Kallon kanta ta ke yi a mudubi. Wannan ne kaya na biyar da ta saka ta na cirewa. Yanzu riga da skirt ne na Atamfa brown.
Ya karɓe ta sosai. Ba wata kwalliya a fuskarta ban da jagirar da ta yi. A sati ɗayan nan da Khadija ta koya mata jagira ta zama ƙwararriya.
Kamar ba ita ba. Ga hannunta ya sha ƙunshi. Har gida su Khadija suka kawo mai kunshi jiya ta yi nata jan lalle da baƙi a hannuwa da ƙafa.
Murmushi ta ke yi ita kaɗai. Ba ƙaramar kewar Fu’ad. . .