Skip to content
Part 41 of 43 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

*****

RUMASA’U & MK

Wannan shi ne karo na biyu da Ruma ta yi bari, Sai dai wannan karon barin wata biyu ne, sabanin wancan karon da ya zama na wata uku.

Sannan wannan lokacin ba ta sha wata wahala ba, kamar wancan lokacin.

Ɓarin na Ruma ba karamin dagawa Mk da masoyan Ruma hankali ba, bayan ɓarin har asibiti ya kai ta, amma Iyakar bincikensu basu gano wani abu da yake kawo mata ɓarin ba.

Shi ya sa Alaramma ya ce za a rika yo mata rubutu tana sha. Aljanu ne ke shafar cikin sai ya bare.

Shi ya sa duk ranar kasuwar Malamawa Alaramma ke aikowa da Ruma rubutun sha na kwanaki bakwai.

Shan rubutu ba bakon abu ba ne a wurin Ruma, shi ya sa ba ta wasa da shan, kullum za ta sha kulli daya kamar yadda dokar shan rubutun take.

To Allah Ya sa a dace.

Jama’a ku zo mu raka Madiddi garin Nasara…

*****

AHMAD

Friday 10am

Tsaye yake gaban mirror yana karewa kwalliyar tashi kallo , shi kanshi ya yaba ya kuma ba kanshi maki mai girma, sai yake jin ina ma kai tsaye wurin wacce yake muradin gani zai dosa.

Turare ya kara fesawa sannan ya fice zuwa sashen Hajiyarshi.

Kamar dai ko wane lokaci haka ya rika amsa gaisuwa ƴan aikin gidan har sai da ya shiga falon Hajiyar, a lokacin waya take amsawa. Dalilin da ya sanya shi neman wuri ya zauna, yana sauraron ta.

Bayan ta gama amsa wayar ta dube shi da kyau kafin ta ce “za ka je wani wuri ne?”

“Eh zan je Nasara ne” ya  amsata hade da gaishe ta

“Za ka koma wurin aikin ne kuma tun yau?” ta kuma jefa mishi wata tambayar bayan ta amsa gaisuwar ta shi.

“A’a zan je yin wani abu ne, ba zan jima ba ma Sha Allah zan dawo”

“To Allah Ya tsare, za ka tafi da ƴan rakiya ne?”

Kai ya girgiza alamar a’a

“To amma dai sai ka karya ko?”

Bai ce komai ba ya nufi dining area din, Hajiya ta bi shi da kallo, tana yaba kwalliyar tashi a zuciyarta.

Koko da kosai ya sha, yana son koko sosai, ko kunun tsamiya da kosai, bayan ya gama ya cire tissue hade da goge bakin shi.

Sannan ya ce bari in je wurin” Alhaji” (haka suke kiran Galadima.

“Daga can za ka wuce?” Hajiya ta kuma tambaya

“Eh” ya amsa ta daidai yana tsaye a tsakiyar falon

“To Allah Ya sa aje lafiya a kuma dawo lafiya”

“Amin Ya Rabbb” ya amsa hade da ficewa gabadaya daga falon.

Gudu ya yi sosai shi ya sa 11:30am yana cikin garin Nasara, dalilin da ya sanya shi turawa Juwairiyya text cewa ya shigo.

Ba jimawa ta turo mishi da na ta sakon kamar haka “_Idan ka shigo cikin makarantar ka zo female gate, Sai ka sanar min_”

Bayan ya karanta sakon, sai ya dauki hanyar da za ta sada shi da makarantar, kasancewar yana da ido sosai a Nasara, ya taba yin zaman watanni shida a garin.

Tun da ya shiga school din yake karewa gine-ginen makarantar masu daukar hankali ido, komai tsab babu kazanta, ga gine-ginen a akan tsari. Yayin da daliban ma suke a kan tsari, saboda tun da ya tunkaro makarantar yake cin karo da su maza da mata.

