Skip to content
Part 38 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Shi kuma ya yi dariya, ba, tare da ya ce komai ba.

“Ya Tukuro wallahi ka fara ba ni tsoro. To ni me ka sani game da ni?”

“Abubuwa da yawa, wasu sun faru, wasu kuma har yanzu basu faru ba. Sai dai in fada miki wanda zai faru kwanan nan”

“ina ji” ta fada hankalinta kaf a kanshi

“Akwai wani mutum da yake ta neman ki…”

“Me zan yi mishi?” Hafsat ta yi saurin katse shi

“Allah kadai Ya baiwa kansa sani, amma yana neman ki, kuma yana a wani gari mai yawan gidaje da ababen hawa, Sai dai ban san wane gari ba ne”

“To zai ganni?” Hafsat ta kuma tambaya cikin rashin gamsuwa da maganarshi

“Ban sani ba gaskiya”

Murmushi ta yi mai ma’anoni da yawa kafin ta ce “To sai kuma me?”

“Sai kuma za ki yi aure kwanan nan”

Yanzu kam dariya ta fashe da ita kafin ta ce “Gaskiya a wannan karon ka fadi, ni da ko saurayi ba ni da shi”

Shi ma cikin wata irin kalar dariya ya ce “To ni dai sau uku ina mafarkinki kina a kan doki, wannan ya tabbatar min da za ki yi aure nan ba da jimawa ba”

Cikin wata dariyar ta ce “Gaskiya ban yarda da wannan hasashen naka ba Ya, Tukuro. Ta ina zan yi aure kwanan nan? Tun da nake ban taba jin ko Mama Halima ta yi maganar aurena ba, bare Babanmu”

“To za mu ga ni, ni da ke waye zai ci wannan wasan”

“Shi kenan mu zuba…”

AHMAD

6:00pm

Yau kam rai bace ya baro unguwar Bye pass, duk yadda yake son tursasa kanshi wajen ganin ya daina wahalar neman Hafsat ya san zuciyarshi ba za ta ba shi hadin kai ba.

Saboda ba tun yanzu yake son yin hakan ba, amma baya sanin ya je unguwar Bye pass sai yana dawowa rai bace idan ban ganta ba, yake tuna kudirinshi na daina neman nata.

Tsawon watanni biyar da yake neman ta, kullum son ganinta kara azalzalar zuciyarshi yake yi, yayin da mafarkanta ke taya shi bacci. Hade da debe mishi kewar rashin mace a kusa da shi. Da tunaninta sai ya ji kamar tana gefenshi ne.

Slowly yake tukin, har zuwa lokacin kuma zuciyarshi zafi take yi mishi. Ba zai ce ga, dalilin shi na bin titin da zai sada shi da babbar kasuwa ba, kawai da ya gan shi, a kan titinyayin da cunkuso ababen hawa da na mutane ya kara sanya shi jan motor a hankali. Ya san cunkuson ba ya rasa nasaba da yadda yamma ta yi kowa na kokarin zuwa gida.

Dayan tsallaken titin ya mayar da hankalinshi, inda nan din ma a cunkushe yake da ababen hawa da kuma mutane.

Wani shock ya ji, lokacin da ya yi tozali da fuskar Juwairiyya ta fito daga wani shagon Pos hannunta rike da leda, gefenta kuma wani matashin saurayi ne, yana mata magana, Sai kuma ya ga sun yi dariya a tare, hade da tsayawa a gefen shagon suna ci gaba da magana.

Da wani irin hanzari ya rika neman wurin parking, bai damu da yadda yake saɓa dokokin tukin ba.

A cikin cunkuson ya gangara gefe daidai wani shagon katifu ya Parker.

Yadda ya fito da wani irin hanzari zai tabbatar maka da ya samu irin training din irin wannan fitar ta gaggawa.

Har ya fito Juwairiyya na kofar shagon tare da saurayin, Sai dai tun kafin ya samu damar tsallakawa bangaren da take ya ga ta tare mashin, shi ma saurayin ya kara gaba.

