Asma’u.
Babban titi ne wanda ya hada hanyoyi hudu, duk da karfe biyu ne na rana, hakan bai hana motoci da sauran ababen hawa zirga-zirga ba.
Daga can tsallaken gabas katon gida ne mai girman gaske wanda aka kayata da ginin sarauta na mazani.
Daga wajen gidan za ka iya hango firda-firdan Dawakai suna harbin iska.
A kofar kuma dogarawa ne da ƴan sanda da ke kula da masu shige da ficen gidan.
A daidai kofar Napep ya sauke Asma’u, fitowarta ke da wuya dogarawan da ke kofar gidan suka nufo ta cike da girmamawa.
Ta rika motsa bakinta kadan a lokacin da take amsa gaisuwarsu, cikin ƴan dakiku suka kwashe duk tulin kayan da Asma’u ta iso dasu zuwa kofar part din ta.
Kai tsaye kofar da za ta sadata da bangarenta ta nufa. Yayin da Dogarawan suka jibge mata kayan da suka dakko a kofar dakinta
A kasalance ta murza kofar shiga babban falon, sassanyan kamshin da ya kama falon ya daki hancinta.
Ido ta lumshe hade da bude su a hankali tana kallon kayataccen falon nata kamar ranar ta fara ganin shi.
Babban falo ne sosai , wanda aka kayata shi da kujeru royal blue haka ma labulayen,
Bayan su ba komai sai katon tv wanda yake zaune cikin wata stand ta zamani, Sai kuma sauran decoration na pop da ya kawata falon.
Akwai dinning area daga can karshen falon, yayin da sauran kofofin dakunan suke ta cikin wani corridor da ya ratsa daga wajen dinning area din.
Cikin corridorn ta shiga, kofar kitchen ta bude, ta yi tsaye tare da kallon yadda komai yake a mazauninshi babu datti.
Kofar ta rufe tafiya kadan ta kai ta kofar falon ta, ba ta shiga ba ta juya damanta hade da tura wata kofar.
Nan kuma wani tangamemen falo da aka kawata shi da kilisai da tuntaye kallo daya za ka yi ma wurin ka fahimci fada ce aka shirya ta ganawa da muhimman baƙi.
Idanunta ta dora a kan hoton Ahmad da ya dauka a kan doki cikin shiga ta sarauta.
Sosai ya yi kyau duk da yadda aka nade fuskarshi da rawani.
A kusa da hoton still wani hoton Ahmad din ne cikin kayan airforce, hoton da ya fito da ainihin kyawun gami da kwarjininshi.
Kofar ta jawo kai tsaye kuma ta nufi dakinshi
Falon a gyare tsab, Sai dai komai a kashe, ta wuce cikin bedroom.
Nan din ma komai a gyare yake sai kamshin turarurruka da maya-mayan da yake amfani dasu.
Katon hoton shi da yake tsaye cur ta zubawa ido.
Sanye cikin manyan kaya na fara kal din shadda, kayan da suka karbe shi tare da kara mishi kyawu.
Ido ta lumshe cike da takaicin abin da ta aikata.
Daga lokacin da suka rabu da Mk zuwa yanzu wata irin nadama ce ta cika mata zuciya.
Ita kanta tana jin cewa ba ta kyautawa Ahmad ba.
Ba ta taɓa tunanin kalar ƙaddarar da ta same ta jiya za ta same ta ba.
Kafin yanzu idan an ce za ta aikata zina da auranta za ta ce karya ne
“Oh Allah!” ta fada cikin kasalalliyar murya lokaci daya kuma ta zauna jabar a gefen gadon, ta dauke idonta daga kan hoton Ahmad, ji take yi kamar ya san abin da ta aikata.
“Me ya sa na aikata?” ta tambayi kanta a hankali cike da jin zafin kanta.
“Ka yafe min don Allah Ya Ahmad, ba ka cancanci wannan daga gare ni ba. Kana nuna min duk wani so da kauna, ka ba ni duk wata kulawa da mace ke nema a wurin mijinta.
Ban nemi komai a gidanka na rasa ba. Kai mutum ne da ko wace mace ke fatan samu a matsayin mijinta. Ga shi na ci amanarka duk da irin yaddar da ka yi min. Don Allah ka yi hakuri, na dauki alkawarin ba zan sake ha’intarka ba. “
Ta kai karshen maganar hade da lumshe idanunta.
Ta kwanta sosai saman gadon tana kara shakar kamshinshi da ya kama dakin.
