"Innalillahi wa inna ilahi raji.un..."
Momma ta faɗi bayan Haneef ya gama gaya mata ko me yake faruwa.
"Yanzun duka Fu’ad ɗin nawa yake? Hankalin kirki bashi da shi Haneef."
Jinjina kai ya yi ya gyara zama yace,
"Na sani Momma. Amma ki kalli fa abinda yake yi. Wallahi zai iya samun matsala. Ni kam dai a taimaka aje a ji."
"Hmm bayan tozarcin da ya yi musu kana zaton za su saurare mu ne? Ka fi kowa sanin halin Abbanku. Da wahala yaje."
Shiru Haneef ya ɗan yi kafin yace,
"In ya ga yadda Fu. . .