Tun da aka yi rasuwar har kwana biyu ba ta ga Ahmad ba, shi ya sa ba ta san halin da yake ciki ba. Kuma babu hanyar da za ta samun sanin hakan, saboda ko wane lokaci gidan cike yake da mutane, wadannan su zo, za wadannan su tafi.
Ita kam ma ta kanta take yi, saboda wannan cikin sosai laulayi take yi, ga shi ba ta son hayaniya, ga kuma jimamin mutuwa.
Saboda Galidima uba ta dauke shi, duk da Sai ta yi zuwa sama biyar gidan basu hadu ba, time da za ta zo yana fada, time da za ta tafi ma yana fada.
Tsab halinshi ne Ahmad ya kwaso na hak’uri da rashin son hayaniya, sannan shi din jigo ne, ya tsayawa al’ummarshi wajen kawo masu ci gaba, da kare dukiyoyinsu ta hanyar toshe duk wata kafa da za a samu baraka.
Tun da ta yi sallah azhur take kwance a kan sallayar, Nabila, Ruma da Aunty Jhu kuma suna hirarsu, da yake gobe ake uku duk sun zo gidan.
Aunty Jhu dai goyo take, Nabila ce ciki tsoho, Sai Ruma ma da take da ƙaramin ciki, saboda waccan yarinyar ita ma ta rasu.
Duk hirar da suke yi Hafsat na ji ba ta sanya baki ba, illa tana jin yadda Hibban ke saman jikinta yana ta sukuwa.
Daidai lokacin aka bude kofa, Aunty Aisha ce ta fara shigowa sai kuma Asma’u a bayanta.
Baki bude Asma’u ke kallon Ruma, kamar yadda Ruman ma ke kallon Asma’u, dukkansu sun kasa janye idanunsu a kan junansu
“Aunty Queen (Duk haka suke kiran Hafsat) ga bakuwa za ta yi miki gaisuwa” Cewar Aunty Aisha lokacin da take zama kan gado ta kuma nunawa Asma’u sofa kasancewar duk suna cikin bedroom ne
Hibban ta fara janyewa a kan jikinta kafin ta tashi zaune tare da saka kwayar idanunta cikin ta Asma’u, take kwakwalwarta ta shiga laluben ina ma ta san Asma’u. Ita kam Asma’u kallo daya ta yi wa Hafsat ta gane ta, a wancan lokacin ma da ta kasa gane ta, Kiba ta yi mata, amma har videon bikinsu tana da shi a cikin wayarta.
Suna tsaka da gaisawa ne Aunty Safiya ta shigo dauke da tire wanda aka zubowa Asma’u abinci. Kamar wasa sai ga shi duk kannen Ahmad da yayyunshi mata sun yo wa part din Hafsat kabbara. Wannan ya tabbatar mata koma wacece Asma’u lallai tana da muhimmanci a wajensu.
Hira suke yi da ita sosai, wacce da yawan hirar korafi ce a kan wai ta share su, babu kira ba komai. Musamman da suka ji a Nasara take aure kuma haihuwarta biyu.
Hafsat ta jima da jin sunan Asma’u a bakin ƴan’uwan Ahmad da kuma Hajiya sai dai ko hotonta ba ta taba gani ba.
“To idan ita ce me ye hadinta kuma da Mk har ta kai mishi yaro? Ko bayan sun rabu da Ahmad ta auri Mk din?”
Wadannan sune tambayoyin da take ta jerowa kanta, Sai dai ba ta samu amsar su ba Aunty Safiya ta ce “Aunty Queen, wannan ita ce Asma’u, wacce ta auri Ahmad, an yi zaman kirki da mutumci sosai”
Yaƙe Hafsat ta yi kafin ta ce “Allah sarki, sannu da zuwa”
Asma’un ma ta mayar mata da “yauwa na gode”
Hirar kam kin karewa ta yi, shi ya sa Hafsat ta sabe zuwa dakin Ahmad, saboda kanta har ya fara ciwo. Sam ba ta son hayaniya.
