Da rarrafe ta fito, tsakar gidan ba kowa sai kannenta da suka yi la’asar alamun kowa na jin yunwa.
Biscuit ɗaya ta basu cikin biyu da ta dakko sannan ta fice
A hankali kuma a nutse take tafiya, kamar ba ta son zuwa, inda ta dosa din.
Kallo daya za ka yi mata ka fahimci akwai ilimi, nutsuwa da kuma yar karamar wayewa a tare da ita.
Kyawunta na daya daga cikin abin da yake fisgar mutanen kauyen, amma tsoro da fargabar na hanasu isa gare ta. Wai kar su hada iri da mayu.
Shi ya sa ba ta da saurayi ko daya, duk da ya kamata ace zuwa yanzu tana da tsayayyan saurayi, ko ma an zo gaisuwar neman auranta, kamar yadda ake ta zuwa na kawayenta wadanda suke gama makaranta a wannan shekarar.
Kamar wasa, Sai ga shi ta yi nisa sosai a tafiyar tata, har ta na hango rugar Bammi, sai dai maimakon ta nufi can din, Sai ta karkata akalar tafiyar tata zuwa wurin da Tukuro ke kiwo, shigarta dajin kadan ta fara hangen fararen tawagar shanun Tukuro gami da kananun dabbobi har ma da zabbi suna ta kiwo cike da kwanciyar hankali.
Saman bishiyar ƙoƙiya ta same shi.
Zuwanta ne ya sanya shi sakkowa, ka san bishiyar suka zauna, ya mika mata ledar da aka zubo mishi dambun da ya sha tafasa gami da manshanu.
Tana ci tana kuma kallon yadda yake zazzage ƙoƙiyar da ya debo, ta yi yellow shar alamar ta nuna
Yar wukarshi ya sanya ya shiga fafata kamar ƙwarya, da yake yanayinsu daya da ƙwarya sai dai ita kanana ce kuma ana shan ƴaƴan cikinta ne.
Sai da ya fafa guda biyar sannan ya tura a gaban Hafsat, wacce tuni ta gama cin dambun ta kuma dora da ruwa, Sai ta rika shan ƴaƴan cikin ƙoƙiyar cikin jin dadi, musamman kamshi mai dadi.
Sai da suka shanye tas, sannan ya taya Hafsat gyara ɓawon ƙoƙiyar wanda ta ce za ta yi ƙoran wasa. Suka gyara su tsab. Sannan ya juye musu ƙwala, suka shiga fasawa suna ci cike da nishadi.
Ƙwala ƴaƴan bishiyar danya ne, dabbobi ke ci, amma daga baya sai su yi tuƙar ƴaƴan, to a cikin ƴaƴan akwai wani abu kamar gyada idan an fasa.
Sai da aka kira sallahr la’asar suka yi sallah, kafin suka bar jikin bishiyar ƙoƙiyar, zuwa wajen dabbobin su, yayin da suke hira cikin Nishadi.
*****
AHMAD
Misalin karfe 6pm ya sauka gida, kamar ko wane lokaci idan ya kunso damuwarshi zuwa gida, da zarar ya yi arba da ƴan’uwanshi sai ya ji kaso ma fi tsoka a damuwar ya ragu, wannan karon ma haka ta kasance.
Tun da ya iso Hajiya ke sanyawa ana hidima da shi har sai da ya kwanta bacci da dare sannan kowa ya huta.
Idan ka dauke shi da ya kasa runtsawa haka ya yi ta juyi bacci ya ƙi zuwa. Sai wajen biyu saura sannan ya dauke shi, shi ma cike da mafarkan Hafsat, wasu masu dadi wasu akasin haka.
Bayan ya dawo sallahr asuba ma baccin ya so komawa amma fir ya ƙi zuwa, haka ya gaji da juyinshi ya yi wanka
Ya shirya cikin Ash color riga shirt, Wacce hannunta ya tsaya iya gwiwar hannun shi, sai wandon jeans black, Sosai ya yi kyau musamman kamshinshi mai dadi da ya cika dakin.
Yanayin fuskarshi tana nan dai very cool and innocent.
A kan hanyar zuwa part din Hajiya ya daura agogonshi.
