Bangaren Ahmad kam, bude ido ya yi sosai a cikin motar yana kallon Hafsat, mace daya a duniya da ta fara rikita mishi lissafi. Mace ta farko da yake jin zuciyarshi na bugawa ta dalilin ta. Mace ta farko da take canja mishi yanayi koda kuwa tuno ta ya yi.
Kamaninta sunanan basu ɓata ba, sai ma kara haske gami da ƴar ƙiba da ta yi, don fuskarta a cike take.
Ganin tana kokarin bude murfin kofar sai ya saurin kwantar da kanshi jikin kujera hade lumshe ido. Sai dai tana bude murfin, shi ma ya bude na shi idanun a kanta, wannan ya ba ƙwayoyin idanunsu damar haduwa.
Da sauri ta sake murfin hade da janye idanunta cikin na shi, ta kuma mayar da kallon nata a kan su Nabila, tun ba Juwairiyya da take dariya ƙasa-ƙasa ba.
Sai kuma ta juya a hankali da zummar komawa inda ta fito, saboda ko ba ta tambaya ta san wannan shi ne Ahmad, shi ne dai ake cewa zai zama mijinta.
Tun da take a duniya ba ta taɓa jin zuciyarta ta yi irin bugawar da ta yi yau ba, a lokacin da suka hada ido.
Time da ta shiga cikin gidan ba kowa, sai Goggo Amarya da ke zuba shara cikin dustbin.
A falo ta samu Mama na taɓa wayarta, yadda ta shigo din ne ya sanya ta dakatawa hade da zuba mata idanuwa, har Hafsat din ta zauna saman kujerar da ke fuskantar Mama.
“Me ya faru na ga kin dawo kama a tsora ce?” Mama ta tambaya
Maimakon ta ba ta amsa, Sai ta fashe da kuka.
“Subhnallah me ya faru?”
Daidai lokacin su Nabila suka shigo falon suna dariya.
Cikin dariya Nabila ta ce “Babu komai Mama, kawai daga ta ga Ahmad, shi ne ta juyo”
“Yau na ga sakarci. To me ye na gudu kuma kamar wata sakarya. Haba Hafsat, ga ki kamar wayayya kuma za ki yi kauyanci”
Komai Hafsat ba ta ce ba sai dauke hawayen da take yi.
“Ku fita ku ba ni wuri, zan yi magana da Uta” cewar Mama tana kora su Nabila zuwa waje. Suka fice suna ta dariya.
Mama kuma ta tattara hankalinta a kan Hafsat tana fadin “Tun da kika zo ba mu yi maganar da ta shafi Ahmad ba, wannan ya faru ne saboda yadda abubuwa suka yi yawa, yau ne ya kamata a yi, kuma yau din ma ni ban zauna ba.”
Ta ɗan tsahirta kadan kafin ta dora “Hafsat! Ki nutsu da kyau ki ji abin da zan fada miki. Ke kanki kin san ina sonki, ina kuma son farin cikin ki. Shi ya sa ba ni da kwanciyar hankali idan na tuna cewa dole za ki yi aure. Amma yaushe? Wa kuma za ki aura din? Ya Ya zaman auran zai kasance? Ina raye ko ba na raye? Kin ga wadannan tambayoyin suna matukar tayar min da hankali. Shi ya sa na yanke shawarar Tajuddeen ya aure ki, saboda na san ba za ki wulakanta a hannunshi ba. Sannan ina da ikon a kanshi. Dana samo wannan mafitosai hankalina ya fara kwanciya. “
Bayan ta nisa ta ci gaba” Kwatsam kuma, sai ga Babanki ya kira ni yana shaida min cewa yaron Galadima ya zo neman auranki kuma ya ba shi. Amma don Allah in yi hak’uri, ya yanke hukunci ba tare da ya tuntube ni ba.