” Me ya sa? Why? “
Ta yi tambayar a bayyane tare da mikewa zaune kan gadon ta shiga bubbuga kafafunta kamar za ta yi kuka.
“Ban so na aikata ba, me ya shiga kaina ne! Astagfirullah Allah! Mijina bai cancanci haka ba, ya rike ni da gaskiya me ya sa na yi mishi haka?”
Ta koma ta kwanta lakwas kamar wacce ba ta da ƙashi. Lokaci daya kuma ta shiga tuno farkon haduwarsu da Ahmad.
Jama’a babbar jaha ce da take daya daga cikin biranen da kasa ke alfahari dasu.
Idan ka dauke yawan zafin jihar to ba ta da wani aibu da zai za zama abun ƙi a wurin mutane.
Akwai kasar noma, ruwa don noman rani da kuma kifaye.
A hankali kwakwalwarta da dauketa shekaru uku can baya.
Shekarun da suka haɗata da Ahmad
Kasancewar mahaifinta Nigerian airforce ne, a bakinshi ta fara jin labarin Ahmad, yake fadawa momynsu an kawo musu sabon commander, yana da kirki sosai.
Kullum za a sako hirar aiki to sai Babanta ya yabi Ahmad.
Ba shi kaɗai ba, kusan kowa alkairin Ahmad yake fada.
Ba ta taɓa ganinshi ido da ido ba, Sai dai ta ga wucewarshi a mota za shi ko ya dawo daga office tare da convoy din shi.
Watarana ta dawo daga kasuwa da kaya masu yawa, ga shi mashin baya shiga ciki, Sai dai ya aje su gate.
Ta rika daukar kayan dakyar, tafiya kadan take ajiyewa ta huta.
A hankali wata mota mai kyan gaske ta tsaya kusa da ita, ya sauke glass din motar tare da fada mata ta shigo.
Wannan ba sabon abu ba ne ga duk wanda ya tashi a cikin barrack din, dalilin da ya sanya ba ta ji komai ba, ta bude baya hade shigar da kayayyakin da ke hannunta, kafin ta zauna shi kuma ya ja motar cikin kwarewar tuki.
Sannu a hankali take kwatanta mishi block dinsu, har zuwa lokacin da ya isa
Sosai ta yi mishi godiya a lokacin da take fita, duk da rashin amsawarsa hakan bai sanya ta damu ba
An yi haka da 1week Babanta ya zo mata da zancen Ahmad ya nemi auranta, kuma shi ya amince mishi.
Ko sau daya ba ta nuna ƙin amincewar ta a hada su auran ba ko bacin rai ba, abun ma dadi ya yi mata.
Duk da akwai Kb a zuciyarta na tsawon shekaru, amma ba ta jin za ta yada Ahmad saboda shi.
Musamman da ta san cewa ba auranta zai yi ba, don a lokacin yana tsaka karatu ne.
Ko ba haka ba, mahaukaciyar mace ce kadai Ahmad zai nuna yana son auranta ta ƙi amincewa.
Ko makaho ya laluba ya san bambancin Ahmad da Kb kamar bambancin da ke tsakanin sama da ƙasa ne
Ba wata soyayya suka yi da Ahmad mai tsawo ba, aka daura musu aure, auran da ya samu halartar manyan mutane.
Ba ta gama tsinkewa da lamarin Ahmad ba, Sai da aka dakkota zuwa asalin garinsu na Dawuri ta kara fihimtar waye shi, ɗan kuma waye? shi ne ɗa babba namiji a wurin Hakimin Dawuri Muhammadu Inuwa.
Hausawa sun ce arziki, talauci da kuma ilmi suke bayyana kansu ga mai shi, duk da wadannan ababen biyu wato ilmi da arziki sun bayyana kansu gare ta daga Ahmad ba ta yi tunanin abun ya kai haka ba.
Bai taba faɗa mata Babanshi ne Hakimin Da wuri kuma Galadiman Tunga ba.
Za ta iya cewa masarautar Dawuri na daya daga cikin masarautun da suka tara zuriya masu yawa, masu ilmi, da sanin ya kamata ba kuma girman kai ko ɗagawa.
Sun rike ta kamar jininsu, wata matsalar dangin miji ba ta santa ba.
mijinta kuma na yi mata wani irin so da kaunar da har mamaki abun ke ba ta, tun ba da ta ga basu yi wata soyayya a waje ba.
Tana jin dadin zama da shi, mutum ne shi mai son kyautatawa iyalanshi. Sannan ba mai son hayaniya ba. Shi ya sa ba a fada da shi.
