Skip to content
Part 6 of 6 in the Series Addininmu by Salis M. Reza

A.J. Duk yanda yakai da son kud’i yaukan yaji ya tsorata da wannan kud’in, shi babban tashin hankalin sama shine… kar Daddy ya kama Sahra ita kuma tace shine yake turata. Haka ya shiga gida jiki babu ‘kwari.

Ko sallama baiyiba ya shiga gidan nasu yana tinanin mafita, Nana ce kad’ai a tsakiyar gidan tana cin abinci, hakanne yasa ta tsaya tana kallon yanayin yayan nata. “Yaya Lafiya kuwa kake?. Shikuwa A.J baima san tanayiba. Ganin bai bata amsa ta ce  “Yaya kiran sallar isha fa a keyi kuma naga kashigo gida? Cikin hanzari ya dawo daga tinanin na sa ya ce “Sorry na mantane yanzu zanje nayi. Tana kallosa ya bargidan da alama dai wani abun na damun sa.

Salis POV

Kallon ‘kanwar tasa ya keyi cikin soda ƙauna, tinda suke tare da ita basa ɓoyewa junann su komai domin kuwa ko saurayine yazo gurinta tofa saita sanar da shi haka shima, dukdade shi baitaɓa cewa yana sonwata yarinyar ba. Akaro na farko kenann yakejin bazai iya sanar da ita abun da ke ransaba, saninn halinta na kushe zaɓin wani.

Cikin zuciyar sa ya shiga tinann abun da yafaru yanzu minti kaɗan da suka huce. Tsaye yake a ‘kofar gidan su AJ yana jiran yaga yaro ya aikeshi ya kira masa AJ, kasan cewar yakira wayar AJ ɗin bata shiga. Yana tsaye ya ga yaro yazo shiga gidan, nann take ya sanar da yaron cewar in ya shiga yace ana neman AJ.  Bayan kamar minti 2 yaron yazo ya ce wai bayanann amma ga ƙanwarsa wai zataga kowaye in yazo sai a faɗa masa. Salis ya ce “ok. Sannan ya kira yaron ya masa ihisani. Cikin gidan kuwa Innah ce ta ceda Nana taje ta dubo kowaye, domin kuwa sunsan A.J da abokai kuma duk yaran masu kuɗi.

Hakanne yasa ta saka hijab ta nufo ƙofar gidan. Leƙowa tayi ta hango baƙar mota a fake a ƙofar gidan, ga kuma mutum a jingine a jikin motar, hakanne yasa ta nufi gurin sa. Tana zuwa tayi sallama haɗi da gaishisa. Salis da yake danna waya, ko kallonta baiyiba ya ce “Idan A.J yazo kice masa Salis ne yazo kuma kuce yasameni a gid… Maganar tasa ce ta maƙale a bakin sa sanadiyar tozali da fuskar Nana.

Cikin rikicea ya ce “am am am kikace baya gida ko? Nana ta ce ” Eh baya gida amma yanzu zai dawo.

Ai take Salis yayi mutuwar tsaye jin wata sassaiyar muryarda tamasa magana da ita. Ya ce “To kice Salis ne yazo neman sa, Kuma kice yazo gida yanzu.

Nana ta ce “to zan fad’a masa, tana faɗa ta juya ta nufi gida cikin takunta na yan mata masu natsuwa. Salis kuwa neman fad’uwa ya keyi ganin yanda take tafiya kamar zata karye, haka ya bar ƙofargidan cikin begen Nana.

Sauke ajiyar zuciya yayi bayan ya dawo daga tinanin.

Laɗifa ta ce “bro lfy kuwa  tin ɗazu kazo Kanata tinani kuma kayi shiru?

Salis ya ce “sis ina maganar da hajiya Babba tamana ɗazu?

Laɗifa ta ce “Maganar aure ko maganar yaronnan abokin ka ɗan talakawannan?

Salis kuwa cikin ranshi ya ce “Allah ya sa ban faɗa mataba da wallhi bazata goyi bayana ba. Afili kuwa ya ce ” maganar aure… Na yarda zanyi domin kuwa nasamu wacce na keso. Cikin mamaki Laɗifa ta ce “Yanzu-yanzu daga kaje gidansu A.J ka dawo kace min kasamu matar aure? Salis ya ce “Yes haka Allah yake abun sa. Laɗifa ta ce “Tofa!! Lallai koma wacece ta iya kamu, tabaɗa had’i da yin dariya sannan ta ce “ya sunann ta? Salis ya ce ” ban saniba, bata faɗa min ba.

Laɗifa ta ce “To yanzu dai muje mu sanarwa da hajiya Babba, kaga itama saita dena maganar aurannan nata ko ya kace? Salis ya ce hakane tashi muje?. Haka suka jera suna tafiya Laɗifa na tsokanar sa, wai wata yarinyar tayi WUFF da shi a cikin lokaci kaɗan.