Sosai maganar ta zo min a bazata, mamaki nake yi ke Hafsat diyar Hindatu dan gidan Hakimi zai ce yana so, kuma da aure. A ranar na tambayi Tajuddeen waye Ahmad dan gidan Hakimi? Yadda ya sanar da ni waye shi, Sai na ji ya cancanta ya zama mijin ki, don haka na janye maganar Tajuddeen na bi ki da addu’ar fatan alkairi. Tun daga lokacin da zancen nan ya ɓulla, ban taɓa fasa yi miki addu’ar dacewa ba Hafsat. To kar ki ɓata rawar ki da tsalle, Allah Ya kwato ya ba ki, ke kuma ki tsaya shirme. Me ye abun kuka kuma? Dukan ki ya yi? Ki kalli katuwar motar da ya zo daukar ki da ita, kin san abubuwa nawa ya ture saboda ke? Ke yanzu ba abun alfaharinki ba ne a kai ki Makera a wannan motar. Ke yanzu ba abun alfaharinki ba ne ace ɗan cikin Hakimi ne zai aure ki. To ni ko yanzu aka daura auranki da Ahmad ya sake ki an jima wlh na yi farin ciki. Saboda ko ba komai kin yi wa makiya barazana, ke din nan da ake ganin ba kowa ba kin zama kowa. Don Allah kar ki bari wannan damar ta sille mana.”
Hawayenta ta dauke a hankali ba tare da ta ce komai ba.
Mikewa Maman ta yi hade da dakko hijab dinta ta sanya kafin ta ce” Ta shi mu je. Kin samu dama kina son yin wasa da ita. Wasu da kudinsu suke neman miji kamar Ahmad basu samu ba. Ke Allah Ya ji kanki, Ya, dubi maraicinki kina son yin shirme. Me ye abun kuka? “
Haka Mama ta rika korafi har sai da Hafsat ta bude kofar gate sannan ta yi shiru.
Ganin Mama biye da bayan Hafsat ya sa Ahmad saurin fitowa don gaishe ta.
Hafsat kuma ta bude motar ta shiga front seat ta zauna. Har zuwa lokacin hawayen da ba ta san ko na menene ba suna kara sakko mata.
Ba ta san lokacin da ta lumshe idanunta ba, hade da sauke ajiyar zuciya, saboda wani sanyi gami da daddaɗan kamshin da ta shaƙa. Duk yadda za ta fasalta abun ya fi karfin nan, Sai ka ce ba mota ba.
A can waje kuma bayan Mama ta amsa gaisuwar Ahmad sai ta dora da “To sai fa ka yi hakuri ka san Hafsat yarinya ce, har yanzu ba ta fi 17years. Don Allah ka rika kawar da kai. Ko idan ta yi ba daidai ba, ka sanar ma Juwairiyya ta fada min. Don Allah!”
Murmushi kawai Ahmad ya yi ba tare da ya ce komai ba. Yayin da Mama ta yi mishi godiya ta koma cikin gida.
Su Juwairiyya da suke laɓe, Sai suka kwasa da gudu zuwa cikin gida suna dariya.
Shigowar Ahmad cikin motar sai ta ji kamar ya cika ko ina, babu sauran wuri duk ta yi tsumu da ita, ta takure kanta, Sai wasa take da yatsunta kamar wacce aka ce hakan shi ne aikinta.
Ya ɗan saci kallon ta kadan, sai kuma ya yi ɓoyayyen murmushi. Kafin ya zaro tissue ya mika mata ba tare da ya ce komai ba.
A hankali take dauke hawayen, wasu kuma sabbi na zubowa, Ahmad ya kwantar da bayanshi jikin kujerar hade rufe idanunshi, yana shakar tattausan kamshinta mai narkar da zuciya.
Almost 10mns,kafin ya yi motor wa key hade da juyawa zuwa hanyar da za ta fitar da shi daga cikin unguwar.
Da wani irin salo yake tuƙin, wanda ya sanya Hafsat nutsuwa, ta rika jin kamar ta tsira daga dukkan wani abu mara kyau ko dadi.
