Skip to content
Part 48 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Sai ko gashi ya waigo din, don tsaye ya yi a tsakiyar dutsen hade da cusa hannayenshi cikin aljihunshi yana karewa ko ina kallo. Lokaci daya kuma yana kokarin cooling kanshi.

Don sosai ranshi ya baci da yadda ya ga Hafsat din ya tsani ganganci. haka kawai ta jika mishi aiki

Ya ja dogon tsoki, hade da mayar da idanunshi a kanta.

Yanzu kam nono take tatsa cike da kwarewa, yadda ta shige karkashin saniyar tana tatsar nonon babu tsoro sai abun ya ba shi mamaki. Da alama ta saba yin hakan, saboda babu alamun tsoro ko kadan a tare da ita

Kamar ba yanzu ya gama yi mata fada a kan irin wannan gangancin ba, yanzu idan saniyar ta take ta fa, ko ta soke ta da tsinin kahonta.

Hannayenshi ya fitar cikin aljihun hade da mayar dasu a kan kirjin shi, yana kallon yadda take take shayawar da jiririn saniyar, bayan ta gama tatsar nonon a cikin gora.

Yayin da Danladi ke tsaye kusa da ita, da alama magana suke yi.

Tabbas maganar suke yi, don tana tambayarshi yaushe Ahmad din ya zo, ya ce mata ba jimawa, shi ne Babansu ya ce a rako shi inda suke yin kiwo. Kai ta shiga jinjinawa alamar gamsuwa. Sai kuma Danladin ya ce “Tatuwa yarinyar kin ji  motar dadi.”

Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba, Sai kuma Danladin ya kuma cewa “” Kin ji wani sanyi da kamshi kuwa, kamar a aljanna “

Yanzu kam Hafsat dariya ta yi sosai, har fararen haƙoranta suka bayyana. Karon farko da Ahmad ya ga dariyarta, Sai ta kara mishi kyau sosai kamar kar ta daina dariyar.

Sai bayan da ta kammala komai, sannan ta mike zuwa kan dutsen.

Sannu a hankali take hawa, saboda tana jin idanunshi na yawo a kanta.

Da gaske kare mata kallon yake yi, saboda yanayin jikinta babu mai cewa 17years gare ta. Ko wace kira ta jikinta ta fita.

“Sannu da zuwa” ta fada a nutse lokacin da ta iso wajen shi

“Da alama kin saba da dabbobin nan, kamar ba yanzu na gama yi miki fadan gangancin da kika yi ba. Sai kuma ga shi kin shige karkashin saniyar ma gabadaya” idanunshi kyam a kanta ya yi maganar ba tare da ya amsa gaisuwar ba. Saboda shi ne abin da yake ci mar zuciya.

Kasa ta kuma yi da kanta, ba tare da ta ce komai ba.

“Ke kadai ki kula da duk wadannan dabbobin?” ya yi tambayar idanunshi a kan dabbobin

Kai ta girgiza alamar a’a, sannan ta ce “Mu biyu ne, dayan ya je ya dawo”

“Shi ne zai bar ki a tsakiyar daji, idan wani abu ya faru fa?”

Shiru ba ta ce komai ba. Ya dora da “Let’s assumed ni din nan mugu ne. Daga lokacin da na iso zuwa yanzu ban yi abin da ya kawo ni ba? Tun da na iso wane mutum ne ya gitta?”

Nan ma shirun ta yi, komai ba ta ce ba “Kuna da ganganci, ni kuma ba na son ganganci yana ɓata min rai” ya yi maganar da alamun ɓacin ran a muryarshi.

“Ka yi hakuri!” ta yi karfin halin fada.

Numfashi ya sauke a hankali kafin ya juya zuwa inda ya ga kayan Hafsat ya zauna a daya daga cikin dutsen da ke wurin. Kokarin cire bacin ran da ya ji yake yi.

Hafsat ma ta kara so, hade da zama a kan daya dutsen.

A sanyaye ta ce “Ina wuni, ka zo lafiya?”

“Lafiya kalau, fatan ke ma kina lafiya”

“Alhamdulillah” ta amsa

“I see!” ya amsa

Sai ta murmusa kadan, tana kara kasa da kanta, saboda ta fahimci bai gama hucewa ba

Ita kuma ba ta ga wani abu na tayar da hankali ko ɓata rai ba.

Duk suka yi shiru kamar ba kowa a, wurin kafin ya ce “Za ki je thumbprint Monday, ya za a yi?”

Kanta ta dago, da sauri kuma ta janye idanunta gefe kafin ta ce “A ina ne?”

“Great Ambassador” ya amsa ta

Yanzu kam waro idanunta ta yi kaf a, kanshi, alamun mamaki.

Saboda Great Ambassador babbar makaranta ce ta ƴaƴan manya, ba iya Dawuri da take LGA ba, hatta makwabtan state suna kawo yaransu.

Ya Tajuddeen ya taba kai ta gate din makarantar ya ce mata duk yaro daya ana biya mishi kudin term 150k.

