Wani sama-sama ya ke jinshi. Ƙarar motocin da ke wucewa can ya ke jinsu a nesa. Saboda abu ɗaya ne ƙwaƙwalwarshi ke iya processing a yanzu.
'Yar shi na da cancer'. Can sama-sama ya ke jin kamar muryar Sofi na kiranshi. Bai ko bi takanta ba saboda ba ta gabanshi a yanzun.
Komai na rayuwarshi a gefenshi ya ke a ajiye. Nana ce kawai ya riƙe gam tun da ya sauke idanuwanshi akanta.
Da gudu Safiyya ta ƙarasa ba ta damu da mutanen da ke wurwucewa ba. Ta sha gabanshi. Kallonta ya ke ya dauna fuska. . .