“Da alama ƴar’uwarshi ce. Amma ni ban san ta ba. Kila na a nan kusa take ba, su din nan akwai yawan dangi”
“Muma ai sai mu yi sallah, mu ɓulla gidansu Mk din a gaisa mu kama hanya, yanzu kin ga Tajuddeen ya dawo”
Cewar a Mama
“Gaskiya kam”
Goggo ta amsa
Asma’u na fita AG ya bude mata kofar motar ta ciki.
Bayan ta shiga ne ta kwantar da kanta jikin kujera, hade da lumshe ido, Sai kuma ta saki murmushi hade da bude idon a kan AG ta ce “Mu je gidansun”
Kan motar ya juya zuwa hanyar da za ta sada shi da Family house na su Mk. Saboda kafin ya kawo Asma’u sai da ya yi bincike sosai ya gano gidan Mk da kuma gidan iyayenshi.
Kasancewar Baban Mk Reps ne a wannan lokacin, shi ya sa gidanshi yake da tsaro sosai, sai dai kallon Abdallah da ke rike a hannun Asma’u ya zame musu ID card, kuma gate pass. Don haka ba a tsananta musu bincike ba suka wuce, har bangaren Hajiya Fatima aka yi wa Asma’u jagora, yayin da AG ya tsaya cikin mota yana jiran fitowarta
Ruma kam bayansu Mama sun shiga yin sallah Mk ta kira a waya hade da shaida mishi sakon Asma’u .
Kwatanta tashin hankalin da ya shiga, ba zai yiwu ba, saboda har ji ya rika yi baya gani, shi ya sa cikin sauri ya nufo gidansu a ruɗe.
Asma’u kam da sallama ta shiga babban falon Hajiya Fatima, a lokacin zaune take tana amsar kiran, shigowar Asma’u da kuma arba da fuskar Abdallah da ta yi, ya, sanyata yanke kiran cikin sauri, idanunta a kan Abdallah, saboda Mk take gani a lokacin da yake yaro, komai na yaron na Mk ne, tafiyarshi, structure na jikinshi, gashin kansa, hatta idanu da yanayin kallon shi irin na Mk ne.
Kasa Asma’u ta zauna hade da mikawa Hajiya Fatima gaisuwa, ta amsa gaisuwar a sanyaye, tun ba ta ji abin da ke tafe da Asma’un ba.
Jin shirun ya yi yawa ne ya sanya ta fadin “Baƙuwa ban shaida ki ba”
“Sunana Asma’u, daga jama’a na zo wurin Mk ne”
Gaban Hajiya Fati ya shiga dukan uku-uku, har wani fitsari take ji, a zuciyarta take fadin “Me kuma ya hada Mk da wata Asma’u a garin Jama’a, ga ta har da yaro mai kama da shi” kafin ta gano amsar Mk ya sako kai cikin falon a matukar kidime.
Kai tsaye idanunshi a kan Asma’u suka sauka, wacce take zaune a kasa ta lankwashe kafafunta, kanta a kasa, Sai Abdallah da ke gefen ta
Shigowarshi ya sanya ta dago kai kwayar idanunsu suka hadu, ta janye nata a hankali, bayan ta aika mishi da wani kallo.
Saman kujera ya zauna, yanzu kam idanunshi a kan Abdallah wanda ya zama kamar kumbo kamar katanta ko kamar ya yi kakinshi ya ajiye.
Gabanshi ya ci gaba da faduwa lokacin da Hajiya ta ce “Yauwa, ga baƙuwa ka yi, wai daga jama’a.”
A karo na biyu Mk ya kuma dora idanunshi a kan Asma’u, Sai dai a wannan karon ba ta kalle shi ba, idanunshi ya dauke ba tare da ya ce komai ba
Jin shurun ya yi yawa ne Hajiya ta ce “Asma’u ga Kamaladdeen, ko ba shi kike nema ba?”
Daga yadda take ta ce “Shi ne” a hankali.
