Skip to content
Part 2 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

19 February 2017

Da kanta ta sauke Nana a makaranta sannan ta wuce wajen aiki. Ko jakarta ba ta ajiye ba ta ji an ƙwanƙwasa kofar.

“Shigo”

Ta furta cikin sanyin murya. Kamar yadda ta yi zato, Ansar ne. Murmushin nan na shi ya yi mata.

Duk da yanayin nauyin da zuciyarta take ɗauke da shi bai hanata mayar mishi da murmushin ba. Zama ta yi akan kujerar office ɗin. Shi ma ya samu wata kujerar ya zauna.

“Ina kwana…”

Ta gaishe da shi ya amsa da,

“Lafiya ƙalau Sofi. Kin tashi lafiya? Ya nana?”

Ta langaɓar da kai gefe ɗaya ta ce;

“Alhamdulillah. Kawai dai bana son ganin ɗokin dake cikin idanuwanta ne, kuma yau zan ga doctor ɗinta kan test ɗin da aka yi last week.”

Jinjina kai Ansar ya yi cikin alamar fahimtar halin da Sofi ɗin take ciki.

“In sha Allah za a ganshi.”

Wani murmushin takaici ta yi.

“Ansar idan an ganshi ba zai donating ba fa? Bai san da zamanta ba ma. Ba ma na zaton ko da ya ji zai dawo tunda baya son yara and…”

“Please!”

Ansar ya katse ta yana ci gaba da faɗin;

“Babu wanda zai ga Nana bai so ta ba. To hell with him not wanting children. Zai yi donating in dai da zuciya a ƙirjin shi.”

Shiru Sofi ta yi. Don kuwa ita take da tabbacin zuciyar dake manne a ƙirjin Fu’ad. Kamar yadda a duk kallon da Nana za ta yi mata, cikin idanuwanta take ƙara ganin zuciyar Fu’ad.

Miƙewa Ansar ya yi yace;

“Ina office ɗina if you need me.”

Kai kawai ta iya ɗaga mishi saboda wani abu da ya dunƙule mata a maƙoshi. Tana kallon shi ya fice daga office ɗin ya ja mata ƙofar. Kanta ta ɗora kan table ɗin tana mayar da numfashi.

*****

Hankalinta na kan rigar da take kallo sam ba ta ji shigowar shi ɗakin ba.

“Me kike yi haka?”

Maganar Nawaf ta dawo da ita daga tunanin da take yi. Cikin sauri ta yi ƙoƙarin kawar da rigar gefe.

“Ba….babu komai”

Ta amsa a daburce. Rigar da ke gefenta ya zo ɗauka ta riga shi ta ƙanƙame rigar sosai a jikinta.

Hannu yakai ya riƙo rigar.

“Har yanzu ba ki daina tunanin shi ba ko?”

Ya tambaya rai a ɓace. Rigar ya fizge daga jikinta ya miƙe daga kan gadon ya nufi hanyar waje.

Da sauri ta ƙarasa inda yake ta riko masa hannu tana faɗin;

“Nawaf wallahi ba haka bane ba. Don Allah ka bani rigar.”

Hankaɗe ta ya yi ta faɗi. Duk da zafin da ta ji bai hanata tasowa ta sake riko shi tana magiya ba.

Kamata yayi yai mata wani irin riƙo kamar zai karyata.

“Duk ranar da na sake ganin wani abu na shi a kusa da gidan nan zan baki mamaki wallahi.”

Hawaye cike fal a idanuwanta saboda azabar riƙon da ya yi mata. Muryarta na rawa take faɗin;

“Ka yi haƙuri. Don Allah kayi hakuri. Amma ka bani rigar zan ajiye ba zan sake fito da ita ba.”

Sakinta ya yi yana girgiza kai. Bai san me ke damun Nuriyya ba. Ba ta san yadda ya ke ji idan ya kalleta ya yi tunanin wannan banzan Farhan ɗin yana yawo a kanta ba. Duk bai isheta ba sai ta dinga ɗauko abubuwanshi tana tasawa a gaba tana kallo.

Wucewa ya yi har ya kai ƙofa. Ta matso ta sake riƙe mishi ƙafa. Tana magiya ya bata rigar.