Bai sha wahala ba ya isa female gate Kamar yadda ta shaida mishi. Ya kuma tura mata text din ya iso.

Yana daga cikin mota ya hango fitowarsu su biyu.

Gabanshi ya shiga faduwa yayin da zuciyarshi ke bugawa fat-fat, har yana ganin yadda rigar shi ke dagawa a hankali.

Tabbas sune, mutum daya ce babu, wato wadda yake nema, ko me ya sa ba ta? Ya tambayi kanshi, kafin ya samo amsar sai ga kiran Juwairiyya.

“A ina kake?”

“A wajen gate” ya amsa idanunshi na kanta, yana kallon yadda take waige-waigen neman shi

Kafin ta ce “Kwatanta min”

“A cikin wata bakar mota” ya fada hade da yanke kiran, saboda a wurin dai babu wata mota sai ta shi.

Juwairiyya ta kalli Nabila bayan ta sauke wayar tare da fadin “Bala’i! Wai shi ne a cikin waccan bakar motar”

Cikin waro ido Nabila ta ce “Ah dole ya yi shan kamshi, yana da dalilin. Wancan motor ai sunanta wane yaro”

“Ai ni na kosa ma in ga shi wlh, in ga kalarshi” cewar Juwairiyya

“Ni kaina” Nabila ma ta fada. Suka yi gajeriyar dariya a tare, saboda sun zo gab motor.

Isar su wurin ya yi daidai da ɓalle murfin motar, ya zuro kafafunshi masu dauke da farin half cover na maza mai shegen kyau, yayin da farin wandon da ke jikinshi ya kara kawata takalmin na shi.

Ba jimawa ya fito gabadaya sanye cikin lemon green shirt mai dogon hannu, wacce ta lafe a jikinshi kamar wa shi kadai aka yi wa irin ta saboda yadda ta karbin jikin na shi.

Cikin second kamshin shi ya toshe kofofin hancin su Nabila.

Wadanda suka yi tsam, ko iya kallon inda yake ba sa son yi, take ya yi musu wani irin kwarjini, duk wani rashin ji da raini na ƴanmata da suka zo da niyyar yi mishi, sai suka neme shi suka rasa.

Sosai suka nutsu kamar tuwo a kula.

Kamar mai koyan magana Juwairiyya ta ce “Sannu da zuwa ina wuni?”

“Lafiya kalau, ya school?” ya amsa kamar dama jiran gaisuwar tata yake yi

“Alhamdulillah! Ka zo lafiya?” duk maganar da take yi ba ta dago kanta ba. Nabila kam kamar wacce aka kulle wa baki, ta kasa furta komai

“Alhamdulillah na zo lafiya”

“Ma Sha Allah” Juwairiyya ta amsa

“Kuna da wurin zama ne, ina son mu yi magana ne, ko ba damuwa za ku ci gaba da tsayuwa”

Still dai Juwairiyya ce ta shiga waige-waige, har zuwa lokacin da ta dora idanunta a kan SUG chairs ta ce “Za mu iya zama can idan ba damuwa”

“ok let’s go”

Tare suka jera har wurin kujerun, suka zauna a daya du su biyun, shi kuma ya zauna a ɗayar.

Duk sai suka yi shiru, kamar daman zaman shiru suka zo yi.

Ahmad ne ya kawar da shirun da fadin “Zuwa yanzu kuma na san kun gane ni”

A tare suka girgiza kai, alamar a’a

“To ai ba ku kalle ni ba” ya yi maganar idanunshi a kansu, yana kallon yadda suke a takure kamar suna jira ace ar! Su kwasa da gudu

Kuma har lokacin basu kalle shin ba

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “Juwairiyya!” sai ta dago kai, ganin ita yake kallo ya sanya ta saurin dauke idanunta, Sai ya dan yi murmushi tare da fadin “Ya sunan ƴar’uwar ta ki?”

“Nabila” ta ba shi amsa.

