sakin akuyar dole.

Amma ya juya kan Hafsat ya shiga dukanta ta ko ina a kokarinshi na son guduwa, Sai dai duk irin dukan da yake mata ba ta bari ya gudu  mata ba.

Duk wani lokaci ya kan yi nasarar kwacewa har ya kama katanga, amma cikin karfin hali sai ta kuma jawo shi. Ga bakinta bai mutu ba. Ihu take tana karawa ba ƙaƙƙautawa.

Babanta ne ya fara fitowa daga cikin daki a firgice hade da dallare su Hafsat da touch light din hannunshi.

Tsaf ya haske fuskar Danjuma da suke ta shan kokawa da Hafsat yana ta haurinta gami da nushi

“Kai! Kai!! Kai!!!” Malam Ayuba ya fada cikin tsawa hade da rugawa da gudu zuwa inda suke

“Danjuma! La’ilaha’illalahu! Danjuma!”

Cewar Malam Ayuba cike da mamaki gami da bacin rai.

Danjuma ya dakata da dukan da yake kaiwa Hafsat

“Don ubanka kashe ta za ka yi? Wato kai ne ɓarawon da ka zo yin satar kenan”

Komai Danjuma bai ce ba. Haka ma mutanen gidan da suka fito babu wanda ya tanka, Sai dai ko wane fuskarshi dauke da mamaki.

“Ni ban daukar mata komai ba” cewar Danjuma cikin hakki saboda kokawar da suka sha.

Cikin kuka Hafsat ta ce “Wlh karya yake yi, ya mika ma wasu a waje Ragona commander, kuma dama ranar an sace min waya da awakina guda biyu, uwar biyu da kyalla”

“Ke! Don uwar ki nine na, daukar miki wayar?”

Cikin kuka ta ce “Ba dai uwata ba wlh”

“Zan kakkaryaki wlh”

“Kai ne zan kakkarya ai, mutumin banza ɓarawo, Allah dai ya tsinewa halinka Danjuma, ga ka babba, amma na banza, girman ɗankatakore girma ba hankali. Yanzu kanwar taka kake yi wa sata?”

Cewar Malam Ayuba cike da bacin rai

“A’a Malam, ba fa zan yarda ba, ya ce ba shi ya dauka ba, ko ta ganshi da awakinta ne?” cewar Inna Kuluwa a kokarinta na kare Danjuma duk kuwa da ta san halinshi a bangaren sata

“Ke matsa can! Za ta yi mishi sharri ne, tun da Hafsat take a gidan nan ta taba cewa ga abin da aka yi mata? Bayan kuma na san kuna yi mata din.”

Cikin kuka Hafsat ta ce “Wlh ba ƙarya na yi mishi ba, dabbobina guda 15 ne, a ƙirga su yanzu a gani”

“Ke amarya ƙirga min dabbobin nan”

Amarya Murja ta matsa sosai cikin garken ta shiga ƙirga dabbobin, bayan ta gama ta ce “Guda 12 ne yanzu”

Malam Ayuba ya dallare fuskar Inna Kuluwa da touch light Yana fadin “Kika ce karya aka yi mishi?”

Ya juya kan Danjuma “Don ubanka ina ka kai mata dabbobinta? Kai da waye kuka daukar mata a awaki?”

Ai kawai sai Danjuma ya dankara da gudu, wannan ya kara sanyawa suka gasgata lallai shi ne ya dauki awakin.

Sai fadan Malam Ayuba ya koma kan Inna Kuluwa, suka yi ta yi har asuba. Abin da ya ba Hafsat mamaki kenan, ba ta taɓa tunanin zai tsaya mata haka ba.

Yadda ya yi ba karamin dadi ya yi mata ba, ko ba komai ya nuna musu ita ƴa ce, kuma yana son abar shi.

Dakyar ta iya alwala, saboda Danjuma duk ya naushe mata ido gami da baki, hannu ne kamar rodi. Shi ya sa tana yin sallahr asuba sai bacci.

Cikin bacci ta kuma jin sabon rikici ya ɓalle a cikin gidan, Inna Kuluwa har da kuka, wai Malam Ayuba na fifita Hafsat a kan sauran ƴaƴan shi.

<< Abinda Ka Shuka 31Abinda Ka Shuka 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×