Skip to content
Part 20 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Safiyya ya kalla yace, “Bari in ga Haneef a waje.”

Kai ta ɗaga masa. Ya fice da sauri. Tun daga nesa da ya hango Haneef jingine jikin mota. Jikin shi  sanye da manyan kaya ya ɗaga hannuwanshi alamar surrender.

Yana ƙarasawa ya wani yi rau-rau da idanuwa tare da faɗin,

“Don Allah ka ce ba faɗa za ka yi min ba. Wallahi jiya na yi sub ɗin wata biyu.”

Haneef bai san lokacin da dariya ta kuɓce masa ba. Fu’ad ya wani dafe ƙirji daidai inda zuciyarshi take yana sauke numfashi.

“Hankalina ya kwanta. Ina wuni.”

Ɗaure fuska Haneef ya yi. A ranshi yana faɗin dole ka gaishe da ni tunda ba ka da gaskiya.

Idanuwa kawai ya zuba mishi. Abinda ya san baya so. Gara kai masa masifa a wuce wajen.

Cike da ƙosawa yace,

“Alright ka min faɗan….”

Shirun dai ya sake masa.

“Please…”

Hakan ya sa Haneef faɗin,

“Ban san me zan ce maka ba Fu’ad. Ko me na faɗa ta gefen kunnenka zai wuce.”

Da sauri yace,  

“Zai tsaya ciki. Da gaske nake amma karka yi fushi. In babu kai ba zan iya fuskantar su Abba ba.”

Yanayin da ya ƙarasa maganar da wani sanyi ya ɗan taɓa Haneef ɗin. Kallon shi ya yi da kyau.

“Ba ka jin magana. Abinda ka yi ba ƙarami bane ba. Bance ba zai yafu ba. Auren da aka gina ta hanyar da ya dace ma yana zuwa da matsala Fu’ad. Ballantana naku da babu amincewar iyaye ballantana albarkarsu. Kasan rayuwarta ta gama canzawa kenan?”

Cikin ido ya kalli Haneef yace,

“Na sani. Ina sonta sosai. Ba ni da wani zaɓi ne shi yasa.”

Sai da Haneef ya sake gyara tsayuwa tukunna yace,  

“Na yarda baka da zaɓi. Amma kana da son kanka da yawa. I really hope za ka so ta rabin yadda kake son kanka.”

Dariya Fu’ad ya yi.

“Em’ noh’ dah’ selfish fa. We’re good?”

Girgiza kai Haneef ya yi.

“Not even close.”

Mota Fu’ad ya ga yana niyyar shiga ya riƙo masa riga da sauri.

“Fu’ad menene haka kamar yaro? Sake min riga karka daƙuna min…”

Haneef ke faɗi yana kiciniyar ƙwacewa daga hannun Fu’ad da ke riƙe da shi gam.

“Allah sai kace we’re good sannan.”

Ikon Allah Haneef ya ware ido yana kallo.

“Wai kai ba ka san ka girma ba? Kana da aure fa yanzu. Haka za ka yi yara kai kanka yarinta ba ta gama sakinka ba?”

Rigar Haneef ya saki ya wani daƙuna fuska yana faɗin,

“Banda wajen yara a zuciyata. Naku kawai sun ishe ni…”

Girgiza kai kawai Haneef ya yi ya buɗe murfin motar. Sake riƙo shi Fu’ad ya yi.

“Please mana. I need mi’ bro.”

Sauke ajiyar zuciya Haneef ya yi. Shi kanshi ya san ba zai iya wani fushin kirki da Fu’ad ba.

“We are good. Tana sonka Fu’ad, karkai mata butulci please.”

Murmushi ya yi sosai sannan ya ɗaga hannunshi alamar salute yace,

“Yes sir!”

Dariya Haneef ya yi ya shiga motar. Ta window Fu’ad ya tsaya yana faɗin,  

“Na siya gida fa. 3-bedroom ne. Bari in ɗauko maka takardun ka ajiye min a wajenka.

Please ina son siyan furnitures da za a saka anjima. In zo mu je tare?”

Girgiza kai Haneef ya yi.