Wani shirun ya kara ratsa falon, a wannan karon Hajiya Fati ba ta kara cewa komai ba, har lokacin da Asma’u ta mike hannunta rike da Abdallah, a kan cinyar Mk ta dora shi tare da fadin “Zai yi hutu a nan, idan hutu ya kare zan zo in dauke shi” Daga haka ta, daga kafa da niyyar ficewa daga falon
Hajiya Fati ta yi saurin fadin “Waye zai yi hutun a nan, waye shi?”
Cikin rashin fahimta ta yi tambayar
Komai Asma’u ba ta ce ba, kafarta ta kuma dagawa da zummar ficewa cikin falon.
Da sauri Hajiya Fati ta riko ta tare da fadin “Ina za ki je? Waye wannan yaron”
“Ɗanshi ne” Asma’u ta amsa
Ba iya Hajiya Fati ce kawai ta ji maganar kamar dirar kibiya a kirji ba, har da su Ruma da suke niyyar shiga dakin, shi ya sa cak suka tsaya, without any making sound.
“Ɗanshi?” Hajiya Fati ta tambaya a kiɗime
Kai Asma’u ta jinjina ba tare da ta ce komai ba, Hajiya Fati ta sauke idanunta a kan Mk tana fadin “Da gaske ne abin da ta fada?”
“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!” ta shiga maimaitawa, saboda shurun da Mk ya yi ya, tabbatar mata da Abdallah yaronshi ne, ko ba haka ba ma, kammannin da ke tsakaninsu ya isa ta gasgata Asma’un
“Auran ki ya yi?”
Kai Asma’u ta girgiza lokaci daya kuma tana ficewa daga falon idanunta na zubar da hawaye.
A nan ta yi kicibis da Ruma, Hafsat, da su Mama wadanda suka yi kamar an zana su.
Da ido suka bi ta da kallo har ta ɓacewa ganinsu, kafin suka saka kai cikin falon, saboda tuni Hajiya Fati ta gansu, Idan ka dauke kukan Abdallah ba komai da ke motsi a falon.
Cikin rashin kuzari Hajiya Fati ta ce “Sannunku da zuwa”
Su ma a kasalance suka amsa, sannan suka yi mazauni, aka shiga gaisawa, Mk dai ko kanshi bai dago ba bare ya hada ido da kowa a cikinsu, har suka gama gaishe-gaishensu suka fita Hajiya Fati kuma ta fita don yi musu rakiya.
Jiki babu ƙwari Ruma ta yi sallama da su Goggo, su kansu su Goggon jikinsu a sanyaye yake, shi ya sa tafiyar tasu ba ta yi armashi ba, kamar lokacin da suke zuwa.
Har kofar gida suka aje Hafsat, kafin suka wuce.
A bangaren Hajiya ta yi sallahr magariba da isha’i ta ci abinci, kafin ta koma sashenta, saboda a gajiye take likis, chat ma sama-sama ta yi da Ahmad ta kwanta.
*****
Mk
Zuwan Abdallah zuriyar Alhaji Bashir abubuwa da yawa sun faru, wadanda duk marasa dadi ne, musamman bangaren Hajiya Fati, ta fi jin zafin abun, kowa ya sani, Mk shi ne ɗa ma fi soyuwa a wurin Alhaji Bashir, har ya kasa boye wannan soyayyar da yake mishi ta fito fili. Shi ya sa Mk din ya yi bakin jini a wurin wasu ƴan’uwamshi musamman wadanda suka hada uba. Basu kadai ba har da abokan zaman Hajiya Fati. Shi ya sa daga Hajiya Fati zuwa Mk kullum cikin kokarin ganin Mk bai yi wani abun aibu ba suke. Yanzu kam da wannan batu ya fito, ta tabbata ko ba su nuna jin dadinsu a zahiri ba, to a badini har Allah ya ƙara sai sun yi.
