Agogon shi yake ɗaurawa. A cikin kanshi babu komai sai son barin ƙasar gaba ɗaya. So yake ya bar komai inda ya kamata ya zauna tun daga farko. Amma abinda yake so a zuciyarshi da kanshi ya sha banban. A 'yan kwanakin nan mafarkan da yake sun yawaita. Har idanuwanshi sun faɗa saboda ba shi da wata wadatacciyar nutsuwa. Komai baya masa daɗi. Ba ya son zama shi kaɗai. Don ma Lukman na hutu sai abin ya yi masa sauƙi.
Gudun Haneef yake don ba ya son gaya mishi asalin abinda ke damun shi. Ta ina. . .