Skip to content
Part 37 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ba jimawa kuwa aka fara announcing din saukar jirgin. Misalin biyar cif ya yi landing. Bayan ya daidaita passengers suka fara sauka.

Asma’u ta rika kallon yadda mutane reception din ke ta shi zuwa tarar ƴan’uwansu.

Ita ma sai ta mike a nutse hade da saɓa Abdallah ta bi rubibi.

Sai ko ga AG yana sakkowa, kafadarshi sagale da madaidaiciyar jaka irin ta matafiya.

Jikinshi kuma sanye yake da wani yadi fari tas, wanda aka yi wa dinkin zamani mai kyau.

Sosai dinkin ya zauna jikinshi hade da haska farar fatarshi mai nuna alamun tana samun hutu gami da abinci mai kyau.

A yau ne ta kara tantance AG miji ne na nunawa a taro, saboda duk masu sakkowa daga cikin jirgin, babu wanda zai nuna mishi komai ta ko wane bangare.

Da alama ya hangota saboda yadda ya fadada fuskarshi da murmushi, ita ma ba ta san lokacin da ta fara murmusawar ba, har zuwa lokacin da ya sakko suka hadu.

Ba zato ta ji rungume ta, hade da kissing din goshinta, Sai kuma ya zame ta daga jikinsa ya dauki Abdallahn da yake ta zillo hade da miko hannu.

“Oyoyo my little Commando, how are you”

Sai ko Abdallah ya kara kankameshi cike da jin dadin ganinshi.

Duk suka yi dariya a tare, saboda yadda Abdallahn ya yi.

Hannun Asma’u AG ya riko, suka shiga takawa a kokarinsu na barin wurin.

Cikin dabara Asma’u ta zare hannunta cikin na shi. Ta yi wa Allah alkawarin ba za ta kara kusanta kanta da zina ba

“kin yi kyau Gimbiyata” ya yi maganar idanunshi a kanta

Murmushi ta yi kadan kafin ta ce “Kai ma ai ka yi kyau Alhajin, da alama anko mu ka yi”

Siririyar dariya ya yi gami da kallon jikinsu, sannan ya ce “Kuma mun yi kyau”

Kafin ta ce wani abu ya ce “kin iya mota ne?”

A hankali ta shiga girgiza kai alamar a’a

“Ya kamata ki iya, yau sai na ji Ina ma a mota kika zo. Ina son ki fara koyon tuƙi sai a saya miki ke ma. Tun da Maman Nawwara ma tana da ita”

“Zan jaraba”

“Ya kamata”

“Ina muka nufa?” ya yi tambayar hade da gyara zaman Abdallah saman kafadarshi

“Gida” ta amsa a hankali

Wani kallo ya bi ta da shi, wanda ya sa dole ta janye idanunta a kan fuskarshi

“Ba za ki ga masaukina ba?”

Ido ta fitar waje alamar tsoro, Sai kuma ta shiga girgiza kai alamar a’a

Murmushi ya yi kadan kafin ya ce “Matsoraciya”

Siririyar dariya ta yi, idanunta a kan AG da yake tare musu napep.

Daga airport din gidan Aunty Hajara suka yi wa tsinke.

*****

RUMASA’U

Kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar an samu canji, canji na abinci da kuma wurin kwana.

Saboda ta murje hade da ƴar ƙiba mai kyau, fatar nan ta fara yin taushi, bakin nan ya fara zama mai, kyau, sakamakon maya-mayai masu kyau da take amfani dasu.

Mk da ke kan doguwar kujera yana lasar wayarshi hade da kallon shirin da Rumar ke kallo a Arewa24, zumbur ya mike zaune, saboda yana bude status din mutane yana kallo, sai kawai ya ga na Asma’u ya bude.

Hotonta ne sanye cikin farar doguwar riga, fuskarta zagaye da veil din rigar. Ta yi masifar yin kyau. Babu mai ganinta ya ce ta haihu.

Hannu ya sanya gami da danne status don kar ya gudu.

Lokaci daya kuma kirjinshi na yi mishi wani irin bugu da karfi.

Sabon so gami da kewarta suna taso mishi. Rabon da su yi magana wajen wata biyu kenan, shi bai kira ba, ita ma ba ta kira ba. Wannan yana nufin ta yi fushi kenan. Yana son kiranta ya ba ta hak’uri amma yana jin tsoron ɓallo ma kanshi ruwa. Kar ya kira kuma ya tuna mata da kawo mishi yaro.

Ya dage yatsanshi, hoto na gaba ya bayyana.

