Skip to content
Part 48 of 47 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Girarshi ya tattare du biyu hade daga su alamun tambaya. Saboda yadda take kallon shin ya ba shi mamaki, sannan hakan ya yi mishi kyau, musamman yadda ta dan bude baki, da sakin lebenta na kasa, ya rasa me ya sanya ta yin wannan reaction din.

Ta shiga kokarin janye idanunta daga kan fuskar shi a lokacin da ruwan hawaye ya fara taruwa.

Allah Ya sani kullum cikin kewar mutane ukun nan take, Inna, Ya Nasir da kuma Uncle Najib.

Ta kan ware lokaci na musamman ta yi kukan kewarsu, musamman idan aka yi mata wani abu mara dadi.

“What?” ya yi saurin tambaya ganin yadda hawaye suka digo a kan hijabinta

Ta yi saurin share dauke hawayen, ta shiga kokarin bude baki ta ce ba komai sai dai ta kasa yin hakan, Sai ma kawai ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka mara sauti, motsin jikinta kawai yake gani wanda yake nuna mishi shessheka take yi.

Sosai yake mamaki, saboda bai san me ya yi ba, da zai sanya ta irin kukan nan.

Sai kawai ya kwanta da kanshi hade da lumshe idanunshi ba tare da ya kara cewa komai ba. Idan akwai abin da zai ce, to bai wuce ya janyo ta jikinshi ya rarrashe ta ba, kuma ba shi da damar yin hakan, ko don mutanen da suke kallon su ma, ga shi kofar motar a bude take

Kukan ya dauki Hafsat ku san 10mns kafin ta dago kanta, ba tare da ta kalle shi ba, ta zira kafafun ta da niyyar fita

“Ni!” ya furta a hankali har zuwa lokacin idanunshi a lumshe suke

Dakatawa ta yi da fitar, sai dai ba ta gyara daga yadda ake ba

“Me ya sanya ki kuka?what did I do wrong?”

Komai ba ta ce ba, Sai ma share sabbin hawayen da ta shiga yi.

“Ba kya son in tafi ne?” haka nan ya yi tambayar, duk da ya san kukan nata ba ya da alaka da wannan

Kai ta girgiza alamar a’a

Ya mike zaune sosai yana fadin “Juyo kike kalle ni” yadda muryarshi ta canja babu alamun wasa ya sanya ta saurin juyowa tana satar kallon.

“Look at me very well” Dole ta kalle shi saboda yanzu ma babu alamar wasan a muryar shi.

Yadda fuskarshi ta canja mata, Sai ta rasa da wa yake mata kama. Tuni dai ta shiga nutsuwarta, ta rika mar-mar da idanu, kamar mara gaskiya a gaban jami’in tsaro mai kwarjini. Ta shiga kame-kame inda za ta ajiye fuskarta

“Me kike yi wa kuka?”

Ba ta san lokacin da ta ce “Na tuna Innata ne, ita ce take kirana da Hafsa,tun bayan da ta rasu babu wanda ya kara kirana da sunan sai kai”

Ita kanta ba ta san ya aka yi ta zubo mishi duk wannan bayanin ba. Kuma sai da ta kammala ne ta ji ta nutsu.

Ya fara warware fuskarshi a hankali, har ya koma yadda ta san fuskarshi a baya

“I’m very sorry, and I don’t mean to hurt you. Just it’s coincidence.”

Kai ta jinjina alamar ta yi hak’urin

“And from now on, your name is Queen, do you like it?”

Kanta kuma jinjinawa alamar eh.

“Thank. I’m very sorry”

Kokarin mayar da hawayenta ta shiga yi, ba tare da ta ce komai ba

“You can go now”

“Na gode, Allah Ya saka da alkairi ya kiyaye hanya”

Amin Ya amsa yana kallon yadda take sauka daga cikin motar.

Bai tafi ba, sai da ya ga ta shige cikin gida, kafin ya juya kan motar, zuciyarshi cike da tausayinta ya bar kofar gidan.

RUMASA’U

ASABAR

Yau dai tun asuba suka isa asibiti sakamakon nakudar da ta tashi da ita.

Kuma tun asubar ba ta haihu ba sai Azhur, kuma yaron ya zo ba rai.

Wannan shi ne an ga tsulum an ga kuma tsame.

