Hannu ta sa ta goge hawayen da suka zubo mata.
“Safiyya da baki mare shi ba.”
Wani guntun murmushi ta yi da bai kai zuciyarta ba. Tana jin yadda komai ya kwance mata.
Tun ɗazun ta kasa manta shi. Da ta rufe idanuwanta shi yake mata yawo. Ta kuma rasa dalili.
Ba ta taɓa zaton za ta sake ganin shi ba. Saboda bai mata kama da ‘yan garin ba. Da ƙyar ta iya samun ‘yar nutsuwar da ta ce, “Babu wanda zai ɗaga hannu ya mare ka a gabana kawu.”
Girgiza kai ya yi yace,
“Yanayin shi ɗan masu da shi ne. Ina gudun abinda zai je ya dawo. Ba ki ga yadda ya tafi a zuciye ba?”
Ita kanta ta tsorata sosai da yanayin da ta ga ya tafi dashi. Tana jin maganar shi da ya faɗa mata kafin ya tafi.
“Fu’ad. Sunana Fu’ad don ina son ki san sunan mai fuskar da kika taɓa. Ki san sunan wanda kika taro ma dangin ki rikici da shi.”
Wasu hawayen suka sake zubo mata. Ta sa gefen hijabinta ta goge su.
“Bari in shiga gida kawu.”
Ya jinjina kai sannan yace, “Allah ya miki albarka. Na gode safiyya. Allah ya jishe mu alheri.”
Ta amsa da amin ta shiga gida. Yanayinta inna ta kalla tace,
“Lafiya Safiyya?”
Abinda ya faru ta zayyano mata. Inna ta sa salati.
“Ni maryama me ke faruwa da mu ne haka? Yau ɗan uwanki ya sha da ƙyar a hannun ‘yan sanda ke kuma kina son janyo mana wani rikicin?”
Murya can ƙasa-ƙasa tace, “Inna Kawu fa ya mara. Kuma shi ne ba shi da gaskiya. Ina wajen tsaye komai ya… “
Harara Inna ta watsa mata ta katse da faɗin, “Rufemun baki. Shine me? Kema da nake gani da hakuri kin fara ɗaukar halin ɗan uwanki ko?”
Wasu hawaye ta ji suna bi mata fuska.
“Ki yi haƙuri Inna. Ba zai sake faruwa ba in shaa Allah.”
Safiyya ta faɗa tana miƙewa. Inna ta kalle ta tace,”Allah shi kyauta. Ina kuma za ki?”
Rausayar da kai ta yi. Muryarta a sanyaye tace, “Makaranta wai ko addu’ar tashi in samu.”
“Ai sai dai ki haƙura yau tunda yamma ta yi sosai. Ki zauna ki taya ni ƙarasa tuwon nan kawai.”
Hijabinta ta cire ta amsa Inna da to. Ta shiga ɗaki ta ajiye ta fito suka shiga hidimarsu tare.
*****
Yana ƙarasawa wajen motarshi ya buɗe ya shiga ciki. AC ya ƙure ya ɗora kanshi kan sitiyarin motar.
Numfashi yake mayarwa. Yarinyar nan ta yi babban kuskure. Ba zai saurari ɓangaren zuciyar shi da ke ƙoƙarin tausar shi ba. Ba zai saurare shi ba saboda tsakanin safiyar yau da yammacinta wani abu ya samu matsala a ciki. Wani abu ya kwance a cikin zuciyarshi da bai san yadda zai ya gyara ba. Kafin koma meye ya ci galaba a kanshi ya zaro wayarshi.
Hamza ya kira. Kafin Lukman da Haneef da zuciyarshi su hana shi ya kira Hamza.
Ringing ɗin farko ya ɗauka tare da faɗin.
“Moh…”
Bai ɓata lokaci ba yace:
“Ina Bichi Hamza. Ina son ko me kake kai dropping. I will pay you. Mota uku nake so ta ‘Yansanda. You call me in kun ƙaraso. I don’t care how much it will cost and be fast.”
Bai jira amsar da zai ba shi ba ya kashe wayar. Sauke kujerar ya yi sosai ya kwantar da bayanshi yana lumshe idanuwanshi.
Marin yana dawo mishi kamar lokacin akai komai.
*****
One hour later.
Zaune suke a wajen zaman makokin suna ta hira abinsu.
“Nikam ka ƙarasa kallon The 100 kuwa?”