Abdalh POV

Cikin tsananin ɓacin rai ya bargidan ya nufi gidan sa wanda ke unguwar hotoro ɗan marke, yau ransa in yayi dubu to duk sunɓaci, baisan yazaiyi da Maryam ba, a’ce wai ƙanwarsa da suke uwa ɗaya uba ɗaya itace keyin rawa, rawa da waƙar ƴan bidi’a!!?. Yanufi gidansa da niyar bazai dawo ba sai gobe domin a’san yanda za’a yi da Maryam, kawai aure za’a Mata. Wata zuciyar ta faɗa masa, ai kuwa ya aminta da hakan.

Maryam kuwa bayan Abdalh ya fi ta, ta yunƙura da niyar tashi amma Ina, take ta sake rusa ihuuu, hakanne yasa nura da tin shigowar yayan nasu yagudu,. ganinn yanda fuskarsa ta ɓaci. Dukda nura bashida ƙarfi haka ya taimaka mata ta miƙe tsaye ,ya kwantar da ita a kangado. Abin dariya amma ba damaryi, haka ya gintse dariyarsa ganinn yanda takeyi kamar wacce a ka ɗaye fatar jikin ta, ga ihuu da takeyi. Ganinn kamar nura nason yin dariyane yasa cikin kuka ta ce “Wallhi nura in kasake naji dariyarka saina kusan karkaryaka.

Shikuwa nura jin yanda tayi maganar cikin kuka da rakici ne yasa dariyarsa kufcewa, aikuwa ya saki dariyar, haɗi da sakin ta ta faɗa kangadon da ƙarfi. Aiku mai neman kukane aka jefeshi da kashin a waki, nann take kuka ya dawo sabo, tadin buɗe baki tanayi, shikuwa nura yabar ɗakin yana dariya.

Zainab VOP

Dariya takeyi wacce rabon da tayi irin ta harta manta. Kallon Isa tayi ta cigaba da bashi labari. “To bayan ya tafine mukayi wa’azi sauran abokan nasa harda wani kafeni da ido, Nikuwa ko ta kansu bambiba.

ISA ya kwashe da dariya sannan ya ce “Amma fa kin burgeni Wallhi, wani abuma saigobe in munje kusa da gidansa gabatar da walimar da zamuyi, nifa Allah har na matso naji wannan sabuwar wa’kar da kikace zakiyi mai taken bud’ad’d’iyar wasi’ka.

Zainab ta ce “Yanzuma zan je na ƙarasa aikinta, ai i’na sane da Al’kawarin da na ɗaukarwa mlm. Isa ya ce “Ɗazu Aliyu yazo wai ya kira number ki baki ɗaga ba? Zainab ta ce ” Oo!! Allah sarki ban sanar dashi batun zuwana walimar bane, Kuma kasan idan i’na kan aiki bana ɗaka waya, Allah dai yasa baije gurin mlm ba?

ISA ya ce “Nima agurin mlm ɗin na ganshi, kuma nasan maganar ce ta kawoshi, kuma zakigani mlm zai miki mgn. ISA ya cigaba da cewa “To Zainab in kina sonsa kawai kiyarda ayi auran mana tindade shi yace ko yaushe kika shirya?. Zainab ta miƙe ta bargurin haɗi da cewa Yaya zamuyi mgn anjima yanzu inada aiki.

Ladifa da Salis POV

Salis ya ce “No Sistar karmu sanarwa da hajiya tukunna, saboda ban samu mun yi magana da yarinyar ba, kibari nann da kwana biyu lokacin mun shirya da ita. Lad’ifa ta kwashe da dariya sosai kamar zata faɗi sannan ta ce “Kai bro karfa kodai kaima irin mazannanne masu tsoran mata?

Salis ya ce “Dama a kwai mazan da suke tsoran Mata?

“Hh mana ga ɗaya ma a gabana.

“Haba yarinya aini jarumin mazane, ke bama niba duk mai irin sunan Salis to yanmata ma shakkarsa sukeyi.

Laɗifa ta ce “Tom zade mugani

Haka suka bari sai ya shawo kan yarinyar( Wanda ya kasance ranar ne A.J yaje gurin Hajiya)

A.J POV

Bayan ya dawo daga sallar isha ne ya shigo gida, cikin kwarin gyiwa domin kuwa zuciyar sa ta bashi tabbacin kawai yaci kuɗin domin Sarah bazata tona masa asiri ba. Kallon Nana yayi ya ce “NANA goba zan baki wayata iyah kuma zansiyo mata ƙarama, amma fa bance ki dinga tara number samari a waya ba, kuma kullum sai na Kar’bi wayar naduba, kin yarda?