Yanzu kam Abdallah ya wangale baki, siraran hokoranshi guda biyu sun bayyana. Kayan jikinshi kadai sun isa sun fahimtar da kai yaron yana samun gata.

Ya kafe hoton da ido, yayin da yake ganin Abdallahn na juye zuwa kamanninshi.

Idanu ya lumshe a, hankali kaunar yaron na tsarga mishi cikin jini, Allah Ya sani yana son yaron gami da Asma’un, amma duk sun fi karfinshi, zaman su nesa da shi, shi ne ma fi alkairinshi.

Amma kam ya san ba hadi tsakanin Asma’u da Ruma ta ko wane fanni.

Idanunshi ya bude kan Ruma, wacce ke zaune kan kujera jikinta sanye da doguwar rigar atamfa, kanta dauke da kananan kitso chuku, ta nade karshe kitson hade da soke shi. Gefenta kuma littafan da suka gama karatu ne zube.

Ya dauke idanun nashi zuwa kan hoton Abdallahn da ya dafe da hannu, Sai kuma ya dage hannun, videonshi ya bayyana, cike da kuzari yake kazar-kazar a cikin videon. Ya wuce zuwa nxt picture yanzu kam shi da Asma’un ne cikin fara’ar da ke nuna suna farin ciki.

Next kum a airport ne nan ma video ne hade da waka mai sanyi

Hoton gaba ne ya sanya shi mikewa da sauri zaune.

Saboda Asma’un ce tare da wani, hannunshi sabe da Abdallah, amma ta dade fuskar mutumin da emoji na love.

Kirjinshi ya shiga bugawa da sauri da sauri, wata irin fargaba na kama shi, kar dai Asma’u ta yi aure ita ma?”

Bai san lokacin da ya mike zuwa bedroom ba, ba tare da sanin abin da ya kai shi bedroom din ba.

Haka ya rika safa da marwa, har dai ya amince da zuciyarshi ta hanyar kiran layin Asma’u.

A lokacin ta fara da nisa duk da goma saura na dare, Sai da wayar ta kusa yankewa sannan ta daga, cikin muryar bacci ta ce “Hello!”

Idanunshi ya lumshe a hankali, yayin da yanayin muryarta ya jefa cikin wani yanayi mai wahalar misiltuwa

“kina lafiya?”

“Uh!” ta amsa shi

“Har kin yi bacci”

“Uh!” ta kuma amsawa cike da jin zafin shi

“shi kenan za mu yi waya da safe.”

Komai ba ta ce ba, ta yanke kiran, yayin da shi kuma ya zauna gefen gadon a sanyaye.

A kan Ruma ya warware gajiyar da Asma’u ta tara mishi a cikin yan mintuna.

AHMAD

Yau ma a masallacin unguwar Bye pass ya yi sallahr magriba, Sai da kowa ya fice daga masallacin, kafin ya fito a nutsenshi, yayin da zuciyarshi take cushe da damuwa, tsawon sati bakwai kenan yake rangadi a unguwar, amma har yanzu bai samu, abin da yake so ba.

Ga zuciyarshi ta ki aminta da barin neman Hafsat, yanzu ko sati biyu baya iya haɗawa a wurin aiki, duk sati yana gida, kuma safe da yamma yana unguwar Bye ko Allah zai sa ya ga Hafsat.

Ga shi duk wannan wahalar zuciyarshi ba ta taɓa saduda wajen son ganin Hafsat din ba.

Da kanshi yake tambayar kanshi, neman me yake mata? Idan ya ganta me zai mata? Bayan ganta daga nan kuma sai me?

Sai dai har yanzu bai samu amsoshin tambayoyin ba, shi dai kawai ya ganta.

Da haka ya taka zuwa wurin motarshi, bayan ya yi mata key ya tilla saman lafiyayyen titin kai tsaye kuma AMI Shopping complex ya nufa, kila zai ji saukin nauyin da kirjinshi ya yi mishi.

*****

HAFSAT

Yau Juma’a suka gama exam din su ta 1st term SS3, cike take da farin ciki sosai, ko ba komai za ta huta, za ta samu lokacin zuwa Dawuri, ta ciyo dadi, ko kuma ta samu damar kasancewa wajen dabbobinta ita da Tukuro.

Ana sakkowa daga masallaci Inna Luba na gama abincin rana, danwake ne ta yi, amma babu mai bare yaji, kowa za a mika mishi gaya ne, Sai ka nemo mai da yaji.

Haka kuma ta zuba shi ta mikawa Hafsat wacce ke zaune jikin dakin kajinta tana kwance kai.

Haka ta rika daukar danwaken tana jefawa baki, saboda yunwa take ji ba ta wasa ba, komai na ci ba ta shi a cikin dakin nata ya kare.