Tun da ya fito ma’aikatan gidan ke gaishe shi, har zuwa lokacin da ya isa babban falon Hajiyar wanda yake fitar da kamshin turare mai dadi, yadda falon ya yi shiru sai karatun qur’ani da yake fita a hankali, ya sanya shi samun kujera ya zauna hade da lumshe idanunshi.
Ya dauki kusan minti ashirin a haka kafin Hajiya ta bude kofar bedroom dinta ta fito, sanye cikin riga da zane na atamfa, hannunta kuma rike da Ja’afar, daya daga cikin ƴaƴan kannen Ahmad mata.
Baki bude ta ce “Yaushe ka shigo?”
“Ban jima ba” ya amsa a hankali hade da bude idanunshi a hankali.
“Na dauka ba ka tashi ba”
“Na tashi” ya ba ta amsa hade da gyara zaman shi sosai a kan kujerar yana kallon Ja’afar wanda ya zuba mishi idanu
“Wannan yaron a nan ya kwana?”
“Eh. Maman tashi ce ba lafiya.” Hajiya ta amsa daidai tana kiran layin Asabe
Ba jimawa Asaben ta shigo, cike da girmamawa ta duka kai a kasa gaban Hajiya
“Haɗawa Ahmad break fast”
“To ranki ya dade” cewar Asabe, hade da mikewa zuwa dining area inda aka shirya manyan food flask, da tea flask, GA bowl da plate gami da kananun cups gwanin sha’awa.
Pepesoup din kayan ciki ta zuba mishi, sannan ta zuba doya da kwai kadan a cikin plate, Sai kuma ta, tsiyaya mishi empty tea wanda ya sha kayan kamshi.
“Ranki ya dade! Na kammala”
“To je ki an gode Asabe” cewar Hajiya, kafin ta mayar da hankalinta kan Ahmad tana fadin “Je ka karya”
Ba musu ya mike zuwa dining din, ya fara cin abinci a nutse, yayin da suke hira da Hajiya, da yawan hirar a kan matsalolin family din ne, wasu ya san dasu, wasu kuma a lokacin yake jin labarinsu.
Sai 11am ya fita gidan a cikin wata Hadaddiyar baƙar mota, kai tsaye kuma unguwa Bye pass ya yi wa tsinke, da inda suka fara haɗuwa da Hafsat ya fara, ya kwashe kam 30mns a wurin yana jiran ya ga ko za ta ɓullo, ganin ba ta ɓullo ba ya sanya shi yi wa motar key, zuwa wuri na biyu da suka hadu, nan ma haka ya gama zaman shi bai ga mai kama da Hafsat ba.
Haka ya dawo gida jiki ba ƙwari.
Kwanaki biyun da ya yi a garin safe da yamma sai ya je unguwar Bye pass, amma ko mai kama da Hafsat bai taba gani ba, haka ya koma wurin aiki zuciyarshi babu dadi.
*****
HAFSAT
Yau ma kamar ko wane lokaci, zaune suke kasan bishiyar ɗinya, yayin da Hafsat ta ɗebi ɗinyar da yawa, da zummar yi wa yaran gidansu tsara.
Tukuro kuma naman tsari yake babbakewa cike da kwarewa.
Daga inda Hafsat din take zaune ta saita wata kurciya da danko, sai ga kurciyar a kasa, a guje ta je ta dakko ta, Tukuro kuma ya yanka mata. Shi din ne kuma ya gyara hade da barbadeta da gishiri ya kanga ta a jikin wuta. Ba jimawa suka gasu tare da tsarin Tukuro, suka riga yagar naman cikin jin dadi suna, ci sai da suka cinye tas, sannan suka mike a tare zuwa kan dutse, inda a gefen dutsen ne dabbobinsu ke kiwo. Kafin su karasa ne Tukuro ya nuna wata ciyawa da ke karkashin wata bishiyar geza ya ce “Kin san wannan?”
Ta bi ciyawar da kallo kafin ta ce “Ban san ta ba”
“Sunanshi shashatau, yana maganin tarin da ya ƙi ci, ya kuma ƙi cinyewa. Sannan ana hada asiri da shi, musamman idan mutum ya ci bashi, kuma yana son wanda ke bin shi bashin ya manta, Sai a yi mishi asiri da shi. Ko ya zo da niyyar tambayar bashin sai ya manta. Haka ana haɗawa da shi wajen yi wa budurwar da ba a son ta yi aure asiri. Da maganar aure ta tashi sai kuma maganar ta shiririce”
Cikin gyada kai Hafsat ta ce”Kalle shi da siriri amma sai mugun abu”ta kai karshen maganar hade da dukawa ta tugo shi.
