Skip to content
Part 43 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Lokacin da ta rufe gate din, shi kuma ya gama parking, bai fito ba har ta karaso wurin, glass din ya sauke a hankali tare da fadin “Haka za ki tare ni? Almost 2weeks ba ki ganni ba”

Murmushi ta yi hade da rufe fuskarta da tafukan hannunta.

Tana jin lokacin da ya bude motar ya fito ya shiga karkada mata keys din a saitin fuskarta, wannan ya sanya ta dauke hannuwanta a kan fuskarta

Key din ya mika mata hade da fadin “Yanzu sai ki koyi tukin da motarki ai”

Baya ta ɗan ja kadan, yayin da yanayin mamaki ya bayyana a fuskarta

“Yes! Ina son ki iya kafin nan da 1month,don da kanki nake son ki tuko kanki zuwa gidana” ya yi maganar cikin dariya.

Ita ma dariyar ta yi kadan kafin ta ce “Are you serious?”

“I’m very serious dear”

Kai ta langabe sannan ta ce”Duk wannan bai yi yawa ba Abban Nawwara, da ka bari sai gaba ai”

“Ba ki yi farin ciki ba?”

“Na yi” ta amsa a hankali

“That’s what I want dear, Ina son in ga kina farin ciki hakan yana min dadi sosai”

“To na gode, Allah Ya saka maka da mafificin alkairi, Ya kara…” sai kuma ta kasa karasawa, saboda hawayen da suka shiga sakko mata.

Da alama AG shi ne sakamakon tuban ta, ta hanyar shi komai da ta rasa har da kari yana neman dawo mata.

A gidan Ahmad kam ba ta da mota tata ta kanta, Sai dai akwai motoci na alfarma, wadanda duk wacce ta zaba za ta iya hawa.

Yanzu kuma ga AG ya mallaka mata mota, addu’arta da fatan ta Allah Ya albarkaci zamansu, ya basu zuriya dayyiba.

“Cry-cry! Komai kuka, ko Baba ma baya haka. Idan kina, wannan za ki sanya na rika hugging dinki ko ban yi niyya ba. Yanzu ma kadan ya rage, don dai ina tsoron ko Aunty na kallon mu ta window”

Ya karasa maganar hade da nufar kofar da za ta sada shi da sitroom din.

AHMAD

Zuwa la’asar tuni ma fi yawan ƴan’uwan Ahmad maza da mata sun ji maganar baikon.

Hatta Galadima ma ya tsinci zancen ta bakin Asad, sosai ya yi mamaki, musamman da ya ji yarinyar wai a ƙauyen makera, Sai dai ya yi addu’ar Allah Ya sa haka ne ma fi alkairi.

Misalin karfe biyar na Aunty Safiya ta iso gidan, inda ta iske Asad na jiran ta, basu ɓata lokaci suka wuce AMI don hado kayan baiko da na sanya rana.

Basu dawo ba sai bayan magriba sosai, don suna isowa gidan ana kiran sallahr isha’i.

Nan fa aka baje kaya aka shiga dubawa, kaf babu na yarwa, an kashe kudi an kuma yi bajinta, tun daren aka ware wadanda za su tafi kai kayan gobe idan rai ya kai.

A lokacin ne kuma Asad ya kira Malam Ayuba ya shaida mishi gobe za su kawo kayan baiko.

Ai Malam Ayuba sai ba zama, ya shiga bin dangi na kusa yana shaida musu, sannan ya kira Mama ya shaida mata duk abin da ya faru, cike da tu’ajjibi ta ce “Ikon Allah! Haka lamarin ya faru, to Allah Ya tabbatar mana da alkairi gaskiya ni wannan labari ya faranta min, hade da yaye min duk wata damuwa.”

Baki Malam Ayuba ya washe kamar Mama na kallon shi ya ce “Yanzu matsalar Halima shi ne abincin da za a basu, kin san an ce tuwon girma miyarshi nama ga, shi kuma ke ba kya kusa”

“wannan ba wani abu ba ne Malam Ayuba, ba dai sun ce idan an yi sallahr azhur za su taho ba, to sha Allah zuwa lokacin ni ma na iso, kuma daga nan zan yi komai ba fita kunyar baƙi. Dama Ina, son zuwa abubuwa ne suka yi yawa”

“Kai Yaya Halima, ubangiji Allah Ya saka miki da alkairi, ya ba ki ladan zumunci, yadda kike aikatawa zumunci, Allah Ya sa ya yi sanadin shigar ki aljanna, an gode, an gode”

“Ba komai, ai yi wa kai ne, Hafsat ƴata ce daga duniya har lahira”

Malam Ayuba bakinshi bai mutu da addu’a ba, Sai da su ka yi sallama.