Ji yake kamar ya kama mutanen wajen kawai yayi ta duka, wani ɓacin rai yake ji wanda ya fi wanda ya taho da shi, hakan bai hana shi tsallakawa zuwa shagon Pos din ba.

Maimakon ya tambayi dalilin zuwan na shi shagon, Sai ya ji kamar ya fado, musamman yadda ya ga mai shagon ya nuna kamar ya san shi

ATM ya mika mishi ba tare da ya ce komai ba.

Bayan ya sanya katin cikin ATM machine din ne ya ce “Yallaboi nawa za a cire”

“Ko ma nawa” Ahmad ya amsa a hankali bayan da hankalinshi ya dawo kan mai Pos din

Cikin rashin fahimta ya ce “Ban gane ba”

Sai a lokacin ya fahimci abin da ya yi, don haka cikin dakewa ya ce “Cire 50k”

“Sa pin din” cewar mai Pos din, a lokacin da yake mika mishi machine din”

Yana tsaye mai Pos din ya gama ƙirga kudin cif ya mika mishi.

Ya amsa cikin rashin sanin abin da zai yi da su, ya fito shagon jiki ba ƙwari.

Har ya kusa fita shagon sai kuma ya dawo, dawowar da gangan jikinshi sam ba ta so ba. Zuciyar shi ce kawai ke bukatar hakan. Shi ya sa fuskar shi take hade kicin-kicin komai baya mishi dadi.

“Ka san yarinyar da ta fita shagonka yanzu ba da jimawa ba?” Ya jefawa mai Pos din tambayar ba tare da ya san ya yi ta ba. Har zuwa lokacin kuma fuskar shi a hade take

Wannan ya sa mai Pos din ya dan tsorata, har tsoron ya bayyana a kan fuskar shi. Hakan ya sa Ahmad sassauta daure fuskar da ya yi

” Wacce kenan?”

“Wacce ta fita yanzun nan, har ta tsaya da wani a nan kofa suna magana”.

Shiru mai Pos din ya yi kafin ya ce “Wata fara ko?”

Kai Ahmad ya jinjina alamar eh kamar baya so.

“Gaskiya ban san ta ba, duk lokacin da ta shigo kasuwa dai mostly a nan take cire kudi”

“Da yaushe take zuwa kasuwar?”

“To ya danganta, wani lokaci a sati sai ta zo sau biyu, wani lokaci kuma tana jimawa gaskiya, kamar yanzu ma ya kai wata uku ma ban ganta ba”.

Lumshe ido Ahmad ya yi cike da jin haushin yadda bikin zuwa ya samu amma babu zanen ɗaurawa, yanzu kuma bai san me zan yi. Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya ce “To wanda suka fita tare fa?”

Nan ma shiru mai Pos din ya yi kafin ya ce “AK ne”

“Ya za a yi in hadu da shi?”

“Eh to yana dan zuwa shagon nan sai dai ba sosai ba, kuma wallahi ba ni da lambar shi.”

50k din Ahmad ya aje mishi akan kanta tare da fadin “Ka yi amfani dasu wajen nemo min lambarshi, ko kuma idan ya zo shagon ka kira ni. Please ba na son ya dau lokaci” daga haka ya lalubo katinshi ya aje saman kudin ya juya zuwa inda ya yi parking din motar shi.

*****

ASMA’U

Zaune take cikin falo suna kallo, zaman da ya yi wa Aunty Hajara dadi, tana son ganin Hafsat cikin jama’a, hakan ba karamin dadi yake yi mata ba.

Abdallah kuma koyon tafiya yake yi, yadda yake daga kafar da aje ta, ba karamin dariya yake da sanya su ba.

Ba tare da Aunty Hajara ta dakatar da dariyar da take yi ba ta ce “Yaro ya girma saura yaye”

Murmushi Asma’u ta yi tana fadin “Haka AG ma ya ce last week da ya zo. Wai Abdallah ya ƙi yin tafiya ne saboda ba ya son a yaye shi.”