Suna tafiya tana kara kare mishi kallo, maganar Tukuro ce ta dauke mata hankali inda ya ce “Ya ma sunan waccan ciyawar kika ce min kwanaki?” ya yi maganar hade da nuna wata ciyawa da ta mannu da tushen dawa mai purple din fure
“Ƙuduji” Hafsat ta amsa
“Kin san yana maganin hanta wa dabbobi?”
Kai ta shiga girgizawa alamar a’a.
Sai kuma ya ce “Yauwa kin ga bishiyar gamji can, ga ta can da wasu manyan ganye”
Kai Hafsat ta daga tare da fadin “Wacce take kusa da tsuntsun Dalo din can”
“Ƙwarai kuwa ita. To ita ce na ce ki samo ganyenta guda bakwai, amma sai wanda ya fado kasa, kuma kore ba yellow can ba, sannan busasshe ba.”
Kai Hafsat ta gyaɗa alamar fahimta
“Yauwa, duk wanda kika ɗauka sai ki tofa ƙulhuwallahu kafa bakwai a kai, har sai kin tsinci guda bakwai din. Ki zo gida ki jika, Sha da wanka tsawon kwanaki bakwai to ba dai mutum sai dai Allah”
Cikin dariyar Hafsat ta ce “Wai kai duk ina ka san wannan?”
Shi ma dariyar ya yi yana fadin “Idan kina tare da ni, ba wuƙa ba ko bindiga ta bar fasa jikinki, sannan mutum ko a kan kukar mulukiya yake kwana kin fi karfinshi” ya kai karshen maganar hade da takawa da gudu yana yi wa shanun da suke son shiga wata gona tsawa.
A hankali Hafsat ta janye idanunta a kan Tukuro, bai fi Shekara ashirin da biyar ba, amma yana da baiwar sanin magunguna, kuma a hankali yake sanar da ita. Ya kamata ta samu littafi ta rika rubutawa, akwai wani maganin kunama ma da ya fada mata, ranar da ta ga ya dauki kunama da hannunshi amma ba ta cije shi ba.
Cikin sauri ta taka saman katon dutsen, tana fadin “Ya Tukuro ya ma ka ce min maganin kunamar nan?”
“Tsamiyar kasa za ki samu, ki rika tafasawa kina sha”
“Yauwa fa” ta fada alamun ya tuna mata. Tarkacen da ke hannunta ta ajiye tare da fadin “Zan je wurin zanzaryata”
Dariya ya yi idanunshi a kan dutsen da take zanzaryar, ƙa’ida suka hau dutsen sai ta yi je ta zanzara take samun kwanciyar hankali.
Wuri ne mai bisa da santsi, idan ta zauna sai ta zanzara suuuuuu zuwa kasa, Sai ta kuma zagayawa ta hau dutsen ta kuma zanzarowa.
Haka take yi har sai da kanta ta ji ta gaji sannan take bari.
Yanzu ma bayan ta zube tarkacen hannun nata can ta nufa, ta fara zanzarawa cike da nishadi. Yayin da Tukuro ya mayar da hankalinshi a kan kiwonshi.
Sai da ta yi mai isar ta kafin ta dawo wurin shi, gefen shi ta zauna, tana kallon yadda dabbobin ke ta kiwonsu hankali kwance.
A duniyarta idan akwai lokacin da ta kasance cikin nishadi babu tarin damuwa to wannan lokacin ne. Duk da ta rasa abubuwa da zasu sanya ta farin ciki, hakan bai hana Allah yi mata kyautar farin cikin a cikin zuciyarta ba.
Sai kawai ta ji ta komai yana mata dadi.
Yanayin garin ta kalla wanda ya tabbatar mata shidda ta yi da ƴan mintuna.
“Ya Tukuro a tatsar min nonon” ta fada a hankali idanunta a kan dabbobin
Cikin ƙwarewa ya kira daya daga cikin saniyar da suke tatsar nonon, Sai ko ga shi ta ware kanta cikin sama da shanu hamsin da suke wurin, ta tako tinkis-tinkis zuwa wajen su.