A haka ta cinye danwaken tas, ta kora da ruwa, Sai ga shi cikin nata ya dan tasa.

Zuwa la’asar ta yi wanka hade da yin sallah, gidan su Farida take son zuwa.

Riga da zane na atamfa ta sanya, daurin zanen nan ya zauna cif gwanin sha’awa, coffee color din hijab din ta ta sanya hade da fesa turare mai sansanyan kamshi.

A tsakar gidan ta ce “Na tafi gidansu Farida.” babu wanda ya amsa mata, wannan kuma ba sabon abu ba ne.

Sai gab magriba ta baro gidansu Faridan, tana isowa ta yi sallahr magriba, Sai bayan isha’i Inna Kuluwa ta gama tuwon dare.

Nan ma haka aka liko mata shi kamar dole, ta lasa, saboda ba ƙoshi ta yi ba.

Can cikin dare gari ya narke da wani irin ruwan sama mai karfin gaske, kamar zai daga gini.

Cikin bacci ta ji kamar ana kokarin shigo mata daki, da sauri ta farka hade da haska touch light din hannunta Sai ko ga Danladi kanen yana kokarin shigowa

A tsorace ta ce “Danladi lafiya”

“Dakinmu ne zai fadi”

Kafin ta ba shi amsa sai ga sauran kannen nata suna kutsowa, can kuma sai ga Inna Kuluwa ita ma ta kutso kai, duk sun jike jagab.

Shiru ta yi komai ba ta ce ba, Sai sune suke ta surutansu, har suka gaji suka yi shiru.

Inda Allah Ya taimaka dakin yana da fadi, ba shi dai da bisan da za a mike tsaye.

Haka suka tutsu a ciki har asuba.

Abun bai tashi ba Hafsat dariya ba, Sai da ta ga suna fitowa da rarrafe kamar dai kajin, Sai ko dariya ta kufce mata daidai ta sako kai za ta fito.

Inna Kuluwa kuwa ta warware hannu ta sakar mata shi a baya, saboda a fusace take.

Duk hayaniyar da suke yi, a daren jiyan Malam Ayuba bai leko ba, kuma ta tabbatar yana ji. Saboda kawai yana dakin amarya ne.

Hafsat ta karasa fitowa hade da dukawa gefe ta shiga kuka cikin silent murya Shi ya sa babu wanda ya ji a gidan.

A haka ta yi alwala hade da yin sallah, yayin da Inna Kuluwa da yaranta ke ta faman kamkamta kayan dakinsu waje daya. Inna Luba na taya su.

Yadda Hafsat ta ga an wayi gari a gidan kowa kanshi a sama, ya sanyata sulalewa tun bakwai ta nufi ruggar Bammi.

A can ta ci dumamen tuwon masara miyar kuka da manshanu. Sannan Jaɓɓa ta yi mata kitso zanen kwance guda takwas.

Sai fuskarnan ta fito fayau, baƙin gashin girarta ya kara fita fiye da baya.

Sai da ta yi sallahr azhur ta kuma ci tuwon rana, sannan ta dauki na Tukuro don ta kai mishi.

Tun da ta ɓullo ta hango shi kan dutse zaune, wannan ya tabbatar mata da ya kai dabbobi sun sha ruwa ne.

Kai tsaye kan dutsen ta dosa, tana kokarin aje abincin ne ya ce “Amma kitso aka yi miki?”

“Ya aka yi ka sani?” ta yi tambayar bayan ta aje abincin

“Alama na gani a goshinki”

Dariya ta yi lokaci daya kuma tana shafa goshin kafin ta ce “Kawai ka fito ka ce ina da katon goshi Ya Tukuro”

Shi ma dariyar ya yi lokaci daya kuma yana wanke hannu.

Sai da ya yi loma daya sannan ya dakata da dariyar yana fadin “Ba laifi kam akwai shi”

Ta kara sautin dariyarta hade da jawo jakar gefenshi saboda ta san ba za a rasa abun ci ko sha ba.

Sai ko ga kaɗanya (Taɓo) a ciki.

Maimakon ta dakko, Sai ta daga jakar ta zazzage.

Wata irin kara ta fasa hade da mikewa tsaye ta watsa da gudu.

Karar da ta dakatar da kaso biyu cikin ukun na dabbobin daga kiwo. Duk sai suka yi cirko-cirko suna kallon yadda take gangarowa daga kan dutsen a matukar kidime.

Sai da ta tabbatar ta sauka kasa, sannan ta juyo tana hangen Tukuro da tun dazu yake sanar da ita macijin matacce ne.

