Yana so ya buɗe idanuwanshi ya kasa. So ya ke ya ƙwace daga inda tunanin shi ke son janshi.
Ya gwammace ya ziyarci ko'ina banda nan. Banda ranar farko da ya karɓi abinda ya rusa mishi rayuwa. Sai dai ya zamana bashi da karfin komai.
Bashi da ƙarfin fisgewa daga riƙon da koma menene ya yi mishi. A hankali ya bayar dakai. Ya daina ƙoƙarin kokawar da yake yi.
Ya bari koma menene ya ɗauke shi ya ja shi inda ya ke son kaishi.
*****