“Nope. Allah ya sanya alkhairi. Ka dai ƙara addu’a sosai, ɗauko min takardun sauri nake yi.”

Da sauri ya je ya buɗe motarshi ya ɗauko takardun ya kawo wa Haneef. Wani langaɓe fuska ya yi.

“In zo mu je?”

“Ku tafi da Lukman mana.”

Haneef ɗin ya faɗi yana tada motarshi.

“Fushi yake yi da ni.”

Kallonshi Haneef ya yi ya ɗaga gira alamar ‘matsalarku ce’. Sannan ya maida hankalin shi kan motar yana janta.

“Thank you”

Fu’ad ya faɗi yana kallonshi har ya fice. Wani sanyi ya ji.

“Saura Lukman, Sannan su Abba.”

Ya faɗi yana komawa cikin gida. Inda ya bar Safiyya a nan ya sameta. Ya ƙarasa kan kujerar da take zaune ya zauna daf da ita.

Yana kallon yadda jikinta ya yi wani iri alamar tana son matsawa. Basarwa ya yi, dole ma ta saba da shi.

“Fita zan sake yi. Ki ɗan yi min haƙuri kaɗan. Komai zai dai-daita in shaa Allah.”

Ba fitarshi bace ta dameta. Yadda take jin hucin fitar numfashinsa dab da ita. Zuciyarta a kwance take yana zama ta soma tsalle-tsalle. Manyan idanuwanta ta sauke masa kan fuska.

Kasa daurewa ya yi. Hannu ya sa ya taɓa kuncinta. Ta ɗan janye fuskarta. Hakan ya sa shi sauke hannunshi.

“Bari in tafi Sofi.”

Miƙewa ya yi. Ta bi shi da idanuwa. Abinda ke cikin idonta ya fizgeshi. Komawa ya yi ya tallabi fuskarta da hannuwanshi duka biyun. Pecking ɗinta ya yi a goshi. Sannan ya miƙe ya fice. Hannuwa ta sa ta taɓa inda nashi hannun ya bari.

Ta lumshe idanuwanta tana jin yadda har lokacin ɗumin hannunshi bai bar wajen ba.

*****

Kai tsaye gidansu Lukman ya wuce. Ya ko yi sa’a yana ɗakin shi a zaune yana cin abinci.

Da sallama ya shiga ya ƙarasa. Amsa shi ya yi ya sauke idanuwanshi kan takalman da ya shigo da su.

“Takalmi Fu’ad….”

Inda yake tsaye ya tsaya. Nan ya cire takalmin ya bar su a tsakiyar ɗakin ya ƙarasa. Zama ya yi. Lukman ya ci gaba da cin abincin shi yana danna waya kamar ma Fu’ad ɗin ba ya ɗakin.

Wayar ya karɓa ya sakata a key ya ajiye gefe. Kallon Lukman ya yi sosai.

“Ka yi haƙuri. I know em’ a shitty friend. Hell ion’ even deserve aboki kamar ka.

But ina buƙatar abokina. Don Allah ka yi haƙuri.”

Cokalin ya ajiye a cikin plate ɗinshi ya ɗago ya maida hankinshi kan Fu’ad da ya wani yi rau-rau da idanuwa yace,

“Kasan dai za ka iya tarata da kowanne irin magana. Bance ko yaushe kake yin abinda ya kamata ba. Ban kuma damu da ka saurari shawarwarina duk sanda na baka su ba. Imagine Fu’ad za ka yanke hukunci irin wannan ba za ka faɗa min ba.”

Hannuwanshi ya haɗe alamar neman afuwa tare da cewa.

“Na riga da na yi. Ka yi haƙuri.”

Murmushi Lukman ya yi. Fu’ad yace,

“Menene na murmushi cikin maganata?”

Ɗaga gira Lukman ya yi duk biyun tare da faɗin,

“Ɗan dawo baya kaɗan. Kamar haƙuri na ji kana ta bani.”

Dariya Fu’ad ya yi yana ɗaukar pillow ɗin kujerar da yake kai ya jefa wa Lukman.

“Shut up.”

Dariya suka yi gaba ɗaya. Kafin cikin serious voice Lukman yace masa,

“Safiyya ta maka abinda ba kowace mace za ta iya ba.