“Da gaskiyarshi ai, tun yaushe yake gwada mikewa”

Suka yi dariya a tare kafin Aunty ta ce “kuma ko yanzu kika yaye shi ba shi da matsala fa. Yanzu ranar can ba wuni ya yi wurin su Momy ba, tun safe sai yamma”

Komai Asma’u ba ta ce ba, hakan ya sa Aunty Hajara dorawa da “Wlh Asma’u kar ki bari Abubakar ya sille miki, zai wahala ki samu wani”

Kamar Asma’un ba za ta ce komai ba, Sai kuma ta ce “Ni ba na son auran nesan nan kuma Aunty”

“To me ye, ina ne aure ba ya kai ƴa mace? Kin san Allah Abdallah yana kara wata biyu ni da kaina zan yaye shi, in kuma ce Abbakar ya turo a yi maganar aure. Wannan wahala da yake ina dalilinta. Ya yi miki, ya yi mana ya yi ma yaronki, Haba ido ba mudu ba ai ya san kima Ma’u. “

” Wallahi Aunty tsaron zama da kishiya nake yi”

“Kuma dai. Da kin ce auran nesa, yanzu kuma kishiya, ina, ruwanki da ita. Kila ma ba gida daya zai aje kuba”

“Du biyun Aunty” cewar Asma’u kamar za ta yi kuka

Zama Aunty ta gyara tana fadin “Zama da kishiya kam ba shi da daɗi, Sai dai a yi zaman hakuri. Kodayake ko ba kishiyar ma aure dan zaman hak’uri ne. Amma idan Allah Ya kaddara Abbakar mijinki ne kuma za ku zauna gida daya da matarshi, to dole ki zamo mai hakuri, Juriya da kuma kawar da kai. Ki zauna da ita da zuciya daya, ki kyautata mata ita da yaranta ban da yawan kai kara ko yawan korafi kuma”.

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, ban da kaddara ta ratso rayuwarta, da yanzu wata ce za ta rika fargabar haduwa da ita. Kila ma ba za ta san wani abu kishiya ba.

Tana zaune cikin dadi, ba tare da damuwar komai ba, kaddara ta yi wankan tsarki ta fada mata, babu ranar da za ta daina nadamar abin da ya faru da ita. Kila ma nadamar gaba sai ta fi ta yanzu lokacin Abdallah zai fahimci kanshi, sannan kuma ya san a ta hanya mara kyau aka same shi. Ba ta san wane irin kallo zai yi mata ba, ita kanta ba ta san da wane idon za ta kalle shi ba.

*****

RUMASA’U

Yau dai da wani irin matsanancin ciwon mara gami da baya ta tashi, komai cikin karfin hali take yin shi.

Ga Mk ya tafi aiki, tana sallahr azhur ta ji abu na bin kafafunta, da sauri ta yanke sallahr hade da dage zanenta.

Jinin da ta gani ba karamin tsaro ya ba ta ba, duk da ta dauki tsawon watanni uku ba tare da ta gan shi ba…

Bedroom ta koma hade da gyara jikinta kamar dai lokacin da take al’ada.

A hankali kuma ta ji zubar jinin ya wuce tunaninta, har tunkudo kunzugun da ta yi yake yi. Cikin kankanen lokaci sai ga ta cikin jini face-face.

Da kuka ta kira Mk a waya ta sanar mishi, ga shi a Maafa yake aiki, sai can gidansu ya kira aka yi asibiti da ita.

Basu sha wuya wurin ganin likita ba, tun da dama Babansu Mk sune ke da garin.

After some minute aka tabbatar musu Ruma ta samu miscarriage, amma tana lafiya.

Mk ma ba a tashi ba ya nufo gida, kai tsaye kuma ya zarce asibitin, yadda ya ga Ruma da sauki sai ya dan samu relief, Sai washegari da safe aka sallame ta.

A can Malamawa kuma Alaramma ne ya kwaso su Yaya zuwa duba ta gida.

Bayan ya aje su gidan Ruma ya wuce wurin Alhaji Bashir.

A nan Alhaji Bashir ke mishi tayin shigowa cikin gwamnati a dama da shi. Akwai wani wuri gwaggwaɓa da ya yi mishi tanadi.

Kuma yana da vacancy na mutum biyar, don haka cikin yaranshi ya kawo mutum uku.

