Yana jin Lukman na ƙwanƙwasawa har ya gaji ya tafi. Ba ya son magana da kowa. Su bar shi ya sha iska abin shi. Ai komai ya yi su ba dai dai bane ba. Komai ya yi rashin mutunci ne. A ɗakin shi ya yi sallar isha’i ya je ya watsa ruwa sannan ya dawo ya yi kwanciyar shi.
Yana jin wayarshi na ringing. Ya duba ya ga Haneef ne. Rejecting ya yi. Ya sake kira ya ƙara kashewa. Text ya ji ya shigo ya buɗe Haneef ne.
“Stop acting like a kid and pick the call.”
Share shi ya yi. In ya gaji ya haƙura. Ai kam daya sake kira har huɗu bai ɗauka ba wani text ɗin ya yi masa ya ce sun koma Bichi.
Yana karantawa ya kashe wayar shi gaba ɗaya ma. Gara su tafi abin su su bar mishi gidan.
A haka bacci ya ɗauke shi. Wannan karon ma Safiyya ta kutso masa kai a cikin mafarki. Zaune take a gaban wata bishiya tana ta kuka. Shi kuma yana tsaye a gefe yana kallonta. Tana ɗagowa ta kalle shi da fuskarta a kumbure idanuwanta cike da hawaye.
Ya farka da sauri. Wani numfarfashi yake fitarwa. A ranshi yana tunanin wannan yarinyar ko dai mayya ce.
In ba haka ba shi mafarki ma ko yana yin shi to da ya farka ba ya rikewa. Amma karo na biyu kenan da mafarkinta ya hana shi bacci.
Wanka ya shiga ya sake yi saboda wani iri duk yake jin shi. Da ya dawo ya kwanta ko ya ya rufe idanuwan shi Safiyya yake gani.
Da ƙyar ya samu bacci ya ɗauke shi.
Bayan Kwana Biyu
Zaune yake a ɗakin shi yana kallo. Gaban shi kuwa ledojin snacks ne da yake ci tuli, guda kuma wanda ya cinye. Lukman ya turo ƙofar ya shiga tare da yin sallama. Amsa mishi ya yi.
“Wai ba dai ba ka shirya ba. Ƙarfe tara ne fa addu’ar nan.”
“Allah ya jiƙanta. Na ɗauka na faɗa maka babu inda zan je?” Fu’ad ya amsa shi hankalin shi na kan ball ɗin da yake kallo.
Girgiza kai kawai Lukman ya yi yace, “Sadakar ukun Hajiya Babbar ne ba za ka ba Fu’ad? Ka kyauta kenan?”
Sai lokacin ya juyo ya kalli Lukman.
“Nake jin ance addu’a duk daga inda ka yi ta zuwa take? Na ce Allah ya jiƙanta ko akwai inda aka wajabtamin zuwa ne?”
“Allah yaye maka.” Lukman ya faɗa yana juyawa.
“Amin. Ka ja min ƙofar Mr. I know what is right.”
Bai ko juyo ya bi takan Fu’ad ba. Ƙofar ya bari a buɗe kuma ya san da gangan ya yi don haka ya tashi ya kulle ƙofar shi. Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi yana sauke wani dogon numfashi da bai san yana riƙe da shi ba. Ƙirga ɗaya zuwa goma yake yi cikin kanshi yana son ya dai-daita bugun da zuciyarshi ke yi. Kwanakin nan biyu dai a daddafe ya yi su. Ga rashin wadataccen bacci.
Ga iya ƙoƙarin shi da yake na ganin ya ƙaryata dalilin da ya sa yake son zuwa Bichi. Hakan ya sa shi ganin yayi duk wani ƙoƙarin shi na ƙin zuwa wajen addu’ar yau. Tun da dare Haneef ya kira shi. Bai ma ko ɗaga ba duk da ya huce fushin marin da ya yi masa. Yana jin share shin ne kawai.
Yanzun da Lukman ya shigo ya kira Bichi ba ƙaramin ƙara mishi son zuwa ya yi ba.
Cake ɗin da ke hannun shi da ya ci rabi ya ajiye saboda ji ya yi ba zai iya ƙarasa cinyewa ba. Ya maida ƙafafuwanshi kan kujera ya kwanta cikinta sosai yanajin wata kasala ta rufe shi. Lumshe idanuwanshi ya yi duk da ba baccin yake ji ba. Wayarshi ya ji ta soma ruri. Ya yi niyyar share ta da fari, ya dai ɗauko ya duba.
Da sauri ya ɗaga yana faɗin, “Hello momma.”
“Fu’ad lafiya dai ko? Haneef ya ce min ba zaka zo wajen addu’a ba. Yanata kiranka ma ka ƙi ɗauka.”