Girgiza kai Haneef ya yi yace, “Ni zaman makoki nake fa.”
Dariya Lukman ya yi.
“Zaman makokin wa?”
Ya tambaya. Haneef na dariya yace, “Finn mana.”
Dariya suka yi su duka kafin Lukman yace, “Ko ni fa na ji haushin mutuwar Finn. Wannan banzar Clark ɗin haushi take bani wallahi. Na fi son Octavia.”
Taɓe baki Haneef ya yi tare da faɗin, “Octavia broke my heart. Ina son shegiyar ta je ta zaɓi Lincoln.”
Wata dariyar suka sake yi a tare. Haneef ya fara jin jiniya kamar ta ‘Yansanda. Ya juya ya kalli Lukman shi ma da alamu yaji.
“Ina Fu’ad?”
Haneef ya tambaya yana kallon Lukman. Miƙewa ya yi daga kishingiɗar da yi ya ɗauko wayarshi.
“Damn it. Chargy na ya ɗauke. Goddammit Lukman call him yanzun nan.”
Lukman jikinshi har kyarma yake. Ya lalubo wayarshi ya yi dialing lambar Fu’ad. Wayar shi a kashe take. Sake trying ya yi. Still a kashe. Ya kalli Haneef ya girgiza masa kai. Miƙewa Haneef ya yi. Da gudu gudu ya ɗauki takalmin shi. Lukman na bin bayan shi.
Fa’iza suka ci karo da ita ta fito daga cikin gida. Kallo ɗaya ta yi musu tace:
“Lafiya kuwa?”
Girgiza mata kai Haneef ya yi yace, “Lafiya ƙalau. Ki ajiye wayarki kusa dake dai.”
Lukman Fa’iza ta kalla ta ce, “Yaya Lukman me ya faru?”
Shiru ya yi baice komai ba. Zuciyarshi bugawa kawai take yi.
Haneef ne yace mata, “May be Fu’ad ne. We are not sure yet. Za mu je mu duba mu gani.”
Dafe kai Fa’iza ta yi. Ba ta kawo ma a ranta wani abu bane ya samu Fu’ad. Yana faɗar haka ta soma addu’ar Allah ya sa ba wani bane ya haye masa. Tasan yana yawan shiga rikici. Wasu su sani wasu kuma Haneef da Lukman su ɓoye musu.
“Zan bi ku please.”
Haneef ya soma girgiza mata kai Lukman yace, “Ta biyo mu please. In har abinda nake tsoro ne ya faru. We need all the help we can get.”
Tare da Fa’iza suka tafi. Sai da suka fara duba Fu’ad ko za su ga motarshi amma wayam wajen yake. Motar Haneef suka ɗauka suka miƙe hanya. Ba tare da sun san ina za su fara neman Fu’ad ɗin ba.
*****
Ruwa take ja amma zuciyarta ba ta mata daɗi. Ga wani irin yanayi tana ji kamar wani abu zai faru da su. Kamar daga sama ta ji muryar babansu yana cewa, “Safiyyaaaa!”
Da hanzari ta ƙarasa janyo gugar daga rijiya. Ko juye ruwa. Ba ta yi ba ta ajiye ta nufi hanyar soron da ta jiwo muryarshi. Iccen da ke kanshi ta kama mishi suka sauke tana faɗin, “Sannu da dawowa Baba. Ruwa nake ja shi ya sa ban jika ba.”
Murmushi ya yi mata yana faɗin, “Ba ki je makarantar bane yau?”
Gabanta ta ji ya yanke ya faɗi. Ta buɗe baki za ta amsa shi. Jiniyar ‘Yansandan da suke ji nesa-nesa ta matso kusa.
“Oh Allah dai ya sa lafiya. Tun da na taho nake jin kukan nan kamar motar asibiti kamar ta ‘Yansanda”
Safiyya ta amsa da.
“Amin dai baba. Ni ma na ji. Allah ya sa ba gobara bace.”
“Allah sarki. Amin kuwa. Kau da itacen nan gefe mana. Ko ki ɗora su saman na jiyan can da na kawo.”
Iccen ta tsugunna ta fara shirin ɗauka kafin su ji kukan kamar a cikin gidansu ake yin shi. Fasa ɗaukar iccen ta yi ta ɗago kai ta kalli Baba da ke tsaye fuskar shi ɗauke da mamaki.