Sosai kowa ya damu da mutuwar jinjirin Ruma, ita kanta har kuka sai da ta yi, kuka sosai, musamman idan ta tuna yadda kowa ya rika bayar da gudunmuwarshi wurin ganin cikin ya tsaya.

Cikin ikon Allah kuma ya tsaya din, Sai kuma ga shi an haihu babu rai.

Haka aka salloma ta daga asibitin kowa zuciya babu dadi. Tun ba Mk ba. Kallo daya za ka yi mishi ka fahimci yana cikin damuwa. Sai ma lokacin da ya ga an saka yaron a cikin kabari, bai san lokacin da ya fara kwalla ba

Duk a waya a ka sanarwa da ƴan’uwan Ruma, Sai Alaramma ya ce su jira ranar Monday sai ya kawo su, tun da dama zai zo interview.

Mk bai shigo gidan ba sai wajen kar 10pm a lokacin ne sawu ya dauke, saboda gidan na shi cika ya yi. Kamar yaron da aka haifa din yana raye.

Time din Ruma bacci ya fara daukar ta, shigowarshi ce ta sanya ta bude a ido, Sai kuma ta mike zaune, tana fadin “Sannu da zuwa” ya amsa a hankali hade da zama gefen gadon yana kallon ta cike da tausayinta

Baiwar Allah ko ya take ji oho? Shi kanshi ya damu bare ita, da ta rike cikin tsawon watanni tara da wasu kwanaki. Ga wahalar laulayi da ta sha, ga magunguna na asibiti da na gargajiya da ta yi ta sha. Ga kuma wahalar nakuda, Sai dai kuma ta rasa ɗan da ta haifa din.

Jiki ba ƙwari Ruma ta mike zuwa falo, da zummar kawo mishi abinci, wanda aka aiko daga gidansu.

“Ki bari zan je can in ci. Ya jikin naki?” ya tambaye ta cike da kulawa. Saboda sosai yana sonta, duk wani rashin wayewa nata bai dame shi ba. Saboda duk abin da yake nema a wajen mace ya samu a wajen ta.

Ruma kyakkyawa ce sosai duk da baƙa ce. Akwai manyan idanu, ga gashin gira irin a ciken, hanci kam ba a yi mata kwauronshi ba. Ga tsawo Kiba ce dai kawai ba ta da ita. Sai kuma rashin ilimi zamani da kuma wayewa irin ta zamanin. Wacce ya san a hankali ita ma za ta waye.

Abu ma fi soyuwa a wurin shi shi ne yadda take girmamashi, kamar za ta yi mishi sujuda, ba ya fada tana fada. Idan ya ce Eh, ko bai yi mata dadi ba, haka nan take bi. Sai shi da kanshi ne wani lokaci sai ya janye zuwa ga abin da take so.

Tashi ya yi zuwa falon hade da zama kan dining, serving kanshi ƴa yi, sannan ya shiga cin abinci ba don yana jin dadinshi ba. Kawai dai ci yake yi. Hannunshi daya kuma yana taɓa wayarshi, karon farko da ya ga Asma’u ta yi status tun bayan auranta.

Kanshi tsaye ya bude status din, kasancewar ya off na read and recipients na shi.

Hoton farko Abdallah ne, cikin wata dakakkiyar shadda blue, kanshi sanye da hular da ta dace da kayan haka ma ƙafarshi sanye da bakin takalmi mai kyau na yara.

Fuskarshi kawai yake kallo a fuskar Abdallah, kammanin nasu har sun yi yawa.

Wani abu mai kama da tausayin yaron ya rika tsirga mishi cikin zuciya. Sama da shekaru biyu kenan, bai taba aikawa da Asma’u Naira ba, don ta siya wa Abdallah wani abu.

Sosai abun na damun shi, Sai dai yana jin tsoron kar ya tsokano ta ta ce za ta kawo mishi yaro. Ya san halin ta sosai ƴar daru ce.

Kawo yaron nan yana nufin tashin alkiyamarshi, saboda ita ce ranar  YAUMA TUBULAL SARA’IR ɗin shi.

Hoto na gaba ya matsa, nan kuma sanye yake da bakar riga, sai farin wando na jeans Iya gwiwa, kafar shi kuma sanye da farin kambas mai kyau. Hoton ya yi kyau, musamman yadda ya dan saki baki kamar yana kallon wani abu.