Ko da ni ne a matsayinta bayan abubuwan da suka faru sai dai sonka ya kasheni wallahi.

Don Allah ka riƙe ta.”

Dafe kai Fu’ad ya yi.

“Seriously. Me yasa kuke faɗa min abu ɗaya ne wai. Ina sonta. Kun kasa ganewa and zan riƙe ta in shaa Allah.”

Daƙuna fuska Lukman ya yi.

“Na ji sarkin soyayya Shahid Kapoor. Ba sai ka gartsamun cizo ba daga faɗar gaskiya.”

Dariya kawai Fu’ad ya yi. Ya san indai Lukman da Haneef na tare da shi zai yi winning kowa a hankali. Hira suka shiga yi. Fu’ad ɗin na bashi labarin yadda komai ya faru da maganar gidan da ya siya. Nan ya jira Lukman ɗin bayan ya gama cin abinci ya je ya yi wanka ya fito sannan. Sai da suka biya ta wani shagon sai da wayoyi. Ya basu wayarshi ya ɗauki wata ƙaramar HTC da kuɗin. In ba dole ba ya fi son ya siya wayarshi a can.

Lukman ya taya shi zaɓa wa Safiyya wata Tecno mai kyau. Sannan suka wuce wajen furnitures.

Pictures aka dinga ɗauko musu Fu’ad na faɗin ba su yi mishi ba. Shi sam ba ya son kayan katako.

Wasu ya zaɓa. Na black silver. Lukman ne ya yi magana da su suka gama cinikin komai.

Tare da motocin kayan suka tafi har gidan. Da yake in kana buƙata su za su haɗa maka komai su jera.

Haka aka jera musu komai. Lokacin magriba ta yi. Daga shi har Lukman a gajiye suke.

Bayan sun dawo sallar Magriba ne Fu’ad ya kalli Lukman a gajiye yace,

“Wai dama haka haɗa gida yake da wahala?”

“Ni kaina ban san da wahala haka ba. Kuma har yanzu akwai abubuwan da babu fa.”

Ɗan yamutsa fuska Fu’ad yayi.

“Babu TV…”

Girgiza kai Lukman ya yi.

“Ba wannan bane kaɗai. Akwai abubuwan da babu.”

Sauke numfashi Fu’ad ya yi.

“Zan kira Fa’iza, hopefully ita ba ta yi fushi ba. Sai ta zo ta gani ko?”

Jinjina kai Lukman ya yi alamar yarda da abinda Fu’ad ɗin ya faɗi.

Kulle gidan suka yi. Sai da ya sauke Lukman a gida. Ya sake biyawa ya siyo musu takeaway sannan ya nufi gida.

*****

Tayi kallo har ta gaji. Tunani kala-kala a ranta. Da ta ga tunanin su Inna da ko ya suke ciki na neman haye mata yasa ta ture su gefe. Don wata irin kewar Inna ke damunta. Lumshe idanuwanta ta yi tana tunanin Fu’ad.

Yanda take mafarkinshi da yadda take ji akanshi. In yana gabanta ta fi jin hakan sosai.

Goshinta ta sake taɓawa kamar za ta dangwalo peck ɗin da ya yi mata ɗazun a jiki.

Ta ga ya daɗe sosai dai. Take addu’ar Allah ya sa lafiya. Ta tashi ta leƙa ƙofa ya fi a ƙirga mussaman yanzu da dare ya yi.

Sallar Isha’i ta je ta yi. Ta sake watsa ruwa duk da sanyin shi don kam ko gida takan dafa wasu lokutan.

Ta yi alƙawarin in Fu’ad ya dawo za ta tambaye shi domin ruwan akwai sanyi ba kuma bokiti ta gaji da wahalar nan.

Wata riga ta saka doguwa fara. Ta ɗaura ɗankwalin akanta. Tana buƙatar inner wears. Su ma ta fi buƙata fiye da kayan sakawa.

Tunanin faɗa wa Fu’ad kawai ta yi sai da wata kunya mai ƙarfin gaske ta kamata. Ta dawo falo ta zauna kenan ta ji sallamar shi.

