A.J. Duk yanda yakai da son kud'i yaukan yaji ya tsorata da wannan kud'in, shi babban tashin hankalin sama shine... kar Daddy ya kama Sahra ita kuma tace shine yake turata. Haka ya shiga gida jiki babu 'kwari.
Ko sallama baiyiba ya shiga gidan nasu yana tinanin mafita, Nana ce kad'ai a tsakiyar gidan tana cin abinci, hakanne yasa ta tsaya tana kallon yanayin yayan nata. "Yaya Lafiya kuwa kake?. Shikuwa A.J baima san tanayiba. Ganin bai bata amsa ta ce "Yaya kiran sallar isha fa a keyi kuma naga kashigo gida? Cikin hanzari ya. . .