Ɗago ta ya yi daga jikin ƙafar shi ya yi mata wani irin mari da sai da ta ga walƙiya. Kafin ta gama wartsakewa ya sake ɗauketa da wani marin. Wannan karon sai da ta faɗi. A fusace yace;

“Ina Farhan yake lokacin da na hana a yi miki fyaɗe? Ina Farhan yake lokacin da na ɗauko ki daga cikin ƙunci da ƙangin rayuwa? Da abinda za ki sakamun kenan Nuriyya?”.

Kuka take yi sosai. Ta san ya taimaketa. Ba kuma ta ce ba ta gode ba. Sai dai babu wanda zai iya rabata da tunanin Farhan. Ko ƙaddara da ta raba su da kanta ta bar mata Farhan a zuciyarta da tunaninta. Duk da iƙirarin Nawaf, tana kallonshi ya jefar da rigar ya fita daga ɗakin. Kukan da take yi bai hanata rarrafawa ta ɗauko rigar ba.

Fuskarta ta rufe da rigar tana wani irin kuka da za ka san ba shi da alaƙa da marin da Nawaf ya yi mata.

*****

01 January 2010

“Zan dawo Nuri. Daga lokacin da na tsaya da ƙafafuna. Mutuwa ce kawai za ta hanani dawowa gare ki.”

Kuka take yi sosai. Ta ɗago da jajayen idanuwanta ta kalle shi.

“Yaya Farhan ya rayuwa za ta zame mun babu kai? Ta ina zan fara?”

Wani irin ɗaci yake ji har ƙasan zuciyarshi. Bai taɓa zaton akwai yiwuwar ka tsani mahaifinka ba.

Amma ya tabbata da za a ba shi wani zaɓi zai ce a ɗauke mahaifinshi. Ya dai na ganin shi ya huta. Daurewa ya yi don shi kanshi yana gab da soma kukan.

“Na biya miki kuɗin makaranta gaba ɗaya. Ga wannan….”

Ya zaro ATM daga aljihun shi da wasu takardu ya miƙo mata.

“Ki ɓoye su. Duk sanda kike da buƙatar kuɗi, ki cire. Kuɗin da na zuba miki ba su da yawa. Su kaɗai suka rage min Nuri.”

Kasa iya tsayawa ta yi. Durƙushewa ta yi a gabanshi tana wani irin kuka da ya karya masa zuciya. Shi kanshi bai san ta yadda zai fara cikakken numfashi babu Nuriyya ba. Sai dai dole ya bi mahaifinshi su bar ƙasar.

Yana buƙatar ya ƙarasa karatunshi. Ya tsaya da ƙafafuwanshi yadda zai dawo ya cire Nuriyya daga wannan ƙangin.

“Yaya Farhan ba na buƙatar wannan. Wallahi kai nake so a kusa dani.”

Lumshe idanuwanshi ya yi da suka sake launi saboda tashin hankali sannan ya buɗe su yana saukewa akan Nuriyya. Tsugunnawa ya yi shi ma. Yana son ya riƙo ko da hannuwanta ne ya nuna mata cewar ba shi da wani zaɓi. Yana tuna exact maganar da babanshi ya faɗa mishi jiya da dare.

“Ko ka bar ‘yar gidan karuwar nan ka bi ni mu tafi. Ko kuma ka zauna da ita anan ka manta cewar kana da wani mahaifi. Amma wallahi zan janye duk wani taimako na akanka. Saboda ba zai yiwu kana zubar min da kima da daraja a idon duniya ba.”

Ya san baban shi sarai. Ya kuma san zai yi fiye da abinda ya faɗa ma. Kuma yana da tabbacin zai ci gaba da saka masa ido ya ga ko ya yanke alaƙa da Nuriyya.

Cikin sanyin murya yace;

“Nuri banda wani zaɓi. Zai tafi da Khadee ne…..”

Cikin sauri Nuriyya ta goge hawayen fuskarta. Ta yaya ma za ta fara son kai har haka?