Wani murmushi ya ƙwace mata. Ta amsa ta miƙe ta ƙarasa inda yake ta karɓa ledojin da ya shigo da su.

“Sannu da zuwa. Ka daɗe sosai…. “

Kallonta yake yi. Rigar ta wani mata kyau. Da murmushi ya amsa da,

“Sorry na sani. Munata siye-siye ne fa da Lukman.  Saura kaɗan in shaa Allah. Babu dai zazzaɓin ko?”

Kai ta ɗaga mishi. Don garau take jinta. Banda damuwar dake danne ƙasan ranta. Ƙarasawa suka yi ya zauna kan kujera. Ƙasa ta ajiye kayan da ta karɓa a hannun Fu’ad ta nemi wata kujerar ta zauna.

“Sofi kaina ciwo yake min fa.”

Cike da kulawa tace,

“Sannu. Da ka je ka kwanta ka ɗan huta. Ko in ɗauko maka magani?”

Girgiza mata kai ya yi tare da faɗin,

“Stress ne kawai. Bari in yi wanka in zo mu ci abinci. Ko kina jin yunwa?”

Tana jin yunwa sai dai kawai ta tsinci kanta da son ta jira Fu’ad ɗin ya fito. A hankali tace,

“Ka je ka fito.”

Wucewa ya zo yi ta gabanta hakan yasa ta ce,

“Umm kaji…”

Juyowa ya yi da duk hankalinshi akanta.

“Ya dai Sofi? Mene ne?”

Yadda ya zuba mata idanuwa da dukkan nutsuwar shi ya sa ta jin wani iri. Kanta ta sadda ƙasa.

“Ba wani abu bane babba ba fa.”

Waje ya samu ya zauna gefenta.

“Ko min ƙanƙantar shi. Ina jin ki.”

Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi tana ƙin yarda idanuwanta su haɗu da nashi sannan a hankali muryarta can ƙasa ta ce,

“Ruwan wanka. Sanyi gare shi sosai kuma babu bokiti sai dai inta tarowa da hannu.”

Ware idanuwa ya yi da mamaki yace,

“Bokiti kuma Sofi? Ruwan ina kike wanka dashi?”

“Ruwan da ka kunna min na yi alwala.”

Baya so ya yarda da maganarta sai ya tabbatar. Miƙewa ya yi yana faɗin,

“Taso ki nuna min.”

Babu musu ta bi shi har zuwa toilet ɗin. Fanfon da ke wajen alwala ta danna kamar yadda ya yi sannan ta kalle shi tace,

“Ka ganshi. Ruwan sanyi sosai.”

Baisan lokacin da dariya ta kuɓce masa ba. Dariya yake yi sosai har da dafe ciki. Kallon shi take da murmushi a fuskarta. A kunyace tace,

“Na yi ƙauyanci ko?”

Girgiza mata kai yake yi kawai ya kasa daina dariya har lokacin. She is just too much, ya faɗa cikin kanshi a fili kuma yace,

“Sofi…”

Kasa magana ya yi saboda wata dariyar da ya ji ta sake kuɓce masa. Da ƙyar ya samu ya nutsar da kanshi sannan yace mata,  

“Zo ki gani.”

Nuna mata yadda za ta haɗa ruwa a bathtub ɗin ya yi. Da inda za ta cire ruwan ya tafi.

Sau uku ya nuna mata tana kallo. Tun a karo na farko ma ta riƙe komai don da wahala dai ka yi abu a gabanta ba ta gane ba. Tsayawa ya yi ta yi ya gani. 

Da murmushi a fuskarshi yace,

“Good girl.”

Murmushi ta mayar mishi a kunyace.

“Bari in yi wankan ko?”

Kai ta ɗaga mishi. Tare suka fice ya yi ɗayan bedroom ɗin ita kuma ta yi zamanta a falo. Kawai dariyarshi take ji cikin kunnuwanta da yake sa ta murmushin da ta kasa fahimtar daga inda yake fitowa.

Tana nan ya fito. Sanye da three quarter loose mai wasu igiyoyi daga ƙasan milk sai riga fara da ta kama shi. Idanuwanshi take kallo. Har yanzun mamaki suke ba ta. Ta maida dubanta kan gashin shi. Yanayin askin shi na ƙara ba ta mamaki tun jiya.

