Skip to content
Part 15 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

“Lukman magana nake maka Fa.”

Fu’ad ya faɗa ranshi a ɓace. Waje Lukman ya samu ya yi parking. Ya maida hankalinshi kan Fu’ad.

“Anan kake nufin za mu tsaya. Ko da ƙafafunmu za mu ƙarasa wai…”

Shiru ya yi ganin yanayin fuskar Fu’ad ɗin. Tsoro ne a bayyane. Don sai lokacin nauyin yanayin da ya haɗa su da Safiyya yake danne shi.

“Mu koma. I can’t, what am i going to say to her?”

Fu’ad yake faɗa a rikice. Yana shafa hannun shi akan fuskarshi saboda wata zufa da yake ji a jikinshi.

Dafa mishi kafaɗa Lukman yayi.

“Hey. Ka manta ba saika mata magana ba. Kawai ko ganinta ka yi. Ka bari mu ƙarasa wajen gidansu mu tsaya ko za ta fito.”

Tunda ya fara maganar Fu’ad ke girgiza kai alamar bai yarda ba. Gaba ɗaya ya wani birkice.

Abin har tsoro ya soma ba wa Lukman. Shi kam indai haka so yake ya fara gudun ya kama shi.

Kalli yadda gaba ɗaya Fu’ad ya wani fita hayyacin shi. Ya kasa samun nutsuwa.

Shi kam Fu’ad ji ya yi iskar da ke cikin motar ta mishi kaɗan. Da sauri ya buɗe murfin motar ya fita.

Jingina bayanshi ya yi da motar. A hankali ya zame ya tsugunna yana wani maida numfashi da sauri-sauri.

Sama sama yake jin Lukman na faɗin,

“Fu’ad? Fu’ad wai lafiyarka kuwa?”

Da ƙyar ya ɗaga mishi kai. Ganin ya ƙi tashi ya sa Lukman kallon shi sosai yace,

“Ka taso to ka dawo cikin motar.”

Ɗago kai ya yi.

“Iskar dake ciki nake jin ta min kaɗan.”

“Okay sai mu sauke glass ko abar murfin a buɗe.”

Miƙewa Fu’ad ya yi yace,

“No ka jira ni. Bari in ɗan taka in dawo.”

Da alamun rashin yarda Lukman yace,

“Anya kam. Ka bari dai mu tafi tare.”

Wani guntun murmushi ya yi yace,

“Karka damu ba na jin a yanayin da nake ciki zan iya wani tashin hankali. Kawai zan ganta ne in dawo.”

Kai kawai Lukman ya ɗaga mishi. Ya kama hanya ya miƙe. Tun kafin ƙafafuwanshi su ƙarasa zuciyarshi ke hango gidansu Safiyya.

*****

Tsaf ta gama shirinta. Ta ɗauki jakarta ta duba duk abinda take buƙata yana ciki. Kasancewar yau asabar tun ƙarfe biyu sun shiga islamiyya. Allah ya mata tsoron bulala. Shi ya sa da ƙyar ta tsaya ta ci abinci. Shima don Inna na ta faɗa ne. Fitowa ta yi tace,

“Inna sai na dawo.”

“Allah ya tsare. A dai kula Safiyya.”

Ta amsa da,

“In shaa Allah.”

Ta fice. Tana ta sauri. Kawai ji ta yi gabanta na faɗuwa ba ta kuma san dalili ba. Ita dai sauri take ta ƙarasa islamiyya ta samu Asiya ta biya mata karatun da akai na sira ranar Laraba. Tana can tana tunani ba ta ji komai ba. Sam ba ta kula da mutum ba sai da suka zo gab.

“Ya Rabbi…”

Ta faɗa tana kaucewa da hanzari don sun kusan cin karo. Kamar ance ya ɗago. Wani irin tsalle zuciyarshi ta yi kafin ya ji ta daidaita a mazauninta. Amma ta wani matse sai da ya fitar da wani numfashi. Kwanaki sittin da takwas. Amma jinsu yake kamar watanni sittin da takwas.