A nan part din Asma’u ta kwana, kwanan da ya rika tuna mata da rayuwarta ta baya, rayuwar farin ciki da jin dadi. Duk da an canja duk wasu kayan da ke cikin part din, hakan bai hana tuno yadda ta rayu a wurin ba.
Safiyar Litinin aka yi addu’ar uku, hade da dorawa Ahmad rawanin Galidima, Sai dai an ce shagalin nadin ba yanzu ba. Sosai Hafsat ta ji dadin zuwan su Inna Kuluwa da kuma Tukuro
Dama ita Mama kullum ma sai sun yo abinci an kawo.
Mutane basu fara ragewa ba, Sai azhur, a lokacin ne kuma Ahmad ya shigo don gaisawa da Asma’u kamar yadda Hajiya ta umurce shi.
Kai tsaye part din shi ya nufa, sanye yake cikin kayan sarauta ya sa rawani gwanin sha’awa, Sai dai kallo daya za ka yu mishi ka fahimci rama gami da rashin walwalar da yake ciki.
Hafsat na daki aka fada mata shigowar Ahmad, da azama ta nufi bangaren, saboda sosai take son ganinshi.
Lokacin da ta shiga dakin yana zaune kan sofa, shigowarta ne ya sanya shi dago kai yana kallon ta.
Sai kuma ya yafito ta da, hannu alamar ta zo
Calmly ya dora ta a kan cinyarshi yana fadin “My Queen sosai kin rame, ba kya cin abinci ne, ko duk ciwon ne?”
Wuyanshi ta shafa, hade da, kallon idanunshi da suka kankance, wannan ya tabbatar mata baya samun bacci.
“Kai ma ka rame ai sosai, ya karin hak’uri?”
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “Alhamdulillah”
“To sannu Allah kuma ya taya ka riko, ya ba ka ikon sauke nauyin da aka dora maka”
“Amin” Ya kuma amsawa idanunshi a lumshe
“Ba ka bukatar komai?”
Kai ya girgiza alamar a’a kafin ya ce “Asad bai fada miki ba ki daina yawan ayyuka?”
“Ya fada min”
“To ki bari ba na so. Hatta hawan stairs din nan ki bari don Allah Queen”
Kafin ta amsa ne suka ji ana knocking din kofa, ganin Asma’u tsaye tare da Hajiya sai Hafsat ta yi saurin rusunawa hade da gaishe da Hajiyar
Ta amsa tana fadin “Ahmad ya shigo ne”
“Eh.”
“Kira shi”
“” To” Hafsat ta amsa hade da komawa cikin bedroom din, tare suka fito da Ahmad, ita dai kofar fita ta nufa, shi kuma saman kujera ya zauna.
Kan Asma’u a kasa, wata irin matsananciyar kunya gami da nauyinshi take ji, ban da Hajiya ta matsa ita kam da basu gaisa da Ahmad, a haka ta gaishe shi. Shi ma ya amsa a sanyaye, duk wani irin babu dadi yake ji. Tun da wancan abun ya faru sai yau ne ya sake ganin ta.
Hajiya ce ta ce “Abin da ya sa na kawo ta da kaina shi ne, don Allah Ahmad ku yafi juna, mu har gobe muna kaunar Asma’u, ita din mutuniyar kirki ce, abin da ya faru da ita kaddara, wacce za ta iya fadawa a kan kowa, don haka don Allah ka yafe mata.”
Kamar ba zai ce komai ba, Sai kuma ya ce” Babu komai, Allah Ya yafe mu gabadaya “
Cikin digar hawaye Asma’u ta ce” Na gode “karshen maganar tata ya yi daidai da mikewarta ta fice daga dakin.
Duk suka bi ta da kallo, zuciyoyinsu babu dadi. A falo ta ci karo da su Ruma wadanda Hafsat ke kokarin yi musu rakiya, duk suka bi ta da kallo, Ruma Hafsat suka kalli juna, Sai kuma Asma’u ta ce “Wai ko ta yi miki magana?”
