Skip to content
Part 5 of 6 in the Series Addininmu by Salis M. Reza

Cikin tsananin b’acin rai Sameul ya nunata da hannu cikin yaran su na tibi ya ce “Oya tell me waye ya shiga room d’in Daddy? Jin tayi shiru ne yasa ya sake zare mata ido ya ce “Tell me waye ya bud’e d’akin Daddy? Cikin rashin kunyar da tasaba Sarah ta ce “Waye zai shiga in bakaiba… ‘barawo kawai kuma in kasake ta’bani Allah sai na had’aka da Daddy tif. Ganinn yayo kantane yasa ta fita dagudu izuwa d’akin Mommy ai kuwa shina sameul d’in yabi bayanta.

Tana zuwa ta fad’a jikin Mommy tana kukan karya had’i da cewa… “Mommy Kinga Samuel wai meyasa na tona masa asiri a kan ya d’auka ma Daddy kud’i, kuma nace masa banice na fad’a ba shine yabini hard’aki yana dukana. Mommy ta kalleshi ta ce “Sameul get out of my room? Ya bud’e baki zaiyi magana ta sake cewa I said get out of my room? Had’i da nuna masa hanyar fita, tana cewa… Kasan dai tinda aka kamaka to dole sai ka fito da kud’in… Yaro baya jin magana kaine daga wancan clop sai wancan ba dole ka koma sataba, kana biyewa yaran banza a unguwa. Haka mommy tacigaba da masa fad’a har ya bardakin yana tafiya yana aiyana abun da yafaru kamar an shirya Masa.

Mommy ta kali Sarah tace “Kema nace kidaina shiga harkarsa bakiji ko? Duk ranar da bama gida ya kamaki ya kark-aryaki babu ruwanmu don kinsan ba han kali yakeda shib… Ai kafin Mommy ta rufe baki saiga Daddy re’ke da hannun Saumel ya na ihun kiran sunann mommy cewa…

Eliza!!… Eliza!!… Eliza!!…cikin tsananin mamaki Mommy da Sahra suke kallun sa. Mommy ta bud’e baki daniyar tambayar ba’asi ya katseta da cewa… “Eliza luck at this sameul Ashe bai fita harkar wannan yaron masu yin sallhanananba!? Na fad’a masa babu shi babu duk wani yaron Hausa domin basa da hakali, yanzu haka ma shine yakesa yake sato mana kud’i?

Cikin kuka da ba’kin ciki Samuel ya ce “waini Daddy yaushe na d’auka maka kud’i, nazo zan shiga d’akin ka naganshi abud’e shinafa nashiga kuma i swear to God ina shiga kaima kana fitowa. Daddy ya ce “Sameul karna sake ganinn ka da yaran Hausa masu sallah bana so? Sameul ya ce “Allah Daddy his my class mate kuma… ” I said is okay bana son ganin ka dasu. Ok sameul ya Yana hararr SARAH wacce tayi mutuwar tsaye tana jin abun da Daddy kecewa.

Mommy ta ce “I don’t like all Muslims… Samuel kafita hanyarsu, mutanan babu abun da kuka had’a dasu, mutanen da suke zagin Addininmu, babu ruwanku dasu, in ba so kuke raina ya ‘baciba karnaji karna gani. Tana kaiwa nann ta bar d’akin cikin ‘bacin rai. Shikuwa Daddy saida ya tabbatar musu da cewar zai cigaba da tarkon mai d’auka masa kud’i kuma zai Kama, sannan ya cigaba da fad’a musu cewar Hausa masuyin sallha ba abokan zama bane.

Ita kuwa sarha duk abun da suke fad’a yana shigane ya fita, domin kuwa ita bataji bata gani a kan A J. Tashi tayi dai-dai lokacin kiran sallha yayi ita kuma ta nufi wadata market gurin AJ. Sameul kuwa yana fita ya tarrar da abokin sa Umar wanda Daddy ya ce karya sake ganinn sa tare da d’ansa. 

Yana fitowa suka kama hanyar su tazuwa gurin da suka Saba. Yayin da Sameul yake mamaki ya a kayi haka, shida bai d’auki kud’i ba yau amma an kamashi, nann ya shiga tinanin kodai Sahra ma tana d’aukar kud’in me!!? To amma anya ita zata saci kud’in Daddy kuwa!? Nannn tai ya keta tinani, daga ‘karshe dai yace zai bibiyeta yaga ina take zuwa.

LAD’IFA da SALIS POV

Hajiya Babba ta ce “Nayarda bazan yi aurenba Amma sai kun cikamin wannan sharud’an? “Muna jinki Hajiya cewar Lad’ifa tana murmishii. 

Ta ce “Abun da nakeso daku shine… Salis kafito da matar aure, kekuma Lad’ifa zaki koma waje ki ‘karasa karatun ki. In dai kun amin ce to nima na Amin ce, in kuma ba hakaba wallhi watarana saide ku nemeni kuga bananan agari, zan tafi nabar muku gidan naje can wani guri nayi aurena, tinda ADDININMU bai haramta ba, ta ‘Karasa tana hawaye.

