Malamawa.
Bangaren Ruma abubuwa sun koma mata daidai, maganar haihuwarta kam ko tashin zance, hatta almajiran Alaramma basu san abin da ya faru ba, bare mutanen gari, iyakar batun kawai a cikin gida.
Ruma dai kasancewar akwai kuruciya ji take kamar komai ya wuce, yanzu ba ta da wani kalubale.
Saboda ba ciki, babu abin da ke cikin cikin, ga shi kuma ta samu lafiya, Sai take jin kamar ba ta taba yin wani abu da ya jefa ta cikin tashin hankali ba.
Ko rashin mahaifiyarta a gidan baya damunta, saboda dama can a ɗakin Yaya suka fi dabdala.
Auwalu dai har zuwa lokacin yana tsare, sausauci daya kawai ya samu shi ne yana dan fitowa waje, har makaranta yana shiga amma har lokacin marin na kafarshi ba a cire ba.
Kuma yanzu ya daina shan dukan nan na safe da yamma, abinci ma ana ba shi sau uku a rana.
Sai dai duk wani aikin wahala na gidajen da shi ake yin shi, zuwa gona, dibar taki, faskare, ko yo itace.
Da cikin gidan ne kawai aka yi mishi shamaki.
Zaune yake a kofar masallacin yana kallon yadda baƙi maza da mata ke sauka wasu bisa mashin wasu kuma a cikin mota.
Ba yau ne Alaramma ya fara rufa sabga ba, amma wannan din kam ta daban ce, saboda akwai diyarshi ta cikinshi cikin ƴanmata hudu da za a daurawa aure gobe, kuma ita ce ƴa ta farko da ya fara aurarwa, shi ya sa hidima ba kama hannun yaro.
Malam Balarabe na da ɗaya, Sai Malam Yunusa da yake da guda biyu Gaje da kuma Ruma.
Wani abu mara dadi yake ji a cikin ranshi, yayin da zuciyarshi kuma ke saka mishi wani abu daban.
Kodayake ba yanzu ta fara mishi wannan sakar ba, amma yana jin lokaci ya yi da zai yi mata biyayya musamman a irin wannan lokacin.
Haka yay ta sakawa yana kwancewa har zuwa sallahr la’asar, daga nan ya lallaba zuwa gidan da aka ajiye shi.
A lokacin ne kuma karatun Kur’ani ya fara tashi a masallacin cikin muryoyi daban-daban. Kamar dai yadda aka saba a duk lokacin da ake wani taro.
Safiyar Asabar da ta kama ranar daurin aure tun safe baki ke kara tuɗaɗowa kofar gidan Alaramma.
Zuwa karfe daya wuri kam ya dinke, sai kiɗan tauri ke tashi da bushe-bushe, maza na ta nuna bajintarsu ta hanyar yanka jikinsu da wuka. , bayan sallahr Azahar aka fara daura auran diyar Malam Balarabe kasancewar shi ne babba, sannan aka daura na Gaje a maimakon na Rumasa’u da take babba, daga karshe aka daura na Maryam, wacce dama idan girman iyaye da kuma na shekaru za a bi ita ce karama.
Abin da ya ɗaure kan mahalarta ɗaurin auran shi ne yadda aka tsallake Ruma ba’a daura nata auran ba.
*****
Kasancewar idon Buhari a rufe yake bai san ina aka nufa da shi ba, abin da ya sani kawai shi ne ba karamar tafiya aka yi da shi ba.
Sun yi tafiyar da aƙalla ta kai awa goma.
Sannan ya ji motar ta tsaya, duk da baya gani ya san cikin ɗaki aka shiga da shi, ba jimawa kuma suka bude mishi idanunshi.
Ya jima kafin ganinshi ya koma daidai, sannan ne ya karewa madaidaicin dakin kallo, mai dauke da katuwar katifa da tv sai wata kofa da ya tabbatarwa kansa toilet ne.
Dakin a wadace yake da hasken lantarki kamar ba dare ba.
Yana tsaye Disko ya sanya mishi sarka ya daure hannunshi gami da kafarshi, daurin da ba zai hana shi yin guntuwar tafiya cikin dakin ba, misalin shiga toilet.
