"Mama na da karamci sosai."
Safiyya ta ce masa muryarta da wani sanyi. Wani murmushi ya yi. Yana so a yabi Momma.
"Momma ba ta da matsala Sofi. Ni na san za ta so ki da ma."
Langaɓar da kai ta yi kawai. Tana tunanin ranar da nata iyayen za su so Fu’ad. Ita kanta a yanzu ba ta san matsayin nata son a wajen su ba ballantana ta yi tunanin za su so Fu’ad.
Hannunshi ta ji kan nata. Ya riƙo tare da dumtsewa. Ba ta san yadda ya ke gane tana buƙatar hakan. . .