Ya wani aske gefe da gefe da bayan kan. A tsakiyar kan nan gashin yake yayi wani coil.

Tsaye ya yi yana kallon yanda idanuwanta ke yawo a fuskarshi zuwa kanshi. Hakan na mishi daɗi. Kula ta yi da ya ga tana kallon shi. Ta sadda kanta ƙasa a kunyace. Ya yi murmushi. Ya ƙarasa ya zauna kan kafet. Daga jiya zuwa yau cin abinci akan kafet na mishi daɗi.

Yanzu ɗin ma shinkafar ta ci. Don ta ɗazun ma ta mata dadi ta sha ruwa ta koma saman kujera tana kallon yanda Fu’ad ke cin abincin shi.

Yana gamawa ya buɗe ledar wayarsu ya dauko tashi ya buɗe. Ya ciro charger ɗin da wayar, dama tun a can shi ya saka sim ɗin shi a ciki.

Don sai da ma aka kunnata ya tura abubuwan shi ya yi wiping ɗayar kafin ya basu. Ta safiyya ya dauko. Ya buɗe ya saka mata sim ɗin da ya siyo mata da Memory Card sannan ya sa batir ɗin ya mika mata.

“Ga wayarki.”

Ware idanuwa ta yi da mamaki. Ta sa hannu biyu ta karɓa tana jujjuya wayar. Daga ganin kyanta ta san tana da tsada sosai.

“Nikam wannan wayar ai tayi tsada”

Dariya ya yi. Ta ɗora da faɗin,

“Ga shi ban iya ba….”

“Karki damu zan koya miki. Kawo a sa a caji, kafin mu tashi kwanciya ya cika.”

Bashi ta yi. Ya saka da nashi da nata ɗin ya koma kan kujera ya zauna suna kallon Arewa24 tare.

Shi kaɗai yake kallon wata drama da ta burgeshi ta Daɗin Kowa. Ita kam Safiyya ta yi shiru.

Ba kallon take ba tunanin rayuwa take yi. Oh da yanzun tana gidan Ado. Ta wani ɓangaren wani sanyi ta ji. Don ba ta son ado ko kaɗan.

Ko kafin ƙaddara ta haɗa ta da Fu’ad ɗin ma ba ta son shi. Tsanar shi ta ƙaru ne bayan haɗuwarta da Fu’ad.

Inda wani ya ce mata rayuwarta za ta juye haka ba za ta taɓa yarda ba. Kalli kuɗin Fu’ad. Ita kanta tasan ko da wasa ba ta dace da shi ba. Sam ba ta ji yana mata magana ba. Lumshe idanuwanshi ya yi. Baya son tunanin nan da take yi. Inda take zaune ya koma.

Ba ta ji ƙarasowarshi ba sai fuskarta da ta ji ya tallaba cikin hannayenshi. Da sauri ta sa nata hannuwan kan nashi tare da riƙewa dam.

Hannuwanta yabi da kallo yana jin su har cikin ranshi. Idanuwanshi ya maida cikin nata. Fuskarshi babu walwala yace mata,

“Ba na son tunanin nan Sofi. Bana so ko kaɗan.”

Wani rauni ta ji na daban. Hawayen dake cikin idanuwanta suka zubo. Cikin rawar murya tace,

“Ka yi haƙuri. Zan bari. Ina kewar su Inna ne kawai…”

“Shhhhhh…”

Ya faɗi yana goge mata fuska da hannayenshi. Amma kamar ƙofar fitowar wasu hawayen yake buɗe mata. Gani ya yi ba zai mishi ba. Riƙo mata hannuwa ya yi ya matso da ita gab da shi. Rungumota ya yi jikinshi yana lallashi. Kuka ta yi sosai. Sai da ya ji tayi luf sannan a hankali yace,

“Komai zaiyi daidai. Komai zai gyaru in shaa Allah.”

Kai ta ɗaga masa a hankali take ƙoƙarin zamewa daga jikinshi don nata jikin duk ya mutu. Sakinta ya yi ya miƙe ya duba wayoyinsu.