Da sauri ta barcin abincin da sukeyi tare da yayan nata ta ce “Yaya wallhi na yarda, ni daga number ka sai number Innah sai kuma number kadija ƙawata shikenan. AJ ya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa na ƙara, yana dubawa yaga number Hajiya wacce ta bashi akan  zata kirashi, da sauri ya ɗaga yana cewa hello Hajiya?. “AJ hajiya Babba ta Kira sunann sa ta cikin wayar.

“Na’am” 

Hajiya ta ce “Kazo gida misalin qarfe goma na safe, kuma banason Africa time?.

“Angama Hajiya in Sha Allah zanzo. Amma hajiya kituro Salis sai mutafi tare da shi?

Da sauri Hajiya ta ce “No banason yasan da zuwanka, Kuma karka sanarmasa da cewa kazo kuma duk aikin da na baka karka nuna masa komai kaide yardarka kawai nake buƙata.

Cikin sauri AJ ya ce “An gama ranki shidad’e, yanda kikeso haka za’a yi. Nann ya kashe wayar dai-dai lokacin inah ta fito daga bayan gida. Ta ce “Yanzu Abdul jabaru inayin magana kafini baki, kacemin kai baka sata, yanzu a ina kasamu kud’ad’an nann da kake cewa zaka siyamana waya?

AJ ya ce “Yanzu Innha fisabillhi sokike mu ƙare a wannan talaucin? Abun arzuƙi ya samemu amma kicewai… to Innah in baki son wayar ai sai kibarta, yanzu ki dubeki daga jiya zuwa yau dan Allah baki ji kinfi samun kuzariba?kinci kaza kin sha yourgot ga kaya mekyu, amma bazaki samin albarkaba.

NANA ma ta amsa da cewa, mudai innah muna son wayar please yaya kabani taka kaji? Haka innah tayi shiru badan batada da abun cewaba sai dan anfita baki.

Washe gari, kamar yanda A.J ya ce, ya siyowa Nana layi, yabata wayarsa, itama Innah yasiyo Mata ƙarama da layinta, yayinda shima yaje shagon siyarda waya ya siyo wayarsa mai kyu. Ƙarfe goma na safe dai-dai aka tafka saɓani tsakanin Salis da A.J. yayinda Salis yake kan hanyarsa ta zuwa neman soyayyar Nana. Shikuma AJ yaje domin jin wani aiki Hajiya zata bashi.

A.J. POV

Kallon Hajiya babba yakeyi cikin tsanani mamaki haɗi da kallon jakar kuɗin gaban sa kafin ya ce “Hajiya ban fahimci abun da kikenufiba?. Cikin shauƙin abunda ta keji a tare da yaron ta ce “Yes kamar yadda kaji na sanar dakai, aure nakeso muyi da kai amma cikin sirri, karkowa yaji, in har ka amin ta to kasanar dani duk abun da kakeso tin daga kan miliyoyin ɗari da kuma gida da kuma mota, zan mallaka maka.

Sanye take da dokuwar riga sai gyale fari. Kallon sa takeyi ganinn shima ya zuba mata ido. Cikin jin kunya ta ce “ina u’ni? Salis kuwa ganinn irin shigar da tayine yabashi damar kafeta da ido, yana jin sonta har zuciyarsa. Bai ankaraba yaji tana cewa “Yaya ɗin AJ bayanann kunyi saɓani yanzu ya fita, amma in yadawo zance masa wannan da yazo jiya yazo neman sa. Tana kaiwa nann ta juya zata koma ciki.

Cikin sauri salis ya ce “Ji’mana, bagurin sa nazoba gurin ki nazo. Ta ɓangare ɗaya kuma yana tinanin meyasa bata riƙe sunann saba. Cikin mamaki Nana ta nuna kanta da cewa ni?.

Duk da uban fankoki da asi da suke aiki a palorn hakan bai hana AJ jiƙewa da zufaba. Cikin rikicewar ya ce “Hajiya aure fa kikace? Kuma dani!?… gaskiya bazan iya ba, yazanyi da salis wanda agirme. Ya girmeni kuma abokina wanda yake temakamin a komai, amma na auri uwarsa? Ina Hajiya dan Allah kibar wannan zancen Please. Ya ƙarasa yana kallon jakar kuɗin da yasan in har ya mallakesu to tabbas shida talauci har abada.

Salis ya ce “Yes gurinki nazo. Nana ta juya tana neman wacce salis ɗin ke magana da ita, domin kuwa tanada tabbacin bada ita yakeba, domin kuwa babu haɗin kwanda da gula. Kayanda kejin sama tasan ba na ƙananan yara bane, bare motar da yake jingine a jikin ta. Cikin mamaki ganinn yanda take ta dube-dube ne salis ya ce “Keɗayace a gurinan, kuma dake nake…kamata yayi a ce kiyi maraba da zuwana domin da alkairi nazo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Addininmu 5

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×