Bayan fitar Disko ba da jimawa ba, aka kawo mishi abinci mai kyau, shinkafa da miya ce har da nama, ruwan gora da coke.
Bai jira cewarsu ba, ya dauki abincin ya cinye, ya kora da ruwa da kuma coke din, sannan ya haye katifar ya yi kwanciyarshi, saboda yanzu dai duk wani abu da zai yi na nuna tashin hankali to a banza ne
Saboda ga shi dai a hannun mutanen da bai san ko su waye ba, bai san kuma dalilin da ya sa suka kawo shi nan ba, idan ma dai kashe shi zasu yi, gara ya rika ci yana koshi, kafin lokacin mutuwar ta shi ya zo.
Tuna mutuwar ne ya sanya shi tashi tsaye zuwa toilet, cikin dabara ya yi alwala, inda yake wankewa ya wanke, inda kuma hannunshi ba ya kaiwa ya bar shi.
Da hasashen shi ya yi amfani wajen gane alkibla, ya shiga sauke sallolin da bai yi ba.
Da agogon da ke jikin tv ya gane lokacin sallar asuba ya yi, kamar jiya dai yau ma haka ya yi sallah.
Misalin takwas aka kawo mishi abun kari, tea da bread ne sai soyayyen kwai.
Yadda wanda ya kawo abinci bai yi mishi magana ba, haka shi ma bai ce mishi ba, bakinshi kawai ya kara wankowa ya yi break din shi.
Misalin karfe goma na safe yana kwance ya ji shigar key a jikin kofar dakin da yake, wannan ya tabbatar mishi da shigowa za a yi, addu’arshi Allah Ya sa wani abincin ne aka kuma kawo mishi.
Da sauri ya mike zaune saboda ganin bakuwar fuska, don a wannan karon wani babban Alhaji ne ya shigo dakin.
Sanye cikin milk color din shadda da ta sha dinki mai kyau da tsada.
Kamshinshi ya cika dakin kamar a lokacin yake fesa turaren.
“Buhari!” AG ya kira shi a lokacin da yake gyara zaman babbar rigarshi
Duk da bai amsa kiran ba, amma yadda ya zuba mishi ido ya san cewa yana tare da shi.
“Na san ba ka san dalilin zuwan ka nan ba, to kana wurin nan ne saboda abu daya ko biyu, da zarar ka ba ni hadin kai, zan sallame ka da kyauta mai yawa, sannan ba zan cutar da kai ba.”
Sosai Buhari ke nazartar yanayin AG, da gaske bai ga alamun zai cutar da shi din ba.
” To amma me ye hadin shi da abin da AG din ke nema, saboda shi dai hanya ko rafi ba ta taba hada shi da mai kama da AG ba, bare AG din kanshi? “wannan ita ce tambayar da yake yi wa kansa, tun bayan da AG ya kai karshen maganarshi.
” Me kake so? “Cewar Buhari a hankali yana kallon AG
“Good question” AG ya fada hade da takowa zuwa inda yake zaune lokaci daya kuma yana tattaba wayar shi
“Wannan abokin naka, nake son ka fada min inda zan same shi, da zarar ka yi min wannan to zan sake ka, tare da alkairi mai yawa.”
Buhari ya zubawa hoton ido, zuciyarshi na yi mishi sake-sake na dalilin da ya sa AG yake neman abokin shi.
Idan kuma ya same shin me zai yi mishi?
To idan kuma shi bai bayar da address din Kb ba, me zai same shi?
” Kar ka ce min ba ka sani ba, ko ka boye min wani abu, saboda za ka ci gaba da zama a nan ne har sai na same shi. Idan kuma ka ki ba ni hadin kai…” cikin aljihunshi ya sa hannu hade da fito da wata karamar bindiga.
“Zan shafe ka a bayan kasa, in tona rami a gidan nan a binne ka, ko sallah ma ba za ka samu masu yi ma ba.” Ya karasa maganar hade da tura bindigar aljihu
Yanzu kam Buhari ya fara tsoron lamarin, babu abin da ya fi sai ya yi kokari ya fita a wajen nan lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba.
