Da wannan taku na za a, ba za a ba, suka isa wurin wata kayatattar kujera, ta hannunta da ke cikin hannunshi ya fahimci kokarin zama take yi, don haka ya yi saurin matsa hannu. Sai ko ta ankare don haka ita ma ta yi tsayen, kamar yadda ya yi.
Yin da sojojin nan suka shiga miko gaisuwa da wani irin salo na parade mai burgewa.
Hafsat kam sosai ta ware idanunta da ke cikin mayafi tana shan kallo. Kara godewa Allah ta yi, da Ya sa ta auri soja, yau kam auran soja ya burgeta, ta. . .