*****

19 February 2017

Turo ƙofar da ta ji an yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa. Cikin wani irin bala’in sauri ta ɓoye rigar. Nawaf ne. Tana jin shi ya tako ya ƙaraso har inda take zaune shima ya zauna. Kallon shi take ta ga ko ya sha wani abu. Idanuwanshi na nan da kalarsu. Ba ta ga alamun ya sha komai ba. Yadda ta yi da jikinta ya taɓa mishi zuciya. Tsoron shi take yi. Ya dafe kai yana jan iska ta bakin shi. Hannuwan shi ya kai ya kamota. Ta ƙi kallon fuskar shi. Sosai ya matso da ita jikinshi. Yana ganin sawun hannuwan shi kwance akan fuskarta. Abinka da farar fata. Wani tsanar kanshi ya ji. Laifin Nuriyya ne, ta san shi sarai. Ta san idan ranshi ya ɓaci ba ya iya controlling ɗin ko me yake yi. Kwantar da ita ya yi akan ƙirjin shi. Tana ta sauke ajiyar zuciya. Ta yi kuka ta gaji. Ya sa hannuwa ya shafi kumatunta duk biyun.

“Ki yafe min please….”

Ya faɗa cikin kunnenta. Shiru ta yi mishi. Don tsoron yin magana take ji. Lokuta da dama tsoron shi take yi. Tana ji ya matse ta a jikinshi.

“Please Nuriyya. I love you. Ai kinsan haka ko? Kinsan ina sonki sosai.”

Kai kawai ta ɗaga mishi. Tana jin shi ya sauke ajiyar zuciya. Ya miƙe tare da ita a jikin shi. Toilet ya kaita ya wanke mata fuska da kanshi. Ya sa towel ya goge mata inda ruwa ya ɓata. Ya kamo hannunta ya fito da ita. Kan gadon ya kwantar da ita. Da ido kawai take binshi. Ganin yana shirin hawowa gadon ya sa ta faɗin;

“Takalmi Nawaf, please!”

Murmushi ya ƙwace masa. Ba mantawa ya yi da takalmi a ƙafarshi ba. Bai damu da ya cire bane kawai. In ba Nuriyya ba wa ya isa ya saka shi canza ɗabi’un shi. Takalmin ya cire ya bar socks ɗin. Ya hau gadon ya kwanta a bayanta ya riƙota jikin shi.  Ba ta damu ba don ta san bai taɓa takura mata don biyan buƙatar shi ba. Lokuta da dama ba ta gane kanshi.

Jikinta ya kwanta. Har kanshi a bayanta yake. Ya wani naniƙe mata kamar ƙaramin yaro.

A haka barci ya ɗauke shi. Yana jin son Nuriyya har cikin fatar shi.

*****

19 February 2017

Miƙewa ta yi da shirin fita daga office ɗin zuwa asibiti ganin ƙarfe sha ɗaya ta yi. Don sun yi da Dr. Jana za ta shiga amsar result ɗin wajen sha biyu. Gara ta fita da wuri. Wayarta ta ji ta soma ringing. A zatonta ma Dr. Jana ɗin ce ta kira ta. Ta sa hannu ta lalubo wayar daga cikin jaka. Zuciyarta ta ji ta wani buga da ƙarfin gaske.

Bango ta dafa ta nemi waje ta zauna. Lambar principal ɗin makarantar su Nana ne.

Addu’ar duk da ta bakinta ita take yi. Ta ɗaga haɗi da sallama tana jiran jin abinda ta fi tsoro. Ko jikin Nana ne ya tashi. A daddafe suka gaisa cikin harshen turanci.

“Akwai wasu ‘yan jarida da suka zo tun misalin awa ɗaya da ya wuce. Sun ƙi tafiya suna son magana ne da Nana. So, na san za ki so ki sani.”

Lumshe idanuwanta tayi ta sauke wani numfashin. Don wannan mai sauƙi ne.

“Kada ku barsu su je ko da kusa da ita ne. Gani nan zan zo school ɗin yanzun.”

Tana kashe wayar ta kira Ansar don ta san ba za ta iya wannan aikin ita kaɗai ba. Last warning na Dr. Jana shi ne kada a ɗora wa Nana wani stress komai ƙankantar shi. A halin yanzun ‘yan jaridar can ba ƙaramin stress bane a wajenta.

<< Akan So 1Akan So 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×