“Nabila, ke ma ba ki gane ni ba?” ya yi tambayar yana kallon ta

Shiru ta yi komai ba ta ce ba

Sai ya dan yi dariya kadan kafin ya ce “Za ku iya tuna wani lokaci almost 4-5 months da kuka ga wasu a kan doki har kuka tsorata?”

Da sauri su Juwairiyya suka dago idanunsu, suka sauke a kan Ahmad. Wannan ya sa kwakwalwarsu ta shiga dakko musu hoton fuskokin wadanda suke kan doki, Sai kuma suka guntuwar dariya a tare alamun sun tuna, kafin Nabila ta ce” Kai ne na saman doki wanda bai sakko ba ko? “

Light murmushi ya yi ba tare da ya ce komai ba

Su ma sai suka yi karamin murmushi, saboda komai da ya faru yana dawo musu, ko haka nan ma suka tuna sosai suke dariya, tun ba idan suka tuna yadda Hafsat ta rika rarrafe cikin ciyayi ba.

Zaman shi ya gyara sosai kafin ya ce “Ina daya ƴar’uwar taku?” da ace za su kalli saitin zuciyarshi da sun ga yadda rigar shi ke dagawa sakamakon yadda bugun zuciyar ta shi ya canja

Juwairiyya ya ce ta ce “Hafsat!”

Idanu ya lumshe a hankali, yayin da ya shiga maimaita sunan a zuciyarshi

Kai ya daga alamar eh

“Tana garin su”

“Ina ne garin nasu?”

“Maƙera” Juwairiyya ta kuma amsawa.

Zaman na shi ya kuma gyarawa sannan ya ce “Ina son ganin ta, ya za a yi?”

“To!” Nabila ta fada, don kamar daga sama ta ji maganar

Kai ya jinjina don tabbatar mata

“To sai dai idan ka je garin, tun da dama hutu take zuwa gidanmu” cewar Juwairiyya

“Ai ban san garin ba, sai dai ko idan za ku yi min rakiya”

Karamar dariya Juwairiyya ta yi ba tare da ta ce komai ba.

“Zan samu rakiyar?”

Kai ta girgiza kafin ta ce “a’a gaskiya sai dai mu ba ka address”

“ok. Ba ni”

Juwairiyya ta yi shiru cikin tunanin ta ina ma za ta fara bayar da address din

“Kin ga da wayarta nan shi kenan, abun zai fi sauki” cewar Nabila

Juwairiyya ta ce “Wlh kam, amma ina ganin idan ka isa garin kawai ka je gidan Maigari ka ce Malam Ayuba mai, kayan miya Baban Hafsat kake nema.”

Shiru ya dan yi kafin ya ce “Hakan babu matsala?”

“Babu in Sha Allah”

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali kafin ya ce “Na gode sosai. Wannan shi ne dalilin da ya sa na nemi ganin ki, ina fatan ban dame ki ba?”

“Kai a’a wlh, babu komai”

“ok thanks, mu je wurin motar ko, Sai in wuce.”

Ya yi maganar hade da mikewa tsaye.

Su ɗin ma sai suka mike suka kuma takawa zuwa wurin da ya Parker motar.

Suna tsaye har ya gama fitar da wasu manyan ledoji masu dauke da tambarin *AMI* daga cikin boot, ya aje a gabansu yana fadin” I’m sorry zan rika damunki a waya”

“Ba komai” Juwairiyya ta fada yayin da suke zuba mishi godiyar kayan da ya zube, suka kuma tabbatar nasu ne.

Komai bai ce ba, ya juya motar zuwa kan titi.

Su kuma suka dauki ledojiin zuwa hostel.

Suna shiga cikin gate din Nabila ta kalli Juwairiyya tare da fadin “Aunty Jhu kin ga wani ikon Allah, kar dai mutumin nan son Hafsat yake yi”

“Abun da nake tunani kenan Nabila, idan ba sonta yake ba, me ye na neman ta” cewar Juwairiyya ita ma cikin alamun mamaki

“Aiko idan haka ne tabbas da na yi farin ciki, wlh da ta yi miji one in town” cewar Nabila cikin murna.