Mama kuma ta kira Tajuddeen da Alhaji Aminu ta shaida musu, sannan ta sanar musu da abun da take so su sawo mata daga kasuwa kafin da safe, ta kara shiga kasuwar.

Bangaren Hafsat kam ba ta san komai da yake faruwa, ana kiran sallahr magriba ta iso gidan tana yin wanka sai sallah ta ci abinci, tana yin sallahr isha’i kuma ta kwanta, safiyar lahadi da safe ta kuma barin gidan zuwa ruga.

Gidan ma idan ka dauke amarya babu wanda ya san  abin da ya faru, Sai da safen bayan sun karya ya ce yana son a gyara gida, saboda masu son auran Hafsat za su zo kawo kayan baiko.

Kamar fadowar gini haka suka ji saukar maganar, ga shi da Inna Kuluwa da Inna Luba ba a magana bare su gulmata su ji dadi.

Haka dai ko wanne tambayoyin shi, amma fa tsinke basu daga ba, Sai amarya ce ta share gidan tsab gwanin sha’awa, ta wanko toilet din cikin gidan kasancewar akwai siminti.

Cikin kankanen lokaci gidan ya yi tsab

Zuwa 12:00pm kuma sai ga Mama Halima Tajuddeen ta kawo ta.

Ana tsaka da fitar da manyan kulolin sai ga Malam Ayuba, saboda yana a kasuwa ya ga wutowar ta, baki ya ki rufuwa, da shi aka rika kama manyan kulolin ana shigar cikin gidan, ga minerals da ruwa package 12.

Dukkansu a dakin amarya aka shigar, kuma a can din Mama Halima ta sauka, sai da suka gaisa sosai, sannan ta karbi key din Hafsat ta shiga dakin saboda tun da aka kammala ginin ba ta zo ba.

Sosai ta yaba da tsarin ginin da kuma yadda Hafsat ke gyara dakin tsab, alamun ba ta da kazanta.

A nan ta yi sallahr azhur sai kuma ta yi kwanciyarta, yayin da take jin mutane na fara shigowa gidan, wadanda za su tarbi yan kawo kaya.

Zuwa karfe biyun gidan ya hada mata ƴan’uwa da kuma abokan arziki, dole Mama ta fito daga cikin dakin ta rufe kofar. Saboda a dakin suke son saukar baƙi.

Kamar yadda al’adar garin take Malam Ayuba ya bayar da gero kwano uku aka watsa cikin turmi.

Cikin minti talatin aka surfe shi tas, aka wanke sannan aka aje, ana jiran zuwan baƙi.

Bangaren Ahmad kuwa, masu kawo kayan baiko karfe uku suka sauka gidan Maigari, kamar yadda Ahmad da Asad suka shaida musu, daga nan ne kuma aka yi musu rakiya zuwa kofar gidnsu Hafsat, inda yake cike da mata kamar yau ne ake daurin aure, Sai gude-gude ake yi.

Shigowar masu kawo kayan sai gidan ya kara rikicewa da gude-gude.

Sannan aka mayar da geron cikin turmi aka shiga yin lugude.

(Kila masu karatu wasu basu san me ye lugude ba. To lugude dai wani abu ne da matan karkara ke yi a lokacin da zasu an shi kayan baiko ƴarsu. Bayan an surfe gero an wanke hade tsane shi, Sai a mayar cikin turmi, yayin da mata zasu zagaye turmi, suna daka. Sai dai dakan mai style da zai rika bayar da wani sauti da idan ka ji za ku ce kida ne. Wani lokaci akan kara da kidan kwaryar don karawa abun armashi. Za aci gaba da wannan daka har sai wannan geron ya koma gari, sannan sai zuba sugar a ciki, a kwaɓa a mayar cikin turmin, a hada gumba. Bayan an gama sai kasa kowa ya dauka)

Kamar yanzu ma hakan ne ya kasance, kida na tashi mata na rawa gami da waƙe-waƙen gargajiya sai gidan ya kara cika.