A nan din ma caption ta yi da _I missed you Rabin Raina_

Next kuma video ne, kan dan karamin keke yake yana koyo. Nan kuma ta yi caption da _Smile_

Ajiyar zuciya ya sauke, ganin status din ya kare, yayin da Abdallah ya tsaya mishi cur a zuciya ya ki guduwa, har bai san lokacin da ya je ya yi saving din hotunan ba.

Haka ya kwan da hoton Abdallah makale a cikin zuciyar shi.

*****

ASMA’U

Misalin karfe 6pm ta ji horn din mota, wannan ya tabbatar mata da AG ne ya dawo, don haka cike da dauki ta nufi kofar, watanta biyu ba tare da ta ga Abdallah ba, Sai yau da AG din ya dakko shi.

Da wani irin hanzari take bude kofar, AG na gama parkerwa ta bude murfin kofar da Abdallah ke zaune.

Sai ko ya fada jikinta, saboda dama tun da ya ganta yake zanbarmar zuwa wurinta.

Cikin wani irin so da kauna ta rumgume shi tsam a kirjinta kamar za a kwace mata shi.

Yayin da hawaye da ba ta san ko na menene ba, suka shiga gangaro mata

Ba tare da ta dauke hawayen ba, ta dago fuskar Abdallah da ke kwance a kan kirjinta, ta yi kissing din goshin shi

Sai a lokacin ya ga hawayen da ke kwance a kan kumatunta, hannunshi ya sanya yana dauke mata hawayen.

Dukkansu AG ya hada hade da rungumewa yana fadin “Ni dukkanku ina son ku, tun da ko yar karar nan ba ki yi min.”

Murmushi ta saki har zuwa lokacin akwai hawaye a kan fuskarta, kanshi ta shiga shafawa tana fadin “I’m sorry dear, ta ka tarbar Sai an je daki”

Hannun nata  ya dauke  daga kanshi ya mayar a kan bakinshi hade da yin kissing din yana fadin “How is my baby”

Ture shi ta yi kadan kafin ta ce “For how long zan fada ma ba ni da ciki”

Dariya kadan kafin ya ce “Tun a karon farko na jefa kwallo a raga. Almost six weeks Kenan”

Bako kawai ta tura hade da yin gaba, a tsakiyar falo ta dir Abdallah kafin ta wuce table tana fadin “Yarorona me za ka ci?”

Bayanta ya biyo ya ce”Ummi tuwo zan ci”

Dariya mai sauti ta yi kafin ta ce “Sarkin noma, har yanzu kana nan da cin tuwon ka kenan.”

“Ba ki gan shi ba kuma kato da shi” cewar AG da ya fito daga bedroom.

Sautin dariyarta ta kara kafin ta ce “Da gaske Abdallah na girma, ko don na rabu da ganinshi ne?”

“Ba son haka ba ne, yana girman ma”

Ya amsa ta a lokacin da yake zama daya daga cikin kujerun da suka kawata falon

Bayan ta ba Abdallah tuwon ta juyo kan AG tare da fadin “Masoyi wankan fa ko ba yanzu ba?”

Kai ya daga alamar eh, hankalinshi a kan wayar da ke hannunshi

“To abincin fa?”

“Duk sai zuwa an jima, da wanka da cin abincin har yanzu ban yi 2hrs da yin su ba.”

“Ai sosai na ga saurin isowarku” ta yi maganar daidai tana zama gefen shi

“” Jirgi ne fa, duka minti nawa ne”

Kai ta jinjina alamar fahimta, kafin ta yi magana tattara hankalinshi a kanta yana fadin “A hakan ne kike cewa za ki mayar da Little wurin Babansu. Ban san ko sau nawa zan fada miki ba kya iyawa ba. Yanzu ma zan maimaita, ni da kaina ba zan amince ba gaskiya. Na yarda dai ki kai shi,mahaifinshi da ƴan’uwanshi su san da zaman shi. Amma kam zamu dawo da shi. Ni Sam hankalina ya kasa aminta da barin little a can.”

Cike da jin zafi Asma’u ta ce” Yana min ciwo sosai idan na ga yadda Mk ya manta da yaron nan, ya bar ni dawainiyarshi. Ko waiwayarshi ba ya yi, saboda ya samu wasu. Sosai rayuwar Abdallah na ba ni tausayi, kowa gudun shi yake yi”ta karasa maganar cikin dauke hawayen da ke zubo mata

“Ya za ki ce kowa? Ba kowa ba Dear ni yadda nake son yarana wlh haka nake son little, ko da ranki ko babu zan iya rike shi hannu biyu in yi mishi gatan da wani yaron bai samu ba.”