Shi ya sa cikin kwanaki kankane da kawo Abdallah Hajiya Fati ta sha ruwa ku san leda goma, kadan za ace sai an kara mata ruwa.
Mk kam kunya har baya son fita, tun da aka kawo Abdallah bai yarda sun hada ido da Alhaji Bashir ba. Ba iya shi kadai ba, hatta Ruma kunyarta yake ji, koda yaushe yana daki kwance, saboda yana jin kila zuwa yanzu a garin nasu kowa ya sani, musamman su da dama kadan ake jira a fara talla da su.
Ruma dai tuni Goggo ta kira ta a waya, ta yi mata gargadin ahir ta tayar da hankalinta a kan wannan batun, nata ido, kar allura ta tono garma, tun da ita ma tana da nata guntun kashin a duwawunta.
Shi ya sa ta kame bakinta shiru, ko sau daya ba ta taba tunkarar Mk da maganar ba. Iyakaci idan Abdallah ya zo ta yi mishi wanka, ta ba shi abinci hade da sake mishi fuska.
Abdallah kam ba shi wurin Ruman ba shi wurin Hajiya Fati, duk wancan tashe-tashen hankalin shi bai shafe shi ba. Yana samun duk wata kulawa babu hantara, saboda a hankali soyayyarshi gami da tausayinshi ke ratsa zukatan ginshikanshi, Hajiya Fati, Mk da kuma Alhaji Bashir.
Yanzu ma kwance yake kusa da Hajiya Fati a akan makadaden gadon ta na alfarma, lokaci daya kuma yana cin biskit din datebase.
Hajiya Fati ce kwance a gefenshi, wani irin ciwo kanta yake mata, tun daga lokacin da aka kawo Abdallah ba ta ƙara lafiya ba, ciwon yau daban na gobe daban
Jin ta take yi duk ta muzanta, wanda ya taɓa riskar kanshi a situation din da take ciki ne kawai zai fahimci yadda take ji.
Amma duk lokacin da ta kalli Abdallah yana wasanninshi a tsakiyar dakinta, ta tuna jikanta ne da aka samar mata ba ta hanyar aure ba, Sai ta ji komai na duniya baya yi mata dadi, ko baƙi ba ta son ta ga an yi a gidan. Shi ya sa idan har za a yi taro take tura shi gidan Ruma.
Mk ya turo kofar ya shigo, a sanyaye, tun daga lokacin da Asma’u ta duro rike da Abdallah kawo yanzu ya koma mara kuzari babu karsashi ko kadan a tare da shi.
Da ido Abdallah ya bi shi har zauna kan stoll din mirror, Saboda hat Yanzu saba dasu ba, rashin uwa ce ya sa yake uwar rana da su.
“Ya jikin?” ya tambaya a sanyaye
“Da sauki, har yanzu dai kan ne yake ciwon” Hajiya Fati ta amsa shi
“Sannu, Allah Ya ba ki lafiya, ki dan rage damuwa”
Yumkurawa ta yi hade da mikewa zaune, cikin yanayin damuwa ta ce “Damuwa dole ce Kamal, Idan aka ce ma kar inda mu to an raina min hankali. Ba ka yi tunani me zai je ya zo ba Sam. Ka manta yadda muke zaune a cikin gidan nan? Kullum neman kuskurenmu ake yi. Ba iya cikin gidan nan ba ma, ka manta waye mahaifinka, haka nan ma an sawo sharri a kasuwa an lika mishi barantana abu da reference. Kuma Kai kanka, ka san me za ka zama nan gaba? To wannan tabon zai iya, shafar siyasarka a nan gaba. Sannan yaron nan me ye makomarshi Kamal, me zamu fada mishi idan yi girma? Wannan shi ya fi damuna “
Ta karasa maganar cikin kuka mai cin zuciya. Abdallah ya mike zaune sosai yana kallon ta. Sai kuma ya juya kallon na shi a kan Mk yana fadin” Ka tafi ka sanya ta kuka”
Haka ya mike hade da han hannun Mk zuwa falo, Sai Mk din ya yi sama da shi hade da nufar part din matasan gidan.
