Bai ma yi ƙoƙarin kula su Lukman ba. Kamar yadda ba su ce masa uffan ba, haka shi ma bai ce musu komai ba har suka kai gida. Lukman ya ce ma Haneef zai je gida ya kira shi in za su koma.
"Haneef ka ban lambar mai gyara ma Abba mota."
Ko in da yake Haneef bai kalla ba ya wuce ya shiga cikin gida. Wani abu Fu’ad ya ji ya tokare masa wuya. Already baya jin daɗin komai. Ga yunwa da ke damun shi, ɗan cake ɗin da ya ci har ya ƙone. Cikin gida. . .