Tun su Aunty Safiya na baya-baya har dai suka warware, suka yi ta kallo hade da dauka a wayoyinsu, kai har da likin kudi.

Misalin karfe biyar suka gama daka gumbar aka ba kowa, aka kuma bude kayan baiko suka gani hade da sanya albarka, Sai kuma suka fara watsewa, alamun an gama komai.

A lokacin su Aunty Safiya suka fadawa Mama suna son yin sallah.

Ɗakin Hafsat ta bude masu, ta nuna musu ruwa a cikin toilet.

Suna sallah ana shigo musu da kayan abincinsu.

Bayan sun idar da sallahr ne Aunty Safiya ta ce “Ni fa gadon nan zan hau, wlh ya burge ni”

Duk suka yi dariya, kafin Ummi ta ce “Hau daya ni ma in hau daya. Sosai na gaji, kamar ni na yi dakan na da rawar nan”

Maman Zarah (Matar Asad) ta ce “Kowa da abun da ya dame shi, ni kuwa wancan hoton ya dauke min hankali, kodai ita ce amaryar tamu?”

Ta karashe maganar hade da nuna musu hoton da hankalinsu bai kai wurin ba da farko.

“Kai Ma Sha Allah! Ahh! Indai wannan ce amaryar to a kyau dai Ahmad bai yi zaben banza, sosai ya tona hade da bude idanunshi. Fatanmu zuciyarta da halayenta su zamo kamar kyawun fuskarta”

Cewar Goggo B

Goggo Nunu ma ta ce “Don Allah ji yadda aka zo aka aje wata mai kyau a kauye, shi ya sa masu kudin nan wasu suke rabowa kauye su samu ta’ala-tsalan mata su aure, Sai su kara gyara su. Ke yanzu wannan ta samu hutu, wlh komawa za ta yi kamar Hurul-In. A Astagfirullah”

Duk suka fashe da dariya, cikin dariya Aunty safiya ta ce “Maganar Allah ta yi ba karya, ya kashe kudinshi a inda ya dace. Ga ta yarinya shakaf, ta yi gudun tsiya wannan ba za ta wuce 16-17 ba”

“Gaskiya! Yo wannan aka yo ma kishiya da ita, ai sai dai kuma ka shige daki ka yi zaman ƴaƴa wlh. Da wannan a gefen namiji to ba zai taba kula irinmu baƙaƙen nan ba” cewar Aunty Ummi

Cikin dariya Maman Zarah ta ce “Ba a nan take ba, Sai ki ga kin fita karbuwa ma a wajen shi”

“Ke Maman Zarah, maganar Allah ban yarda ba, ƙarya da ciwo mari da zafi. Ni kam ba na fatar ayo min kishiya da irin wannan”

Duk suka fashe da dariya, daidai lokacin Mama ta shigo ta ce “Mutanen arziki ku fa zuba abinci ku ci don Allah. Ga shi can an kaiwa direbanku”

Duk suka amsa da to, kafin Goggo B ta ce “Na ce wannan ta hoton ce surukar tamu?”

Mama ta juya kan hoton tana murmushi kafin ta ce “Ita ce. Yarinya ce sai an yi ta kwakkwafa idan ta shigo”

“Ma Sha Allah! Amma kam mun yi suruka ta bugawa a jarida, shi ya sa Ahmad ya tayar da hankalin kowa” cewar Aunty Safiya.

Duk suka sanya dariya, Mama ce ta zuba musu abinci, suna ci suna hirar kyawun Hafsat

Aunty Safiya kam har hoton ta dauka a waya, wai za ta nunawa Hajiya.

MK&RUMA

To Alhamdulillah Ruma dai ciki ya samu, kuma har yanzu da ya kai wata biyar bai fita ba, wannan ya sa duk wata kulawa tun daga ta asibiti zuwa maganin gargajiya babu wacce ba a ba ta.

Alaramma ya ƙara kaimi wajen aiko mata da rubutu duk sati kala-kala

Ita din ma kuma ba ta wasa wajen shan shi.

Zuwa yanzu dai babu wani abu da ita kanta take so irin ta ga ta haihu lafiya, ko don farin cikin mutanen da ke ta dawainiya da ita.