Dakin kannenshi ya bude, kan katifa ya kwanta hade da dora Abdallah a kan cikinshi. Zuciyarshi babu dadi, kukan da mahaifiyarshi take yi, da kuma yawan ciwon da take yi yana matukar daga mishi hankali
“A kira ma Ummee?” cewar Mk ganin Abdallah na niyyar kuka, saboda ya fi sakewa da Hajiya Fati. Ganin ta yake kamar Mommyn Jama’a.
Layin Asma’u ya shiga kira, karon farko da zai, kira ta tun bayan da ta kawo Abdallah.
Gab kiran zai yanke ta daga, shiru ba ta ce komai ba, shi ma Abdallah ya kanga ma wayar bayan ya sa a, handsfree
“Hello Ummee!” Cewar Abdallah da muryar yara
Numfashi ta sauke a hankali kafin ta ce “Little! Kana lafiya?”
“Eh.” Ya amsa kafin ya ce
“Ki zo mu tafi gida Ummee, ban son nan”
“To Little, next week Sha Allah zan zo in dauke ka ji ko”
“To!” ya fada cikin ɗoki.
Mk ya karbi wayar yana fadin “Next week din za ki zo ki dauke shin?”
“Ka ƙosa ne?”
Duk da damuwar da yake ji hakan bai hana shi murmusawa ba kafin ya ce “No. I’m just asking”
“Ranar da ka shirya ka yi min magana in ba ka address ka kawo shi” Daga haka ta yanke kiran.
Ya bi wayar da kallo, wani murmushin ya kuma yi, hade da kwantar da Abdallah a jikinshi. Shi fa sosai yake kaunar yaron, idan ma za ta bar shi zuwa yanzu kam bai damu ba. Tun da aikin gama ya gama.
*****
Hafsat
Yau kam shirin zuwa Maƙera ta yi, karo na farko da za ta je gida tun bayan auran. Shigar sarauta Hajiya ta sanya ta yi, har da alkyabba gami da dogarawa ƴan rakiya. Mota biyu a ka ba ta. Misalin karfe shadaya na safe suka Isa Maƙera, Hafsat wani irin dadi take ji mara misultuwa, ba ta jira dogarawa sun bude mata kofa ba, ta ɓalle murfin kofar hadewa da kwasawa da gudu zuwa cikin gidan
Cikin sa a kuma ta yi karo da Malam Ayuba tsaye a tsakar gida, cikin murna ta makale shi. Shi ma sai ya kasa rufe baki, ya shiga wangale bakin yana karewa Hafsat kallo, wacce ta kara kyau gami ƙiba mai cika ido. Ba shi kadai ba, duk matan gidan da yaran gidan kallon ta suke yi cike da sha’awa, yau ga Hafsat diyar Hindatu ta zo tare da rakiyar fadawa, ita kanta Hafsat din sai ta rika jin ko iya nan aka tsayawa ita kam ta godewa Allah, mutanen da suka tsane ta, hade da gudun hada hanya da ita, yanzu kuma ta fi karfinsu.
Kai tsaye dakinta da yake rufe Goggo Amarya ta bude mata.
Saman gadonta ta fada cike da kewar dakin, ba bata lokaci ta yaye alkyabbar nan ta shiga gyara dakin, zuwa azhur ya fito fes. Wanka ta yi hade da cin abinci lokaci daya kuma tana taba hira da yaran gidan suna ba ta labarin abin da ya faru.
Daidai lokacin Malam Ayuba ya kuma shigowa gidan, har ɗakin Inna Kuluwa ta bi shi, suka sake sabuwar gaisuwa, hankalinshi ya tattara kanta yana fadin “To Hafsat babu dai wata matsala ko?”
A nutse ta shiga girgiza kai alamar a’a
“Mai gidan na ki bai dawo ba?”