Cike da murna Alaramma ya ce “Akwai yara kam, ko guda dari ake so, to za a samu bare uku. Amma Alhaji ya tsarin yake?”

“Ma Sha Allah! Ai abu ne mai sauki, za su kawo takardun haihuwa, sai shaidar kammala primary da secondary. Idan akwai wata takardar shaidar karatu duk za a iya kawowa”.

Fuskar Alaramma ta fara canjawa zuwa wani abu daban kafin ya ce “Dole duk sai da wannan?”

“Ai Malam aiki irin wannan dole a samu wadannan takardun”.

Cike da sanyin jiki Alaramma ya kuma cewa “To nawa bangaren fa”.

“Shi din ma kamar wannan ɗin ne Allah Ya gafarta Malam”

“Ku matsalarku kenan ƴan boko, komai sai da takarda, me ye wani takardar haihuwa bayan ga mutum tsaye gabanku kuma kowa ya san iyayenshi, mutum zai fado daga sama ne?”

Dariyar manyan Alhaji Bashir ya yi tare da fadin “Haka tsarin yake ne Allah Ya gafarta Malam”

“To idan babu fa?” Alaramma ya kuma tambaya.

Shiru Alhaji Bashir ya yi kafin ya ce “Ya kamata ace akwai din, saboda wannan babbar dama ce, ka ga kamar kai, idan har na kawo kujera ta, aikin da nake son ba ka, za ka iya daukar 150k a wata daya. Yaran kuma za su iya samun 50k a wata”

Cikin zaro ido Alaramma ya ce “Gaskiya wannan babbar dama ce, ba zan so ta wuce ni ba. Yanzu ya zan yi kenan?”

“Zuwa za a yi samo takardun, in ya so a zauna jarabawar fita daga secondary, shi kuma primary certificate din sai a biya kudi a samu”

Kai Alaramma ya shiga jinjinawa a hankali, yayin da zuciyar shi ke kai kawo, ba zai so ya rasa wannan damar ba, amma kuma daga shi har yaran nashi babu mai takarda ko ta haihuwa bare ta gama makaranta. Dole ya nemo mafita kar ya zama ga koshi ga kuma kwanan yunwa.”

Haka suka baro garin zuciyarshi fal tunani, tare da lalubar ta ina zai fara.

Primary certificate kam zai samu, amma ta ya zai fara rubuta jarabawa, jarabawar da bai san ya ake rubutata ba ma.

Sai dai ya tuntubi masana abun, su yi mishi karin bayani.

Bayan kwana biyu da zuwan su Alaramma Goggon Ruma ma ta zo a karo na farko. Sosai ta ji dadi gami farin cikin ganin inda ƴarta ke rayuwa. Ko a mafarkin ba ta taɓa tunanin Ruma za ta yi aure a wannan gidan ba.

Matsala daya take hango ma ƴartata ita ce ta rashin wayewa gami da ilimin zamani. Abin da ta fahimta duk masu shigowa duba Ruma ƴan gayu ne, da ilmi ya yi musu ado da kwalliya.

Koda aka yi mata rakiya ma gidansu Mk sai ta ji ta kamar wata almajira, duk irin yadda take ganin ta ƙure adaka, sai ta ga ko ƴan aikin da ke gidan ma sun fita kyan kalla.

Shi ya sa lokacin da ta dawo gidan Ruma jiki a mace ta ce “Ya kike rayuwa da mutanen nan,  gayu ƴan boko”

Fuskar Ruma ta canja zuwa yanayin damuwa kafin ta ce “Wasu lafiya kalau babu matsala, wasu kuma akwai rainin wayau”

“Ai na san za a rina, kina ganin ko wace mace fes, da faska-faskan waya a hannu”

Dariya Ruma ta yi tana fadin “Ni da Baba Alaramma zai bar ni ma da makarantar na shiga, Allah Goggo ba na jin dadi. Ki ji suna ta turanci ni sai dai in yi gum. Sai yanzu ne ma na iya hada baƙi kadan”

“Ba komai, ai ke ma kin iya karatun qur’ani, a qur’ani ina ne ba ki sani ba?”

<< Abinda Ka Shuka 37Abinda Ka Shuka 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×