Da gira ya yi mata alamun kallon fa. A lokacin ne ta tuna ashe kallon shi take yi, don haka ta, janye idanun nata, kamar ba za ta ce komai ba, Sai kuma ta daure ta ce “A can zan yi jarabawar?”

Kai ya jinjina alamar eh, hankalinshi a kan wayar shi.

“Hu’umm!” ta fada a hankali

“Me ya faru?”

“Ba komai” ta amsa, hankalinta a kan Tukuro da yake hawowa kan dutsen hannunshi rike da wata shimfidediyar kasa.

Da sauri Ahmad ya mike, don har ga Allah ya tsorata, sam bai san daga inda Tukuro din ya bullo ba, Sai dai kawai ya gan shi rike da katuwar kasa.

Gaban Hafsat ya aje Kasar yana dariya, ga mamakin Ahmad sai ya ga ba ta razana ba, kamar yadda ya yi zato, ta dai dan janye kafafunta kadan.

Abin ya sanya Ahmad tattara hankalimshi kansu yana kallon Ikon Allah

“Gorko am” cewar Tukuro cikin harshen fulatanci

Murmushi kawai ta yi cikin jin kunya, Tukuron kuma ya mikawa Ahmad hannu suka gaisa.

“ke ba za ki tashi  a nan ba wai? ” cewar AHMAD hade da ɓata fuska

Rufe bakinshi ya yi daidai da mikewar ta hade da matsawa gefe.

“Ita wannan yarinyar ba ta da tsoro ne?” Ahmad ya yi tambayar idanunshi a kan Tukuro

Dariya Tukuro ya yi kafin ya ce “Hafsat wai? Tsoro gare ta sosai, daga baya ne ta dan rage”

“Amma ka daina irin wannan kasadar, ya za ka dakko abun cutarwa ka kawo cikin mutane, yanzu idan ya sare ta fa?”

Tukuro ya juya kan Kasar wacce ta yi lamo kamar ta mutu ya ce “Haba yallaboi! Wannan Kasar ko kai a yanzu dai ba ta isa ta sara ba bare Hafsat. Da ace Hafsat za ta kwanta a kanta ta yi bacci, babu abin da za ta iya yi mata da iznin Allah. Bari ka gani…” Tukuro ya nufi Kasar hade da damutso ta ba alamun tsoro ya nufo Ahmad da ita. Duk irin yadda yake son dakewa kasawa ya yi, ya mike da gudu zuwa gefe yana fadin” Ba na son irin wannan wasan. “

Daga Hafsat har Tukuro dariya suke yi, shi ma  tuntsurewa  da dariyar ya yi, karon farko da Hafsat ta ga dariyar shi. Sosai ta shagala da kallon shi.

Cikin dariyar ya ce” Ka aje ta can, ni nan ban sha komai ba”

Shi ma Tukuro cikin dariyar ya ce “Allah Ƴallaboi ka yarda da ni, babu abin da za ta iya maka”

“Ni fa ban yarda”

Duk sai suka kuma fashewa da dariya.

Hafsat ya nuna daga inda yake tsaye yana fadin “Ke sauka mu je, ni Sam ba na ganewa wannan gangancin naku”

“Ka jira a tatsar ma nono ka yi tsaraba” cewar Tukuro da ragowar dariya a muryar shi.

“Ta aje wannan abun hannun naka” Ahmad ya kuma fada daga inda ya yi gudun Hijira

Cikin wata jaka Tukuro ya saka Kasar, sannan ya dauki jarkar da yake zuba ruwa, ya mika Hafsat yana fadin “je tatsar mishi nonon.”

Lokacin da ta fito idanun Ahmad zube a kan kofar, shi ya sa ta kara daburcewa, ya rika bin farar takardar da ke hannunta da kallo, kallon da duk ya, dimauta ta, ba ta samu, damar barin wurin ba, Sai da ya, janye idanun na shi a kanta, kafin ta nufi waje kai tsaye.

Tana gab da isa wurin motar ta ji yar kara hade da kawo wasu danjoji wannan ya shaida mata ya unlocked na motar ne, a nutse ta bude kofar ta, shige.

“Ko me suke tattaunawa oho? Tun da suka hadu suke magana amma ta ki karewa.” cewar Hafsat a bayyane ganin har 6:pm na neman wucewa suna a asibitin.

Kamar Ahmad ya san abin da ta fada sai ya nufo motar, Asad na bin shi a baya.

“Madame Allah Ya kiyaye hanya” cewar Asad lokacin da Ahmad ke kokarin fita daga cikin parking space din, kai kawai ta jinjina komai ba ta ce ba.

Sai da suka fice daga cikin asibitin, sannan ya dayan hannunshi hade da zare farar takardar da ke hannun Hafsat.

Da ido ta bi shi da kallo, lokacin da yake karanta takardar ba ta fahimci komai a kan fsukar shi ba, har zuwa lokacin da ya nade takardar ya mayar mata.