Cikin tashin hankali Salis da Lad’ifa suka juyo suna kallon juna, ita dai Lad’ifa nata da sau’ki domin kuwa zata iya, shikuwa Salis cikin muryar tausayi ya ce “Haba hajiya aurefa kikace? Yanzu Dan Allah ina zan iya wani zaman aure yanzu!!? Jin haka yasa Lad’ifa fashewa da dariya ta ce “Haba bro sai kace wani mace wai yaushe zaka iya zaman aure. Hajiya ta ce “to in bazakiyi to wallhi aurena sainayi, da sauri Lad’ifa ta ce “No hajiya Babba mun yarda zamuyi! Da sauri salis ya kalleta ya doka mata harara sannan ya ce “Hajiya Wallhi nifa ban shir… ” Kafin ya karasa hajiya Babba ta tuna da wani abu sai ta ce…

“Naji kuje zanyi tinani. Sun tashi zasu tafi hajiya ta dawo dasu had’i da cewa ina wannan yaron da kukazo gidannan dashi har ka ce abokinane? Cikin sauri Salis ya ce…

“Ok AJ? 

Hajiya Babba ta ce ” Eh shi. Kafin Salis ya ce wani abu ta ci gaba da cewa… “Ina son ka kiramin shi zan bashi aiki, domin naji Kuna maganar cewar shi yanzu aiki ya keso ko?

Cikin jin dad’i Salis ya ce “Good hajiya wallhi dama ina so namiki maganar yaron, amma wannan wawan bazawarin naki… Da sauri ya ri’ke baki yana cewa I’m sorry na mantane. Ya ci gaba da cewa wallhi hajiya yaron yana burgeni, gashi ba dan kowaba sai tsafta, in kika ganshi yasin zakiyi tinanin dan mai kud’i ne, amma y’ay’an talakawa ne sosai, saboda haka Hajiya muna godiya sosai, yanzuma gidan su zanje na kirashi.

Ita dai Lad’ifa tinda ta ga A.J har zuciyar ta gayan bai wani burgetaba dan ita tana jin har yabar gidan bama zata iya masa maganaba, haka dai Hajiya ta tashi ta nufi d’akin ta tana zancen zuci. haka Salis ya nufi gidan su AJ.

(IN BAKU MANTABA A BAYA SALIS YA JE HAR GIDAN SU A.J YA KIRASHI, SHINE YAZO GURIN HAJIYA BABBA HAR TA BASHI WANNAN KUD’IN AKAN ZAI MATA AIKI, TO KUNJI DALILIN KIRAN, DAMA KUMA SALIS YA CE MASA HAJIYA CE TAKE KIRAN SA. MUJE ZUWA)

A.J POV

Har ya gaji da jiranta amma shuru bata zoba, ya kira number ta amma no amsar, yana dai tsaye a gurin har a ka fara kiran sallar magariba, nann ya ganggara yayi, yana cikin sallar ne yaji wayarsa na ‘kara. Bayan ya idar ya ro’ki Allah yasa Hajiya ta kirashi gobe, sannan ya ce Allah yasa kud’in da sarha ta sato masa sukai dubu hamsin (500k) cikin zuciyar sa ya ce “Ai kuwa Nana zan baiwa wannan wayar tawa, Innah kuma na siya mata ‘karama nikuma naje na siyo mai kyau. Yana cikin Addu’ar ne yasake jin ‘karar wayar sa, hakanne yasa ya fita daga masallacin kafin ya d’aga.

SARAH POV

Tin tana harabar gidan su take kiran wayar sa, amma baya d’agawa har ta iso gurin da zasu had’u, tana sake kira ya d’aga, ta bud’e baki zatayi magana ta hangoshi yana isowa gurin. Kana kallon fuskarsa zakaga hasken musulunci irin wanda ke fita daga goshin duk wani musilmin da ke tseda sallharsa, hoton tabon sallahr dake goshin sa ta ‘kurawa ido, dukda duhun dare ya farayi amma hasken gurin bai hanna ta hango abun da yake bata sha’awa a goshin nasaba.

Cikin sakin fuska ya ‘karaso gurin dad’in da yin sallama wacce shikaidai zaiji kayarsa. Kallonta ya keyi kamar yanda Itama take kallon sa. Cikin d’an ‘bata fuska ya ce “Meyasa yau baki saka hulaba kika fito da kanki a haka? SARAH ta ce “sorry I’m forgetting. Kallon ta ya sakeyi yaga kamar tayi kuka sai ya ce “lafiya kuwa naga kaman kinyi kuka?

Sarha ta ce ” Samuel ne ya cuceni d’azu. take ta kwashe yanda sukayi da shi ta fad’a masa, amma bata sanar dashi akan d’aukar kud’i bane. Tin da yake bai ta’ba jin sontaba ko tausayin taba sai yazu, cikin ransa ya ce yanzu ma haka duk a kainane!!! Afili kuwa ya ce…

“Ok sorry stop crying.

Da sauri ta kalleshi jin yau shine yake bata ha’kuri, ta tsayar da kukan… 

Ta ce “please AJ dan Allah kana sona?