Ita kanta Safiyya kallo ɗaya za kai mata ka ga tsantsar razanar da ke fuskarta.

Hannu ta sa ta shafa fuskarta. Don ta kasa tabbatar da gaskiyar da ke gabanta. Gani take kamar mafarkin daren ne ya biyota da ranar nan. Wani rauni ya ziyarci zuciyarta. Lokaci ɗaya ta rasa ko me take ji. Ko me ya kamata ta ji.

Kallonta kawai yake yi. Idanuwanta ta sauke cikin nashin nan da kalar su ke ba ta mamaki.

Idanuwan da ta kasa mantasu. Idanuwan da suke farautarta duk dare tun da ta gansu.

“Sofi… “

Ya kira da wani yanayin da zuciyarta kaɗai ta fahimta. Innalillahi ta shiga jerowa a zuciyarta. Ba wanda ya taɓa kiranta da sunan da ya kirata.

Idanuwanta ta sauke daga cikin nashi ta kafe su a ƙasa. Ji take kamar ƙasa ta buɗe ta haɗiyeta.

Ga ƙafafunta ta kasa ko da ɗaga su. Ji take ma kamar sun daina aiki. Don ta kasa motsa su.

So yake ta ɗago ta ci gaba da kallon shi. Zai iya rantsewa yanajin dawowar abinda ya rasa da duk numfashin da yake saukarwa.

“Sofi…”

Ya sake kiran sunanta. Kamar da kanshi kaɗai yake magana. Saboda sanyin muryar da ya yi amfani da shi wajen kiran sunan nata. Aman ta ji shi. Ba kiranshi kaɗai ta ji ba. Har kusancin shi da ita. Ta ƙi ɗagowa ne saboda tana ta neman inda ta adana tsanarshi ta rasa. Fatan da ta yi ya tabbata yau. Kuma fata take wani abu da zai kauda shi ya zo. Saboda yanayin da take ji ya girmi wanda take zaton tana ji a baya.

Ji take zuciyarta kamar ruwa ce ba tsoka ba. Tana jin yadda take narkewa tana mata yawo a wurare da ba za su faɗu ba.

Da ƙyar ta ji ta iya cira ƙafarta. Ta motsa ɗayar ƙafar don ta tabbatar ba su daina aiki ba.

Gani ya yi tana shirin raɓa shi ta wuce. Ya ji zuciyarshi ta wani yawata tana son binta. Da hanzari ya tare hanya.

“Karki tafi. Ki min magana in ji.”

Ji take kamar ta toshe kunnuwanta ta daina jin muryarshi.

Wani irin tasiri take mata na ban mamaki. Wucewa ta sake zuwa za ta yi ya tare hanya. Da ƙyar cikin muryar da ita kanta ba ta gane ba saboda rauninta ta ce,

“Ka matsa don Allah.”

Ajiyar zuciyar da ya sauke yasa ta ɗagowa cikin hanzari. Suna haɗa ido ta yi saurin sauke nata saboda abinda ke cikin idanuwanshi suna neman jan zuciyarta inda bai kamata ba.

“Keep talking. Ki ce koma mene ne.”

Kanta a ƙasa ta ce,

“Me kake yi anan?  Duk abinda kai min bai isheka ba sai ka biyo ni?”

Lumshe idanuwanshi ya yi. Ya sake buɗe su.

“Banda kalaman da zan ɗora abinda ya faru akai. Karki ɗauka da zaɓi na na zo nan. Inda wani zai hangomin yanayin nan ba zan taɓa yarda ba.”

Idanuwanta cike taf da hawaye ta ce,

“Ka ƙyale ni. Don Allah ka bar ni kawai.”

Yanayin yadda muryarta ke rawa ya taɓa shi. Da sauri ya ɗaga hannuwa yace,

“Zan ƙyale ki. Ina so mu yi magana ne kawai. Ki ban lambar wayarki.”