A kofar *AMI SHOPPING COMPLEX* ya yi parking, ba tare da ya kalle ta ba ya ce “Ina zuwa” karon farko da ta ji muryar shi, Sai, kuma ta tsinci kanta da bin bayan shi da kallo.
Sanye yake da yadi mai taushi, kamar onion colour haka, tsakanin yadin da dinkin ba ta san wanne aka kashewa kudi ba. Kanshi sanye da bakar dara, kafafunshi kuma da takalmi black color mai kyau.
Duk da bayanshi ya juya, amma hakan bai hana kirarshi ta lafiyayyen namiji mai ji da kurciya bayyana ba.
Tafiyarshi cikin nutsuwa, cikin mintuna ashirin da ta yi da shi ta fahimci ba ya son hayaniya. Haka komai a nutse yake yin.
Yadda yake takunshi ba karamin burge ta ya yi ba.
Kan ta a dauke daga kanshi, hade juyawa daya bangaren tana tuna maganganun Mama.
Lallai kam ta yarda ta tsinci dami a kala. Ahmad irin mazan da take karantowa a novel, ga kudi, ga,
Sarauta, ga ilmi, ga nutsuwa ga kuma kyau.
“To ni ko me ya gani a wurina oho?” ta tambayi kanta da kanta, Sai kuma ta ba kanta amsa da “Kodayake an ce Babanshi ne ya zaɓa mishi ni.”
Ta dan yi shiru, Sai kuma ta ce “Bawan Allah sai kuma ya amsa. Yana da hak’uri da alama” ta kuma fada a hankali hade da juya bayanta tana kallon kofar fitowar.
Sai ko ta hango shi yana fitowa, wasu maza, biyu dauke da manyan ledoji masu tambarin AMI din, a duk hannayensu biyun.
Idanunta ta kasa janyewa daga kanshi, sosai take kallon ko wace gaɓar ta jikinshi.
Tun daga kanshi mai karancin suma, zuwa kan fuskar shi mai dauke da dogon hanci da matsakaitan idanu.
Idan akwai wani da aka ba Ahmad a jikinshi ba a yi mishi ƙwauron ba to tsawo ne da gashin gira. Ga shi nan kwance bakikkirin, sosai ya karawa fuskar ta shi kyau.
Ba Za a kira shi ramamme ba, kamar yadda baya cikin masu ƙiba. Yana nan a tsakiya, kila, kuma tsawonshi ne ya boye kibar
Da kanshi ya bude musu boot suka zuba kayan a ciki, kafin ya bude motar ya shigo hade da sallama.
Hafsat kam dama tuni ta janye idanunta a wajen, yanzu ma amsawa ta yi ba tare da ta juyo ba. Har ya yi wa motar key, Sai kuma ya dakata alamun ya yi mantuwa.
Reaction din da ya yi ne ya sanya ta juyowa idanunta a kanshi.
“Kina bukatar wani abu ne?” ta yi saurin dauke idanunta, hade da girgiza kai alamar a’a
Bai ce komai ya kuma yi wa motar key a karo na biyu. Wannan ya fahimtar da ita, abin da ya tambaye ta, yanzu shi ne ya hana shi tafiya da farko.
Sai da suka hau hanya sosai, sannan ya saka hannu cikin aljihun rigarshi, ya fito da wani box mai alamar heart, cikinshi kuma alawa ce golden color.
Daya ya mika mata, a hankali ya ce “Bude min”
Hafsat da kanta ke gefe ta juyo hade da karbar akwatin ta bude, sannan ta mika mishi
Bayan ya aje, guda daya ya dakko hade da mika mata “Saura wannan”
Kara karɓa ta yi, ta shiga bude chocolate din, Sai da ta bude tas, ta yadda a baki kawai zan sanya sannan ta mika mishi.
Ya karɓa idanunshi a kn fuskarta yana kokarin laluben kwayar idanunta, Sai dai bai samu damar hakan ba, har ya karɓi chocolate din.
A nutse yake tauna chocolate, yayin da Hafsat ke ta imagining dadinta, ta san dole ta dadi. Tun ba yadda yake tauna ta ba.