” Ba na son ɓata lokaci, wanda na ɓata a baya ya isa. “AG ya katse mishi tunani.
” Ban taɓa zuwa garinsu ba” Buhari ya amsa da dusassar murya mai cike da tashin hankali.
“Amma ai ka san sunan garin?”
Ya daga kai alamar eh, hade da lasar busasshen laɓɓansa
“Faɗa min” Cewar AG idanunshi zube a kan Buhari.
“Ɓurma yake.”
“Woww! Ashe ma makocina ne. Wane karin haske za ka yi min?”
“Ina jin babanshi ya taba rike shugabar karamar hukumarsu, kuma har yanzu mahaifinshi babban dan siyasa ne. Ina jin samun Kamal din ba zai yi wuya ba”
“Sunan shi Kamal dama ba Kabir ba?”
“Eh. Sunanshi Muhammad Kamal Bashir” Buhari ya amsa a hankali.
“Da wane suna yake amfani a media?” AG ya kuma tambaya a hankali.
“MK Bashir” Buhari ya kuma amsawa.
“Da kyau.” Cewar AG lokacin da yake tunkarar kofar fita.
“Uhmmm… Yallaɓoi!”
AG ya juyo hannunshi rike da handle din kofar yana kallon Buhari.
Murya a daburce ya ce “Don Allah ba cutar da shi za ka yi ba?”
“Is just something like what’s happening to you right now” Daga haka ya fice.
“Waye shi?” Buhari ya tambayi kanshi a hankali.
“A ina ya san sunana?” ya kuma tambayar kanshi
“Me yake nema a wurinmu da sai ya kawo ni nan, in don wannan ne ko a can ai na amsa musu, ba sai mun zo nan ba” Ya fada cike da jin haushin kawo shi wurin da aka yi a karo na farko
“Na san Hajiyata hankalinta yana a tashe saboda za ta ji wayata a kashe” Ya kai karshen maganar hade da jin wani ɗaci, yanzu kam akwai bukatar ya fita, ko don kwanciyar hankalin mahaifiyar shi.
*****
Hafsat.
Ta kalli Najib, wanda shi ma ita yake kallo, a hankali ta ce
“Mahaifiyata ita ce ta biyu a wurin mahaifina, Malam Ayuba, ita mace ce me jajircewa wajen neman na kanta, ba zan iya ƙirga yawan sana’ar da ta yi ba, ta yi wannan ta saki ta yi waccan , shi ya sa ta fi karfin bukatunta, ba ta jiran mahaifina sai ma taimaka mishi da take yi, hakan ba karamin ƙona ran abokiyar zamanta yake ba Inna Kuluwa.
Ka san Hausawa sun ce tsinuwa ba ta yi wa kare komai sai dai ta sanya shi kaurin bindi.
Duk hassada da asirin da Inna Kuluwa ke yi na ganin komai na Innata ya lalace a banza, saboda kullum Innata gaba take yi ba baya ba, har zuwa lokacin da mahaifina ya auro Inna Luba, suka hada kai da Inna Kuluwa kullum suna yawon neman magani wai komai na Innata ya lalace, amma kamar suna karawa samunta taki.
Saboda a lokacin ta mallaki gonaki, dabbobi da filaye.
Tana ɗaya daga cikin mata masu kudi a garin nan.
Ban san ta ina maganar Innata tana da maita ta fara ba, ban san kuma daga bakin wa aka fara jin ta ba.
A hankali dai maganar ta rika ratsa gida-gida da kauyukan gefenmu.
Wai duk dukiyar Innata ta jinin mutane ce, ita ce take kashe duk yaran da su Inna Kuluwa suke haifa ba rai, ko bayan sun yi girma su mutu. Wai kuma ita ce ta lashewa kanta kurwar haihuwa shi ya sa daga kaina ba ta kara haihuwa ba.
Abu kamar wasa sai mutane suka fara gudun Innata, ba ta isa ta shiga taron biki ko suna ba, Sai kawai ka ga mata na darewa.