Ba ta son hawayen da suka cika mata ido su zubo. Ba ta son ta nuna wani rauni a gabanshi fiye da na yanzun.

Ita ina ta ga waya. Koma tana da ita akan me zata ɗauki lambarta ta ba shi. Ta ga alama in ba amsa ta ba shi ba ba zai ƙyale ta ba.

“Ni bani da waya. Ka tafi kawai don Allah.”

Hannuwanshi ya haɗa duka biyun waje ɗaya alamar roƙon ta sannan yace,

“Zan tafi. I promise.”

Aljihunshi ya laluba. Ya ɗauko Nokia ɗin shi. Sim ɗin ciki ba amfani yake yi da shi ba.

Fa’iza ta siya mai double. Ta ba shi ɗaya. Sai ma ya zo Nigeria ne yake buɗe wayar. Kuma ɗayar wayarshi ma akwai Etisalat.

Miƙa mata Nokia ɗin ya yi yace,

“Zan kiraki a wannan wayar sai mu yi magana.”

Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi. A tsorace take girgiza masa kai.

“Aa. Ni ka ƙyale ni kawai.”

Kanshi ya ji ya soma ciwo nan take. Shi kam bai san yadda zai yi ba. Ya ɗauka zuciyarshi za ta gamsu da ganinta kawai.

Yanzun kam ya ji yana son jin muryarta. Kuma ta ƙi karɓar wayar.

“Zan dawo gobe to.”

Ji take kamar ta rusa ihu. Me ya sa ba zai gane bane. Ba ta so ya dawo gobe. Ba ta so ya dawo jibi. Ba ta ma so ya sake dawowa kwata-kwata.

“Karka dawo…”

Kallon da yake mata ya maƙalar da sauran kalaman. Muryarshi a dake gashi ya kafeta da idanuwan nan yace,

” Ki karɓi wayar mu yi magana inba haka ba ban san yadda za a yi in kasa dawowa ba.”

Ganin ta yi shiru yasa shi cewa,

“Ki kalleni sosai. Da ina da wani zaɓi ba za ki ganni anan ba.”

Ita ma da tana da wani zaɓi da ba zata ko tsaya inda inuwarshi take ba. Ballantana ma ta saurare shi.

Amma rashin zaɓin ne ya bar ta da tsayuwa take jin abinda yake faɗa. Bayan duk abinda ya yi musu. So yake ta ce wani abu. Shi kanshi zuciyarshi ke magana.

“Sofi… Ki karɓa.”

Kai take girgiza mishi. Ganin hankalinshi na kan ta karɓi wayar ne ya sa ta yin saurin raɓa shi ta wuce.

Rufe idon shi ya yi ya buɗe su yana faɗin,

“Damn it…”

Bin ta ya yi. Ganin sun jera suna tafiya. Ta kuma tabbatar da sun ƙara gaba mutane na zaune a majalissa. Bayan haka kowa zai iya zuwa wucewa ya gansu. A koma ace an ganta ta jero da wani.

Tsayawa ta yi. Hawayen da take ta tarbewa suka zubo mata. Hannu ta sa zata goge su. Bai san yadda akai hannunshi ya yi ƙoƙarin kaiwa fuskarta ba. Sai ganin ta kauce da sauri ya yi.

“Kar hannunka ya sake ƙoƙarin kawowa kusa dani.”

Safiyya ta faɗa tana share hawayenta. Jin yadda ranta ya ɓaci ya sa shi saurin cewa,

“Ki yi haƙuri…”

Kalmomin ya sake maimaitawa a zuciyarshi. Yadda suka fito a sauƙaƙe ya ba shi mamaki.

Zai iya ƙirga mutanen da ya taɓa ba haƙuri a rayuwarshi. Amma yau ga shi ta fito a sauƙaƙe kan laifin da bai yi ba ma. Ture wannan ya yi gefe. Yana cikin ƙananun abubuwan da ba su bane a gabanshi. Kallonta yake yi. Wasu hawayen suka sake zubo mata.