Ba yau ne abubuwa suka fara ba ta mamaki gami da tu’ajjabi a kan dabbobi ba. Amma sosai yadda dabbobin Tukuro ke jin magana gami da bin umurninshi yana ba ta mamaki kwarai
“Je ki tatsa” ya fada yana dubanta
Cikin maƙale kafaɗa ta ce “Tsoro nake ji”
Dariya ya yi tare da fadin “zuwa yanzu fa sun saba da ke, ya kamata ki rika gwada yin abubuwa kai tsaye, ta yadda za su kara sabawa da ke”
Shiru ta yi cikin nazarin maganganunshi, Sai kuma ta mike tsaye hade da daukar gorar da ke gefensu ta shiga gangarawa ƙasa zuwa wurin da saniyar ta yi tsaye tana jiran umarni.
Tukuro kuma mikewa tsaye ya yi ta yadda zai iya hango su sosai.
A ɗan tsorace Hafsat ta je gaban saniyar ta yi tsaye suna kallon juna
Daga can saman dutsen Tukuro ya ce “Ba ki san yadda nake yi ba?”
Idanunta a kanshi alamun tsoro ta shiga shafa bayan saniyar, yayin da saniyar ta rika shinshinnata ta ko ina.
Umurnin da Tukuro ya ba ta na ta duƙa ta tatsi nonon ne, ya sanya ta duƙawa a tsorace, nonon ta kama zuwa bakin gorar ta shiga tatsa, tun tana yi a tsorace har ta saki jiki, Sai da ta cika gorar tab, kafin ta fito daga karkashin saniyar, ta shiga shafata a hankali kamar yadda dai ta ga Tukuro na yi.
Daga can saman dutsen Tukuro ya ba saniyar damar tafiya, saiko ta juya tinkis-tinkis zuwa wurin sauran ƴan’uwanta, Hafsat ta bi ta da kallo, cike da godewa Allah da ya halitto ta a mutum, da a saniya ya halitto ta, kila da yanzu ita ce wannan saniyar da aka tatsa.
Tukuro ma gangarowa ya yi daga saman dutsen, saboda shi ma lokacin tashin shi ne, don haka tare da Hafsat suka shiga hada kan dabbobin zuwa gida.
*****
ASMA’U
Zuwa yanzu kam, a hankali AG ya rage kaso ma fi tsoka na damuwarta a kan Mk, sai ta mayar da hankalinta wurin Abdallah da kuma shi kanshi AG, saboda ta fahimci yanzu dai shi din ne ya kamata ta ba igiyar ragamar rayuwarta ya ja ta.
Kuma da alama hakan ya yi mishi dadi hade da kara karfafa mishi gwiwa fiye da baya.
Baya gajiya da hidimarta da kuma Abdallah, duk bayan sati biyu yake zuwa wurinta ya yi kwana daya ya koma.
Da yawan zuwan na shi ya fi zuwa ne da yammacin ranar Juma’a, Sai ya koma da yammacin Asabar ko ya bi jirgin karfe takwas na dare.
Yau ce ranar ta farko da za ta taro shi daga airport.
Shi ya sa ta shirya cikin fara tas din doguwar riga, ta nade fuskarta da veil din, chocolate color fatarta tan fito Shar. Light make up ta yi.
Abdallah kuma shirya shi ta yi cikin farar shirt mai taushi, wacce take da top blue, wandon ma blue ne, yayin da kafafunshi ke sanye ciki farin takalmi mai kyau na yara
Kamshi mai dadi na fita a jikinsu. Yadda suka yi kyau ne ya sanyata riko Abdallah ta yi musu hotuna hade da guntayen videos masu kyau.
Ta fito kafaɗarta ta hagu saɓe da Abdallahn yayin da ta sagala baƙar jaka a kafadarta ta hagu.
Cike da sha’awa Aunty Hajara ta ce “Haba ko ke fa! Amma kullum kina daki cikin kunci, ya kamata ko dan rika zagayawa, hakan zai rage miki damuwa.”
Murmushi kawai Asma’un ta yi kafin ta ce “Bari mu je, na san sun kusa sauka”
“To Allah Ya tsare, ki kuma kula”
“In Sha Allah” ta fada hade da ficewa daga cikin falon
Fitar ta ba jimawa ta samu keke zuwa airport din.
Ta shiga jerin masu jiran saukar ƴan’uwansu a reception.