Tsintar kanta ta yi da bude takardar hade da bin kyakkyawan rubutun da kallo. Guntun rubutu ne mai dauke da gwala-gwalan kalamai na soyayya, daga karshe a ka roki a taimaki zuciyar a karɓi rokon ta, Sai kuma lambar waya.

Kyawawan fararen idanunta ta sauke bisa fuskarsa bayan ta gama karanta wasikar. Ganin hankalinshi ba a kanta yake ba.

Ita ma sai ta kawar da kai gefe, zuciyarta na kara maimaita abin da idanunta suka gano.

AMI ya fara biyawa, ya fito tare da rakiyar ma’aikatan wurin.

Kafin ya wuce da ita gida, Sai dai suna isa gidan su Mama Halima na fitowa daga cikin mota, wai ɓurma suka je, yarinyar Goggo ta haihu ɗan bai zo da rai ba.

A gurguje ya gaishe da Mama, saboda ana ta kiran sallahr magriba, sannan ya shaidawa Hafsat idan bai tafi da wuri ba gobe, to zai bullo, idan kuma ya tafi Asad zai zo jibi ya kai ta wurin thumbprint. Sannan akwai waya a cikin kayan ta fara cajin nata kafin ta yi amfani da ita

Godiya ta yi mishi kafin suka rabu.

*****

ASMA’U

JUMA’A 4:30PM

Sanye take cikin doguwar rigar shadda ash, wacce ta yi mata kyau sosai, hade da boye girman cikinta ɗan watanni bakwai.

Kallo daya za ka yi mata ka fahimci tana jin dadi, tana samun kulawa. Fatar nan very smooth, ga ƙiba mai kyau, da ta kara mayar da ita cikakkar mace, takalmi take sanyawa Abdallah, wanda yake sanye da irin shaddar jikinta, da aka tsayarwa da dinki, sosai ya yi kyau gami da girma, girman da har ya zarta shekarunshi

Bayan ta gama sanya mishi takalmin ne, suka fito hade da rufe ko ina, da kuma kashe kayan wuta, idan ka dauke fridge.

Ba ta ji ma da fara tafiya Abdallah ya ce “Ummee ga Sister Nawwara nan da Akhee suna zuwa”

Kai ta daga don tabbatar da abin da ya fada, Sai ko ta ga su Nawwarar sun nufo kansu da gudu, suna dariya.

Ammar Asma’u ta daga dakyar , kafin daga bisani ta shafa kan Nawwara, saboda Nawwara ta girma, za ta kai 10-11years Ammar kuwa yana 8years, Sai Kubrah da take 5years,yanzu kuma Ladifa din tana goyon Assidiq.

Yaranta hudu cif, biyu maza biyu mata.

“Dama Ammy ta ce kina zuwa, shi ya sa na ce bari mu zo mu taro ki”

Cewar Nawwara cikin dariya

“Shi ne za ku taho a kafa” Asma’u ta fada tana dariya

“Kuma Ammy ta siyo mik i burnudin goruba mai yawa” Ammar ya katse Nawwara

Cikin jin dadi Asma’u ta ce “Ku ce in kara sauri”

“Kuma ta siyowa Little game Ummee, mai kyau shi da Kubrah”

A nan gabar kam Abdallah ne ya ce “Kuma irin ta su Hasheem sister?”

“Yaro ta fi ta su Hasheem ma kyau” Ammar ya amsa tambayar.

Da gudu Abdallah ya kwasa, Sai duk suka rufa mishi baya suka bar Asma’u, ta bi su da ido har suka shige cikin gidan, kasancewar dama sun kusa zuwa.

Ta lumshe ido a hankali hade da bude su, tana jin ina ma ace Abdallah yana nan kamar ko wane yaro, ma’ana an same shi ta tsabtatacciyar hanya, da ba ta jin akwai wani abu dai zai zame mata kamar kashin wuya a nan duniyar dai. Ji take kamar a koma baya a goge samuwar Abdallah. Koda ba ta koma gidan Ahmad ba, wanda take kewa a kullum, to za ta zauna da AG cikin farin ciki. Saboda shi ma miji na gari ne

Laɗifa mutuniyar kirki ce, ba wai ba sa kishi ba ne, suna yi idan ya motsa, amma kuma suna girmama juna.

Da wannan tunanin ta tura gate, tun daga farfajiyar gidan take jin hayaniyarsu.

Murmushi ta saki kafin ta karasa ciki, hankalinsu duk yana a kan game, Sai da suka ji maganar ta da Ladifa ne sannan Abdallah ya shiga nuna mata game din shi da Kubrah.

Nawwara kuma ta ruga kitchen ta dakko mata garin gorubar da Laɗifan ta siyo mata.

Tana cin burbudin gorubar suna hira, yayin da yaransu ke ta wasansu. A gidan ta yi sallahr magriba, sannan Laɗifa ta yi mata rakiya da zugar yaran har kusa da gida

Abdallah dai cewa ya yi wurin Ammy zai kwana, ba ta damu ba, tun da dama ya saba kwanan, su ma yaran suna zuwa gidanta su kwana watarana.

<< Abinda Ka Shuka 47Abinda Ka Shuka 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×