Duk yaron da ya kama ciwo a kauyen nan sai ace Innata ce ta kama shi, haka duk wanda ya yi mutuwa irin ta fuju’a za ka ji an ce Innata cdw, idan ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinyewa nan ma Innata ce .
Dole Innata ta daina fita, daga gida sai gida, gidanma ba tsira ta yi ba, saboda kullum su Inna Luba cikin gwaɓa mata magana da habaici suke.
Yaro ko babban tari ya yi, yanzu ka ji suna cewa “Kurwarka kur, wlh ta fi karfin maye, mun sha aradu mun sha yasin mun fi karfin baƙin maye.”
Babu mai hada saba da Innata, kai ko abun siyarwarta ba kowa ne ke saye ba. Kai ko kyauta ta yi ba a karba.
Abun bai tsaya kanta ba har da ni, saboda lokacin ina primary 4 sai ya kasance ba ni da ƙawaye, ba mai zama kusa da ni, ga hantara, tsana da kuma tsangwama.
Duk wani wasa na yara ban isa in shiga cikinshi ba, ba iya wasa ba, kai ko kallon yaro na yi, sai ka ga sun rufe ni da duka wai na yi gadon maita zan cinye mishi kurwa.
Idan aka tashi kuwa kafin in iso gida ba karamar wahala nake sha ba saboda jifa da dukan da yara ke min, wai ni ƴar mayya ce na yi gadon maita. Tun ban fahimci abin da ake nufi da kalmar ba har na fahimta, tun abun ba ya damuna har ya rika damuna, na sha tambayar Innata in ce Inna da gaske ke mayya ce, Sai ta ce min a’a Hafsa, ban san ma me ye maita ba.
Wani lokaci kuma sai in ce Inna, idan dai da gaske ke mayya ce, ki cinye min (In lissafo mata sunayen masu takura min) in ce ta cinye min su in huta. Ko na rika zuwa makaranta cikin salama.
Saboda duk takurar da nake fuskanta bai sa na daina zuwa makaranta ba.
Musamman da na samu wani malami yana rike min hannu idan an tashi, Sai ya kawo ni gida sannan ya wuce.
Haka mu kai ta rayuwa da Innata cikin kyara da hantara kullum, har zuwa matakin da ba wanda yake siyar mana da kayanshi kuma babu mai sayen namu, Sai ƴan kauyukan gefenmu su ma a tsorace . Last 2wks kuma suka ce mahaifiyata wai ta kama kurwar wata mata, shi ne suka zo har gida suka dauke ta zuwa fada suka yi mata tsi…. ” Sai kuma ta kasa karasawa, ta fashe da kuka, da ke nuna tana jin zafin abun sosai.
Najib ya yi shiru, cike da tausayinta, wannan abun sosai yana faruwa a kauye, da zarar an ga mutum yana da ɗan canji sai ace yana da maita.
Ko yanzu ma da ya yi bincike a kan Innar dalilin da mutanen da ya bincika suke ba shi guda uku ne, wai idan ta yi noma amfanin gonarta ya fi na kowa kyau, sannan komin kankantar gona sai a rika fitar da hatsi mai yawa.
Dalili na biyu kuma wai ba ta haihuwa, saboda ta lashe kurwarta, kuma wai ta ta hana kishiyoyinta haihuwa
Da ya tambayi ko ya batun matar nan da dalilinta aka yi wa Inna tsirara sai aka ce an kai ta asibiti ta samu sauki, amma sai da aka hada mata da maganin mayu.
Ya girgiza kai cike da takaicin kazamin tunani irin na mutane
“A kan abin da ya faru, shi mahaifinki bai dauki mataki ba?”
Hafsat ta sauke hannunta da take share hawayenta tana kallon Najib, kafin ta ce
“Wai Babana, shi kam ko kashe Inna za a yi zai yi magana ne, abun da an ce wai ita ce take kashe mishi ƴaƴa, kuma take hana amfanin gonarshi ya yi kyau sai nata. Wai ciwon kafar da yake ma ita ce ta dora mishi saboda ta kasa cinye shi.”