Idan ranshi ya baci shiru kawai yake yi, idan kuma ke ce ya yi wa ba daidai ba, take zai ce ki yi hak’uri saboda rashin son hayaniyar shi.
Surukarta ma babu wani sabani a tsakaninsu, rikon ƴa da uwa take mata.
Duk wannan bai sa ta raba gari da Mk ba. saboda shi din ya zama jini da tsokarta.
yanayin nisan da ke tsakanin Dawuri da jahar Jama’a ya sa take daukar lokaci ba ta je gida ba.
Wannan shi ne zuwanta na 3 gida tsawon shekaru biyu da wani abu da auranta.
Kuma a wannan karon ne suka shirya haduwa da Mk a lokacin da take hanyarta ta dawowa gidan auranta
A tasha ta bayar da ajiyar kayanta, ita kuma ta taho wurin Mk ta kwana, da safe kuma ta koma tasha wurin kayanta ta dakko su zuwa gida. Wannan dalilin na daya daga cikin dalilin da ta ce ba sai an zo Ɓurma an dauke ta zuwa Dawuri ba, ta ce za ta taho da kanta, don dai kawai ta samu damar haɗuwa da Mk
Ta sauke numfashi a hankali lokaci daya kuma ta shiga girgiza kai cike da bacin rai gami da takaicin abin da ta yi.
Kamar wacce aka tsunkula ta mike zuwa babban falo inda ta watsar da hand bag din ta.
Wayarta ta dakko ta zare Sim din hade da jefa shi cikin bakinta, ta shiga taunashi a hankali , so take ta taune duk wata alaƙa da ta yi saura tsakaninta da Mk ba ta taba aikata abin da ta kasance cikin nadama ba irin wannan.
Babban abin da ke damunta shi ne, babu wani appreciation daga kb din, tun da suka rabu ko flashing din shi ba ta kara gani ba.
Idan har kb ya yi watsi da ita ne saboda ba ta gamshe shi ba ko kuma ya samu abin da yake so, lallai da ta yi faduwar baƙar tasa. Kuma za ta sanya shi a layin mutanen da ta fi tsana a duniya.
A nan mijinta duk lokacin da ya kusance ta ya yi ta yaba ta kenan gami da lallabata, sai ga shi wani ya same ta a ɓagas kuma ya ci moriyar ganga ya yada kwaronta.
Kwankwasa kofar da aka yi ne ta sanya ta saurin daga kai tana kallon kofar kafin ta ce “Waye?”
Daga can waje Asabe ta ce “Ni ce.”
“Turo kofar a bude take”
Ta shigo falon hannunta rike da babban tire wanda aka jero manyan flask biyu da ƙanana guda biyu.
Daga nesa ta zube cike da girmamawa tana fadin “Barka da hutawa rankii-ya dade. Allah Ya kara lafiya da nisan kwana. Hajiya Babba ta ce tana miki sannu da zuwa”
Ta dakata hade da daga hannayenta du biyun alamun jinjina.
Ajiyar zuciya Asma’u ta sauke mara dalili, kamar ba za ta ce wani abu. Sai kuma ta daga hannunta daya ta yi wa Asabe nuni a kan ta tafi. Kamar mai tsoron magana ta ce “Na gode Asabe, a yi min godiya wajen Hajiya”
“Sako ya isa rani-ya-dade”
Cewar Asabe cikin girmamawa.
Bayan fitarta Asabe, Asma’u ta samu damar yin wanka, ta yi Sallahr azhur ta jira la’asar. Sannan ta ci abinci.
Turare kawai ta murza, ta dora karamar hijab a kan doguwar atamfar da ke jikinta.
Kai tsaye bangaren Hajiya Babba (surukarta) ta nufa.
Har ta isa bangaren ba ta yi karo da kowa ba.
Ta tura kofar falon ta shiga, ta lumshe ido tana shakar kamshin turaren room freshener mai dadi.
Daya daga cikin kujerun falon ta zauna, har lokacin zuciyarta ba dadi.
Ba ta jima a zaune ba Hajiya Babba ta fito sanye cikin riga da zane na atamfa mai kyau, hannunta rike da casbaha.
Ganin Asma’u zaune sai ta kawata kyakkyawar fuskarta da murmushi tana fadin “Mutanen jihar Jama’a , kun sha hanya”
Cike da girmamawa Asma’u ta zame kasa tana murmushi, sannan ta gaishe da Hajiyar.