Ganin zai kama ta tana satar kallon shi ya sanya ta janye kwayar idanunta cikin dabara.
Shi kuma ya rufe box din hade da mika mata ragowar chocolate guda biyu na ciki.
Kai ta girgiza alamar a’a, Sai dai kallon da ya yi mata ne ya sanya ta mika hannu biyu ta karɓa
hade da fadin “Na gode, Allah Ya saka da alkairi. Na gode sosai”
Ya juya kan tukinshi ba tare da ya ce komai ba, Sai tafiyar ta kasance shiru, ita dai Hafsat hankalinta ya fi karkata a gefen hanya tana kallon gono ki, tare da motocin da suke wucewa, shi kuma na shi hankalin ya fi tafiya a kan tuƙin da yake yi.
A baɗini kuma wani nishadi da farin ciki yake ji, ga shi ga Hafsat, ji yake kamar ya bude kirjinshi ya saka ta a ciki. Ya yi shiru ne bai yi mata ko wane zance ba saboda still she is young. Yana kallon bayyana mata abin da ke cikin zuciyarshi kamar child abuse ne.
Shi kanshi auran zai yi ne don ya, samu nutsuwar cewa tana gidanshi. Amma, zai ci gaba da rainonta har zuwa shekarun da yake ganin ya dace.
30mns kawai ya dauke su zuwa cikin garin Maƙera, Hafsat ta riƙa yi mishi kwantancen gidan da hannu har suka isa kofar gida.
Take yaran makota hade da na gidansu suka fito kofar gida cirko-cirko suna kallo. Yayin da iyayensu ke satar leke ta cikin zaure ko kan katanga.
Ku san a tare Ahmad da Hafsat suka fito, hakan sai ya bayar da wani style mai kayatarwa.
Sai da ta bari ya isa wurin boot yana fito da kayan ciki sannan ta isa, ta rika kwasa tana kaiwa cikin gida.
Sai da ya rage saura manyan ledojin da ya sawo ne, Sai ta yi tsaye ba ta dauka ba, har ya rufe boot die, Sannan ya ce “Wannan din fa? Naki ne”
“Na gode, Allah Ya saka da alkairi” ta fada silently hade da duƙawa ta dauki kayan zuwa cikin gida.
Har zuwa lokacin masu leken basu bar wurin ba
Time da ta fito yana cikin motar, ganin fitowarta sai ya bude mata daya kofar, wannan ya tabbatar mata da yana nufin ta shiga ciki.
Ya rika bin yanayin ta da kallo lokacin da take shiga cikin motar har ta zauna, sai dai ba ta rufe kofar duka ba. Bai damu da hakan ba ya ce “A ina kike makarantar?”
“GGSS Maƙera” ta amsa a hankali
“Which class?”
“SS 3”
Kamar ba zai kara cewa komai ba, ai kuma ya ce “Art Ko science?”
“Science”
Kai ya jinjina alamar fahimta, sannan ya ce “Ina wayarki?”
“Ba ni da waya” yadda ta amsa mishin ne ya sanya shi dago kai yana kallon ta.
Da sauri ta janye idanunta, murmushi ya yi mara sauti sannan ya ce “A ina kika samu wacce aka ce ta ɓata?”
“Uncle Najib ne ya ba ni”
“Waye shi?”
Ya yi saurin tambaya
“Malaminmu ne a makaranta”
Yanzu kam juyowa ya yi sosai yana kallon ta kafin ya ce “Hafsa!” yadda ya kira sunatan ne ya sanya ta dagowa da sauri, hade da zuba mishi idanunta, yayin da wani abu yake diga a cikin zuciyarta.
Innarta ce kawai ke kiranta da wannan sunan, kuma tun da ta rasu ba ta kara jin wani ya kira ta da shi ba sai yau, wannan ya sa ta ji kamar Inna ce ta kira ta.
Hindu yahuza hindatuyahuza@gmail.com