“To Ina ƴan’uwan Inna din, su ba zasu dauki wani matakin komai ba?” Najib ya kuma tambaya rai a bace
“Waye zai dauka to, duk tsoro ma suke ace ƴar’uwarsu ce, saboda kada ace su ma suna da maita”
“Kai Subhnallah!” Cewar Najib cike da taikaici
“To yanzu shi kenan haka za ku ci gaba da rayuwa?”
Cike da sarewa Hafsat ta ce “Ban sani ba.”
“To ya maganar makarantarki kuma, shi kenan kin daina zuwa?”
Ta zuba mishi jiƙakkun idanunta da suka yi jawur, cikin muryar tausayi ta ce “Ni ba zan fita ba a yi ta kallo na.”
Ya sassauta murya alamun lallashi “Haba Hafsat, Sai da kika gama hawan tudu za ki gangara sannan ki ce za ki juya baya, ko ba kya son karatun ne?”
An taba mata inda ke mata kaikayi shi ya sa ta fashe da kuka sosai, cikin kukan ta ce “Ina so.”
“To tun da kina so, ya kamata ki koma kin ji ko, kin ga kina da kokari sosai”
“Sai Inna ta samu lafiya to” ta yi maganar hade da share hawayenta.
“Zan iya shiga in duba Innar?”
Ta jinjina kai alamar eh
“To je ki sanar da ita”
Ta juya zuwa kofar gidan hannunta a kan fuskarta, tana dauke ragowar hawayenta.
Su Inna Kuluwa ne zaune a tsakar gidan suna kulla manja da farin mai a leda na siyarwa, rashin amsa sallamarta da suka yi, ba ta hana mata fada musu Bako zai shigo ya gaishe da Inna ba. Babu wanda ya kalle ta, bare ya nuna ya san abin da ta fada, dalilin da ya sanyata wucewa dakin Inna ta shaida mata zuwa Najib.
Sai da ta sanyawa Inna hijab sannan ta fita suka shigo tare da Najib.
Cike da girmamawa ya gaishe da Inna ya kuma yi mata ya jiki, ita ma a sake ta amsa mishi hade da yi mishi godiya, daga nan kuma dakin ya yi shiru tsawon mintuna kafin Najib ya katse shirun da fadin “Inna kodai za a kai ku asibiti ne?”
Inna ta dago kai suka hada ido da Hafsat sannan ta ce “To zan duba in gani, Idan ya kama sai mu tafi ai, kuma Ina jin sauki ma”
“Allah Ya karo sauki.” Cewar Najib cikin ladabi.
“Amin.” Inna ta amsa daga nan ya yi sallama da Innan ya fito waje, yayin da Hafsat ta biyo bayan shi.
A kofar gidan ya tsaya yana fuskantar Hafsat, hannayensa du biyun rungume a kan kirjinshi ya ce “Me zai hana a kai Inna asibiti, ya kamata ta ga babban likita”
“Ai ni ban san asibitin ba” cewar Hafsat a hankali
“Nemo shi za a yi ai, don haka ki shirya zuwa Monday mu kai ta babban asibiti na Dawuri.”
“Allah Ya kai mu, ka ga daga nan ma sai in ga Mama”
“Wacece Mama?” Najib ya tambaye ta
“Yayar Inna ta ce, a can take aure, tana sona sosai…”
“Ke ma kuma kina son ta.” Najib ya katse ta
Karon farko da ta yi murmushi
“You see! Kina sonta sosai”
Dariya mai sauti ta kubuce mata, ta sanya tafukanta a kan fuskarta yayin da sautin dariyarta ke fita kadan-kadan.
“Zan tafi, Allah Ya ba Inna lafiya.”
“Amin Ya Rabbb, na gode, Allah Ya saka da alkairi.”
“Amin” cewar Najib hade da juyawa ya nufi hanyar komawa makaranta.
Zuciyarshi cike da tausayin Hafsat da kuma tunanin hanyar da zai bi wajen ganin ya taimake ta.
Abu na farko da ya fara zuwa kanshi shi ne, bayan Inna ta samu sauki, to zai yi kokarin samarwa Hafsat boarding school, ta tafi can ta yi karatunta cikin ƴanci, ba tare da kyara ko hantara ba.