Wani ƙunci ya ji ya lulluɓe shi.

Ba ya son kukan nan. Bai taɓa zaton kukan wani zai dame shi ba sai yau. Ba damunshi kaɗai ya yi ba. Tokare mishi zuciya ya yi.

“Ki daina. Ki bari. Ba na son ganin kukan nan…”

Sai ta ji ma kamar da ya yi magana sake buɗe wa hawayen hanya ya yi. Wasu na bin wasu haka suke zubo mata.

Da ƙyar cikin kuka tace,

“Na ce ka tafi. Sai wani ya ganni tsaye da kai?  Me kake so inyi?”

Ja yake yi da baya. Don yana jin zai iya jure komai banda kukanta.

Da baya baya yake tafiya. Yace mata.

“Na tafi. Na tafi sofi. Banda zaɓi ne…”

Tana kallo ya juya da gudu ya tafi. Sai ta ji tana son ya juyo ko da sau ɗaya ne ta sake ganin fuskarshi.

Ko hakan zai zama na ƙarshe a rayuwarta. Wani irin abu take ji da ta kasa samo masa kalma.

Waje ta samu jikin bango ta ƙarasa. Hijabinta ta sa ta goge fuskarta. Ta san ba za ta iya zuwa Islamiyya ba. Juyawa ta yi ta koma gida. Da sallama ta shiga muryarta a dakushe tana ƙoƙarin ɓoye ko me take ji sai ta shiga ɗaki.

“Safiyya?  Lafiya dai ko?”

Kanta a ƙasa tace,

“Inna kaina ke ciwo sosai. Shi ne na dawo gida.”

Cike da kulawa Inna tace,

“Subahanallahi. Sannu. Ki je ki kwanta. Ko Usman inya shigo yaje ya siyo miki magani.”

Ba ta amsa Inna ba ta shige ɗaki. Jakarta kawai ta ajiye ta kwanta.

Dunƙule jikinta ta yi waje ɗaya. Ko hijab ba ta cire ba. Wani irin kuka marar sauti ya ƙwace mata.

Ji take yadda kukan ke fitowa daga zuciyarta kamar Fu’ad ne zai fita.

Amma ina. Yau ya sake dasa mata abubuwan da ta san ba za su gogu ba. Kuka ta yi har bacci ya ɗauke ta.

*****

Yana ƙarasawa ya buɗe mota ya shiga. Ya ja murfin ya rufe. Kanshi ya haɗa da gaban motar yana jin wani irin yanayi.

“Fu’ad mene ne?  Lafiyarka kuwa?”

Lukman yake tambaya cike da kulawa. Ba tare da ya ɗago ba yace masa,

“Mu je gida.”

“Ban gane mu je gida ba. Me ya faru wai?  Ka gan ta ne?”

Ɗagowa ya yi a ƙufule.

“Do me a favour. Shut the fuck up.”

Dariya Lukman ya yi.

“Easy shah Rukh Khan. Karka kawo min cizo. Daga tambaya. In masifa kake ji ka sauke ta wa zuciyarka ba Lukman ba. I am just trying to help.”

Kauda kai kawai Fu’ad ya yi gefe. Baice komai ba. Ƙila in ya yi banza ya ƙyale shi ya gane cewar ba ya son magana ne gaba daya.

Aikam hakan aka yi . Waƙa ma Lukman ɗin ya saka. Da gangan ya sa duk waƙoƙin da ya san Fu’ad na cewa ba ya so.

Ya kula bai ma san yanayi ba. Tunda ya jingina kanshi da kujera ya kalli gefe bai juyo ba.

*****

Ko parking bai bari Lukman ya yi ba ya buɗe murfin motar ya fita. Da gudu ya shiga gida ya haura sama zuwa ɗakin shi.

Maida ƙofar ya yi ya kulle. Sannan ya zare takalmin da ke ƙafar shi. Nan inda yake tsaye ya cire kaya. Daga shi sai boxers ya shiga toilet.