Wato akwai daraja da kima sosai a cikin aure, a wancan lokacin da ta samu ciki, boyewa ta rika yi daga mutane.

Yayin da hankalin mahaifiyarta ya fi na kowa tashi. Ko bacci mai kyau ba ta yi. Kullum cikin jike-jike magunguna don kawai ya zube, amma hakan bai samu ba. Abin da mahaifiyar tata ta guda sai da ya faru.

Yanzu kuma so ake ya zauna, kullum cikin neman maganin da zai zauna ake yi, sai take jin wani dadi mara misultuwa.

Bangaren Alaramma kuwa ya shiga fafutukar neman certificate, da taimakon Malama Aisha ya samu takardar haihuwa da kuma primary certificate. Saura secondary certificate wanda shi ne yake ta faman kai kawo a kai.

Wani lokaci sai ya ji kamar ya yi zuciya ya hak’ura, idan kuma ya tuna damar da za ta wuce shi sai ya fasa.

Saboda yanzu haka dai mahaifin Mk shi ne Ɗanmajalisa mai ci. Kuma yana daya daga cikin tsanin da Alhaji Bashir ya taka har ya kai ga gaci. Ya san kuma ba zai saba alkawarin da ya daukar mishi ba.

ASMA’U

To bangaren Asma’u ma abu na ta kara kyau, wai kishiya ta ga kishiyarta na kwasar kaya.

Saboda AG ya kawo lefe tun ana sauran sati daya biki, lefe ne da aka yi shi kamar da gayya, komai da AG yake yi a kan Asma’u sai ya rika yin shi kamar yana son ba wani haushi

(Ni ban san wa AG ke son ba haushi ba, Mk ko Ahmad)

Babu wani abu da za ka gani a cikin lefen Asma’u ka ce an saya da kudi kadan. Wannan abu kuwa ba karamin faranta ran iyayen Asma’u yake yi ba. Ko ba komai AG ya wanke musu wani bangare na damuwarsu, yanzu kawai fatansu shi ne Allah Ya sa a zauna lafiya, Ya kare dukkan fitina. Ana saura kwana uku daurin aure AG ya zo Jama’a inda ya matsa lallai sai sun yi pre wedding pictures Studio mai kyau suka je aka dauke su hotuna masu tsabta, babu inda suka taba jikin juna, amma kallo daya za ka yi musu ka fahimci sun dace da juna, sannan akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu, musamman AG.

Abin da yake bukatar kila shi ne ya faru, saboda cikin 24hr hotunan nasu suka rika leka shafukan sada zumunta na zamani. Masu fatan alkairi na yi, masu kushewa na yi.

Haka hotunan suka rika yawo har zuwa lokacin da suka fada a kan idanun Mk.

Wani irin shock ya ji mai wahalar fassarawa, wani irin ɓacin rai ya rika ji mara dalili, dakyar ya rika tausar zuciyarshi wurin ganin bai yi wa Ruma abin da ranta zai baci ba, amma kam komai haushi yake ba shi.

Idan ya kalli mutane na dariya sai ya ji kamar ya rufe su da duka, saboda gani yake yi kawai da, shi suke.

Ranar Juma’a dubban mutane suka shaida auran Asma’u da AG, auran da Asma’u ke kallon shi kamar mafarki. AG kuma ji yake yi yanzu ya auru, idan ya tuna irin baƙar wahalar da ya sha  irin kudin da ya kashe da kuma irin yadda ya rika shiga damuwa duk a kan Asma’u, yanzu kuma ya ga ya same ta, sai ya ji lallai babu abin da aiki tuƙuru baya samarwa, haka ma jajircewa, duk abin da ka sanya kanka, lallai Allah zai iya taimaka maka ka samu, abun nan mai kyau ko mara kyau.

Hausawa sun ce so hana ganin laifi, to da gaske son Asma’u ya rufe mishi idanuwa ruf, ta yadda bai iya hango ko wane irin kuskure na ta. Bukatarshi kawai ita ce ya mallake ta. Kuma ya samu hakan.

Sai washegari Asabar aka dauki Asma’u zuwa Nasara da ƴan rakiyarta mutum hudu ciki har da Aunty Hajara. Sai dai ba a tafi da Abdallah, daga baya za a kai shi.

<< Abinda Ka Shuka 42Abinda Ka Shuka 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×