Juwairiyya ma cikin murnar ta ce “anya ba shi ne yaron Galadima ba?”

“That’s what I’m thinking, Saboda Sosai yake kama da Baffahn nan da mu ka fara secondary school tare”.

“Exactly!” Juwairiyya ta fada cikin gasgata zancen Nabila.

“Allah Ya sa cewa zai yi zai aure ta”.

“Amin Ya Rabbb” Juwairiyya ta amsa

Bangaren Ahmad kuwa sai da aka sakko masallaci sannan ya bar garin Nasara zuwa gida.

Yana isa garin Dawuri ana kiran sallahr la’asar, shi ya sa ya tsaya masallacin bakin hanya ya yi sallah.

Bayan ya fito ne kuma ya kira Asad hade da shaida mishi gobe around 10am zai yi mishi rakiya zuwa Maƙera.

Ba tare da tunanin komai ba Asad ya amsa mishi da to.

Daga nan kuma gidan Aunty Safiya ya wuce, ita ce babbar yayarsu gabadaya.

HAFSAT

ASABAR

Haka nan gabanta ke ta yawan faduwa yau din nan, a haka ta gama gyara dakinta tsab gami da jikinta, sannan ta fice daga gidan zuwa Ruga. Tun da dai ta san tuwon da ya kwana ko ta tsaya jiranshi ba koshi za ta yi ba, a can kuwa sai ta ture.

Lokacin da ta isa Rugar Tukuro bai fita kiwo ba, ana dai tatsar nono ne, shi ya sa har sai da ta gama cin dumamen tuwonta, sannan Tukuro ya fara kora dabbobin

Sai kwai ta dauki gora ta cika da nonon gami da sanda ta bi shi suka tafi

Jikin bishiyar kanya ta zauna bayan sun isa wurin kiwon, tana kallon yadda yake sai ta dabbobin don kar su yi wa mutane ɓarna, saboda ana ta aikin kaka ne, da yawan abinci duk ya je gida.

Sai da ya gama daidaita dabbobin sannan ya dawo kusa da ita ya, zauna, cikin kulawa ya ce “Me ya faru ne? na ga kin yi laushi”

“Ban sani ba, gabana ne yake ta yawan faduwa, tun da na tashi” ta amsa shi cikin damuwa.

Idanumshi ya dauke a kanta kafin ya ce “Kin sau kuwa jiya na kara mafarkinki a kan doki, wannan yana kara nuna min auranki ya kusa”

Duk yadda take jin damuwa hakan bai hana ta yin gajeruwar dariya ba tare da fadin “Allah Ya Tukuro kana ban dariya da maganar nan, na fada ni fa ko saurayi ba ni da shi. Babu wanda ya taba cewa yana sona”

“Sai Nasiru da Najibu ko?”

Kadan ta murmusa kafin ta ce “Su ma ba irin son da kake tunani suke min ba ai”

Shi ma murmushin ya yi kafin ya ce “Najibu ya yi nisa sosai, bayan haka da ya zo wurin ki”

Shiru Hafsat ba ta ce komai ba, kamar ma ta tafi wata duniyar tunani ne.

Sai da Tukuro ya kara cewa “Kin san yana ƙasar waje karatu?”

“Ya aka yi ka sani?”

“a mafarki na gani”

Idanunta ta dauke daga kan fuskar shi komai ba ta ce ba

“Idan abubuwan da nake fada miki suka fara faruwa, na san za ki fara yadda da maganata”

Dariya ta yi sosai, still ba ta ce komai ba.

Shi din ma sai ya mike don zuwa taro wasu awaki da suke son kauce hanya. Don ya fahimci yau Hafsat din ba ta cikin yanayi mai kyau.

*****

<< Abinda Ka Shuka 40Abinda Ka Shuka 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×