Kai Ruma ta girgiza alamar a’a, sannan ta ce “Tun dai da muka gaisa din nan shi kenan”
Komai Hafsat ba ta ce ba, Sai Jhu ce ta ce “Kin santa ne?”
“Kaɗan” Ruma ta amsa ta
Sai kuma suka watsar da hirar suka shiga wata, a haka ta yi musu rakiya.
Bayan ta dawo yadda Ahmad bai yi mata maganar Asma’u ba, haka ita ma ba ta yi mishi ba, suka ci gaba da amsar gaisuwa, idan ya futa tun safe to sai goma na dare yake shigowa, da haka har aka yi bakwai suka koma gida. A satin kuma Asad ya kawo mata Admission din da ya nemar mata a midwifery Dawuri. Ahmad kam ya ce bai yarda ba, Sai dai ta hak’ura ta haihu. Sosai ranta ya baci, abun da ta fahimta kamar baya son ta yi karatun, kawai dai ya ki ya fito fili ne ya fada.
Tun tana fushi har dai ta warware, suka ci gaba da rayuwarsu.
Karfe goma yake fita fada, ya dawo gida karfe takwas na dare, saboda tuni ya ajiye aikin sojan da yake yi. Abin da ya yi wa Hafsat dadi, saboda ta fi kaunar ta gan shi a gida suna tare.
Satin da aka yi arba’in din Galadima aka yi bikin bude Madarasatul-Hindu wat-Tahfizul qur’an Islamiya.
Bikin da ya tara manyan mutane, ya kuma kara daga darajar Hafsat a idanun makiyanta.
Katuwar makaranta ce mai dauke da da azuzuwa sama da ashirin, ga masallaci, akwai solar, borehole, ga Kuma shaguna da aka zuba a kofar makarantar
Kwararrun malamai aka zuba, shi ya sa dan-da-nan makarantar ta yi fice.
Ba karamin farin ciki Hafsat ta yi da wannan ba, ko iya haka aka tsaya ta godewa Allah.
Bayan bikin bude makaranta, Sai kuma aka shiga shirin bikin nadin sarauta, zuwa lokacin dai Hafsat cikinta ya yi girma, saboda ya kai wata bakwai.
Don haka duk wasu shirye-shirye su Aunty Safiya ne ke yin shi. Har da renovating na masarautar aka yi, aka kara gyarawa Hajiya daki, aka fente gida, hade da sawo sabbin dokuna.
Tun ana saura kwana biyu baƙi ke sauka garin, ranar bikin naɗin kam, garin cika ya yi maƙil, kofar fada kamar za ta, tsage don jama’a. Kida da busar algaita sai ta, shi yake yi.
A haka Ahmad ya zauna fada, sarkin nadi ya kuma naɗe shi tsab gwanin sha’awa, yayin da fadawa gami da Dakatai suka rika kawo gaisuwa.
Sai yamma kuma aka rako shi gida a kan doki, yayin da Affan da kuma Hibban suke gefenshi a kan nasu dokin.
Sun sha ado irin na sarauta har da rawani, mutane da yawa yaran ne suka fi burgesu fiye da Ahmad din.
Tun da suka doso gidan Hafsat ta haura sama, wannan ya ba ta damar ganinsu tun daga nesa, gayya guda, kidan sarauta hade busar algaitu yana tashi.
Wani hawayen dadi ya rika sakko mata, yau ita Hafsat diyar Hindatu da Malam Ayuba, mai kwana akurkin kaji, wacce kowa ke kyarar nan, ita ce mijinta da yaranta a kan doki, tare da rakiyar dumbin al’umma.
“Alhamdulillah Ya Rabbb!” ta fada hade da juyawa da zummar sauka, saboda ta san yanzu za su shigo.
A tsakiyar falo kuwa suka hadu, yau kam ba ta ji nauyi ko kunya ba, ta fada jikinshi cike da farin ciki. Shi din ma cike da wani irin shauki ya rungume ta.