Ƙasa ya yi da murya sosai yace, “Kaina ciwo momma. Ba na jin zan iya handling hayaniyar shi ya sa.”
“Ayya ka sha magani. Ka kwanta. Mu ma anjima da yamma za mu taho gaba ɗaya ai. Allah ya ƙara sauƙi.”
Ya amsa da, “Amin Momma. Allah ya dawo da ku lafiya.”
Ta amsa shi ta kashe wayar. Baya son ana mishi maganar zuwa Bichi ko kaɗan.
5:30pm
Yau ba ya jin zai iya zuwa ball. Dama Lukman na nan sai su fita tare. Babban falo ya fito. Jin cikin shi yake wayam kamar ba ɗazun nan ya gama loda mishi burger da milkshake ba. Sallamar su Fa’iza ya ji. Ganin har da Abba ya sa shi ƙarasawa da fara’ar shi.
“Abbah sannunku da dawowa.”
Da fara’a suka amsa mishi. Haneef yace, “Ya ciwon kan?”
Hankalin shi ya maida kan ‘yan biyu da suke rikici kan waya ya share Haneef ya ce musu, “Ku ba kwa gajiya da rigima ne?”
Idanuwan Hassana cike da hawaye tace, “Hussain ya fasa min screen ɗin waya.”
Kallon Fu’ad ya yi yace, “Na fa ba ta haƙuri. Kuma har tawa wayar na ba ta na ce mu yi musaya. Ta ce ba ta so wai tawa duk ta gurje.”
Dariya Fu’ad ya yi. Ya san Hassana tana da rikici sosai. Su Momma kam wucewa suka yi abinsu suka bar su nan. Wayar Hassana Fu’ad ya karɓa ya ga ɗan tsagewar da ta yi ba ma wata bace can. Shi ya siya musu samsung ɗin wancan zuwan da ya yi.
“Yanzun ya kike so ayi?” Fu’ad ya tambaya. A shagwaɓe tace, “A sake min screen ɗin. Kuma na san zai yi tsada sosai.”
Wayar ya miƙa mata yace, “Kuje da Hussain to. Ki kai a gyara in za ku karɓo sai in ba ki kuɗin ko?”
Wani murmushi ta yi mishi kamar ba ita ke shirin yin kuka yanzun nan ba.
“Thank you bro.” Ta fadi.
Murmushi kawai yai ya wuce abinshi.
*****
Da dare su duka suka haɗu akan dining table suna cin abinci. Kamar koda yaushe Hassana da Hussain rigima suke ta yi. Hakan ba ya nufin babu jituwa a tsakaninsu. Sai ka yi ƙoƙarin taɓa ɗaya za ka ga yadda suke ƙaunar junansu. Fa’iza hankalinta na kan Fu’ad, tunda suka dawo ta ganshi wani iri dai. Da yanzu ya damu kowa da tsokana. Ko yana tambaya wane irin abinci ne Momma ta dafa da kanta wanne kuma ‘yan aiki suka jagwalgwala.
Sai da ta haɗiye abincinta sannan ta ce mishi, “Bro me ke damunka?”
Kafaɗa ya ɗan ɗaga mata sannan yace, “Me kika gani?”
“You are strangely quiet.” Kai kawai ya langaɓar gefe bai amsata ba.
Momma tace, “Da gaskiyar Fa’iza, me ke damunka?”
Yamutsa fuska ya yi tare da faɗin, “Kawai ba na jin daɗin jikina ne.”
“Ka tashi in raka ka asibiti.” Cewar Haneef da ya ture plate ɗin abincin shi da alamun shirin miƙewa.
“Fa’iza miƙo min robar ruwan can.”
Fu’ad ya faɗa kamar ba da shi Haneef ke magana ba. Abbah ke kallon su yana murmushi yace, “Fu’ad ba ka jin Haneef na magana ne.”
Sake daƙuna fuska Fu’ad ya yi yace, “Na ji shi Abbah.
Ba sai na je asibiti ba.”
Miƙewa Fu’ad ya yi yace musu, “Ni kam sai da safenku. Zan kwana a gidansu Lukman ne.”
Su duka suka amsa shi momma ta ɗora da, “Ka gaishe da Hajiyar su Lukman din.”
Ya amsa da, “In shaa Allah” Ya wuce.
Ba abinda ya ɗauka don har kayan sawa yana da su a ɗakin Lukman.
*****
“Kasan babu abinda na tsana sai a tusani a gaba ana dariya.”
Fu’ad ya faɗa yana jin kamar ya kwaɗa wa Lukman mari. Dariya yake yi har da riƙe ciki da ƙyar ya iya cewa, “Mayu fa ka ce Fu’ad.”