A.J ya ce “please yanzu duk ba wannan ba, kinga dare nayi bani kud’in ki koma gidan kar Daddy ya dawo bai gabkiba.

Cikin sauri ta ce “please AJ amsar me. Kana sona?

A.J cikin jin haushi ya ce “Yes Sarah I really love you, kibani kinga dare nayi?

Da gudu ta rungumshi had’i da cewa I’m so happy my AJ. 

Lokaci d’aya tsikar jikinsa ta tashi, in ka gansu a haka zaka rantse da Allah Sarah babu wando a jikin ta, domin kuwa wandon ruwan tokane kuma iya cinya ya tsaya, ga kuma yanda jikin su ya had’u da juna kamar irin suna cikin wani yanayi.

Da sauri AJ ya janyeta daga jikinsa had’i da cewa… “Na fad’a miki cewar Wannan abun babu kyu a *ADDININMU*, please karki… “Cikin sauri ta ce ” muma babu kyu a namu addinin amma in dai da wanda zaka aurane babu laifi.

Cikin sauri ya ce “To mu koda kuwa an saka muku ranane in dai ba’a d’auraba to babu kyau, saboda haka kikiyaye, ADDININMU da naku a kwai babban ci, ta bud’e baki zata sakeyin mgn ya ce “please ina kud’in dare nayi kingama an kusa kiran sallar isha.

Cikin jakar da tazo da ita ta sa hannu ta d’auko kud’in ta mi’ka masa. AJ ya zaro ido waje Yana kallonta ya ce “Sarah sarh sarhh wannan kud’in nawaye? Ganinn yanda kud’in suka bud’e masa ido, nann fa ya rikice ya shiga tambayarta.

ABDULLHA POV

Tin Yana mota yake tinanin irin cin mutuncin da abokin sa ya kaishi a ka masa, cikin ransa kuwa yana kallon lokacin da take kallon sa har wani hararra take masa. Palorn Mommy ya nufa tin kafin ya ‘karasa ya fara jin kamar sauti ko surutan mutane, yana isa ya tsaya chak Yana kallon abun mamaki.

Maryam ce tsaye cikin shigar ‘kanana kaya ta kunna waqar Zainab Ambato ita da wasu ‘kawayanta mata guda biyu, kasan cewar Mommy bata gidan, Nusaiba da Sadiya ma duk tare suka fita da Mommy. Daga ita sai nura d’an autansu, sai ‘kawayan nata guda biyu. yayinda d’aya ta tashi suke bin waqar ita kuwa d’ayar tana chatting a waya.

Dukkansu basu ga shigowar saba tsabar sunshiga hadaya, Saida yayi a’kalla mt5 yana tsaye yana kallonsu, yama rasa mai zai fara musu, sannan sai mamaki ya keyi, da gaske agidan su a keyin kad’e-kad’e da rare-rare!? Kuma Maryam!

Lokaci d’aya haushin abun da Zainab d’in tamasa da kuma abun da ya tarar d’in suka had’e masa yanzu, yanufi gurin da suka jona wayar, yana zuwa ya cire wayar daga cikin abun speaker d’in, baiyi wat-wataba ya buga wayar da ‘kasa.

Ita kuwa Maryam jin an katsemata yasa ta juyo da niyar zagin qawar tata, a tinaninta itace ta kashe. Ai kuwa tana juyowa sukayi ido hud’u da shi, kafin kace me ya d’auke ta damari, had’i da bin kawayen nata. Sukuwa basubi ta kan jakokinsu ba da ta’kalmin su, ita daiyar ma harda gyalenta da wayarta. Haka suka fita da gudu, shikuwa ganinn sun gudune yasa ya dawo gurin Maryam, itama ta nufi d’akin ta da gudu tana kiran sunann Mommy.

Dai-dai ta turo ‘kofar zata rufe shima ya iso d’akin, kafin ta tura ya rigata, ya turo, hakane yasa ta fad’a a tsakiyar d’akin. Nann ya cire hular kansa,. Sannan ya zare wayar caja dake d’akin ya shiga lamta mata, tana ihuuu yana zabga Mata, saida ya mata shegen duka kafin ya ce “Bade ke mai taurin kaiba muje zuwa ina dai-dai da ke… tsabar kin raina mutane kizo har gida kina kunna mana wa’ka!? Ya kara d’aga wayar ya labtamata, har saida Maryam ta daina kuka tsabar azaba.

AJ POV

Sarah waye ya baki wannan kud’in!? Yafad’a yana ‘kura mata ido?

Sarha ta ce “please ‘kar’ba in kuma bakaso tom na koma dasu?. AJ ya kar’ba ya ‘kirga yaga dubu d’ari dai-dai, kallonta yayi ya ce “To amma yanzu yazaa…” Zamuyi waya kar Daddy ya dawo yaga bananan. Haka ta sake rungumarshi sanna ta tafi, ta barshi tsaye yana kallon ta. Shima cikin kasala ya kama hanyar gida…..📝

Littafi mai fuska uku sai a hankali. kodai ku kasan ce da S REZA 

<< Addininmu 4Addininmu 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×