Kallon Fu’ad take sai kai kawo yake da Nana akan kafaɗar shi yana ta bubbuga bayanta a hankali. Tunda suka dawo daga ganin Nawaf yake lallashinta har ta yi bacci.
"Ka kwantar da..."
"Shhhhhhh."
Fu’ad ya katse ta yana daƙuna fuska. Shirun ta yi ta zuba masa idanuwa kawai. Da alama baya ji da ganin kowa banda Nana a yanzun.
A hankali take jin wani abu a zuciyarta yana dokawa a hankali. 'Ina sonki Sofi' kalamanshi suka faɗo mata.
Kowa ya turo ƙofar ya taimaka mata ba kaɗan ba. Murmushi ta ɗora kan fuskarta. . .