Juya idanuwanshi ya yi yace, “To in ba mayu bane suka kama ni. Ni bana jin daɗin jikina and ba zan iya cewa ga exact abinda ke damuna ba.”
Abin dariya yake ba wa Lukman, wai mayu.
“Kai ba mai ciki ba balle in ce mood swing ka…”
Bai ƙarasa ba saboda pillow ɗin da Fu’ad ya jefa mishi akai yana dariya shi ma. Babban dalilin da ya sa ya ce a gidan su Lukman zai kwana kenan. Yasan zai ji shi light ko yaya yake. Beside ba ya son magana da Haneef. Saboda yana da wani abu a tattare da shi da yake sa ka ji kana son gaya mishi duk abinda ke damunka. Ya san in ya tambaye shi zai iya faɗa mishi. Lukman kam zai iya faɗar wani shirmen su yi dariyar su. Lukman ya riga shi yin bacci. Har tsoron rufe idanuwanshi yake yi kar ya ga Safiyya.
Amma kamar abin baki, bacci na ɗauke shi abinda yake gudu ya faru.
*****
“Da yawan Lokuta ƙaddara kan haɗa abubuwan da hankali ba ya taɓa iya ɗauka.”
Murmushi ta yi ta ce, “Kamar yanda ƙaddara ta haɗa ni da kai.”
Kai ya ɗaga mata cikin yarda da abinda ta ce kafin ya sauke idanuwan nan nashi da kalarsu ke ba ta mamaki a cikin nata. Ba ta san lokacin da ta ce, “Idanuwanka na ba ni mamaki.”
Murmushi ya yi mata da ta ganshi har cikin idanuwan shin nan kafin yace, “Yadda ki ka shiga nan yana bani mamaki.”
Ya dafa ƙirjinshi dai dai inda zuciyarshi take.
*****
Buɗe idanuwanta ta yi. Muficin dake gefenta ta ɗauka ta tashi zaune tana fifita, amman a banza. Wata irin zufa take yi da ba ta da alaƙa da yanayin zafin da ake yi.
Ta gaji da wannan abin. Jan ƙafafuwanta ta yi ta haɗa kai da gwiwa wasu hawaye masu ɗumi na zubo mata. Wannan wane irin abu ne. Sati ɗaya kenan. Da duk numfashin da za ta ja ta fitar da tunanin shi a ciki. Ta ma rasa me take ji game da shi. Saboda wani irin yanayi ne take ji kala-kala.
Ko lomar abinci za ta kai baki yana nan cikin kanta. Da shi take komai a manne. Ba ta da ikon bacci mai lafiya ba tare da shi a cikin mafarkinta ba. Gashi wani irin mafarki take yi da duk in ta farka sai ta ji shi kamar gaske. Kalaman da suke wa juna a mafarkin ya fi komai ɗaga mata hankali.
Kamata ya yi ace ko mafarkin shin za ta yi ace rashin mutunci yake mata. Yadda ta ga fuskarshi haka take ganinta a mafarki.
Ko jiya da dare sai da ta yi kuka saboda ba ta san abinda ya dace ta yi ba. Saurayin da ta san ba zata sake ganin shi ba. Akan me zai manne mata har haka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ja jiki ta koma ta kwanta. Addu’o’i ta yi sosai. Bacci mai nutsuwa ya ɗauke ta ba tare da mafarkin komai ba.
*****
Jikinta babu wani ƙarfi ta samu ta gama sharar gidan. Sai da ta yi wanke-wanke sannan ta ja ruwa ta je ta yi wanka. Shafa man take yi amma hankalinta na wani wajen daban. Ji ta yi an taɓa ta, da sauri ta ɗago.
“Safiyya me ke damunki ne kwana biyun nan? Sai ai ta magana ba kya ji?”
Inna ke faɗa da alamun damuwa. Cikin sanyin murya Safiyya tace, “Yi hakuri Inna. Ban ji ki bane shi ya sa.”
“Nasan ba ki ji ni ba ai. Ina tambaya ne ko lafiyar ki?”
Saida ta langaɓar da kai sannan ta amsa da, “Ba komai.”
Da alamu Inna ba ta yarda ba komai ba. Ta dai ƙyale ta ne kawai. Da hanzari ta ƙarasa shafa man.Ta tashi ta ɗauko wata doguwar riga ta atamfa ta saka. Kasancewar ranar alhamis ce babu makaranta. Hakan ya sa Safiyya ta koma kan tabarma ta yi kwanciyarta. Tun da abincin rana ba lokacin za ta ɗora ba. Addu’a take yi sosai ta fatan yadda ta san ba za ta sake ganin Fu’ad ba, Allah ya sa ya fita daga tunaninta har abada.