“Bari in… “
Bai karasa ba ‘Yarsanda mace ta shigo ko sallama babu. Ba ta ko bi takan Baba da Safiyya da ke rafka salati ba.
“Ku shigo,” ‘yarsandar ta faɗa. Wasu guda huɗu ne suka shigo maza. Cikin rawar murya Baba yace,
“Subahanallahi. Lafiya kuwa? Me ke faruwa…? “
Alamun sun gane me yake nufi basu nuna ba ma ballanta na su yi yunƙurin amsa shi. Cacumar shi suka yi kamar ɓarawo suna janshi yana turjewa suka yi waje da shi.
Safiyya da ta ruga cikin gida ‘yarsandar na bin bayanta ke kiran, “Inna mun shiga uku. Inna ‘yansanda sun tafi da Baba.”
Da gudu Inna ta fito daga ɗaki tana gyara ɗaurin zani. Hannunta da na Safiyya ‘yarsandar ta kama tana jansu suna kuka har ƙofar gida.
Lokacin unguwar har ta cika kamar za ta fashe. Mutane na tsaye cirko-cirko suna kallon ikon Allah. Wasu kuma na tambayar me Malam audu zai aikata haka har ‘yansanda mota uku su biyo shi. Don kowa ya san halayyar shi. Mutum ne mai fara’a, ba a taɓa ganin ya yi rigima da kowa ba.
Safiyya da ke wani irin kuka tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga rikon da ‘yarsandar ta yi mata.
“Me muka yi muku? Me…”
Cik maganarta ta tsaya mata a wuya ganin Fu’ad jingine a jikin mota. Kayan ɗazun ne a jikinshi. Sai dai fuskarshi sanye take da wani bakin gilashi na rashin mutunci. Wani ƙarfi ta ji ya zo mata. Ta ture ‘yarsandar ta ruga da gudu tana ƙoƙarin ƙarasawa inda Fu’ad ke tsaye wasu ‘yansanda suka sha gabanta.
Cikin isa da iko yace,
“Allow her wasu cikin ku su tafi da wancen mutumin gidan kawunta ku tattaro min kansu gaba ɗaya. Bance ku bar ko jariri ba.”
Suna ba ta hanya ta ƙarasa. Tsugunnawa ta yi a gaban shi. Kuka take kamar za ta mutu.
“Don Allah….. Don….. Don girman Allah ka sake su. Ni… Ni nai maka laifi. Ni za ka hukunta.”
Wani rawa ya ji zuciyarshi na yi. Glass ɗin idon shi ya sauke. Ya kafa idanuwanshi kan Safiyya da ke durƙushe a gabanshi tana kuka.
Gaskiya ta faɗa. Rikicin shi tsakanin ita da shi ne da kuma kawun ta. Sai dai yadda yake jin wani yanayi na saukar masa da kasala ya tabbatar masa ita ba zai iya hukuntata ba. Ba kuma zai yafe hannun da ta ɗaga mishi ba. Ba halin shi bane a taka shi a ba shi haƙuri ya haƙura ba. Ba halin shi bane a roƙe shi ya amsa.
Yana da tabbacin abu ɗaya ne, za a taɓa kowa banda ita. Zai tabbatar da marin shi ya fita a jikin duk wani wanda ta damu dashi. Wani numfashi ya sauke yana cije leɓen shi na kasa. Kallonshi ya maida kan ‘Yansandan da tuni sun tura Inna a bayan mota.
Baba kuma an tafi da shi aje a ɗauko su kawu. Da ido ya kira’ Yarsandar da ta riƙo Inna.
“Ba na son ganinta. Don’t touch her. Ki haɗata waje ɗaya da mahaifiyar ta.”
Babu musu ta cacumi safiyya. riƙe masa ƙafa ta yi tana rushewa da kuka.
“Na shiga uku ni safiyya. Don Allah ka rufa mana asiri. Ka ƙyale min su Inna. Ni ko me za kai min ka yi mun. Ni na yi maka laifi ba su ba.”
Tsugunnawa ya yi ya sa hannu ya ɓanɓare ‘yan yatsun Safiyya yana faɗin:
“Let go of me…”
Tureta ya yi ‘yarsandar ta cumimiye mata hijab ta ja ta tana ihu. Wani irin abu ya ji ƙirjin shi na yi. Kai yake girgizawa saboda ba ya son me yake ji.
Sam ba ya son abinda yake ƙoƙarin faruwa…!