Kan ta kuma dagawa alamar eh.
“To ki rika yi mishi addu’a kin ji, Allah Ya tsare shi, ya dawo da shi guda lafiya. Duk wanda aka ce miki ya je Kasar waje yaƙi ai dole a rika yi mishi addu’a”
Gaban Hafsat ya shiga dukan tara-tara. Saboda ba ta san yaƙi ya tafi ba, kawai dai an ce mata yana wurin aiki. Shi ya sa idan ya kira video call, Sai ta ganshi cikin wasu kaya irin wanda sojojin Kasar waje ke sanya idan suna yaki.
Take tsoro ya kamata, tun da ya tafi ba ta taba shiga farga ba irin ta yanzu ba. Idan aka kashe shi kam ai ta shiga uku.
“Ki zauna da kowa lafiya kin ji, mijinki da danginshi mutanen kirki ne, kin ga duk wata sai sun aiko min da kayan abinci.”
“Mun gode” Hafsat ta amsa a aanyaye
“Ya makarantar?”
“Saura sati biyu mu fara jarabawar fita gabadaya”
“Ma Sha Allah! Allah Ya taimaka”
“Amin” ta amsa, shi kuma ya ci gaba da yi mata nasihohi masu rasa zuciya, duk sai jikinta ya kuma mutuwa, haka ta baro dakin babu kuzari.
Sai da aka yi sallahr la’asar sannan ta yi shirin shiga gari.
Dogarawan nan basu bar ta, ta tafi da kafa ba. Ko ina a mota suke kai ta. Gidansu Farida, gidansu Ni’ima. Har wurin Tukur. Shi ya sa sai 6pm suka dawo.
Zuciyarta ta dan yi wasai, musamman da Tukuro ya ce mata Ahmad yana lafiya, kuma kwana nan zai dawo.
Tun da ya fadi haka, jikinta yana ba ta akwai makamancin abin da ya fada a tare da Ahmad din.
Basu baro kauyen ba, Sai ana sallahr magriba, boot dinsu dauke da tsarabar nono mai kyau, fura da manshanu
Sai kubewa busassa, wake, daddawa, kuka har da dakakken yaji.
*****
Tun daga lokacin da ta ji cewa Ahmad yaƙi aka tura shi hankalinta bai sake kwanciya ba, abinci da take ci da yanzu kam ba ta iya cin shi, bacci ma sai dakyar take yin shi, shi ya sa take yawan tashi sallahr dare.
Ba ta san ta damu da shi ba sai a wannan lokacin, shi ya sa always tana online checking on him. Har abun mamaki ya rika ba shi, da shi ne yake nemanta, yanzu kam ita ce take neman shi ko wane lokaci.
Da zarar ya dauki some hours baya online zai zo ya samu sakonninta da yawa.
Babu abin da take so irin ta ji yaushe zai dawo, shi kuma sai dai ya ce mata soon in Sha Allah
Kamar yau ma da ta kira shi a video call din korafin ba zai zo ranar graduation din ta ba take yi mishi
Salon yadda ta yi maganar ne ya sanya shi lumshe idanu kafin ya ce “Yaushe ne graduation din”
“Next Saturday”
“Saura 9dz kenan?”
Kai ta jinjina a hankali alamar eh.
“Allah Ya kai mu, ko ban zo ba, akwai Mama, akwai Hajiya, akwai Asad, ga Aunty Safiya, ga Aunty Ju. Duk basu ishe ki ba?”
Narke fuska ta yi kamar za ta yi kuka, komai ba ta ce ba.
Murmushi ya kuma yi, kwanakin nan sosai take kara shiga ranshi, musamman canjawar da ta yi, na yawan neman shi da take.
Cikin sigar lallashi ya ce” Shi kenan zan duba in gani “
Fuskar tata ta shiga warwarewa, hakan sai ya kara sanya shi murmusawa.
Fatan ta kawai shi ne ya, zo din, saboda yanzu babu abin da take so irin ta gan shi.