Ta amsa da nuna kulawa tare da tambayarta mutanen gida da yadda ta baro su.
Ta rika amsata cike da ladabi.
Hajiyar ta gyara zama cikin tausasawa ta ce “Sai kuka sha bam-bam da maigidan na ki”
Shiru Asma’u ta yi komai ba ta ce ba.
“Ki kara hakuri kin ji, na san wani lokaci ba ki jin dadin abin da yake faruwa. Yanayin aikinsun ne sai a hankali. Musamman yanzu da aka tura shi Arewar nan, Sam babu zaman lafiya. Ke dai ki yi ta addu’a Allah Ya kare su”
“Amin.” cewar Asma’u a hankali. Saboda duk inda za a doki jaki dai tabon jiya ne
Ta saba da wannan tun a kan mahaifinta
“Wlh bai so tafiyar nan ba saboda dawowar ki, kawai sun matsa ne.”
“Ba komai” Asma’u ta kuma amsawa a hankali.
“Sai na ji an ce keke ya aje ki a waje. Na ce wato ba ki jin magana ko?”
Suka yi siririyar dariya a tare, Hajiya ta dora da
“Wlh ina ji miki tsoron ranar da Ahmad zai kama ki, ni dai ba ruwana”
“Ba zai kama ni ba” cewar Asma’u har lokacin da sauran dariya a muryarta
Hira suka shiga wacce da yawanta a kan tafiyarta ne da kuma aikin maigidanta Ahmad.
Wannan kenan. Bari mu leka AG da Hacker.
*****
Daga can karshen shagonsu Hacker AG ya yi parking, bai jima ba Hacker ya fito kunnensa manne da earphones zuwa wurin motor.
Shi ne ya bude kofar ya shiga hade da zama kusa da AG.
A takaice suka gaisa, kafin AG ya tafi kai tsaye a kan dalilin zuwan shi wurin.
“Ya ake ciki?”
“Ba komai a ciki fa, shiru ne.”
Cike da zolaya Hacker ya yi maganar.
AG ya juyo sosai yana kallon shi, irin kallon nan mai nuna ban son wasa
Hacker ya gyara zama tare da zare earphone din da ke kunnensa duk da ba waƙa yake ji ba ya ce
“Akwai matsala ne yallaboi.”
“Me ye matsalar? ” cewar AG yana kallon shi.
Hacker ya kuma gyara zamanshi hade da tattara duk hankalinshi a kan AG yana fadin
“Iyakar bincikena, ban samu account mai dangantaka da hoto da kuma sunan da ka ba ni ba”
Damuwa ta bayyana ƙarara a kan fuskar AG, da alama bakinsa ya mutu, saboda uffan bai ce ba.
Ganin haka ya sa Hacker ya mika mishi wayar hannunshi tare da fadin “Duba wannan hoton ka gani, ya yi kama da wanda ka ba ni?”
Jiki a sanyaye AG ya karba hade da zubawa hoton ido.
“Shi ne ka ba ni hotonshi?” Hacker ya tambaya idanunshi zube a kan AG.
Kai ya shiga jinjinawa alamar shi ne.
“Wani friend dina a Facebook ne mai suna Buhari na ga ya yi post din shi a shafin shi, ya kuma rubuta flash back. Sai kuma na ga akwai wanda kake nema a cikin hoton. Matsala daya bai yi tagging din sunan kowa ba. Sannan ina ta bibiyar comment section, cikin wadanda suka yi comment babu wanda kake nema.” ya dakata hade da kallon AG wanda har zuwa lokacin bai dauke idanunshi a kan hoton da ke kan wayar Hacker ba.
Kamar ba zai ce komai ba, Sai kuma ya ce” And what next? “
” Na yi bincike a kan shi, na gano dan jihar Maiha ne, amma yana karatu a jami’ar Dawaki , so ina tunanin idan har aka same shi, tabbas za ka samu duk abin da kake so a kan wanda kake nema. “cewar Hacker idanunshi zube a kan AG.
Cike da gamsuwa AG ya riga jinjina kai kafin ya ce” You’re right. Tabbas samun Buhari zai taimakamin wajen farautar Muhammad Kabir. And ka tura min hotunan Buhari sannan ka bar sauran aikin a hannuna. “
Cikin jin dadin ganin yadda AG ya muhimmantar hade da amincewa da maganarshi da kuma yabawa aikin shi Hacker ya ce” An gama yallaboi.”
Kudi AG ya mikawa Hacker masu yawan gaske, sannan suka yi sallama.