Komai ba ta ce ba, saboda a bangaren nan, za ta iya cewa AG shi ake kira da mijin marainiya.

Saboda zuwa yanzu ta fahimci da gaske so daya jal yake yi mata. Ba Ta kukan komai a gidanshi.

Komai ya samu zai ce Abdallah. Bukatar shi dai kawai shi ne ta yi farin ciki. Kuma tana yi.

Ta san Abdallah bai rasa komai ba, haka kuma ba zai rasa ba a wajen AG. Sai dai a hakan za ta kai wa Mk shi. Tana son mahaifanshi su ji irin abin da nata iyayen suka ji. Tana son ya dandana irin abin da ta ɗanɗana.

Hannunta AG ya ja tare da fadin “Mu je ki ba ni Oyoyo dina” ya yi hakan ne don datse igiyar da ta kullu tsakaninta da tunani yanzun nan.

“Abdallah fa!”

“Hankalinshi na a kan tuwo”

Yadda ya yi maganar ne ya sanya ta murmusawa.

*****

HAFSAT

Riƙe take da kahon saniyar duk biyun, a kokarin ta na ganin Saniyar ta ba dan jaririnta nono, Sai dai saniyar ta ƙi tsayawa, da zarar yaron ya kama nonon sai ta buga tsalle, tana kokarin kwace kahonta, Hafsat kuma ta rike kahon gam.

Ahmad da tun daga nesa ya hango wannan gangancin, daga nesa ya daka mata tsawa, “Ke! What are you doing?” kamar daga sama ta ji tsawar, hakan sai ya tsorata sosai.

Saboda wurin ita kadai ce, Tukuro ya dan tsallake zuwa wani labi neman wani magani

Ta yi saurin sakin kahon saniyar idanunta a kan Ahmad wanda yake takowa cikin sauri, bayan shi kuma Danladi ne kanenta

“Are you in your common sense, babu Kowa a kusa shi ne kike wasa da rayuwarki, da saniya za ki yi kokawa?” rai bace yake maganar.

Dalilin da ya sanya ta yin kasa da kanta ba tare da ta ce komai ba. Lokaci daya kuma tana mamakin zuwan shi wurin kamar aljani. Gibe sati daya kenan cur da ya kawo ta gida.

Tsoki ya ja alamun dai ranshi a bace yake, sannan ya ce “Who ask you to do it”

“I’m asking” ya fada a tsawace ganin ba ta amsa mishi tambayar farkon ba.

A tsorace ta ce “Babu kowa, ba ta bari yaron ya sha nonon ne sai an rike ta”

“And you’re the one da ya kamata ki yi hakan? Da rayuwarki da ta shi wacce ta fi muhimmanci? Kar ya sha mana”

Shiru ta yi ba ta amsa ba, Sai wasa da take yi da hannayen

“This is the last time da za ki sake wannan gangancin ba na so”

Kai ta jinjina, a hankali kuma ta ce “” Ka yi hakuri “

Komai bai ce ba ya shiga karewa matsakaicin dajin kallo. Babu wasu gidaje a kusa sai gonaki da kananun labuka,  ji ya yi hankalinshi bai kwanta ba Hafsat na zama a wurin, idan wani abu ya faru fa.

Da wannan tunanin ya mayar da kallonshi kan shimfidadden dutsen da ke kusa da su, yana da bisa gami da fadi.

Kuma da alama a can ne mazaunin Hafsat, saboda ya hango wasu kaya a kai, da ya tabbatarwa da kanshi na ta ne.

Dutsen ya nufa, Hafsat ta bi shi da kallo, har zuwa lokacin da ya rika hawan dutsen da wani irin style na kwarewa. Wanda ke nuna mata ba yau ne ya fara hawa dutse irin wannan ba

Sanye yake da baƙin wando mai santsi, Sai blue shirt mai dogon hannu, sosai ya yi kyau. Kananun kaya na yi mishi kyau.

Sai da ya gama hayewa dutsen sannan ta janye idanunta, saboda ta san sai ya waigo. Yayin da hancinta ya ci gaba da shakar kamshin da ya bar mata.

<< Abinda Ka Shuka 46

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×