MK
Address din da Asma’u ta turo mishi ya rika bi, har zuwa lokacin da ya yi parking a gaban katon gate din gidan. Ya juya yana kallon Abdallah wanda yake ta murna sakamakon ganin gate din gidansu, kokarin bude kofar motar kawai yake yi ya fita.
Mk ya kai wayar kunnen shi sakamakon daga kiran da Asma’u ta yi “Ga ni a kofa”
“OK” ta amsa hade da yanke kiran.
Tsakanin yanke kiran nata da fitowar AG bai fi 5mns ba. Sanye yake cikin jallabiya milk colour’s.
Wani abu mara dadi ya soki zuciyar Mk, har yanzu yana jin zafin AG ba kadan ba.
Kofar ya budewa Abdallah, saboda tun da ya ga AG ya fito yake buga murfin alamun dai yana son fita.
Da gudu kuwa ya karasa jikin AG, shi kuma ya daga shi cike da farin cikin ganin shi, kafin ya sauke shi yana fadin “Je ka ciki Ummee ta gan ka”
Da gudu kuwa ya nufi gate din
AG kuma ya shiga cikin motar yana mikawa Mk hannu a lokacin da ya zauna.
Hannun kawai Mk ya mika mishi ba tare da ya ce komai ba. Ko lokacin da ya kai Asma’u gidan irin wannan gaisuwar Mk ya yi mishi.
Numfashi ya sauke a hankali kafin ya ce “Na san na yi maka abubuwa marasa dadi, da kila kake ganin ba za ka yafe min ba, ko kuma duk abin da na yi maka ba zan burge ka ba, amma ka sani ni da kai yanzu mun zama daya. Sati uku baya ni ne a kofar gidanku, yanzu, kuma tarihi ya maimaita kanshi ga ka a kofar gidana. Kuma ka san yau ne farko ba kuma ka san ranar karshe ba”ya dam tsagaita yana kallon Mk, wanda ya jingina bayan shi da kujera yana sauraro maganganun.
“Ka duba farkon labari, aka daga hotel za a siyar, Sai na siya, ashe saboda kai na saye shi, ta wannan hanyar ce kadai zan iya ganin Asma’u a matsayin matar da zan aura. Ranar da na je hotel din ba ranar zuwana ba ce, ashe kai ne za ka zo a ranar. Sai kuma ga shi ka zo din, tare da Asma’u. Daga ranar ban kara samun nutsuwa ba, Sai da na, ganta a dakina a matsayin mata. Wannan duk wasu kaddarori ne da Allah Ya tsara, kaddararka ta neman Asma’u ta hadu da tawa ƙaddarar, ta hanyar kaddararka kawai zan same ta. Abu na biyu. Don haka ka manta da komai, mu hada hannu wajen rainon little, ni din zan wanke duk wani laifi nawa ta hanyar rike maka little, abin da kawai muke so, shi ne ka san akwai shi a raye, haka ma, ƴan’uwanka, ni ban kai Little wurinka da niyyar tozarci ba. “
” Na gode “karon farko da Mk ya yi magana.
Sai kuma ya fita, hade da dakko ƙaramin akwatin little ya ajiye. Wannan ya sa AG ya sakko hade da jan akwatin zuwa gida.
Cikin motar Mk ya koma, maganganun AG na yi mishi zagaye, wato ƙaddarar wani, na iya yi ma hanya zuwa ga ta ka ƙaddarar. Allah Ya kaddara ta hanyar shi AG zai hadu da Asma’u. Shi kuma baya jin akwai wata hanya ta haduwarsu da AG idan ba a wannan hotel ba. Bai taba ganin mai kama da shi ba. Yanzu ga shi a kofar gidanshi.
Tabbas ko don rikon da ya yi wa little ya kamata ya yafe mishi duk wani abu da yake jin da can ba zai ya fe mishi ba.
Da wannan tunanin ya bar kofar gidan.