“Na fada miki na kashe shi, ke matsalarki kenan tsoro”

Ya yi maganar da alamun jin haushinta

A darare ta ce “To me za ka yi da shi, ba sai ka yar ba”

Komai bai ce mata ba, ya shiga nade macijin kamar yana nade igiya, bayan ya gama ya cusa shi cikin jakar yana fadin “Sai ki zo ki zauna ai, matsoraciya”

Jiki a sanyaye ta rika hawa saman dutsen, har ta isa dan nesa da shi sannan ta zauna, shi kuma sai ya watsa mata ƴaƴan kaɗanyar, cikin rashin karsashi take sha.

“Don Allah Ya Tukuro me za ka yi da maciji?”

Ta yi mishi tambayar da ke damunta

“Na ce miki so nike, amfani zan yi da kitsen”

“Hala maganin?”

Yadda ta yi tambayar ne, ya sanya shi murmusawa.

“Ya aka yi ka kama shi?”

“A cikin raminshi na koro shi”

Ido ta waro tare da fadin “Ya aka yi ka san raminshi ne?”

“Har ramin aljani na sani” ya amsata daidai yana suɗe kwanon.

“Za ka iya, tun da ƴan’uwanka ne”

Cikin dariya ya ce “Ni din aljani ne?”

“Yo daban ne Ya Tukuro, kodai ba shi ba ne kana aiki dasu” a shagwabe ta yi maganar.

Sautin dariyarshi ya kara hade da fadin “Ba na aiki da su”

Harara ta aika mishi kafin ta ce “Duk a ina kake sanin magungunan da kake fada min, idan ba sune suka fada ma ba? Ranar can muka ga maciji ka ce wai mace ce ƙwai za ta je ta yi. Ya Tukuro ta ina ka san macen maciji”

Cikin dariya ya ce “Kai Hafsat Allah Hoini wollah”

“Haka ranar can zan shiga ruwa ka ce kar in shiga akwai bakon ruwa, don Allah ta ya ka tantance bakon ruwa da ɗan gari? Kuma ranar can ma cewa ka yi wai waccan bishiyar tsamiyar baƙi sun sauka kar in kora dabbobi zuwa can. Haka watarana kana ganin mata da goyo ka ce wai ɗan ma na bayanta ya rasu, Sai ga shi kuma ta dawo tana kuka, wai ba ta san ya rasu ba sai da ta kwanto shi likita zai duba shi. Abu yana lullube ta ya ka san ya rasu? Idan rami ka gani ka iya fadin wannan ramin kusu ne a ciki, wannan na gafiya ne, waccan na bushiya ne, wannan tsari ne a ciki, wannan kuma damo, wancan na maciji ne, haka dai, ko wane rami ka san abin da ke ciki, kamar ka shiga ka gani. Ko suna fada ma sune a ciki? “

Wata irin dariya yake yi sosai, yayin da Hafsat ke ta aika mishi harara.

Cikin dariya ya ce” Ko ke na san abubuwa da yawa a kan ki Hafsat ban dai fada miki ba ne kawai “

” To me ya sa ba ka fada min ba? “

“Haka nan”

“Kana duba ne?”

Kai ya shiga girgizawa a hankali kafin ya ce “Wlh ba na duba, haka kawai Allah Ya yi min wannan baiwar, Sai ina karantar abubuwan da suka shafi mutum a kan fuskarshi. Idan na ga mugu ina ganewa, idan kuma na ga mutumin kirki ma ina ganewa. Sannan na kan rika jin kaza zai faru da wane, Sai kawai ki ga ya faru din. Magunguna kuma wlh Allah ne ke sanar da ni, ni kaina ba na ce miki ga yadda aka yi na san kaza zai yi maganin kaza ba. Ni dai da zuciyata ta amince shi kenan, Sai ki ga maganin ya yi. Da haka na san maguna da yawa.

Wuri kuma idan bai da kyau sai in ji tsigar jikina na tashi, zuciyata ta ƙi aminta, Sai in fahimci abu bai da kyau. “

“Ya akai kake gane mara lafiya zai rasu to. Ranar can da mu ka je duba Laminu, ka ce rasuwa zai yi, sai ga shi kuma ya rasun”

“ji na yi yana warin gawa”

Cike da mamaki ta ce “Warin gawa kuma?”

Kai ya jinjina alamar eh, sannan ya ce “Idan mutum zai rasu, da ya kusance ni sai in ji yana warin gawa, idan kuma kwance yake ina shiga dakin sai in ji warin gawa.

“Innalillahi! “Hafsat ta, fada a, firgice.

<< Abinda Ka Shuka 36Abinda Ka Shuka 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×