Duk sun cika. Cirewa ya yi ya ƙarasa wajen Safiyya ya kama hannunta ya ja ta suka yi bedroom ɗin tare. Sai da ta hau ya ja mata blanket ɗin tukunna ya zagaya ya zauna kamar jiya.

Wayarta ya kunna yace mata,

“Matso ki gani.”

Duk da tana jinta wani iri bai hanata yin abinda yace ba. Bayan duk wannan nan da nan ɗin da yake da ita gudun zama kusa da shi shi ne ƙarshen abinda za ta yi.

Ko ba komai ba haram bane ta san da hakan. Kawai ji take jikinta n ɗaukar wani ɗumi ga zuciyarta na bugawa sosai.

Shi ma matsawa ya yi sosai kusa da ita. A hankali yake nuna mata yanda za ta yi amfani da wayar. Inda za ta danna ta yi kira da sauran abubuwa.

Miƙa mata ya yi. A hankali take taɓawa kamar wadda hannunta zai maƙale a ciki. Mamaki wayar take bata.

Da ta taɓa sai ta ga komai ya wuce. Muryarta ɗauke da farinciki tace masa,

“Ana ɗaukar hoto?”

“Sosai ma. Kawo ki gani.”

Miƙa masa wayar ta yi. Hannunta ya riƙe wayar na ciki. Yasa ɗayan hannunshi ya kai camera ɗin ya kunna flasher ya danna.

“Kai…”

Ta faɗi cike da mamakin ganin yadda ya ɗauki hoton ɗakin. Yanayinta na bashi dariya. Sakar mata hannu ya yi yana kallonta.

Miƙewa ya yi zaune ƙafafuwanta mike kan gadon. Ɗaukar hoton ta sake yi ta ga yayi. Ta yi wata dariya. Saita Fu’ad ta yi da camera ɗin ta ɗauka. Hasken kawai ya gani. Ya zaro Idanuwa ta sake ɗaukar shi.

Dariya yake yi. Ya kai Hannu yana karewa.

“Sofi daina ɗauka ta duk fuskata ta yi maiƙo kina min hoto…”

Tana dariya ta sake ɗaukar wani. Hannuwanta ya riƙo duka yana janyota ta faɗa kan cikinshi.

Dariyar da take yi ta ɗauke lokaci ɗaya. Wani numfashi ta ja da ya sa shi fadin,

“Fuck me….”

Cikin kanshi. Idanuwanshi ya kafa mata. Gaba ɗaya jikinta ya mutu. A hankali muryarta kamar wadda aka shaƙe tace,

“Yi haƙuri na daina.”

Sai da ta yi gyaran murya, don jinta take ta maƙale. Shi kanshi abinda yake ji na neman ƙwacewa daga control ɗin shi.

“Tsayawa za ki yi in rama.”

Ganin ya sake mata hannu ya sa ta miƙe daga jikinshi ta maida numfashi ko zuciyarta za ta ɗan rage gudun da take yi.

Hasken wayarshi ta ji cikin Idanuwanta yana ɗaukarta hoto. Dariya ta yi, ya sake ɗaukar wani.

Pillow ta janyo tana karewa a dole ba ta so yana ɗaukarta. Ci gaba ya yi da ɗauka yana jinshi wani so light.

Gajiya ta yi ta cire pillow ɗin ta kwanta. Sannan ya sauke wayar yana duba hotunan da ya ɗauketa.

Juyowa ya yi ya nuna mata ya ga bacci ya ɗauketa. Dariya ya yi. Ya zare wayar dake hannunta ya ajiye gefe. Kanta ya ɗaga ya gyara mata kwanciya.

Ya ƙara ja mata blanket ɗin sannan ya kai hannunshi ya kashe musu wutar ɗakin. Addu’a ya yi musu dukkansu sannan ya kwanta da wani kwanciyar hankali na daban a zuciyarshi.

Hannunta ya laluba ta cikin blanket ɗin ya riƙe dam. Lumshe idanuwanshi ya yi a hankali ya ce,

“I love you Sofi..!”

Kafin wani bacci mai nauyi ya ɗauke shi.

<< Akan So 19Akan So 21 >>

1 thought on “Akan So 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×