Ruwa masu sanyi ya sakar wa kanshi. Yanajin yadda sanyin ruwan ba ya kaiwa inda yafi buƙata. Lumshe idanuwanshi ya yi. Zuciyarshi na wani irin abu. Fuskar Safiyya na masa yawo cikin idanuwanshi.

Kunnuwanshi na jin muryarta. Komai ya sake cakuɗe mishi. Bai san iya mintinan da ya ɗauka a banɗakin ba.

Sannan ya fito ya sake kaya. Kwanciya ya yi don ji yake kamar wanda akai wa dukan tsiya.

Wani ciwo ko’ina na jikinshi yake yi da ba shi da alaƙa da gajiya.

Ƙwanƙwasa kofar ya ji ana yi. Ya yi niyyar sharewa. Jin muryar Haneef ya sa shi tashi da ƙyar ya je ya buɗe ƙofar.

Komawa ya yi ya zauna kan gadon. Haneef ya ƙarasa ya zauna kusa dashi.

“Fu’ad?”

Muryarshi can ƙasa yace,

“Haneef ban san ya zan yi ba ni. Ta ƙi karɓar wayar mu yi magana. Kuma tace in tafi ba ta so in dawo. Bazan iya ba…”

Yana maganar yana watsa hannuwanshi alamun komai ya kwance masa. Ganin Haneef ɗin ya nutsu yana saurarenshi ya sa shi sauke numfashi kafin ya nuna kanshi da hannun shi yace:

“Kalle ni. Kamar wanda ya zautu. Em’ clueless…”

Gyara zama Haneef ya yi haɗe da faɗin,

“Ka min magana yadda zan gane Fu’ad. Mene ne?  Wace ce?”

A hankali yace,

“Sofi… Safiyya. Yarinyar nan ta Bichi…”

Hannu Haneef ya ɗaga mishi yana girgiza kai.

“Don’t. Please Fu’ad karka ce min son ta kake yi. Karka fara…”

“Too late. Abinda nake ji ya fi so.”

Fu’ad ya faɗa yana dafe kanshi cikin hannuwa. Haneef kam ya rasa abinda zai ce. Kawai abu ɗaya ne yake a bayyane. Ko shi ne a matsayin iyayen Safiyya. Ko za ta mutu ba zai ba ta yaron da ya wulaƙanta su ba.

Sau wajen huɗu yana buɗe baki zai yi magana. Amma ya rasa me zaice.

“Hmm… “

Fu’ad yace yana kauda kai. Da yake nuna cewa ya fahimci Haneef kanshi na hango rikicin da ke tattare da hanyar da ƙaddara ta ɗora shi.

A nutse yace,

“Munje ɗazu ni da Lukman. Kuma gobe ma zan koma saboda ina buƙatar sake ganin ta.”

Sai lokacin Haneef yace,

“Karka yi haka Fu’ad. karka sake zuwa ka ƙara complicating ma kanka abubuwa. It will not work and you know why.”

Cikin idanuwa ya kalli Fu’ad.

“Issue ɗina da ita ne ba da family ɗinta ba.”

Kallon baka da hankali Haneef yake mishi.

“Waye zai baka yarinyar? Ka ga Fu’ad ka haɗa kayanka gobe ka koma. Zai fi ma kowa kwanciyar hankali.”

Fito da idanuwa ya yi.

“Kana nufin in bar ta?”

Kai Haneef ya ɗaga masa.

 “I can’t. Ba zan iya ba Haneef. Ka tafi ka bar ni kawai…Just go!”

Sanin halin Fu’ad ya sa Haneef tashi ya fita. A yanayin da yake ba zai saurari wani abu ba. In ya ɗan nutsu sun yi magana.

Yana fita Fu’ad ya kwantar da fuskarshi cikin pillow yanajin gaba ɗaya duniyar ta masa wani irin ƙunci….

<< Akan So 14Akan So 16 >>

1 thought on “Akan So 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×