Da sallama ya tura ƙofar, yana shiga ɗakin gefen gadon Nana ya zauna. Idanuwan nan nata ta ware akan fuskarshi.
Ya yi mata murmushi tare da faɗin,
"Ruwan nan kawai zai ƙare mu tafi gida."
Safiyya da ke gefe ta ja numfashi tare da cewa,
"Me ka je ka yi?"
Cikin fuska ya kalleta. Ya wani yi narai-narai da idanuwa.
"Ni kam me zan yi? Roƙonta na yi kawai."
Taɓe baki Safiyya ta yi, don ta san roƙo yana ƙarshen littafin Fu’ad da ba kowane ya ke gani ba. Da fara'a Nana. . .