Tun jiya ya kasa samun wani wadattaccen bacci. Haka ya daure ya je aiki. Yana tasowa ya wuce gida. Wanka kaɗai ya yi.
Abincin ma don Zee ta tusa shi gaba ne babu inda zai fita babu komai a cikinshi ya sa shi ɗan ci kaɗan. Wani irin abu yake ji cikin zuciyarshi da ya jima da manta yadda ya ke.
Tunani da mamakin yiwuwar samun 'ya a wajen Fu’ad kawai ya ke yi. Tunani ya ke zuwansu nawa da shi da Haneef gidan Fu’ad.
A kulle sai mai gadi. Ƙarshe ma ce musu ya yi. . .