Karfe uku da rabi a Crescent ta yi mishi. Sai da ya fara shiga suka yi magana da matar da za ta dinga zuwa gida tana koya wa Safiyya karatu. Ba wata babba ba ce ba can. Yoruba ce sai dai ta ji Hausa kamar ba gobe. Duka ba za ta shige shekaru ashirin da huɗu ba.
Magana suka yi ta fahimta. Fu’ad ya yi mata kwatancen gidansu. Kusan unguwarsu dayae ma. Layi uku ne tsakaninsu.
Suna gamawa ya fita waje ya tsaya a jikin motarshi ya na jiran Safiyya ta fito. Sai ware idanuwa yake yagae ta. . .
Akwai Dadi
Ina sonku