Mutanen wurin wadanda da yawansu danginshi ne na jiki da kuma na ta, Sai suka hau sowa.
Gidan bai yanke da mutane ba, sai goma na dare.
Hafsat tsaye cikin shirin bacci, tana warewa su Hibban uniform din zuwa school gobe, yayin da wayarta kan bedside drower ta kunna wakar Farin wata.
Duk lokacin da take cikin Nishadi wakar take kunnawa sai ta ji kamar don ita aka yi ta.
Yanzu ma bin ta take yi cike da jin dadi, idan ta kare sai ta kuma mayar da ita baya.
Yanzu ma bayan ta kuma dawo da ita, hade bin wakar kamar ita ce ta rerata
“_Labari a zuciya kai ne, soyayya ce taka ta yi tasiri ɗangata”_
” _Eh burina ko dare rana, rokon Allah na gamo da alkairi. Cikin raina, lissafi nake nai gamo da mai nuri_”
“_Kai ne dama, wanda na gani rannan, kana tafiya sawaye a kan tsari. Kai ne dai muradin dai, na kamu da sonka, na damu dangata_”
“_Ehhh abun sona ka zamo nawa, shi ranar farin ciki ba a boyewa. Misali kai ka kasance na nunawa, koma me za a yi kai ba ni canjawa. Ka ƴanta ni, na daina ruɗewa, babbar magana kaunarka ta yelwa. Da kai za ni, taho ja ni. Kalamai na so daure ka yi min ni ɗangata_”
Daidai nan ta shiga juyawa, alamun dai tana cikin farin ciki. Ahmad da ke tsaye tun dazu a kofar ya kara so ciki sosai hade da rufe mata idanunta
Cikin dariya ta ce “Mai girma Galadiman Tunga Hakimin Dawuri, Sardaunan Samarin Dawuri”
Shi ma cikin dariyar ya ce “Kin canja daidai”
Suka yi dariya a tare hade da zama gefen gado.
“” Me ya saki farin ciki har kike rawa, abin da ban taɓa gani ba “
Cikin dariyar jin kunya ta ce” kuma fa ina rawa”
Ya dan dara kadan kafin ya ce “Gist me”
“Kawai ina cikin farin ciki ne, mara misiltuwa”
“Na ji dadin hakan, and ina yi miki albishir, idan kika haihu lafiya za mu je umrah da yaran nan, domin mu godewa Allah hade da rokon tallafinshi a wannan gagarumin aikin da aka dora min”
Yadda ta mike tana tsalle ne ya sanya shi saurin riko ta yana fadin “Kin manta an ce wai ki daina irin wadannan abubuwa”
Cikin murna ta fada jikinshi, tana fadin “Na gode Ya Amad Allah Ya kara budi, ban taba kawo ma raina zan ziyarci garin ma’aiki ba”
“ke mace ta gari ce Hafsat, komai na yi miki ban fadi ba, kina son ci gaba da karatu na hana ki, kuma kin hak’ura duk da kina da kwakwalwa, kina son yin planing Nan ma na hana, ki ka hakura, kalli yadda kika sha wahala a kan cikin nan. Kin rike min yan’uwana da daraja, duk da karancin shekarunki, babu wanda ya taba kawo min korafinki. Hajiya kullum cikin yabonki take. Lallai kin cancanci fiye da wannan. Bayan mun dawo Umrah ma zamu koma aikin Hajji. Next year Kuma Sai a biyawa Baba da Mama su tafi. “
Cikin kukan dadi ta ce” Na gode Allah Ya saka maka mafificin alkairi, ya bar mu tare, ya raya mana zuriya. “
” Amin Ya Rabbb “ya fada hade da janyota jikinshi sosai yana shafa cikinta wanda ya yi girma haihuwa ko yau ko gobe. Tuni ya sanyawa yarinya da ke ciki suna Hindu.
To sai mu ce Allah Ya iso da ita lafiya.
Tammat.
Alhamdulillah
Karshe.